WAYE ANGON CHAPTER 41 BY MARYAM JAFAR KADUNA
Bayan an gama sauraron Karar wasu an kammala, sannan aka gabatar da tasu.
Alkali ya bukaci ganin amaryar wacce kanta ake wannan hargitsin, ina ma amaryar take?
Jikinta ya hau rawa zuciyarta ta karye, a marairaice ta dubi Rafil’atu dake gefenta ta ce,
“Inajin tsoro Rafila ba zan
iya fita ba in tsaya gaban dubban mutanennan duk a tsira min ido wallahi ina jin kunya Rafia.
Ta riko hannunta ta ce “Ki nutsu Mabaruka, ki cire komai a ranki ki dauka ba kowa a nan ke kadai ce. Ki fita ki bayyana gaskiya da abin da ke ranki, kar ki boyewa kotu komai don za tai miki adalci ta ba ki mijinki da ya fi dacewa da ke, kilan ma kiga Sulaiman za a ba.
Amman idan ki ka yi sanya ki ka tsaya kunya ko tsoro za ki rasa shi, ki rayuwa da makiyinki. Fadin hakanne yasa ta samu kwarin gwiwa, zuciyarta tayi kwari.
Don haka bata jin komai ta mike ta tunkari inda ake tsayawa, Alkali ya dubeta ya ce, “Ko za ki gaya mana sunanki da ko wacece?”
Ta ce, “Eh! Sunana Mabaruka, kuma nice amaryar da ake rigima a kanta.
Na taso Karkashin kulawar iyayena guda biyu, Mamana da Babana, a gun matar Babana na taso amman na kan je gun Mamana.
Nayi karatun Firamare da Sakandire masu kyau da tsada, duk daukar nauyin mijin Mamana, wato Baban su Imran har zuwa yanzu da nake karatuna a Jami’a, ina kuma shekarar karshe a karatuna.
Na taso cikin gata da jin dadi, komai na rayuwa ina samunshi ba na rasa komai.
Na kan je gidan Mamana nayi kwana biyu ko uku, haka gidan Babana har zuwa yau da nake kusa da gamawa
Babana bai taba ba ni ko Naira goma ba in sayi fensir,
Duk wani abu na dawainiyar karatuna na ya yi, duk idan na bukaci wani abu gun sa sai ya kama fada, in bar shi ya ji da dawainiyar gabansa na kannena, dangane da ciyarwarsu me zanyi da karatu ni da nake mace aure zan yi.
Haka dinki ko silifas, ko da da sallah ne yanda uba yake dagewa kan kayan sallar ‘ya’yansa, to ban da Babana komai sai Mamana ita ke min ko mijinta Baban Imran, hakan yasa nafizama a gidansu Imran din.
Ya yi karatunsa a Ingila na Pilot tun kafin ya tafi muka shaku da juna, Imran ya koya min cin dadi da ‘yan tande-tande duk in da yasan idan ya kai ni zan ji dadi, to zai yi kokarin kai ni, ga sayen abubuwa na yayi ko naci ko na ado.
• Lokacin da zai tafi karatunsa nasha ciwo bayan tafiyarsa ban saba da rashinsa ba, zan wuni ba kuzari in wuni a kasalance, ba zan ci komai ba duk sanda na dauko abinci zan ci na kan tuno shi, hakan yasa sai in ta kuka saboda dashi muke cin abinci plate dinmu daya cokalinmu daya.
Na koyi abubuwa sosai gun sa dangane da karatuna, boko da Islamiyya, shakuwa sosai mu kayi dashi.
Gefe ita ma Sharifa ‘yar uwa ce kawa ce aminiya ce gare ni, duk idan tazo muna tare ina jin dadi idan Sharifa tazo sai in rasa inda zansa raina don dadi su sani tsakiya kowa ya na bani tashi kulawar,
Shi kuma Sulaiman tashin farko yakan zo gidanmu
kusan kullum yana yawan tsokanata da dan min tsaraba, da dama yakan kira ni da matas!
Daga haka abin ya faru, ban san ya aka yi ba na fara sonshi ba har muka yi nisa.
Gefe kuma muna tare da Imran amman har lokacin ban
san me yake nufi da ni ba.
Koda Babanmu ya ji magana ta da Sulaiman ya yi farin
ciki da murna yaiwa Sulaiman din albishir da ya bada ni gare shi ko bayan ransa.
Inna ma tayi murna matuka da hakan ko don ta sanni nakan yawaita mata alkhairi in dai ina gidan, musamman idan
tana wa Babana tijara kan kudi nakan biyata fiye da yanda
yaci hakan yana mata dadi sosai, shi yasa muke shiri da ita.
Ni kuma abin da take ma Babana bana jin dadinsa
hakan yasa na ke maganinta da kudi.
Wata rana Imran ya dawo ofis, kamar yanda na saba da zaran ya dawo zan taro shi in raka shi har daki tamkar wani mijina in ya cire riga in rike masa muna yi muna hira muna dariya.
Ranar ma haka ta kasance ya dube ni cikin fara’a ya ce, “Lallai kina ji da ni, sai ka ce wani mijinki irin na dawo dinnan ko?” Ya fada yana kallona yana dariya.
Ban fahimce shi ba nima nayi dariyar nace manta da wannan maganar yau ne zamu je wajennan da ka ce ko?” Ya zasro ido ya ce “Ina?” Na turo baki cikin shagwaba na ce, “Kana sane fa tun yaushe muka yi maganar nan don Allah?”
Ganin kamar zan yi kuka yasa ya ce, “Is ok, naji na sani tsokanarki nake, zamu je anjima.”
Nayi dariya tare da cewa, “Thanks my dear bro.”
Ya yi murmushi kawai yana kallona cike da sha’awar yanayi na gefe kuma yana wani tunanin.
Na katse shi “Ka san me?” Ya bazo kunnuwa ya ce, “A’a menene?” Nayi dariya na ce “Ba ka tambaye ni me na girka maka ba?”
Ya ce, “Sorry, na tambaya yanzu me ki ka girkawa tumbin yayan naki?” Nayi dariya tare da make kafada na ce
*Um’um idonka zai baka labari, amman nasan za ka yi farin ciki.”
Ya ce, “Na sani duk abin da za ki, za ki yi don farin cikina, zai sa ni farin ciki am sure.”
Hmmm