WAYE ANGON CHAPTER 29 BY MARYAM JAFAR KADUNA

WAYE ANGON CHAPTER 29 BY MARYAM JAFAR KADUNA

 

babba. Babban laifi, kai kanka mahaukaci ne sakarai har ka yarda aka aura maka ita alhalin an aura da wani.”Ya ce, “Ni fa ban san wani ba, Babanta shi ya aura min ita, shi kuma wancan uwarta ce ta daura kuma kin san mace bata daura aure, don haka nine mai matar, ni kotu zata ba.”Ta ce, “Idan ba kai min shiru ba sai na kwade maka baki, tunda nake ban taba zuwa gaban Alkali ba amman sanadinka sai gani a kotu.

Yau kuma ga ni a wajan ‘yan sanda, kai kanka ba a taba saka a wannan gurin ba, sai dalilin mahaukatan iyayen yarinyar, to ka kyale musu ‘ya ba kai ba Kara Zuwa kotun bare ni, shi kenan magana ta kare.”Da ba uwarsa. ba ce da sai ya naushe mata baki, shi haushinsa ma da takaici da yanzu bai san ina matarsa tayi ba, kar’dai ace tana wajanshi? Kishi ya taso masa, idanunsa suka kada jajir har huci yake idonsa Sun rufe tamkar ya balle karafan yake ji. Ta dube shi ta ce, “Au! Dukana zaka yi ka ke huci?” Sam idonsa ba kanta yake ba, karfi na kara zuwar masa ya ce “Ki bar gun nan.

‘”

Ta ce, “In bar gun nan?” Ya nanata cikin tsawa “Ki bar gunnan na ce.” Ya daki karfen. Ta tsorata ainun, da gudu ta bar gun tana waiwaye, sam bata taba ganinshi haka ba ya bata tsoro.

Ya dinga dukan karfen da bango yana ihu, “*Wallahi idan ya taba min mata sai na kashe shi, matata ce ni ne Angon.’

” Haka ya dinga kururuwa kamar zai fasa gurin ya fito.Har dare sai da sukai mai allura sannan ya nutsu ya kwanta. Mabaruka kuwa tana nan tana ci gaba da kukan har karfinta ya kare, tayi zaune dabas bakin kofa tana ajiyar zuciya.

Taiwa kanta alkawari ko motsi ba za ta yi ba daga. wurin haka za su dawo goben su tarar da ita bakin kofa bare ta juya taga makiyinta, ta dinga ayyanawa a ranta dama ya mutu kan goben sai dai a zo a dauki gawarsa, wallahi da tayi farin ciki, a duniya damuwarta ta kare.

Bacci ya yi mai nauyi, wani ikon Allah ko da ya farka ya ji kansa wasai, nauyin da yake ji babu shi tamkar ba abin da ya same shi, shi kanshi bacci magani ne.

Ya mike zaune yana waige-waige a dakin bai ga kowa ba, ya yi mamaki da bai ga su Momy ba, tafiya suka yi kenan!

A haka idanunsa suka sauka kanta, a durkushe ta juya baya abin ya ba shi mamaki matuka. Mabaruka kuma me take a nan? Da ita aka bar shi kenan? Abin ya daure mai kai, ya a ka yi ta yarda ta tsaya. Ya yi shiru ko ba komai dai ya ji dadin kasancewarta a gurinshi, ina ma za ta yarda da shi?

Gani ya yi ta taso ta tunkaro shi fuskarta dauke da murmushi, yanayin yanda take tafiyar ya daukar masa hankali. Ta Kara masa kyau a fuska matuka, amman anya Mabaruka ce? Ko dai ta canza ra’ayinta ne?

Da zuwa ta sunkuya daidai fuskarshi har suna jin numfashin juna ta ce a hankali cikin salon jan hankali.Ka tashi?” Wani kamshi ya fito daga bakinta wanda har sai da ya lumshe ido don dadinsa. Ya kasa buda bakinsa ya yi magana sai dai ya daga kai “Eh.”

Ta ce, «Ya ka ke jin jikin yanzu?” Ya ce, “Na warke.”Tayi dariya tare da cewa “Gabadaya ma?” Ya daga kai ta Kara cewa “Me yasa?”

. Ya ce, “Saboda kasancewarki a nan tare da ni, gani nake kamar a mafarki wai ke ce haka ki ke min dariya, kin yarda da ni kenan a matsayin mijinki?” Tayi murmushi tare da shafar fuskarsa ta ce da shi.

“Sosai ma kuwa, kai din ba na yarwa ba ne, a ganina idan har nayi ganganci ka rabu da ni na tabbata gauliya, kai din mai tsada ne, karya nake na ce bana sonka, wallahi ina sonka Imran.

. Ta fada a marairaice.

Ya ce, “Amman me yasa da ki ke cewa ba kya so.”

Tayi murmushi ta ce, “Ba haka ba ne, gaskiyar amman gaskiyar ina kaunarka.” Zakin maganar bai san ya zai misalta ta ba, har cikin

Kwakwalwarsa ya ce, “Dan sake fada Please.

” Ta ce,ina sonka.

Ya ce, “Kara.” Ta ce, “Ina sonka.” “Dan

Kara.” Ta ce, “Nima ina sonka.” Yayin da take Kara kusantowa gare shi, har ta hada kawai ta farka ta ganta kusa da shi.

Ya yi murmushi ya ce, “Nima ban san ya za mu kare . da ke ba Mabaruka.’ . Ya kara jawo ta jikinsa ya rungume kam yana jin wani nishadi a ransa. Ya godewa su Momy da suka bar masa Mabaruka yau kawai ya tabbatar zai sami ingantacciyar nutsuwa da farin ciki, ya ce “Ya Allah ka nuna min ranar da zan ganni da wannan baiwar taka a gidana, tana mai amincewa da ni da sona.”Ta gyara kwanciyarta tare da Kara lemewa a saman Kirjinsa duk a cikin bacci, ya yi murmushi yasa hannu ya rungumo kayansa. Daga haka suka ci gaba da baccinsu mai dadi sansanyar numfashinsu na haduwa da junansu shi dai bai san wane irin annuri yake ji ba, kasancewarsa

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE