WAYE ANGON CHAPTER 3 BY MARYAM JAFAR KADUNA
WAYE ANGON CHAPTER 3 BY MARYAM JAFAR KADUNA
“Me? Maza biyu? Ban fahimta ba?” Ta rausayar da kai
*To ya zan miki ma bayanin? Kawai dai maza biyu ake
kokarin aurar da ni gare su, saboda kafiya da naci da
taurin kan iyayena biyu, Mamana da Babana.
Kowa yana ji ya isa da ni, hakan yasa kowa ya nace
lallai wanda yake so shi zan aura, bayan ni din WWW.DAILYNOVELS.COM.NG ni ce
kadai ba cira ni za ayi ba.
Ta fada hawaye na zubowa
daga cikin idanuwanta.
Anti Farida ta ce,
“‘Oh God! Amman ya haka? Wane
irin addini ku ke bi ne?”
‘Ta ce tana kallonta “Musulunci
mana.” Ta kara cewa,
“Amman daman an taba yin
haka?” Ta ce; “A iya rayuwata ban taba gani ko jin
labarin ga inda aka yi cikin sani su fa sun sani kowa ya
dage sai dai daya ya hakura ba me janyewa. Ji suke
kowannensu shi ya haife ni, yana da iko da ni,
• Ta ce,
“To ina iyayensu?
‘Tace; WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
“‘Babu daya daga cikinsu dake
a raye
Ta Kara cewa, “Danginsu fa?” Mabaruka ta ce, “Duk
Kannansu ne babu me iko da su. Hakan ya ba su damar
bin son ransu
Tausayin Mabaruka ya bayyana a idonta, ta dafata
tare da cewa,
“Kiyi hakuri Maburuka amman ya za,ayi
wannan al’amarm ba kiyi wani koKari ba?”
Ta kalleta a sanyaye ta Ce, “Nayi iya bakin koKarina
na nuna musu amman ba wanda ya saurare ni. Karshe na
yanke shawarar kai su Kara kotun Musulunci. Da Rafiatu
naso muje amman tayi kutun-katun ta hana ta dinga
zagina ba ni da hankali zan kai karar iyayena kotu na
tona musu asiri a duniya wannan sirrimu ne ita dai
tasan dole daya zan aura.”
Ta ce, “To ke waye kike so a cikinsu?” Mabaruka ta
ce,
**Sulaiman mana! Kuma shi ne zabin mahaifina,
kowa yasan yanda muke da Sulaiman, tare muka taso da
shi, ina sonsa tuni shima haka duk da kasancewar yana
da matà. WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
Na dace da yin kaura daga gidammu naki zama gun
Babana, haka naki zama gidan Mamana duk don su
Tsorata su hakura su bar min zabina, na dawo gidan su
Ganin hakanne yasa ba tare da sanin Rafi’atu ba na
sulale zan gudu, a kan hanya naci karo da ita dole na
dawo. Yanzu haka a gidansu nake, ta kasa ta tsare ni.”
Anti Farida ta ce, “Kada ki damu akwai Allah, dole
daya za ki aura you will see.” Ta langabar da kai ta ce,
“‘Zan ga yanda za a yi kuwa.”
Daidai shigowar Rafiatun, ta gansu jigum! Ta bisu
da kallo tare da jan kujera ta zauna, sannan ta dubi Anti
Farida ta ce, “Tana nan tana ba ki labari ko?” Ta nisa ta
ce, “Ina ji amman Rafia ya ki ke ganin haka zai yiwu?
Anya ba ki kuskure ba da ki ka hanata aiwatar da WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
kokarinta? Akwai sabo fa a kan hakan.”
Rafiatu ta dubeta da kyau ta ce, “Duk abinda nake
ina sane Anti. Ni dai nasan duk taje ta komo miji daya zata aura, Duk Wanda a Ka riga aka daura da shi shi kenan
magana ta kare
Amman batun ta kai iyayenta kotu bai taso ba, bare ta
gudu bata san hannun da zata fada ba. Me yiwuwa ta ce
gwanda masifar nan, Ita ‘ya mace ce, me mutunci dole
ne ta zauna gaban iyayenta. Don haka ban goyi bayan
hakan ba, kuma ba zan taimaka mata ba, illa iyaka na ce
mu ci gaba da gayawa Allah,”
A nan Mabaruka ta ce cikin fushi “‘Kwana biyu fa ya
rage Anti, me zamu yi lokaci fa ya kure? Zuwa yanzu ya
kamata a ce na gama yanke hukunci amman har zuwa
yanzun ban san wane matsayi nake ba, ban san me zanyi
ba, Wallahi ina cikin tashin hankali.” Ta dafe kai,
Anti Farida ta ce, “Abinda Rafi’atu ta ce haka ne
kam! Zamanki a nan shine mafi kwanciyar hankalinki
da darajarki. Dole dai gidan daya za a kai ki, Kiyi WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
addu’ar kawai Mabaruka,
Ta dube su ta ce, “Ni yanzu ba ma ta in auri wanda
nake so ba nake,ba a,a wannan abin kunyar da suke son
jawo min ne ya dame ni, duk duniya sai ta sani har
tsufana. Duk in da nabi sai an nuna ni, haka yarana za su taso.
Gefe kuma ga babban sabon Ubangiji da a ka yi. Niban ma san meye hukuncin haka ba
RafI’atu ta ce, “Ko ma menene ki sa ido ki gani za a yi
komai ya wuce, ki sa haka a ranki, Ba wani abu da zai dame ki.”
Haka dai suka kasance a shagon Anti Farida uwar
dakinsu, tana musu suna Kara zanta zancen.
Sulaiman Ango ba zama, ya shiga ya fita tuni ya
gama raba katinshi na gayyatar daurin aure ranar Asabar
mai zuwa, da misalim Karfe biyu daidai na rana,
Zuciyarsa fal da murnar samun amaryarsa.
Babanta ya kirata, ta jawo wayar tana dubawa. Sam!
Babu annuri a fuskarta ba kuma son yin magana da daya
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.DAILYNOVELS.COM.NG