WAYE ANGON CHAPTER 33 BY MARYAM JAFAR KADUNA
da taimakon Madam ko?” Ya yi dariya kawai.
Ya sake cewa “Lallai ta kyauta.”
An ba su sallama a ranar zuwan Rafi’atu kenan, ta tarar suna hada kayansu. Taná kallon Mabarukar tasan akwai abin da ya faru.
Suka zauna ta dubeta da kyau ta ce, “Fada min me ya faru? Ko angon yasha dumin amaryarsa jiya?”
Wata harara da ta dalla mata sai da ta tsorata, taja baya tana dariya. Ta sake cewa “Ah to, naga sai wani hada rai ki ke nasan wannan ne kadai zai sa kiyi kuka har idanunki su nuna.
Tayi Kwalkwal zata yi kuka, ta dubeta ta ce, “Kema ba ki sona Rafi’a tunda har kina hadan ni da wannan dan iskan ke a tunaninki shi ne Angon?”
Rafi’a ta ce, “Ban sani ba, don ba zan iya warware wannan hargitsin ba.
‘Ta ce, “Amman dai kin san Sulaiman shine Angon, saboda shi Babana ya aura min ba Imran ba, kuma kowa. ya sani mace ba ta daura aure, kin ga kenan iska ya kama.
Don haka ba zan taba yarda da shi ba, bare wannan abin da ki ke tunani ya faru tsakaninmu, tunda ba mijina ba ne.”
Ta ce, “Eh mace bata daura aure amman ke kin san
‘Baba.shi ya daura muku aure kuma shi ma yana iya
daura miki aure.
Ta ce, “Ko ma dai menene Sulaiman shi ne mijina ba gidan da zan je idan ba can ba.’
Rafi’a ta ce, “Shi kenan naji yanzu ma ki tashi ki tafi kar ki makara, amma dan fada min me ya miki har ya saki kuka idanunki suka kumbura?”
Tsaki taja tare da kauda kai alamar sai ki tayi.
Su suka hada kayansu ko hannu bata sa musu ba har
suka. gama suka fice, Rafi’atu ta jawo hannunta suka rufa musu baya.
Aranar aka sallami Sulaiman saboda sallamar da aka
yi wa Imran din, amma yasha duka.
Koda ya koma gida Inna ta zaunar da shi gabanta ta miko masa biro da takarda ta ce,Sakar musu ‘ya!” Ya
dubeta a torace saki Inna? Ni fa ina son matata, ta ya
zan sake ta?” Ta ce,Ta yanda ka fara jawo mana fitina don ubanka so ka ke na kyaleka ka dinga. zaryar zuwa kotu ana garkame ka a magarkama? To ba zai yiwu ba wallahi.Ga matarka can a daki ita ta dace da kai ba wannan yar mahaukatan ba.’ Ya turo baki “Ni gaskiya ina sonta ba zan sake ta ba, bayan wahalar da na sha ga kudin da na kashe sai su tashi a banza?” Yana rufe baki ta dauka.Sai a biyaka kayanka, ai ba su ci banza ba, nima ban goyi bayan ka bar musu ba, ni da kaina ma sai in amso su ba a bar musu ba,Ko Samira sai ka ba kayan shi kenan.
Ya ce, “Gaskiya ba zan iya ba, kowa yasan matata ce nine Angon.” Ta jawo karan dake kusa da ita.
“Sai in kwade ka wallahi, kai ne Angon, banza!
Sakarai fanko, kai kana gain za a baka ne har zaka iya ja da shi? Shi fa mai kudi ne Karfinku ba daya ba, zai iya sayenta da kudi ya dankarawa kotu da ‘ya’yanta kudi tuni su ba shi sai dai ka sha kunyar banza.
Don haka tun kan ayi ka rabu da ita ka bar masa kawai, ba dai karfin ja da su ka ke da shi ba wahala kawai za ka yi.”
Mikewa ya yi tare da shurar takalma yana cewa, “Ba zan iyan ba, ina son matata ki min addu’a kawai.” Daga haka ya fice. Ta dago murya “Sulaimanu ina magana ka sa takalma ka fice ko?” Ina! Bai ji ta ba tuni ya fice.
Ta kylu matuka, “Za ka dawo- ka same ni don ubanka.”
Samira dake gefe ta ce, “Kema dai Inna ki kyale shi, in ya sha wuya zai gane shi ya sani tunda an fada masa ya ki ji.”Ta ce, “Ba zan kyale shi ba, in bar shi ya kare a zuwa kotu ana sakaya shi tun kan abu ya yi nisa gwanda ya kyale musu mata ba dai tashi ba ce.
* *
Tun a mota ta ce ita a sauketa gidan Babanta za ta sauka. Kallonta Momy bata yi ba bare ta bata amsa.
Su uku ne a motar da Momyn ita ke tuki, sai ita da
Rafia shi kuma suna a motar Sharifa.
Ta dinga turo baki tana fushi har suka iso, ta fito tana
Bata rai duk suka shige amman ita taqi shiga, taja tayi tsaye tana kumbure-kumbure.
Rafia ta ce, “Wai menene haka Mabaruka? Ke dai ba kya jin magana ko tun yaushe ake fama da ke kan abu daya son ranki kike bi ko?”
Hararar Rafi’ar tayi tare da kauda kai.
Ta ce, “Na gode, na sha fada miki ba zan goya miki baya a kan rashin kunya ba, tuni zan kama gabana.
Tunda ke ba kya ji ki zo mu wuce ciki.”
Kallonta bata yi ba bare ta wuce din, don haka ta janyo hannunta da Karfi, amman ta tirje duk iya kokarinta ta kasa janta.
Taji haushi matuka, don haka ta sake ta. Ta ce “Shi kenan kada ki shigo.” Daga haka tai shigewarta.
Koda ta shiga duk suna falo, Mommy ta dubeta ta ce,
“Ina Mabarukan?” Ta zauna tana cewa “Ta ki shigowa.
Shiru tayi ta rasa me zata ce. Mabaruka na son fin karfinta, shin wai ya zata yi da ita?
Daddyn Imran din ya shigo da hancin motarsa, ya fito. Suka yi ido biyu da ita ya karaso har inda take ya dubeta ya ce *Ya aka yi ne Mabaruka ki ke a nan?” Ta ce, “Ba komai nafi son nan din ne.”
Ya yi murmushi, shi yasan dalili. Don haka ya jawo hannunta yana cewa, “A’a yaushe za ki tsaya a nan kowa na ciki, zo muje.
Hmmm