WAYE ANGON CHAPTER 28 BY MARYAM JAFAR KADUNA

WAYE ANGON CHAPTER 28 BY MARYAM JAFAR KADUNA

 

Don haka ba za ta yarda da cutar dan uwanta ba, in ita ba ta sonshi su suna sonshi, fiye da kowa ma, sun fi son rayuwarsa a kan tasu.

‘Tasan ita ‘yar lelensa ce abin da take so yake yi, in har .: ta bata rai ta ce bata son abu bare yaga hawayenta to tabbas zai rikice hankalinsa ya tashi, shi ma wannan abin zai tasiri masa ya yi mata abin da ta keso.

To wannan karon tayi alwashin sai tayi fiye da hakan don ya hakura da auranta.

.Haka dai suka kasance a wannan ranar har dare, Daddy ya dubi Momy ya ce, “Sai mu wuce gida ko, dare ya yi sosai.”Tace To wa zai zauna tare da shi kenan?” Ya yi” murmushi tare da nuna mata Mabaruka da ido. Tayi jim. tana gane hikimarsa, eh tabbas haka ne don haka ta ce

shi kenan. Suka harhada flask-flask din ta dubi Sharifa ta ce, Muje ko.” Ta kalleta ta ce, “Ba a nan zan kwana ba? In na tafi wa zai zauna da shi?” Daddy yaja hannunta yana cewa “Zo kiji Suka fice. Momy ta dubi Rafi’atu ta ce, “Taso muje Raft’a, ki bar Kawar taki sai gobe mun dawo.”

Ita kanta Rafi’ar hakan ya mata dadi, ta mike da sauri yayin da Mabarukan idanuwanta suka fito. Ta dubi Momy a marairaice ta ce, “Kada ki min haka Momy, wallahi zan cutu. Ku bar Sharifa tare da shi.” Ta harareta ta ce, “Idan kun tare da shi sannan ne za ki cutu, amman daga yau kullum tare da shi za ki dinga kwana, ga shi nan mun bar miki amanarshi, marar lafiya ne duk abin da yake bukata ki masa tun kan ya nema, na fada miki.”

Ta riko Momyn tana kuka, “Wallahi ko numfashi ba zan iya maidawa ba in dai daga ni sai shi a dakinnan zuciyata daci take min, don son Annabi kar ku bar ni a nan. Ina ji na tamkar a kungurmin daji nake. Wani irin mari tayi mata wanda yasa ta saki hannunta ba shiri, ta dafe kunci ta ci gaba da harararta. Wawiya wacce ba ta san me take ba.” Daga haka ta fice. Rafi’a ta ci gaba da kallonta cikin bacin rai ta ce, “Kinga ni ko karo na biyu kenan tana dukanki saboda lafiyarki, har kina fadin baki iya maida numfashi. To mu dawo gobe mu tarar kin sankare shi ne za ki nuna mana tsantsar kiyayyarsa.” Ta juya.

“Da sauri ta riko hannunta tana kuka, ta ce “Kema haka za ki ce ba ki ga cutar da aka min ba?” Ta harareta tare da fizge hannunta ta ce, “Tabbas iyaye na cutar

‘ya’yansu wajen zabar musu mijin da ya dace da su don farin cikinsu ba don musgunawa ba, kije kiyi abin da ki .,.ke so Mabaruka, kar ki kasance da shi ki bar dakin.

Daga haka ta fizge hannunta ta fice a fusace.

Ta daki bango tare da fashewa da kuka tà duke a nan, zuciyarta tayi mata nauyi da daci, bata jin akwai abin da ke mata dadi.

Shi kuwa Imran yanakwance bacci ya dauke shi bai san ma me ake yi ba.

Lokacin da Daddy yaja Sharifat zuwa bakin motar tana masa kuka ta ce, “Me yasa zamu bar shi da ita alhalin bata sonsa? Wallahi zata cutar mana da shi Daddy, kar mu bar shi daga shi sai ita, me yiwuwa ya bukaci wani abun ta hana shi.”

Yasata motar ya dube ta ya ce, “Kada ki damu, Yayanki zai kasance cikin farin ciki a yau, ba abin da zai dame shi, za ki gani. Sannan kada ki manta akwai aure tsakaninsu, wata rana za su yi zaman aure na har abada, ke dai ki masa addu’a.Ta ce, “Ba na son aurennan Dady, akwai cutarwa.” Ya yi murmushi ya ce, “Mu muna so shi ma yana so, za ki kuma gani. Me yiwuwa ki samu mai sunan Umminku a samu Sharifat ko kuma ku samu Daddy, ko ba kya son mai sunana?”

Ta dan yi murmushi ta ce, “Ina so.” Ya ce, “Yawwa to ki musu addu’a.” Ta ce, “Amman kana da hakikanin shi ne mai matar?” Ya ce,

“Yes, Imran shi ne mai matar, shi

kotu zata ba Mabarukar don shine Angon a zatona.”Ta rausayar da kai ita dai ba haka taso ba. Su Momy suka fito suka shiga suka wuce a motar tafe suke suna farin ciki a kan wannan tsarin, tabbas haka za su ci gaba da yi da alama komai zai yi daidai.Rafia ta ce a sauke ta kan layinsu zata wuce gida, gobe tazo asibitin da Mamanta, don haka suka sauketa ta wuce gida.

****

Su Sulaiman kuwa ana can ofishin ‘yan sanda an gar kame shi, ba za su sake shi ba har sai an ga tashin Imran. Inna ta dinga cizgar fada, haka nan yaje ya dauko musu jangwamgwam! An zo an garkame shi kan wata yarinya can, to ahir dinka ba kai ba yarinyar nan. Ya ce, cikin jin haushi “To matata ce fa, don me za ki ce haka?” Tayo masa dakuwa. Uwaka nace, ja’iri mato ba mata ba don ubanka, kar na sake. jinta a bakinka ga matarka can a gida ka bar musu can su karata, ai ban san haka auran yake ba, munafuki ka boye min ka san ba zan yarda da wannan mahaukacin auren ba, wanda ko a Musulunci haram ne

Hmmm LABARI fa nata tafiya shin koya zata kaya kudai kuci gaba da kasancewa damu a Koda YAUSHE

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE