WAYE ANGON CHAPTER 37 BY MARYAM JAFAR KADUNA

barka, amman shi ne har ka ke da kwarin gwiwar tambayata wasu. To naki nabayar.”

‘. Ya ce, “Goro fa kawai zan siya ba wani abun zan yi da su ba• Ta taso “Eh goron mana, in kawai ne ka siyo da kudinka yanzu gobe karin safe duk kaina zai kare, in an samu ka kokarta ka bada wazobiya na koko, ni sai na Kukuta na samu na sikari.”

Mabaruka da ke daki taja tsaki tare da tashi zaune. In dai tana gidannan bata hutawa da sauraron abubuwan takaici daga Inna da Baba..

Kullum cin bashi yake, yayin da ita kuma cikin goranta masa take. Sam babu abin burgewa a zamansu.

Kan Naira ishirin sai. su dinga tashin hankali, duk makota sai an jiyo su, shi yasa ta gwammace gwanda tayi zamanta gidan Momy hankalinta kwance.

Jin za su kaure da bala’insu yasa ta mike a kasalance ta jawojiki bayan ta daura gyalanta a kai ta fito taja ta tsaya. Sai sannan ya tuna da ita.

Ya bita da kallo yana cewa “Me kike a daki tun dazu har na manta da ke?” Ta zauna kan daya daga cikin jarkar ruwan da ke ajiye tana cewa “Bacci nake.” Ya ce, “Bacci?” Ta daga kai:

Ya ce, “Da kyau Sarauniya! Kinyi bacci mana hankalinki a kwance.”

Ba ta ce komai ba illa fushi da

take, daga haka ta mike ta shige bandaki don kama

ruwa.

Daidai fitowarta daidai fitarsa, ta tsinkayi Inna na balai.

“Allah ya isa wallahi, shine ka fakaici idona ka dauki ishirin, to wallahi a kudin kokonka.”

Ba ta iya cewa komai ba ‘don wani abun in ya kai intaha yafi karfin magana. Tayi alwala kamar yanda ta saba in zata kwanta.

Ta dubeta ta ce, “Tuwo fa, ba za ki ci ba za ki kwanta haka?” Can kasan makoshi ta ce “Na koshi.” Tare da shigewarta daki.

Inna ta ce, “Um! Nima ba na gajiya, nasan ba cin tuwonmu ki ke ba amman nake tambayarki.” Akilu yaro dan shekara takwas ya shige dakin hade da tabarmar kwanciyarsa shi da Halliru duk kannata ne:

Suka kama kiciniyar kwanciya, ta bisu da kallo tana jin wnai takaici. A kullum idan zata kwana a gidannan sai ta zama bakuwa, kamar ba ta taba kwanansa ba, saboda matsaloli da take cin karo da su.

Duk gidan daki biyu ne, matsattsu, daya na Inna daya nata to a natanne ake cakudata da kannanta duk maza ne su shida ne hudu na kwana tare d aita daya yayayye yana gun Inna sai mai shan nono.

Don haka a nan suke kwanciya. Idan dare ya yi dare suka tsula fitsari su hade da junansu daki ya dauki zarni hade da tusarsu, kafin dare sun yi sau ba adadi kuma irin mai kumbura ciki da gagara maida numfashi.

Ta bude window don shan iska, amman ba wani sauki. A haka dai take wannan wahalallen baccin, ta kagara gari ya waye. A cikin daren sai taji kamar tayi. tsuntsuwa ta tafi gidan Momy tayi kwanciyarta a rantsattsen gadonta, inda daddadan iska da kamshi ke fesowa, bacci mai dadi da sa kwanciyar hankali. Hakan yasa ba ta jera kwana uku a gidan Baban tana kwana, in tayi Kokari kwana biyu ne shi ma a daddafe.

Don haka suka gama shimfidarsu suka kwanta, ta dafe kai tare da salati.

“Oh ni Mabaruka! Yau na shiga uku, da rana ban huta ba sai tashin hankali, yanzu ma ba zan huta ba, kafin dare cikina ya kumbura suntum.”

Ga Kabdagaggen tsoro na intaha da ke gareta, sam bata kwanciya daki ita kadai saboda toro, dole sai tana jin motsin mutum kusa da ita.

Ko gidan Momy takan kwana da masu aiki tunda take ma bata taba kwana ita kadai ba, a kullum Momy na cewaidan ki ka yi aure Mabaruka ban san ya za kiyiba.

Idan ta ce haka hankalinta na tashi ta shiga zullumi to da zata iya da waje zata dinga fitowa tana kwanciyarta saboda gidan ko ana sanyi shi zafi yake saboda yanda

-yake a kuntace ga girki da ake a tsakar gida gaf da dakunan, don haka wajen ba zai yi sanyi ba sosai.

Ta koma ta kwanta lamo tana zullumin yanda daran

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE