WAYE ANGON CHAPTER 38 BY MARYAM JAFAR KADUNA
.. nata zai kasance.
Sulaiman ya kirata ta dauka a gajiye.
Yace, “Kina ina?” Ta ce, “Ina nan gidan Baba.” Ya ce, “To bari in zo.” Ta ce, “Ayya ba za ka samu ganina ba, agajiye nake har na kwanta kayi hakuri.”
Bai so haka ba amman ba yanda ya iya dole ya hakura-suka dan taba hira sannan suka kashe waya, ta koma ta kwanta luum!
Imran ya shiga waige-waigen ina ta shiga har sai da ya tambaya, Rafi’a ce lokacin da take kokarin tafiya tace
“Tana gidan Baba tun dazu baka sani ba?”
Jikinsa ya mutu murus ba kuzari, jin haka ya ce.
A”‘a.” a gajarce, daga haka ya juya ya shige dakinsa, ya fada gado yana tunano tauraruwarsa.
Bai so tafiyarta ba, ina ma zai Kara kasancewa da ita kamar jiya, ko ma dai wayarsa ne da zata dauka da ya ji dadi, ya sani in zai kirata sau dubu ba za ta dauka ba, zai wahala ne kawai gwara ya hakura akwai lokacin da zai kasance da ita har abada.an Amman duk da haka zai jaraba, don haka ya janyo waya ya fara jera mata kira yafi a kirga.
Bacci har ya fara daukarta ta dinga jiyo kiransa ta jawo ta duba wani dogon tsaki taja tare da hararar wayar tamkar yana gurin, ta tillar da wayar tare da canja kafada tayi kwanciyarta tana turo baki.
Shi kuma bai fasa ba da ya tsaya sai ya ji bari ya kara kira me yiwuwa yanzu ta dauka, don haka ya dage ba ji ba gani, ganin ba za ta dauka ba yasa ya fara jera mata ruwan tasa-tasai.
Karar shigowar sakonni a wayar ya isheta, ta jawo wayar gabadaya ta tillar tana cewa, “Fitinannen banza mai shegen naci marar zuciya mugu! Ta koma ta kwanta tana kara jin tsanarsa na karuwa.
Da ya kira ya kira ya ji ta a kashe jikinsa yayi sanyi, tausayin kansa ya kama shi ya aje waya a salube ya yi jugum, shi kadai yasan yanda yake jin radadin sonta har zafi yake ji a ransa, wai da me ya gaza burgeta har yau bata sonsa, meye aibunsa wai?
Da ire-iren wadannan maganganun bacci na tunanin Mabarukarsa matarsa ya dauke shi me cike da mafarkinta.
Darennan ta farka yafi a kirga saboda yanda dakin ya suntume da wari ga zarni zafi kuma ya dameta, ga sauro in ta rufe zafi ta kasa maida numfashi.
Haka in ta bude sauro ya yanyameta, ko ya ta motsa sai taja tsaki daga tsakar gida ta jiyo ana kashe sauro da hannu tare da jin tarin Baban.
Ta mike ta fito, ganinsa tayi kwance kan ‘yar tabarmarsa da ‘yar fitila a noke. Sanyi ya ziyarce ta ganin wani a tsakar gidan, gwanda ta fito nan ta kwanta ya fiye mata kwanciya a akurkin dakinnan.
Don haka ta shiga ta -yayumo tabarma tazo tana
Kokarin shimfidawa, jin motsi ne yasa ya jawo touchlight ya hasko tare da cewa “Waye a nan?” Ta ce
“Nice Baba.”
“Me ki ke yi a nan kuma?” Ta ce, “Zafi dakin, ga su Halliru sunyi fitsari sai zarni suna ta burkice dakin da tusa, shi yasa na fito nan na kwanta.”
Ya mike zaune “A ina za ki kwanta nan ‘yar gulma? Kin ga na fito shi ne kema ki ka fito?”
Ta ce, “A’a Baba.” Ya ce, “Karya ki ke, to ba za mu jera ba a nan, ni nasa tawa tabarmar kema ki sa ta ki.” Ta ci gaba da kallonsa. cikin mamaki, ta ce “Kamar ya ya
Baba?”
• Ya harzuko “Kamar ubanki, za ki koma ciki ko sai na taso miki cikin tsohon daren nan?”
Ta turo baki ta ce “Dan kwanciyan da zan yi kawai.”
Mikewa ya yi zai yo kanta da gudu ta yayimi tabarmar ta shige daki taci karo da kofar langa-langar, kusa ta farketa a hannu tare da ja mata riga ta yage.
Ta fadi zaune jagwaf kuka na son fitowa.
A daren ya dinga sirfa mata zagi yana cigar fada.
Haushi ya tokare ta dama dukanta yazo ya yi yafiye mata fadannan da yake mata cikin dare ko ta ina zaginta yake ita da Mamanta.
Taci gaba da turo baki tana guna-guni har ya gaji ya koma bayan ya rufo kofar ya datse ta gam.
Kwalla ta ciko mata a ido, me ma ya kawota nan da tayi zamanta gidan Momy tayi kwanciyarta a tamfatsetsen gadonta, iskar (AC) na kadota da kamshinsa.
•Ta dafe kai ta ce, “Wallahi ba ka sona, duk abin da ka ke tun ina yarinya ba ka sona.”
Ta ci gaba da matse kwalla da cizon yatsa, me ya kawota? Sam bata yi bacci ba, daren nan tayi zaune tana dode hanci tare da kashe sauro duk wanda ya cijeta, duk tabita soshe jikinta tana cewa tir me ake da talauci?
Sai da asuba sannan su Akilun suka tashi suka kwashe kayan fitsarinsu saboda zuwa Makarantar asuba.
Ta bude window tare da kofa ta dage labule ta dawo tsakiyar dakin kan siminti tasa filo nan da nan bacci ya kwasheta mai nauyi na ramuwa.
** **
A gidan su Sulaiman kuwa, koda gari ya yi shaa, Inna ta fito daga daki, dakin matar Sulaiman a datse da kofa ta nufi dakin tana cewa “Wato ba ka fito ba har yanzu?”
– Ta shiga dukan kofar tana kiran “Sulaiman!
Sulaiman!!” Ya fito yana mika tare da doguwar hamma,
Hmmm