WAYE ANGON CHAPTER 35 BY MARYAM JAFAR KADUNA

“Ba zan iya ba Rafia, ba zan iya rayuwa da shi ba, ko

• na awa daya ne.

Ta ce, “Za ki iya Mabaruka, an yi sau dubu kuma sun zauna lafiya, in kin gan su za ki sha mamakin soyayyar

da suke wa junansu.

Ta ce, “Kin san kuwa me ake kira da tsana da rashin so Rafi’a? har abada ba zan taba sonsa ba wallahi.”

Bakin Rafi’a ya kulle bata da abin cewa, kallonta dai take cike damamakinta.

Ta ce, “Insha’Allahu Sulaiman shine mijina, da shi zanyi rayuwata mai kyau da tsafta, farin ciki da walwala.

Ta ce tana kallonta “Ni kuma ina miki addu’a Allah yasa Imran shine mijinki saboda gujewa da na sani gaba a rayuwarki, kuma shine farin cikinki mai dorewa.”Kallonta take tamkar ta kife ta da mari, amman gain ba za ta iya ci mata fuska har haka ba yasa ta mike gabadaya ta diro daga gadon ba tare da ta ce komai ba.

Ta ce, “Ina za ki je?” Ta ce ba tare da ta juyo ba

“Wanka zan yi. “-Daga haka ta shige.

Rafiar ta taso tazo har bakin toilet din ta ce, “Idan an ce ke da Imran kun dace da juna sai ki ce a’a, alhalin

ra’ayinku daya. Yanzu haka shima yana can ya shiga wankan.Haka nan yaji yana son yin wankan, ke ma gashi nan kin shiga don kiyi kawai don haduwar junanku.

Jin wannan maganar yasa da sauri ta saki sabulun da ke hannunta, ranta ya baci ta yayumo tawul ta daura ta fito tá bita da kallo tana cewa.

“Lafiya, me ya faru ki ka fito?”

Ba ta kallonta ranta a bace ta ce, “Na fasa.” Ta fara maida kayanta. Rike baki Rafi’ a tayi tana kallonta cikin mamaki ga dariya na cinta.

Ta ce, “Kanki ya fara tabuwa ko tsanarsa har ta kai haka?” ba ta saurare ta ba ta koma ta zauna bakin gadon tayi shiru. Ita kuma Rafi’a ta ci gaba da magana.

“Lallai Mabaruka aiki na gabanki ja, mijinki ne fa!” Juyowa ta yi tana galla mata harara, ganin tana mata

dariya yasa ta dauke kanta cikin Kuluwa.

Ita kuma ta ci gaba da Kular da ita, “Wata rana tare zaku shiga wankan har yasa sabulu ya wanke ki tas!”

Wani tuKuki taji a ranta da daci, ta tofar da yawu tare da cewa “Tir! Allah ya sawwake. Tayi dariya ta ce, “Kema ki masa.”Ta juyo cikin

bacin rai ta ce, “Raff’atu don Allah ki min shiru kar ki harzuka ni fa in miki abin da har ki mutu ba za ki manta ba Maida hankali don Allah, don kawai nace haka? To bari kiji ma ba wanka ba, gado daya za ku dinga kwanciya bargo daya, sannan ki fara haifa masa ‘ya’ya. Cikin zafin rai ta mike idanunta suka sauya ja ta ce, Idan ki ka sake furta magana daya a kansa Allah ya isa.Tayi dariya ta ce, “Iye! Matar Imran din ba!”

Ba za, ta iya jure maganganunta ba, idanunta suka rufe ta fice daga dakin a fusace bata ko gani.

Tana bude kofa taci karo da wani abu, sai dai taji ta fada. Bude idon da zata yi ta ganta kwance jikin mijin nata, yasa hannu ya tallafeta kanta saman kirjinsa sun fadi kasa.

Ya sakar mata murmushi tare da cewa “How are you?”

Zuciyarta ta dinga harbawa, ranta ya baci matuka, idanunta suka Kara canja launi, kallonsa take kamar ta shake shi tasan da niyya ya yi haka dan iska kawai.

Ta dube shi da kyau ta ce, “Sakar ni Mallam ba na son iskanci.” Yace,’

“Nibanrike ki ba duba da kyau.”

Ta duba itan ce kwance jikinsa, yayin da hannunsa suke a sake, ta yunkura zata mike a fusace.

Sarkar wuyanta ta riko rigarsa, ta kara fusata ta fara kiciniyar warwarewa amman tá kasa, gata dai kwance a jikinsa. Shi kuma ganin bata bukata bai cire ba yasa ya kyaleta, musamman da yake jin farin ciki kasance warta a tare da shi.

Duk Kokarinta ta kasa, dole ta sauke girman kan don ta rabu da jikinsa da take jin kamar a saman wuta take kwance, fuska turbune ta ce “Ka kwance.”

Ya yi dariya yana kallonta, ta kauda kai tana dode hanci saboda warin turaransa da take ji.

Shima ya kasa warwarewa saboda shine a kwance, ya dubeta ya ce, “Na kasa, sai dai ke ki dawo yanda nake ni kuma in koma yanda ki ke sai na iya cirewa, amman a haka ba zan iya ba.”

Ta dalla masa harara ta ki y in yanda yake nufi.

Ya ce, “To shi kenan kar kiyi ni ban da matsala mu kwana a haka, idan su Momy suka zo sun gane me hakan kenufi.”

Fadin haka ne yasa da sauri ta birkice ta koma kasan shi, shi kuma yana samanta.

Ta runtse ido tana jin wani irin tsanarsa da takaicin kasancewarta a jikinsa.

Ya yi dariya a ransa yana jin daman bata juya din ba, don ya ci gaba da kasancewa. tare da ita, amman ba komai akwai ranar da hakan zai kasance.

Cikin fushi ta ce, “Malam kai nake jira fa.” Ya yi dariya yana kokarin cirewa.

Yana cirewa ta tashi da sauri bayan ta ture shi, tayi gaba tana tofar da yawu. Ya ce, “Amman ai kin tsaya ki min godiya in ba ki ba ni hakuri ba.

Ta jishi sarai amman bata da niyyar dawowa.

Duk a idon Rafila komai ya faru, tayi dariya tare da

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE