WAYE ANGON CHAPTER 25 BY MARYAM JAFAR KADUNA

WAYE ANGON CHAPTER 25 BY MARYAM JAFAR KADUNA

 

saboda tamkar gidansu ne.Yana yawan tsokanar Mabaruka a duk sanda yazo ita

ma takan biye mishi.Tsawon lokaci suna tare da juna tun daga zolayar da suke wa juna har suka fara soyayya tsakaninsu, hakan ta*

bayyana shi da kanshi Sulaiman din ya min maganarta,ya kuma bukaci da na ba shi aurenta a shire yake ya aureta.

Nayi farin ciki da haka, don nasan waye shi. Yana da hankali da ilimi, matata ta kara karfafa min gwiwa. Na.kira Mabaruka na tambayeta ko tana sonshi zata iya aurensa?

Ta ce, Sosai ma Baba na gamsu da Sulaiman na lura da shi yana da hankali da ilimi, wannan yasa na yarda da shi. Na ce, Shi kenan kije na amince da aurenku har bayan raina, ko da na mutu ki aure shi, ni ma na yarda da nutsuwarsa.

Hakan yasa na shaidawa Sulaiman ya turo magabatansa na ba shi auren Mabaruka, bai yi wasa ba ya turo su muka yi magana.

Wannan shine musabbabin da na aura mata

Sulaiman Alkali ya gamsu, yasa aka kira Sulaiman. Ya ce,A takaice wanene kai?” Ya ce,

“Sunana Sulaiman Garba, mahaifina ya dade da rasuwa, na taso karkashin kulawar mahaifiyata, ni da kanwata Samira,nayi aure har sau uku ina da ‘ya’ya biyu, amman yanzu ina da mata daya ne sai Mabaruka.Alkali ya ce, “Ka ba da sadakinta kuma?”• Ya ce, “Sosai na ba da sadakinta da duk wani abu na aure, kuma Kanin Babanta shi ya daura mana aure da ita.Aka kira Baba Hamza.

Alkali ya dube shi ya ce,Kai ne Kanin Mahaifinta?”

Ya ce,Eh ni ne uwa daya uba daya muke, kuma ni na karbi sadakinta kuma na daura auren tare da cikakkun shaidu da waliyyai.”Alkali ya ce,Ya a ka yi ka daura aurenta bayan ka san daura aura mata aure da wani?”Ya ce, “Ban sani ba, nasan dai suna rigimar auren shi da mahaifiyarta.

” Ya kara da cewa,Kuma lallai na daura kafin su su daura, hakan yasa ban yi wasaba na

daura din.”Alkali ya gamsu, ya dubi Momy ya ce, “Ya a ka yi a matsayinki na mace ki ka daurawa ‘yarki aure da wani bayan kin san Babanta ya daura mata aure da wani?”Ta ce, “Ni ba ni na daura mata aure ba, kanin Babanta shi ya daura mata aure, bayan yaga iyayen angon sun ba shi sadakin aure.”Alkali ya ce, “Meye dangantarki da angon? Ya kuma aka yi ki ka hada auren?”

Ta ce, “Kamar yanda na ce Imran dan mijina ne, na dade da yabawa da dabi’unsa, nasan idan har Mabaruka ta aure shi zata yi farin ciki ba gidan da zata ji dadi irin gidansa. Saboda yanda yake sonta da kuma ingantaccen ilimin addini da ya samu, kuma yana aiki da shi. Imran

yaro ne mai nutsuwa da hankali, yana da tausayi

matuka.Idan suna wasa in ta yanke ko ta fadì ina ganin yanda yake damuwa da ita, duk yanayinsa ya sauya duk da lokacin yana shekara sha takwas tana da shekara takwas.

Ya taso da sonta da tausayinta, duk inda yaje ya dawo zai nemeta, sannan yana da matukar saukin kai da hakuri, zan iya cewa ba wanda yasan Mabaruka da yanda zai tafi da ita sai shi.

In ranta ya baci yasan yanda yake lallashinta, ita

‘kanta tana kasancewa cikin farin ciki tare da shi, har ta girma ta kammala Sakandire.

Na barwa kaina suna son junansu ne kamar yanda shima Baban Imran yake zato, wata rana ya gansu tare.Yanda yaga suna nishadì da walwala fuskokinsu a kan na juna suna sakarwa juna murmushi; ba su san da kowa gabansu ba.

Ina kicin ya shigo ya same ni fuskarsa da farin ciki yaCe, “Kin san me?” Na ce, “A’a.” Ina kallonsa.

Ya ce, “Wani abu nake gani a gidannan, ban sani ba ko ni kadai na gani.” Na ce, “Me kenan?” Hannuna ya jawo ya kai ni inda suke ya ce, “Kalli ki gani.”A lokacin sun koma suna hoto tare, da ka gansu zaka fahimci akwai wani abu tare da su, na juyo ina dariya naCe da shi.Ai in wannan ne ni na ma saba da gani kullum, kaine dai ba ka gani tunda ba zama ka ke ba.Ya ce, “Kice haka suke amman ba ki taba sanar da ni

ba da gaggawa.Ya ce, “Baki fahimci komai bane?” Nace, “‘A’a shakuwa ce tsakaninsu.”

Ya kara da cewa, “Da soyayya kuma.” Na zaro ido

ina kallonsa, na ce “Iye!” Yayi dariya ya wuce, ya zauna• yana cewa “Yes.”Ni ma na zauna ina farin ciki, na ce “Amman ya aka

yi haka?” Ya yi dariya ya ce, “Ikon Allah mana, amma fa

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE