WAYE ANGON CHAPTER 5 BY MARYAM JAFAR KADUNA
WAYE ANGON CHAPTER 5 BY MARYAM JAFAR KADUNA
tsakar gida aka dora shi, don haka gidan ya dauki zafi
rau babu in da iska ke shigowa, ga hayaniyar Jama’a ga
zafin wutar girki, don haka koda Imran din ya zo bata yi
musu ba suka sudade suka tafi ko don su sami saukin
cunkuson nan.
Suna tafe tana gaba gefensa duk ta hade rai babu
alamar fara’a a fuskarta, tana yin komai ne don an fi
karfinta, yayin da shi kuma jefi-jefi yake kallonta
zuciyarsa tana masa dadì saboda kusan mallakarta da yayi nan da kwana biyu.
Shi kadai ya san yanda yake jin ta a ransa, sai Allah.
Zuciyarsa har zafi take. Babban burinsa da farin cikinsa
ya samu Mabaruka a matsayin matarsa da a komai ya
gama nema ba shi da sauran damuwa a ransa.
Ya fi kowa dace a rayuwarsa saboda samunta, bai san www.newspawa.com
ya zai misalta irin son da yake mata ba, komai nata burge
shi yake, ko me tayi duk da ba son shi take ba.
Idan yana tare da ita ya kan manta damuwarsa, ya
kan ji shi’ cikin sabuwar duniya me dadì. Idan ko ya same ta akwai alkawurra da ya yi wa kansa tsakaninsa
da Allah, gefe kuma da sadakin da zai bayar.
‘Ita kanta akwai alkawarin da ya mata a bayan
aurensu, ko lefen da ya hado mata abin kallo ne, akwati
set shida kowane dankare da kaya kamar a mafarki.
Ga gwala-gwalai da manyan less-less da atamfofi
(supers), takalmi, jakunkuna, kayan make up (shafe-
shafe) har wanda ba a taba ganin irinsu ba sai a kayanta.
-In da aka zubo su a dalleliyar motarta sabuwa dal duk
cikin lefen take. Mota ce mai matukar tada da kyau
sabuwar shigowa, wannan lefen ya dauki hankulan
mutane haka aka dinga daukarshi a wayoyi ana yada shi
cikin gari.
Sannan Kerarran gidan da za a kaita ba zai kwatantu
ba, girmansa da tsaruwarsa ya wuce misali, ita kadai sai
tarin ma’aikata ma su kula da ita.
Kowa a kagarce yake zuwa wannan ranar. A takaice
Allah ya jarabce shi da sonta kamar me a rayuwarsa.
Yana yi yana dan tsokanarta da hira amman tamkar ba ta motar, a kagarce take so take su isa ko ta sauka
daga motarsa.
Ya yi dariya ya ce wa Rafia,
“Ban san me ya sami
Kawar taki ba take fushi da angon nata.
Daga bayan motar ta ce, ‘
“Kun fi kusa ai Imran. www.newspawa.com
Tambayeta za ta fada maka, tsakaninku ne.
Yayi
murmushi daidai karya kwanarsa in da suka shiga layin
gidan.Ya ce, “Allah ya tabbatar mani da wanna kusancin
tsakaninmu.
.” Ba ta iya ce masa amin ba.
Yayin da Mabarukan da ta juyo ta mai wata muguwar
harara, ji take kamar ta shake shi ya mutu gabadaya shi
kenan wutar ta mutu ta samu kwanciyar hankali su ma
Iyayenta su htu.
Tayi kwafa kawai ta kauda kanta tana kallon
window. A sanyaye ya ce, yana kallonta “Kiyi hakuri.”
. Ba ta ce komai ba, tun kan ya gama parking ta fito har
sai da ta kusan faduwa, amman bata damu ba tana
tadewa da mayafinta ta wuce da gudu-gudu, sauri-sauri. -Ya bita da kallo yana jin wani irin sonta na fizgarshi.
Rafi’atu ta fito ta dube shi ta ce,
“Kayi hakuri Imran,
za ta bari idan har kai ne mijinta.
” Daga haka ta wuce ya
bita da kallo sam maganarta ba tayi masa dadi ba, bai iya
fitowa ba yaja motar ya wuce.
À kullum idan tazo gidannan yana burgeta, a iya
tasowarta ba ta taba taka gida mai tsananin kyau da
tsaruwa ba irin gidan nan da Maman Mabaruka ke
rayuwa cikinsa ba.
Duk sanda take cikinsa mantawa take da kasar da
take Najeriya, tsarinsa irin na Kasashen waje ne, gida
tamkar tangaram ba ko kurjewa ko Kasa, ko’ina kal-kal
ma’aikata suna hidimta masa www.newspawa.com
Kamshi kamar kamfanin hada turaruka,
ga
sassanyar iska da take kadawa mai dadì da Kamshi daga
shuke-shuken gidan, gefe kuma ga nau’ikan abinci masu
dadi da lafiya da ake giggirkawa a cikin gidan da
abubuwan sha masu dadì, wanda duk sanda tazo taci su take tafiya da sabbatunsa.
Dole ne ma mazaunan gidan fatarsu ta canja tayi
kyau, musamman Mama, Maman Mabarukan bare
Mabarukan, gidan ba bakonta ba ne don haka tasan
hanyar da zata sadata da masu gidan.
Kasancewar jibi biki gidan shima ba laifi baki sun www.newspawa.com
fara zuwa amman kasancewar gidan masu kudi katon
gidan babu wani takura, falo-falo ne gasu nan da dakuna
ana ta hidima duk da su ba wai girki za su ba, sai dai ayi a kawo.
Duk dangin Maman sun zazzo wasu sai gobe wasu
ma sai jibin, Bangaren Imran ma nasa duk sun z0, abin
gwanin sha’awa da burgewa.
Lokacin da Mabarukan ta shigo bata saurari kowa ba
da suke tsokanarta da gudu ta wuce dakin Mamyn, da
zuwanta ta fada jikinta tana kuka.
Hankalinta ya tashi, ta rike ta tana cewa
“Lafiya www.newspawa.com
Mabaruka? Menene?” Ta dago fuskarta jike da hawaye;
idanunta sun rikide kana kallon yanda kanta ke ballawa
HMMM LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe www.newspawa.com