WAYE ANGON CHAPTER 40 BY MARYAM JAFAR KADUNA

Ya ce yana kallontà “Lafiya mana, na fada mikikada kidamu?”Ta juya tafi jiki asanyaye

Cikin baccinta me dadita dinga juyo hayaniya tsakar gida tsakanin Inna da Baba, ta saurara da kyau. svInna tana cewas *Ai damanina fada maka wallahi a Kudin kokonka, don haka yau ba ka da kofin koko na talatin Za a siyo ishirin kuma kudina jiya da ka dauka? Ya ce, “Na fada miki rance nayi zan dawo miki dasu?  Tace, «Wallahi saikaita yi.

Ta tashi zaune tana jan tsaki, wannan fitinar tasu: ta isheta duko fadansu a kan kudine in dai ka ji harshensu to kudi ne ya hadasu

Ganin abin nasu yaqi karewa kan Naira ishirin yasa ta mike ta ciro dubu daya daga kudinta ta daura dankwali ta fice cikin fushis

A tsakar gida Suke ta dubi Baban ta ce, Ga shi ka biyata kudinta don Allah.? Yabi kudin da kallo, miyansa ya guda matura, yasa

hannu ya karba yana washe baki, ya dubi Innar ya ce

“Kin ga ni ko na wuce wulakanci tunda na haifa. Ai fa ta taso da bala’i “Yau kasan ka haifa a da me ka ke cewa? Me ‘ya mace zata maka? An ga kudi yau har an manta ko ita wacece.”

Jin fadan kuma zai koma ta nan yasa tai saurin dauko wata dubun ta mikawa Inna tana’ cewa, (Ga shi kin sayi kokon na kwana biyu, kiyi hakuri.”

Ba kunya kuma tasa hannu ta karba baki bude.

Dukkansu sai suka yi mukwi ba bakin wanda ka sake ji kudi sun rufe musu bakin.

A nan ya fice ya bar su yayin da ita kuma Innar ta ci gaba da aikinta. Taja kafa ta shige daki cike da takaicin wannan dabi’a tasu.

Sai da rana tayi sanna ta tafi gidan su Rafi’atu, a can tayi zamanta ta kashe wayoyinta.

Kwana daya ya rage a koma kotu, don haka a nan ta kwana daga nan suka wuce kotun ita da Maman Rafiar sai Rafiatun.

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE