WAYE ANGON CHAPTER 24 BY MARYAM JAFAR KADUNA

WAYE ANGON CHAPTER 24 BY MARYAM JAFAR KADUNA

 

duka na wulakanta a idonsa na koma shara me aiki tafi ni daraja.

•Allah cikin ikonsa, matarsa ta sauka a ranar data haihu a ranar dan ya koma, wannan shine dalilin

rabuwata da shi. Saboda hakan na faruwa ya ce nice na kashe masa da don na yi masa baki cewar ita ma dan ba zai zauna ba,don haka à ranar yai min kora ta wulakanci gaban iyayenta da ‘yan unguwa, yasa bakin wuta ya dinga

dukana gaban jama’ar ina kuka ina rokonsa har ya cillo ni waje bai fasa dukana ba rigata ta yage zani na a kwance amman ya kasa saurara min.

Da kyar ‘yan unguwa suka kwace ni ta hanyar rike

shi. Wani mutum ya cire babbar rigarsa ganin tsiraicina ga mutane dankare, don haka ya rufe ni da ita a nan yamin saki uku gabadaya.

Wata makociyata ta fito ta jani gidanta, ta ba ni

suturarta nasa har zuwa lokacin ban fasa kuka ba, cike da takaicin wulakanci da tozarcin da ya min gaban maza da mata yara da kanana, ta dinga lallashina da ban hakuri, ta ba ni waya na kira Luba. Lokacin da tazo taji me ya faru ta harzuka matuka ta nufi gidansa taci masa mutunci ni na hanata.Tun daga wannan ranar mahaifin Mabaruka ya fice

min a rai, ina masa matsananciyar tsana babu wanda bana son jin ko maganarsa, irinsa bare na gan shi muka yi rabuwa ta har abada.

Dole ina ji ina gani ya kwace Mabaruka ta ci gaba da zama gun matar Babanta wacce ba kalar wuyar da bata sha ba gunta.

Na dawo gidanmu da zama tare da matan Babana zamanmu lafiya har hankalina ya kwanta damuwata ta wuce, mahaifina yaci gaba da min addu’ar samun miji na gari.

Haka Allah ya hada ni da Alh. Umar mahaifin Imran kenan, tun ban amince da shi ba har na yarda muka yi aure. Ban taba tunanin ana samun namijin da ke nunawa matarsa sò da kulawa ba irinshi. Ya damu da ni da matsalata, ya zame min tsani, rayuwata ta canza tayi kyau farin ciki ya zauna tare da ni zamana lafiya da mijina cikin tattali da kulawa,Alh, Umar Allah ya azurta shi da tarin dukiya yana da kasuwanci kasashe-kasashe da gida Najeriya shi kanshi bai, san adadin dukiyarshi. Ba- Mutumin kirki ne me fara’a da son dariya, yana bada taimako ga talakawa koda yaushe ya ware wani abu daga dukiyarsa da yake rabawa mabukata a kullum. Matarsa ta rasu da dadewa, Imran da Sharifat sune kadai ta haifa, Balarabiya.ce a wajan kasuwancinsa ya

hadu da ita a kasar Saudiyya, mai kamala da addini, ‘yar babban Malami ce a can akwai tarbiyya da nutsuwa tare da ita.

Ta ba su Imran tarbiyya da ladabi daidai gwargwado,sun fita daban, ko bayan zuwana sun dauke ni tamkar mahaifiyarsu ban taba fuskantar wulakanci ba, ko rashin kunya ba gurinsu Imran ya yi karatunsa a (England) na Pilot har ya

kammala yanzu haka yana aïki a nan gida Najeriya. Sharifa kuma ta bukaci tayi karatunta a Saudiyya akan Arabic, hakan yasa ta koma hannun dangin Mamanta taci gaba da karatunta sai ta samu hutu take zuwa gida Najeriya.

Ban taba ganin ‘yan uwa masu son juna ba irin su

Imran da Sharifat mai sunan mahaifiyarsu. Imran ya damu da Kanwarsa da damuwarta haka zalika ita ma koda yaushe Yayanta.Ta zauna tare da su Imran tamkar ‘yan uwanta,shakuwar da ke tsakaninta da Imran ya wuce misali, ya dauke ta jininsa kanwarsa, zai fita da ita yawo wuri-wuri. Ita ma tana jin dadin kasancewarta da shi, sai su

wuni tare suna wasa.Ta dubi Alkali «Wanna shine takaitaccen tarihin rayuwata.”

Alkali ya yi ‘yan rubuce-rubuce sannan ya ce yana kallon Baban Mabarukar.Ka ji abin da ta ce, da gaske haka ne ko ka musa?”Ya sunkuyar da kai sannan ya ce, “Eh haka ne.Mabaruka ranta ya baci, hawaye suka dinga zuba ta dinga kallon mahaifinta mugu azzalumi wanda ya wulakanta mata uwa, ya tozartata. Ashe ma ba ya murna

da ita a samuwanta yarsa?

Haba shi yasa a kullum take yawan tambayar

mahaifiyarta me ya raba ta da Babanta? Ashe ba komai bane a labarin sai wulakanci da tozartarwa, tabbas tasan zata tsani mahaifinta, shi yasa taki fada mata.Haushinsa ya darsu a ranta, ta dinga masa kallon mugu.Alkali ya sake cewa. Waye Sulaiman? Meye dangantakarka da shi? Sannan me yasa ka hadata aure da shi?”

Ya ce,Sulaiman kamar kani ne a gurina, don kanin

matata ne Binta, ubansu daya da ita. Ya kasance yana zuwa gidana, idan ya zo kanshi tsaye yake shigowa

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE