WAYE ANGON CHAPTER 7 BY MARYAM JAFAR KADUNA da sanyaya rai bare yana sonki. Duk kimanta da rashin sonsa da ki ke yi, za ki so shi a hankal: shi da kanshi zai koya miki sonshi. Amman Sulaiman din ga talauci ga muni, ko fuskarsa ki ka kalla ta dinga tayar miki da gaba. To bare kuma ba abin moruwa a tare da shi. Wallahi Mabaruka tir! da za6inki, kuruciya na dawainiya dake.” Mabaruka ta ce, “Bai kamata kina fadin haka ba Anti, a tunanina kin yarda da Allah Madaukakin Sarki, talauci ko arziki duk nasa ne, zai iya ba wanda yaga dama ba kuma don yafi sonsa ba, sai don ya ga imaninsa. Haka nan wanda yaba talaucin ba don ba ya sonsa bane, sai don yaga Imaninsa. Sannan shi so Allah ke sa wa bawa in har kana son mutum komin muninsa da talaucinsa ba ka gani, sabida shi ka ke so ba arzikinsa ba. Ba kuma kyawunsa ba, shi ka ke so don Allah, kuma za ka zuana da shi a kowane hali yake, kuma kayi farin ciki da walwala da jin dadì ba ka da damuwa don farin cikin yana tare da shi da jin dadida kwanciyar hankali. In Allah yaso kuna tare sai ya azurta shi kuma babu wanda zai kai ka jin dadinsa, saboda kayi hakuri da shi sanda ba shi da shi, kuma kai ne cikakken masoyinsa. Amma in ka bi son zuciyarka ka auri me kudì alhalin ba ka sonsa,, wallahi za ka yi rayuwarka a hakurce don ba haka ka so ba. Kunci, damuwa da rashin walwala za su sami gurbi a rayuwarka. Ga kudin da akwai amman za ka kasance ko da yaushe zuciyarka a cunkushe, kudin ma su gagara nunawa a jikinka, saboda ana cinsu da damuwa ba farin ciki ba. Shi kuma duk abin da zai yi ba zai taba burgeka ba, sai ma haushinsa da ka ke ji. Sai ka fara rama, ciwo a rasa me ke damunka, ga ka dai kana jin dadì amman a rasa me ke damunka. Daga nan in ka gaza hakuri zuciyarka ta rinjaye ka, shaidan ya yi tasiri a gare ka. Sai ka fara neman wancan masoyin naka koda a waya ne, in abun ya yi nisa sai ku fara mahada. To duk mai ya jawo haka? Saboda ka bi kudi, kuma wallahi sai Allah ya kama ka da wannan laifin. Don haka ni Sulaiman nake so, shine farin cikina da shi zan samu nutsuwa ba Imran ba, ku bar ni na aure shi; ku ku janye naku don Allah don farin cikina da nutsuwata. .”‘ Ta hada hannuwa tana rokonsu. Anti ta ce, “Wallahi kina bani mamaki Mabaruka, kudi ai su ne damuwa, in da akwai su damuwar yayewa take, wannan lokacin har wani duba haka ake kowa fatansa kenan ya samu mai kudin ya kurda ya shige shima ya lasa. Amman ke idonki ya rufe kan wani banza can mai fama da talauci, so ki ke kema ki bi layin wasu à zuri’armu duk in da suka shiga ana tausaya musu, sun kode da su da kayansu sai uban kasusuwa a wuya su da ‘ya’yansu ba suturar kirki, ko pampas ya gagare su sa wa ya yan. Sai a dinga kyamar daukar ‘ya’yan, su kansu ba a soncin abinci da su, duk fa sanadin talauci, kana ji kana gani a fidda kai a danginka, har a gidanku ma. Idan kuwa da kudi, ko ba a sonki anyi da ke, kin yi kyan gani; da namiji ma har za ka biye ma sonshi in ya tashi yo miki tsiya sai ya daga ki sama sannan ya yado ya yi gaba ya nemi wata. To gwanda tun wuri ki wa kanki fada, wallahi ki nutsu Imran dai ba shi da laifi, yanda ki ka shiga ransa hakaza ki wala abinki, ke kadai a gidansa kiyi isarki son ranki, ki juya ki iskancinki ke kadai ba wata daga ke sai “‘ya’yanku, kuma kyan nan ga shi nan masha’Allah.” Momy ta ce, “Ke rabu da ita Karima, ita ta sani. Ni dai na gama maganata da shirye-shiryena, magana tayi nisa me ya rage kwana biyu, sadakinki na hannun Kawunki, jibi daurin aure. Don haka babu abin da za a fasa, ga ki can a gidan Imran a hankali za- ki gane sai kin zo kina min godiya wallahi, kuma son da Sulaiman din yake miki na rantse bai kai na Imran ba, mata nawa ke rawar jikin ya aure su HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

WAYE ANGON CHAPTER 7 BY MARYAM JAFAR KADUNA

 

da sanyaya rai bare yana sonki.

Duk kimanta da rashin sonsa da ki ke yi, za ki so shi a

hankal: shi da kanshi zai koya miki sonshi. Amman

Sulaiman din ga talauci ga muni, ko fuskarsa ki ka kalla

ta dinga tayar miki da gaba.

To bare kuma ba abin moruwa a tare da shi. Wallahi Mabaruka tir! da za6inki, kuruciya na dawainiya dake.”

Mabaruka ta ce,

“Bai kamata kina fadin haka ba

Anti, a tunanina kin yarda da Allah Madaukakin Sarki,

talauci ko arziki duk nasa ne, zai iya ba wanda yaga dama ba kuma don yafi sonsa ba, sai don ya ga imaninsa.

Haka nan wanda yaba talaucin ba don ba ya sonsa bane, sai don yaga Imaninsa. Sannan shi so Allah ke sa wa

bawa in har kana son mutum komin muninsa da

talaucinsa ba ka gani, sabida shi ka ke so ba arzikinsa ba.

Ba kuma kyawunsa ba, shi ka ke so don Allah, kuma za ka zuana da shi a kowane hali yake, kuma kayi farin

ciki da walwala da jin dadì ba ka da damuwa don farin

cikin yana tare da shi da jin dadida kwanciyar hankali.

In Allah yaso kuna tare sai ya azurta shi kuma babu wanda zai kai ka jin dadinsa, saboda kayi hakuri da shi

sanda ba shi da shi, kuma kai ne cikakken masoyinsa.

Amma in ka bi son zuciyarka ka auri me kudì alhalin ba ka sonsa,, wallahi za ka yi rayuwarka a hakurce don

ba haka ka so ba. Kunci, damuwa da rashin walwala za

su sami gurbi a rayuwarka.

Ga kudin da akwai amman za ka kasance ko da

yaushe zuciyarka a cunkushe, kudin ma su gagara

nunawa a jikinka, saboda ana cinsu da damuwa ba farin ciki ba.

Shi kuma duk abin da zai yi ba zai taba burgeka ba,

sai ma haushinsa da ka ke ji. Sai ka fara rama, ciwo a rasa me ke damunka, ga ka dai kana jin dadì amman a

rasa me ke damunka.

Daga nan in ka gaza hakuri zuciyarka ta rinjaye ka,

shaidan ya yi tasiri a gare ka. Sai ka fara neman wancan

masoyin naka koda a waya ne, in abun ya yi nisa sai ku fara mahada.

To duk mai ya jawo haka? Saboda ka bi kudi, kuma

wallahi sai Allah ya kama ka da wannan laifin.

Don haka ni Sulaiman nake so, shine farin cikina da

shi zan samu nutsuwa ba Imran ba, ku bar ni na aure shi;

ku ku janye naku don Allah don farin cikina da

nutsuwata.

.”‘ Ta hada hannuwa tana rokonsu.

Anti ta ce,

“Wallahi kina bani mamaki Mabaruka,

kudi ai su ne damuwa, in da akwai su damuwar yayewa

take, wannan lokacin har wani duba haka ake kowa fatansa kenan ya samu mai kudin ya kurda ya shige shima ya lasa.

Amman ke idonki ya rufe kan wani banza can mai fama da talauci, so ki ke kema ki bi layin wasu à

zuri’armu duk in da suka shiga ana tausaya musu, sun kode da su da kayansu sai uban kasusuwa a wuya su da

‘ya’yansu ba suturar kirki, ko pampas ya gagare su sa wa ya yan.

Sai a dinga kyamar daukar ‘ya’yan, su kansu ba a soncin abinci da su, duk fa sanadin talauci, kana ji kana gani

a fidda kai a danginka, har a gidanku ma.

Idan kuwa da kudi, ko ba a sonki anyi da ke, kin yi kyan gani; da namiji ma har za ka biye ma sonshi in ya

tashi yo miki tsiya sai ya daga ki sama sannan ya yado ya

yi gaba ya nemi wata.

To gwanda tun wuri ki wa kanki fada, wallahi ki

nutsu Imran dai ba shi da laifi, yanda ki ka shiga ransa

hakaza ki wala abinki, ke kadai a gidansa kiyi isarki son

ranki, ki juya ki iskancinki ke kadai ba wata daga ke sai

“‘ya’yanku, kuma kyan nan ga shi nan masha’Allah.”

Momy ta ce, “Ke rabu da ita Karima, ita ta sani. Ni

dai na gama maganata da shirye-shiryena, magana tayi

nisa me ya rage kwana biyu, sadakinki na hannun Kawunki, jibi daurin aure.

Don haka babu abin da za a fasa, ga ki can a gidan

Imran a hankali za- ki gane sai kin zo kina min godiya

wallahi, kuma son da Sulaiman din yake miki na rantse

bai kai na Imran ba, mata nawa ke rawar jikin ya aure su

HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE