WAYE ANGON CHAPTER 39 BY MARYAM JAFAR KADUNA

Ta bishi sama da kasa tana tabe baki ta ce “Meye haka ka ke wata doguwar mika, kana nufin baccin da ka kwasa tun jiya har yau bai isheka ba ko ko so ka ke ka nuna min kana da mata?”

-Ya kalleta yana babbata rai, ya ce “To jiyan karfe nawa na kwanta sha daya fa ta wuce.

Ta ce, “To fada min na hanaka bacci don ubanka!.

Rana tayi gadau ace ba ka tashi ba? Me ka ke tsinanawa a dakin?”

‘Ya ce, “To ya isa ai gani na fito me zan miki?” Ta harare shi tare da nuna masa hanya “Muje.” Ba yanda ya iya, yasan kwanan zancan. Ya shuri takalmi ya wuce zuwa dakin Innar, yana tangadin rashin isasshen bacci.

Ta daga labulen ta dubi Nafisa matarsa tana tabe baki.

“To dadi miji, jin dadin ya Kare a jira wani daren.”

Daga haka ta juya ta wuce.

Nafisar tayi murmushin takaici tare da cewa “Na barwa Allah, kema kina da lokacinki za ki yi ki bari.” Ta mike ta tura kafarta ta koma tayi kwanciyarta abinta.

Koda ya shiga yaja tabarmar da ya saba kwanciya duk sanda tayo masa irin wanna tashin, ya yi kwanciyarsa nan da nan yaci gaba da baccinsa.

Ita kuma ta koma ta zauna tana daura sugarin kokonta hankalinta kwance.

Ka idarta kenan tunda safe irin shidar nan zata taso shi daga dakin matarsa. Sai dai ya dawo nan ya kwanta a dakinta duk don kar ya kasance da matarsa.

Saboda wani tunaninta can marar ma’ana, haka zalika ba zai kwanta ba sai wajen sha biyu na dare sannan zata ce yaje ya kwanta.

SHIN WACECE MA INNA?

Lokacin da taci zamaninta da mijinta Baban su

Sulaiman din kafin ya rasu yana da mata ta same shi amman zuwanta duk ta fatattake su da shegen makircinta da neme-neme, tayi nasara kam ita ke da gida ta hana shi aure sam.

Duk in da yaje neman aure tsoron ba shi ake saboda halinta, ko ta nakasa mutum bayan ta raba shi da gidan, don haka take cin karanta ba babbaka, tayi budurinta son ranta har yazo ya bar mata duniyar gabadaya.su  Sulaiman kadai ta haifa, don haka suka ci gadon gidan da’ suke “Zaune” sai inna matar Baban Mabaruka, don haka ita ma tayo kwas na makirci da fidda matar da duk ya auro ta kuma hana shi wani auren.

Har sarakuwarta bata Bari ba, tasha cusa mata Bakin ciki ta rabata da danta ko keyarshiba ta gani. Hakan yasa take tsoron kar a mata abinda tayi ma

Wata, ta kwace mata Sulaiman din ta hana mata shi. Sam bata barinsa ya kebe da matarsa isasshen lokaci, data jisu shira Zata koro shi.hatta abinci bata barinsa yaci na matarsa matarsa tunaninta kar tasa masa magani yaci ta rabata da shi, döle a gunta zai ci ta hada masa ruwan wanka da kanta, daidai da kayansa a dakinta suke.

Ya taba aure ‘ya’yansa biyu da matar, ba arziki ta gudu sáboda takurar Inna da wahalarta, ta kuma hana ya karbi’ya’yan. Daga nan ya dawo yana rakice-rakicen aure, duk wacce ya aura da taji wuya zata gudu.Har kawo yanzu Nafisa tana da hakuri da maida lamari ga Allah, marainiya ce gidan da ta baro ba dadinsa taji ba, gidansu kenan don haka ta gwammace zamanta a nan din ta barwa Allah ya kawo mata agaji.

Haka nan ma sai ta ce su fito waje su kwanta ita ma tazo ta kwanta anan idonta a kansu.

To bare kuma su fita unguwa tare, ko irin ya kaita unguwa bata bari.

Kayan abinci a dakinta suke, ko kudin cefane ita yake ba haka nan ita zata debo yawan abincin da za a dafa wai bata yarda da almubazzaranci ba, Nafisa zata dafa tasa kujera ta kafa ta ta tsare har sai angama a kawo mata tukunyar gabadaya bata barinsa ya kasance da matarsa, har zuwa yanzu bai sake haihuwa ba.

Muje dai zuwa labarin zai Kara bayyana mana halin

Inna.Koda ya tashi Sharifa ce ke dawainiya dashi 6angaren abincin da zai ci.

Sam ba shi da kuzari haka nan ya tashi sukuku zuciyarsa fal take da mararin son ganin Mabaruka, ina ma zata yarda da yazo inda take don kawai ya samu nutsuwa.

Ya fito daga wanka yana tsane ruwan jikinsa, fuskarsa ba annuri, Sharifa dake gefe tana fito masa da kayan da zai sa ta ce cikin damuwa “Big Bro wai menene?”

Ya dubeta yana cewa, “Me ki ka gani ne?’ Ta ce a marairaice, duk yanayinta ya sauya ba annuri “Me ke damunka?”

Ya yi murmushin da zai kwantar mata da hankali ya matso inda take yana kallonta, ya ce “Ba komai kanwata, kawai nasan don safiya ne amman tunda na dan yi wanka zanji karfi” Ta ce, *Shi kenan Big bros.”

Ta hado masa tea hade da madara.

Ya yatsine fuska ya ce, “Ba zan sha madarar nan ba, kawo min lipton kawai.” Ta kalle shi cikin kulawa ta ce,

“Saboda me lafiya ka ke kuwa?”

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE