Trending

WAYE ANGON CHAPTER 31 BY MARYAM JAFAR KADUNA

WAYE ANGON CHAPTER 31 BY MARYAM JAFAR KADUNA

 

 

Momy ta dube shi ta ce, “Ina Matar taka?” Ya yi murmushi ya ce; “Tana bandaki.” Ta kalle shi da kyau Bandaki kuma, a can ta kwana?” Ya ce yana dariya,A’a a nan ta kwana, yanzunnan dai ta shiga. “. Sai can ta fito tana kumbura baki, fuskarta tayi jajir idanuwan kuma sun kumburo da ka gani kasan tasha kuka Momy ta bita da kallo harta zauna can ciki tace “Ima Kwana?” “Lafiya.” Kawai ta ce ta Kara da cewa-Me ki ke a bandaki tun dazu?” Ta sosa wuya kanta na tasa ta ce, “Abu nake.” Ta kura mata ido kawai

Sharifat ko kallonta bata yi ba bare su gaisa, haka ita ma ta share ta a halin yanzun duk abin da ya shafe shi ba sonshi take ba, ba ya burgeta bare ya tsaya gabanta:

Tana kallon yanda suke nan-nan da shi ko yaya ya (motsa sai sun ji menene, me yake so? Shi kuwa idonshi na kanta duk yadda ta motsa yana jin matsanancin sonta na fizgarshi.Fushin ma da take burge shi, take. Aka fila masa abinci kala-kala ya ci ya gagara kai loma daya bakinsa.

Tunaninsa ita ba ta ci ba shi ma ba zai iya ba, dama ita suke tattali ba shi ba da yafi samun Kwarin gwiwa da kuzari, me yiwuwa yaci ganin tana ci, amman a halin yanzu ba zai iya ci ba.

Yasa abincin gaba yayin da yake kallonta ta wutsiyar ido.Sharifa ta ce, “Big Bro ka ci abinci mana, yana hucewa.” Ya dago yana kallonta tare da sakar mata murmushi iyakarsa fuska ya ce, “To.” Kawai. Momy ta ce, “Ko ba shi ka ke so ba?” Ya ce, ” A’a ina so.” Ta ce, “To maida hankali ka ci ga magungunanka me yiwuwa ma Likita ya sallame ka yau, naga jikin ya yi (kyau sabanin jiya.”Ya yi murmushi yana kallon Mabaruka da har yanzun fuskarta a türbune take. Ya dubi Sharifa ya ce da ita.Dauko plate ki zuba abinci kamar yanda ki ka zuba wannan.”

Ta dube shi tana son sanin me zai yi da shi kuma?

Shima ya dubeta ya ce, “Yi mana.ta wuce tayi kamar yanda ya ce, ta zuba a plate dinsa ta kawo masa. Ya nuna mata Mabaruka ya ce, “Kai mata.” Ta kalle shi da sauri zata yi magana, ganin yanda ya hade fuska yasa ta saurara, amman duk da haka sai da ta ce a shagwabe. “Ni zan zuba mata Yaya, ita bakuwa ce da sai an zuba mata? In ta ci cikinta ne fa in bata ci ba wa ta yi wa?”

Ya kalleta da kyau sannan ya ce, “Ni taiwa.” Ya ki

dauke kansa, ita ma ta kura masa ido.

Ya ce, “Yes kije kiyi abin da na saka ki.” Ta zobaro baki ta wuce. Da zuwa ta dankwafar da shi gabanta ba tare da ta ce komai ba.”

Ta dawo kusa da kafarsa ta zauna tana turo baki, ya yi murmushi kawai yasan duk abin da take don shine, ya dubeta ya ce, “Na gode kanwata.

” Ba ta ce komai ba.

Mabarukar ta dubi abincin ta harare shi, sannan ta dago tana kallon Sharifat din tana hararanta ta ce “Zo ki dauke abincinku ba na so.”

Kan ta gama rufe bakin taji saukar duka a bakinta kuf! Momyn ta ci gaba da kallonta ta ce “Ba ki da mutunci daman ko, ita tasa kanta ne meye laifinta don ta kawo miki abinci? Kar ki ci wa ki kaiwa in ba ki ci ba?” Ta ci gaba da turo bakin ta ce “To kar kici bar shi don Ya dubi Momy a marairaice ji yake kamar shi ta daka har sai da ya zabura. Ya ce, “Sorry Mom! Ayi hakuri zata ci ai ba ki ga yanda ita ta dire shi ba ba ladabi ba da’a, dole ne tayi fushi ta ce bata ci.” Fadin maganar da ya yi yasa ta dago ta harare shi ta kauda kai, ya mayar mata da murmushi.

Momy ta ce, “Kai rabu da ita, kar taci.” Sam bai so haka ba, yana lallaba kayansa sun zo za su hargitsa mishi ita.

Hannu Momyn tasa ta dauke plate din gaba daya ta ce “Mu muna so zamu ci wallahi.” Ana dauke abincin ta mike kafafüwa tana turo baki tamkar daman ya tare mata gurin.

Ya ce, “Ayi hakuri Momy.” Ta ce, “Kai kaci abincinka ka fita bukatar ci.” Shi ya sani sam ba zai iya ci ba in har ita ma ba za ta ci ba.

Ya sauko daga kan gadon, ya dauki abincin zuwa

• gabanta, da Momy da Sharifa suka bishi da kallo, me zai

Ya tsugunna gabanta fuskarsa sake yana jin wani dadin zuwa da ya yi kusa da ita. Ita ko sai turbune fuska take bata ko kallonsa.

Ya ce, “Mabaruka!” Tayi shiru kamar bata gun. Ya. sake kiranta a can makoshi ta ce “Na’am.”

Ya ce,

“Menene wai, me ke damunki?”

Ta dago tana harararsa, ya yi saurin kama kunnuwanta ya ce a hankali “Sorry!” Ta dauke kanta ya ce, “Me yasa ba za ki ci ba, kina son nima kar na ci ko?” Tayi masa banza. Ya sake cewa “Ko ba kya sonsa nasa a siyo miki abin da kike so?”

Tamkar bata nan bare ta amsa, ya sake cewa

“Mabaruka me ki ke so?” Ta ce can kasan makoshi ganin yanda Momy ke harararta “Ba komai.”

Ya ce, “To za ki ci wannan din?” Kai ta daga kurum don ya kyaleta, ta gaji da maganarsa musamman yanda ya tsugunna gabanta gaf har tana jin kamshin turaren jikinsa me sata tashin zuciya.

Yace Kin tabbata za ki ci?” Tace eh.” Ya ce,

“Sosai fa.Ta daga kai. Ya ce “*Yawwa Mabaruka, don Allah kici ba don mu ba, nasan ba mu isa mu sa ki dole ba kiyi abin da ba ki so, amman don Allah zo ki ci don nima na ci, wallahi idan ba ki ci ba ni ma ba zan ci ba. Ta ce a gajiye “Naji zan ci.”

Ya yi dariya ya ce, “Na gode.

” Daga haka ya mike ya

koma ya zauna. Wani Kululun bakin ciki ya tokare Sharifat, mikewa tayi ta bar dakin sam ba za ta iya jurar ganin haka ba.

Momy kuwa duk yanda take jin haushinta taji dadi

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE