WAYE ANGON CHAPTER 32 BY MARYAM JAFAR KADUNA
ganin yanda ya yi tasan lallai watarana sai son da yake mata ya dawo ita ke masa, a dai juri zuwa rafi wataran tulu zai fashe, Imran ba na yadawa ba ne.
Kan dole yasa ta dinga tuttura abincin tana yi tana
•goge kwalla. Wallahi sam bata jin dadin abincin, duk da yanda aka zauna aka kawata shi tana da tabbacin ba mai dandana abincin ya bari.
Idan gasa ake wanda ya girka abincin shi ne zai ci, amman dalilin shi ya dauko shi da hannunsa ya ce taci kuma shi aka dafo mawa yasa take ji ba wani abinci
• marar dadi a duniya da ya kai wannan.
Ko kadan bata jin dadinsa, tamkar tana zuba wuta a cikinta haka take ji har tana fitar da kwalla saboda takaicin cin da take.
Shi kuwa ganin tana ci dinne yasa ya samu Karfin gwiwa yaci sosai yana ci yana motsa kunne ga dadi a ransa na ganin tana ci ga shi ga ita.
Yasan watarana ita zata girka masa suci tare har ma ta ba,shi a baki. Ya ci abincin sosai sai da ya kusa tada shi sannan ya saurara.
•Tura abincin take tamkar ba zata bari ba, tayi alkawarin duk yawansa sai ta cinye ba za ta bari ba, duk da yafi Karfinta ko da zata yi amai ne, tunda har aka matsa mata sai taci.
• Don haka ta dinga tura shi tana yunkurin amai, ya tashi zaune yana kallonta yanda take turawa shi ya sani ba da son ranta ba, amman ai bai ce ta cinye ba, ko ya taci ya isa me yasa to take haka?
Gani ya yi Momy ta daddage ta kai mata dundu a baya cikin tsananin fushi, saukar dundun ya yi daidai da saukar abincin gaba daya ta amayo shi duk a kan plate din. »
r Ya miken a zabure yana cewa,Sannu-sannu
Mabaruka.”Hankalinshi ya tashi ganin tana amai, ya
. dubi Momy a marairaice.
Ita kuwa ta ce “Ke dai ‘yar wulakanci ce Mabaruka,. kin koshi shi ne ki ke turawa wato tunda ya ce kici shi ne sai kin ci wanda yafi karfinki, ke dai ki bata masa ko? Ya ji haushi? To kin kyauta.Shi yasa nima na taimake ki ki ka amayo shi.”
Ran Momy fa ya baci, ta dinga fada inda take shiga ba nan take fita ba, kawai ta suri makullin motarta ta fice fuuu!
Ita kuwa tana duken ko motsi bata yi ba, tayi face- face da amai idanunta sun sauya jajir saboda bacin rai, a ganinta an takura mata, yanzun in ban da so ake a mata fada, don me zata mata dundu don dai ace bata kyauta ba, kuma duk sanadin Imran.
Ta dago tana kallonsa da jajayen idanunta, kallon na tsane ka. Ya tsugunna yana cewa
“Sannu, sannu Mábruka.”
Ba abin da ya fito bakinta sai “Na tsaneka! Na tsaneka! Ba na sonka, ka shiga rayuwata, ka takura min daga farin ciki ka mayar min ita zuwa bakin ciki.
Sanadiyyarka yau na tsinci kaina mahaifiyata na dukana tana zagina, ina gain bacin rai a idonta, wanda da ba na fuskantarshi a gunta, ko kallon banza bata taba.. yi min ba bare duka ko tayi fushi da ni.
Duk kai ka jawo min, don Allah me yasa ba zan tsaneka ba? Me yasa ba za ka zamo makiyina ba?
Wallahi ko numfashinka ba na so, ka takura min, ka takura min!”» Ta fada da Karaji, jikinta har yana rawa
hawaye na zubowa.
Ya ce, “Me yasa har haka Mabaruka? Wallahi ban yi miki sanadin har haka ba. Ni kawai na ce ina sonki ne, don kuma na ce haka bai isa yasa mahaifiyarki ta dinga miki wadannan abubuwan ba, meye laifina? Ni fa. Ta katse shi da tsawa “Na.. .” ba ta karasa ba ta
Kakalo aman ta watso mishi a fuska, tana huci tana kallonsa.
Ya yi cak yana kallonta, fuskarshi dame-dame da
aman har zuwa rigarsa. Farin ciki ya bayyana fuskarta,
ganin ta bata masa rai.
Kamar a mafarki taga yasa hannu ya gogo aman na
fuskar ya tsotse a baki. Sai da ta rintse ido tsikar jikinta
ta tashi saboda kyankyami, zuciyarta ta tashi.
Wani aman yazo, tayi saurin tare shi da hannu taci gaba da kallonsa, bai fasa ba sai da ya lashe aman
gabadaya na fuskarsa duk yana kallonta.
Zuciyarta ta sake tasowa matuka, ta dinga yunkurin
zubo da shi, da sauri ya rikota ba shiri taji bakinta cikin
nasa yana tsotso, ba ta san sanda aman ya koma ba.
Duk wanda ya batata a baki sai da ya lashe shi tas ya
hade da bakin, ta dinga kokarin kwatar kanta amman
ina! Ta kasa duk Kokarinta, sai don karin kansa ya sake ta.
Ta dinga huci idanunta suka fito tamkar zakanya,
tana harararsa yaci gaba da kallonta ya ce, “Ina sonki, na fada miki yafi a Kirga na kuma nuna miki shi a zahirance, ina sonki bar haka a ranki. Ni Imran ina sonki har abada.
” Ya fada yana dariya.
Takaici ya hanata magana har tana ina ma ta bari ya hada bakinta da nashi tir! Ta dinga tofar da yawu tana goge baki.
Mikewa kawai tayi saboda abin ya kaita Karshe ta kalle shi da kyau hawayen takaici suka zubo ta ce,
“Allah ya isa.”Daga haka ta wuce bandaki da gudu,
kuka na son kufcewa.
Ya yi murmushi ya ce, “Na gode.
” Bai damu ba, ko a
jikinsa da kansa ya kwashe aman ya goge wurin.
Koda ta shiga bandakin kuka ta dinga yi kamar ranta zai fita, bata taba jin takaici irin na yau ba, duk yanda take kyamarsa amman ya hada bakinta da nashi yasa mata miyansa.
Ta dinga wanke baki tana kuka har sabulu tasa ta dinga dirza, amman sam ta kasa nutsuwa da ta wanke bakin miyansa ya fita.
Koda Likita yazo yaga jikinsa ya ce yana dariya “My friend ka warware ko?” shi ma ya yi dariyar ya ce,
“Sosai na ware, ina jina zan iya fada da ko da zaki ne.
Ya yi dariya sosai ya ce, “Yes! Yes, I see, amman har
Hmmm