WAYE ANGON CHAPTER 2 BY MARYAM JAFAR KADUNA
WAYE ANGON CHAPTER 2 BY MARYAM JAFAR KADUNA
Damuwa dai akwaita rashin cin abincin ba zai yaye
damuwar ba, illa ma ya Kara damuwa. Amman in kika ci
za ki samu karfin jikinki kuma damuwarki tayi sauki.”
Mama ta saurara.
Mabarukan ta ce,”Zan ci Mama ko zuwa anjima.”‘ Tace,
‘A’a ban yarda ba, yanzu nake son kici. Kinga zaku
je saloon ya kamata zuwa yau kin yi saloon din da lalle,
ga maganinki can a kan wuta anjima za a kawo y an shilar.Ta kalleta zata yi kuka ta ce,
“Duk meye amfaninsu WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
Mama? Ni fa ba na farin ciki, don Allah ku «kyale ni da wadannan abubuwan
Mama tayi murmushi nasu na manya taCe
‘”‘Mabaruka kenan! Ita Amarya an santa da gyara da
kwalliya don angonta da mutanen da za su zo mata
murna su ganta fes! Gwanin sha’awa kowa ya yaba ya
gamsu lallai Amarya ce.
Amman idan ki ka tsaya a haka waye zai zo ya ce ke amarya ce? Kwalliya ya zama dole kiyi Mabaruka, kiyi
hakuri.” Zata yi magana Maman ta katseta “Ya isa!
Dauki ki ci abincin.
Ta jawo mata abincin a gabanta
tare da cewa “‘Oya maida hankali in ga kin ci da yawa.
Yawan musun ba shi da amfani bare ga babbar mata
wacce take ganin girmanta da Kima, uwa ce gareta. Don
haka ba don tana da bukatarsa ba ta fara tsikararsa ranta
cunkushe ba ya mata dadì sam! Ji take kamar ta fasa ihu
ko ta samu sauki.
Maman ta mike tana cewa,
“Yauwa Mabaruka!
Hakuri za ki ki ci abincin ku tafi kar kuyo dare.
» A can makoshi ta ce, “To.”
Bayan fitar Maman Rafia ta ce “Kin ji ko? Don
Allah ki saki ranki ko nima kin karfafa min gwiwa,
kowa da yanda Allah yake tsara masa rayuwa da
jarabarshi. Taki kenan a haka tazo miki, kar kiyi fushi ko WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
ki ja da ikon Allah.”
Ta dubeta ta ce,
“‘Ke tunda ki ke kin taba ganin irin
haka tsakaninki da Allah?” Ta ce,
“A’a ban taba ganiba.
“‘ Ta ce,
“To da wane suna zan kira nawa auren? Ni ba
auren dole ba ko a garin mahaukata ba a haka, bare a
Musulunci wanda hakan babban laifi ne da hukunci mai
girma ga duk wanda ya aikata haka, duk saboda kafiya
irin ta iyayena da jahilcinsu kowa son ransa yake so.”
Ta ce, “Ya isa haka nan. Ki bar kiransu da haka, dole
dai akwai mafita a al’amarin nan, kuma za ki gani.Ta ce,
“To amman meye amfanin yin kwalliyar
Rafi’a? ban san wane matsayi nake ba, ban san wane
angon zan wa kwalliyar ba?”
‘” Ta ce, “Da duk wanda aka
riga aka daura shine zaki kaiwa kwalliyar.
‘Ta numtasa ta
ce, “Tir! Da halin iyayena, da yanzu na dade da kai
Kararsu kotu, amman aka hana ni.”
Ta ce, “Ya isa haka Mabaruka! Mu ci muyi sallar saimu wuce.
” Bayan sun gama sunyi sallah- sannan suka
fice.
Karfin shiga kasuwar daman a su kara tsintsinto
wasu abubuwan da ba a karasa saye ba, ba don son WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
Mabaruka ba. Duk abin da Rafi’ar ta gani sai ta dauka,
suka yi shatar me Adaidaita ta cika dam.
Fitowa tayi daga shagon ta fito ta tsaya bakin motar,
sam! Ba abin da yake burgeta, ba abinda ta zabo don
ra’ayinta duk zaben Rafi’ar ne tamkar ita ce amaryar.
Ta fito ta sameta ta dubeta da kyau ta ce, “*Shi ne ki ka
fito ki ka bar ni da zaben ki ka dawo nan ki ka tsaya?”
Mabaruka ta yatsina fuska tana kallon wani wurin
daban. Ta ce, “Meye amfanin sayen kayan to, alhalin
ban san gidan wane angon za a kai ba, Sulaiman ko
Imran?”
Raf’ar ta ce, “Ko ma wanene kin san dai dole gidan
daya za a kai ki, ko Imran din ko Sulaiman, don haka ki
zage kawai ki dauki abinda kike so.”
Shigewa motar tayi ta zauna tana cewa, “In kin gama
ina nan ina jiranki, rana na dukana.”
Sakin baki tayi tana kallonta, sannan ta kada kai ta
koma shagon tana cewa,
“‘Allah ya shiryaki Mabaruka
Sai da ta gama daukar abinda zata dauka sannan ta
dawo motar suka shiga. A shagon saloon din Anti Farida
suka tsaya, ta ce wa Mabarukan ta shiga ta jirata ta kai
kayan ta dawo.
Mabaruka ta shiga shagon da sallama jiki a mace
tana jan kafa. Anti Farida ta bi ta da kallo har ta zauna, ta
ce “‘A’a amarya ya dai na ganki haka ba WWW.DAILYNOVELS.COM.NG kuzari, ko an
fasa kukan amarcin?”
Mabaruka ta zumburo baki taki cewa komai. Anti
Farida ta ci gaba da fadin «Yanzu nake shirin rufewa in
je in ji lafiya har yau ba ku zo ba, ina Rafi’atun?” Ta ce
ciki-ciki “Ta wuce gida ta dawo.
Ta kalle ta tsaf! Sannan ta dawo kusa da ita ta zauna
tare da data kafadarta, ta ce
“Menene Mabaruka?”
Mabarukan
ta kalleta idanunta sunyi kwalkwal.
Hankalin Anti Farida ya kara tashi ta ce.
«Fada min mana, ko an fasa auren ne?” Mabaruka ta ce,
“Da hakan yafi min dadì da kwanciyar hankali.” Anti
Farida ta ce cikin rashin fahimta.
“Kamar ya?” Ta ce a
marairaice zata yi kuka “Maza biyu fa ake kokarin aurar
da ni gare su.”
Cikin sauri Anti Farida ta zazzaro idanuwa ta ce,
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.DAILYNOVELS.COM.NG