WAYE ANGON CHAPTER 36 BY MARYAM JAFAR KADUNA

komawa daki.

Koda ta fita a harabar gidan ta hadu da Daddy, ta

•wuce gunsa tana turo baki.

Ya dubeta ya ce, “Me kuma ya faru?”

Ta ce, “Ina son naje gun Babana, amman Momy ta, hana ni.”

Ya ce, “Shine kadai matsalarki?” Ta daga kai.

Ya ce, “Ok, zan fita nima. Zagaya ki shiga mota in aje ki sai na wuce, hakan ya yi miki ko?” Ya Karashe yana dariya.

Ta daga kai kurum tare da wucewa ta lalubo lambar

Raff’a bayan ta shiga ta ce, “Ki zo muje ga Daddy nan zai kai ni.” Ta ce,

“Ba zan je ba, ki tafiyarki gida zan wuce.

yanzunnan.” Ta ce, «To.” Tare da kashe wayar.

A daidai kofar gidan ya tsaya da motar, inda Baban Mabarukar. yake tsaye shi da mutanensa. Ta fito daga motar, shi ma Daddyn ya fito ya zagayo.

Ganin Babanta ne yasa ya karasa gunsa cikin fara’a ya mimmika wa mutanen hannu suka yi musabaha. Ya mikawa Babanta amman kememe ya rike hannu yaqi mika masa, kallonsa ma ba ya yi.

•Ganin hakan ne yasa ya yi murmushi ya ce, “To barka da yamma.” “Lafly..” Kawai ya ce har zuwa lokacin ba ya kallonsa.

Ba yau ya saba ganin hakan ba, don haka bai damu ba. Ya yi bankwana da sauran mutanen ya wuce, ya dubi Mabarukar da ke gefe ya ce, “In ba ki wani abu ko ki dan rike?”

Ta yatsina fuska tare da cewa, “A’a bana bukatar komai Daddy, na gode.” Ya kalleta da kyau ya ce, “A’a na san ki Mabaruka kina da kashe kudi.”

Akwai dalilin Kin karbar, amman duk da haka ya ciro kudi daga aljihu dumus ya mika mata yana fara’a.

Ta ce, “*Wallahi ba ni da bukatarsu Daddy.” Ya ce,

“Eh na sani rike dai.” Ta karba tare da godiya kamar. dole.Ya ce, “Shi kenan in tafi ko?”

Tayi murmushi

iyakarsa fuska, ta ce “Eh.” Ya shige motarsa yana cewa,

“Sai yaushe za ki dawo kenan?”

. Ta sosa kai tare da cewa, “Sai dai na dawo din.”

‘ Ya ce, “Ok.” Ya tada motar ya wuce, duk tana tsaye

har ya bace sannan ta nufo gida.

Baban ya kirata ta karasa.

•. Ya hararetà ya ce, “Wannan wane irin iskancin banza ne?” Ta dube shi ta ce, “Me nayi Baba?” Ya ce, “Ban sani

ba. Salon tarbiyya ce haka zai dinga ba ki kudi har haka?

Me za ki yi da su?”

Ta turo baki “Ni ma fa sai da na ce bana so amman ya bani.

.”Ya katseta “Na kwade ki, fitsararra! Me yasa ki ka karba, ko dole ne?” Ta matsa baya tana turbuna fuska.

Ya kauda kai kurum tare da jan tsaki.

Ta wuce cikin gida fuuu!

Koda ta shiga Inna na zaune tsakar gida tana kasawa

yara alalan talla, taga shigowarta sallama kawai tayi ta shige dakinta.

Ta fada kan katifa tare da cillar da kudin. Kuka ya

taho mata ta dode baki kar aji ta, ta sani sarai iskancin da take a can gidan nan ba ta yin shi, tasan Babanta ba a masa wasa, ba bakonta ba ne sai ya shigo da bulala ya mata dukan da zata yi mai dalili.

Inna ta shigo ta bita da kallo ta ce, “Ke Mabaruka me ya faru kin shigo haka a firgice?”

Ta goge hawayen sannan ta dago ta ce, “Ba komai, kaina ke ciwo kurum.

” Ta ce, “Kai kuma?” Ta daga kai

kurum.

Tace, “To kin sha magani?” Ta ce, “Eh. ” Kawai.

Idonta ya sauka kan kudin da ta watsar, ta matso tana cewa “Mabaruka wadancan kudin fa?” Ta dago ta kalleta cikin fushi ta kuma kalli kudin ta kauda ido.

Ta ce a can kasa-kasa “Daddy ya ba ni.” Ta washe baki “Hala ba ki so ki ka wurgar?” Tai mata banza.

Ta zauna tana cewa, “Kinga ko manjan alale bai isa ba daman ina jiran Babanku yazo ya biya ni Naira talatin dita ta shekaran jiyada ya ci min alala sai a karo min, kin ga sai ki biya mishi kawai, nima a dan gutsura min.” Ta Karashe tana dariya.

Ganin zata isheta da surutunta na maula yasa ta ce

“Dauki ki sai manjan don Allah kaina na min ciwo.” Ta bude hakora “Nawa zan dauka?”

‘Yan dubu-dubu ne, ta ce “Dauki uku.”

Ta wangale baki tana dariya ta ce, “Ho Mabaruka

‘yar Baba, akwai kyauta in kinga dama.

» Ta zari kudin

tana cewa “Allah miki albarka ‘yar Mabaru.”

Ta bita da kallo ganin yanda take rawar jiki har ta fice. Taja tsaki sam ba su ne gabanta ba, masifar da ke saman kanta tafi kudin nan ita ke ta kudi.

Da dare Baban ya shigo har zuwa lokacin tana daki a Kule, musamman kasancewar tana hutun sallah, hakan yasa tunda ta shiga bata fito ba,

Yana kwasar tuwo ya dubi Inna dake gefe tana kirgar kudi, ya ce “Dan aro min hamsin nan kafin gobe.”

Ta dago tana kallonsa bayan ta tsaya da kirgar ta ce,

*Kafin gobe ka ji cika baki, sai ka ce su ke gare ka. Irin

“ba canjinnan ko?” Bai saurareta ba ya ci gaba da silbar tuwonsa.”

Ta ce, “Nawa na ara maka? In za a kirga sun kai saba’in, bana damunka ne don naga

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE