WAYE ANGON CHAPTER 23 BY MARYAM JAFAR KADUNA
WAYE ANGON CHAPTER 23 BY MARYAM JAFAR KADUNA
dauki jakata na shige dakin.In da tsari ake bi tunda na kwana da yawa ba na gidan
to yau ni Ke da miji, amman ina ganinshi ya shige dakinta. Na kyale shi yayi kwana biyu kamar yanda muke yi, don haka na share.
Akai kwana biyu duk yana dakinta a zatona zai dawo dakina, amman naga yana kokarin shiga dakinta, na dakatar da shi na ce.
“Ka manta ne yau a dakina kake?” Ya juyo ya harare ni tare da jan tsaki ya bude labule ya shige, na kara daga murya na ce baka ji ni bane yau fa a nan kake kwananka
biyu a dakinta.Ji nayi an turo daki bam! A wannan ranar nasha kuka iya karfina na tabbatarwa kaina lallai a yanzu ba ni da
Kima a gidansa, ba ma da son ransa ya dawo da ni ba mai yiwuwa saboda mahaifina ne.
Sai da na gaji sannan na bari na fito nayo alwala ina jiyo dararrakunsu daga daki na goge Kwallar dake son taruwa a idona na shige dakina. Tun daga sannan na daina kasancewa da mijina dawowata wata biyu kenan, yana gidan amman ya
manta dani ya ma daina maganar girkina, kullum ita keyi kayan abinci suna dakinta in ta gama ta yafo min a plate ta shige musu da sauran dakinta.In ya da wo ina masa magana ya ji tsoron Allah sai dai ya wuce ya bar ni tsaye ya shige daki har da banko kofa.
Lubabatu Kanwata ce ita ke bina wata rana tazo min ziyara. Wuni guda ta gama fahimtar me ke faruwa,musamman da taga an turo min plate daya na abinci ta shige daki ta rufe.
Ta Kare dubana yanda na rame nayi baki kashi har a fuska, ta ce Yaya! Na kalleta ta ce,
“Fada min me ke. faruwa?” Abu daman yana cina a raina kamar jin nake kun san
in kana cikin damuwa idan ka fadawa wani ko ya ya ne zaka samu sauki, ban yi niyyar fada mata halin da nake ba na fada mata.
Hankalinta ya tashi ta dinga kuka, tayi bakin cikin kasancewata a wannan halin ta dinga fada.Ai ba kallonsu za ki dinga yi ba Yaya, gidanki ne fa nan tazo ta same ki taje tayi ‘yan abubuwanta ta anshe miki miji sai ki sa ido kina kallonsu. Na ce,To me zan yi Luba?” Tace,
“‘Nuna mata za ki ita Karamar yar iska ce, ba tare da kin je gun boka ba ko Mallam, nasan kina addu’a amman dabaru hikima za ki
janye hankalin mijin na ce to ba sai in ina ganin mijin bama. Ta ce,Ko yana dakinta ne banka ki shiga ki zare mata ido ki nuna mata ke ma ‘yar bariki ce, ba a fiki wayau ba, don ma tana ganinki laka-laka shi yasa amman in irina ce ai ba inda zata je wallahi,”Na ce,
“Ba mai maganin abin nan sai addu’a, Luba
wani rashin kunya duk ba mafita ba ce, ke dai ki taya nida addu’a kurum.Haka dai Luba ta tafi tana ta fada akan zata dawo
kwana biyu taga ya abin ya sauya, lallai dai inyi abin da tace. Har nayi bacci kamar daga sama naji saukar bulala a jikina na mike ba shiri bai saurara da dukana ba sai da ya
min liga-liga sannan ya kyale ni yana huci wai na fara zama ‘yar iska, wato an zo an zuga ki kun hadu ke da ita ku ka dinga ci mata zarafi zagi ba wanda ba kuyi mata ba, har da duka.
Na kalle shi cikin, mamaki na ce me tace maka?”Ya ce, “Ko zata yi miki Karya ne? Yanzu gata can kwance bata da lafiya, sakamakon dukan da ku ka yi mata har ya shafi cikinta.
Na dube shi hawaye na zuba na ce ” Wallahi-wallahi ba abin da ya shiga tsakaninmu, ko magana bare zagi har ya kai ga duka na rantse me yasa zan dakar maka mata ina
kuma kallon halin da take ciki.”Ya ce,
“Za ki iya ai, sau nawa kina nuna adawarki
saboda kin kasa ki haifa su zauna gatanan shekararmu nawa da ke, me naci riba da ke sai wannan wai ‘ya mace guda daya tal? To meye ma amfaninki?Ni ba farin ciki nake da ita ba wallahi. Ina son magaji namiji, wannan shine musababbin aurena, kuma gashi nan da alama zan samu, yarinya mai albarka tana
kyautata min fiye da ke, ina jin dadinta amman kina kokarin nakasa min ita.Nace,
“Komai na Allah ne, ba ka fi ni son na haihu ba
su zauna, ba daga ni ba ne ko ita ma hakan yana iya faruwa da ita don Allah ya nuna maka ikonsa.Fadin wanna magana yasa ya kara hassala yaci gaba da dukana son ranshi sai da yaga bana motsi sannan ya kyale ni ya fice yana maida numfashi. Darennan ban iya ci gaba da bacci ba, na ci kuka harna gaji hawaye suka kafe sai a sannan na fara nadamar dawowata gidansa bayan tunda na dawo har zuwa yau ban kasance tare da shi ba.Haka naci gaba da zama gidansa ba wanda yasan halin da nake ciki sai Luba, tana yawan kawo min ziyara duk sanda tazo sai mun sha kuka ni da ita, ta so ta yi wani
Kokari a kaina amman na hanata, ni nasan komai lokaci ne, ba abin da ke dauwama.
Na cutu a gidan Baban Mabaruka nayi kuka nasha
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe