WAYE ANGON CHAPTER 22 BY MARYAM JAFAR KADUNA
WAYE ANGON CHAPTER 22 BY MARYAM JAFAR KADUNA
mata,Ta fito tana gyarawa, kayan miya ne da kifi lodi
guda, duk ina kallo ban ce komai ba, sai da ya fito muka gaisa na ce.
“‘Amman abin da ka ke ya kamata kenan? Yau ka sami lokaci kuma aljihunka da nauyi a kullum in dai nice da girki ba ka da kudì sai ranarta? Malam kar fa ka manta baya ka nutsu ka gyara kuskurenka. Ya bata rai “Ni matsalata da ke kenan bakin ciki, kina bakin ciki ana kawo mata ni ba daga ni ba ne kuma
abincin nan in an dafa ana baki kin fi ma kowa ci amman kullum kina bakin ciki da haka.
Raina ya baci, na ce “Kai kasan ban taba maka bakin ciki ba da samuwarka ina son dai ka gyara kuskuranka don ka zamo mai adalci, ka tashi gobe kiyama babu alamar rashin adalci a tare da kai.”Ya ce,To ba zan yi ba, ki dauki mataki.Daga haka ya fice.
Abin kullum gaba yake karawa, musamman da ta samu ciki abin da yake nema kenan, don haka rawar jikinsa ta karu na koma bora a cikin gidansa, ba ni da matsayi a idonsa ko kadan sai dai ita ke juyinta son ranta.
Kullum ita ke yin daidai amman ni ko ya nayi
kuskure duk makota sai sun ji saboda fadansa. Zaman ya koma min na hakuri, ko kadan bana jin
dadinsa, ko yana dakina babu wata mu’amula
tsakaninmu idan ni na neme shi sai ya ce shi ya gaji, don Allah na kyale shi ya huta sai yai ta sharar bacci ya banni zaune cikin tsananin bukata. A kullum haka muke, ta kai ga na fara masa kuka amman ko sau daya bai taba saurarata ba. Kamar wata rana mun yi haka da shi da dare, da safe
yana tashi ya ce in je gida na huta zai neme ni, na tambaye shi dalili sai ya ce naje dai kurum.
Haka nan ba da son raina ba saboda bukatuwar mijina na tafi gida, koda mahaifina ya tambaye ni dalilin
zuwana, na ce shi ya ce na taho gida. Ya dube ni da kyau ya ce,Halima.”‘ Na ce, “Na’am
Baba!” Ya ce, “Kin tabbata ba ki masa komai ba ya turo ki?” Na ce,
“Wallahi ban masa komai ba, kai ma ka sani
Baba a tsawon zamana da shi ban taba zuwa ko yaji ba,ban taba kawo maka Kararsa ba, lafiya muke zaune da shi ban taba jin ya yi min korafi nayi masa wani abu ba.Ya yi jim cikin gamsuwa sannan ya ce Amman abin
da mamaki Halima, ace haka nan miji ya turo mata gida wai ta zo ta huta?”
Nayi shiru dai. Ya ce,Amma zan neme shi yazo in ji me ke faruwa?” Na ce,A’a Baba kada ka neme shi tukunna ka bari muga me yake nufi kenan? Idan abin nasa ya wuce misali sai a tuntube shi.”Ya ce, “Haka ne kuma, shi kenan Allah ya tabbatar mana da alkhairi.”
Haka na zauna gidanmu tun ina jiran zuwansa mu tafi har dai na mike kafafuwa, idanuwana kullum a kofa, duk sanda Babanmu ya shigo ina bin bakinsa da kallo ko zan jiya ce
“Ga mijinki yazo ku tafi.” Amman shiru nake ji ba shi ba alamarsa, ga jarabar son mijina da yake damuna, kullum mafarki nake na
koma gidan har dai mahaifina ya fahimce ni.
Wata rana ya kirawo ni dakina. Bayan na zauna ya ce Kiyi hakuri Halima, nasan kina son komawa gidanki, amman kin ga har zuwa yanzu bai zo ba, bare ya bukaci hakan. Amman na yanke shawarar zan neme shi sai naji dalili. Idan laifi ki ka yi masa ki ba shi hakuri ki koma, idan kuma dai wani dalili ne duk zamu ji.”Na gamsu da hakan, don abin da nake nema kenan fada ne dai ban yi ba.
Don haka kwana biyu da maganarmu, kwatsam na tsinkayo maganarsa zaure tare da Babanmu, farin ciki ya bayyana gare ni, ba tare da naji ya suka yi ba, na hada kayana ina jiran a kira ni Ba wani dalili ba ne nashi illa kame-kame, wai na fiye kishi, tunda naga ya yi auren nan nake kishi da matarsa na takura mata da sa mata ido duk abin da take idona na kai bare da ta samu ciki wai na dinga jin haushi ina mata mugun baki, wai dan ai ba zama zai yi ba, nima haka nayi
Maganganu dai ga su nan da ji kasan tsara su akai, koda mahaifina ya ji bai yarda da zan yi hakan ba, amman dai ya ce
“To ya yi hakuri zai min fada ba zan
kuma ba insha Allah.” Ni kaina nasan ya fada ne amman ba haka ba ne, nayi
hakuri kawai na bar shi akan hakan ne, muka tattara ya wuce da ni.
Koda na shigo gidan kallon banza ta min, tare da jan tsaki. Cikinta ya turo sosai, plate din farfesu a gabanta tana sha. Ta harare ni ta ce, su karya dai an ji haushi ba zuciya an dawo dai to kizo ki zauna ba za ki samu Kima
da daraja ta matar gidan nanba za ki ga wane matsayi zaki zauna. Raina ya baci zan yi magana ya daga min hannu,
“Bana son rashin ha kuri da Allah wuce kawai.”
Ba na son mu fara daga dawowata hakan yasa na
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe