WAYE ANGON CHAPTER 8 BY MARYAM JAFAR KADUNA
WAYE ANGON CHAPTER 8 BY MARYAM JAFAR KADUNA
sai ke ya ce zai aura amman kin nace duk ba ki ga baiwar da Allah ya miki ba sai kin kai kanki mahallaka kan shegen so.
Anti ta ce,Yo ji fa motar da aka kawo mata, koke Yaya ba ki hawan irinta sai ita ta shiga ta kece raini cikin kawaye da dangi, gaba ma wata zai canja mata wacce
tafi wannan.Tace,
“Duk bana so ku tattara ku rike ku kece rainin,
ni bana so Sulaiman nake so, kuma tare da shi zan sami
duk wadannan ta ce sai kije ki tayi ba ki gaji ba, aure dai ba fashi na gama magana,
Anti ma ta ce,
“Aikuwa ga masu tsara dakuna can na
gyara miki, ina ga ma yanzun sun isa su gama, don yazu
nayi waya da su Samira ta ce sun kusa gamawa.
Momy ta ce,
“Kai ai ko sun yi sauri, Gwanda ma su
dawo din su zo suje min kasuwa ko store ne.
Ganin sun banzatar da ita yasa ta fice daga dakin
fuuu ta nufi dakinta, idonta ya rufe taf da hawaye tana
zuwa ta fada kan gado ruf da ciki tana kuka,
Tunda Rafi’ar ta
shigo ta jiyo maganarta dakin
Momynta sai ta wuto dakinta ta zauna tana jiranta.
Ta taso ta tsaya kusa da ita ta dagota ta ce,
“Me yasa
ki kuka?” Tana shesshekar kukan ta ce,
“Wai wane irin
iyaye ne Allah ya bani marassa fahimta sai tsabar son
• zuciyarsu da kafiya?”
Ta nisa ta ce,
“Ba haka ba ne Mabaruka, ki godewa
Allah wallahi wasu ba su sami wanna gatan da ki ka
samu ba, wasu kuma in kinga iyayen nasu zaki yi tir da
su sam ba su cancanci wannan sunan ba,
Ta katseta
“Ni ma kusan hakanne, waye ba zai yi tir
daSu ba?”Ta ce,
“Bana son
maganganun nan
Mabaruka, iyaye iyaye ne ba ki da kamarsu, ba za ki iya
canza su ba, ki sake wasu ke fa matsalarki a kan aure ce
kawai in ba akan wannan ba ba ki taba samun sabani da
su ba, don haka ki bar cewa haka.”
Tasa bayan hannu ta goge hawayen tare da shan
majina ta ce, “To ya zan yi ne? me zan yi da gaske fa kowannensu yake.
Ta zauna tare da dafa kafadarta ta ce,
“Mabaruka a
koda yaushe ina ce miki ki gayawa Allah matsalarki da
damuwarki shine kadai mai miki maganinta.
Wani kuka da tashe-tashen hankali ba za su taba baki
kwanciyar hankali ba, ko mafita. Kiyi addu’a idan Imran
alkhairi ne gare ki Allah ya tabbatar da shi ya cire miki
tsanar da kike masa, ya mayar miki da sonshi ki.
Ta katseta “Kar ki ce haka Rafi’a, ni nasan Imran ba
zai taba zama alkhairi gare ni ba, saboda ba na sonsa.
Kar ki min wannan addu’ar, idan har mai kaunata ce ke.
Kallonta take ta rasa me zata ce mata, wayar Rafiar ta fara. kuka, ta jawo ta tana dubawa ta kalleta ta ce,
“Imranne.
.”‘ tamkar bata gun bare ta amsa mata.
– Ta sake cewa,
“Ina wayarki, kin rufe ne ya kira bai
same ki ba?” Nan ma tanke bata tanka ba. Lura da ba za
ta yi magana ba yasa ta dauka kar wayar ta yanke.Ta ce,
“Kana son magana da Mabaruka ne?” Ya yi
murmushi daga can ya ce,
“A’a da ke nake son maganà,
don nasan ba za ta saurare ni ba. Ina kuma tarè da abokaina.
Ya bata tausayi matuka, amman ta ce
“Ina jin ka to.”
Ya ce,
“Maganar partyn nan ne, ban san ya abin zai
kasance ba. Na fada muku friends dina suka shirya,
yanzu ma haka muna tare da su a hotel din suna son
magana da daya daga cikinku.
Ta juyo tana kallon Mabarukar, yanda tayi kicin-
kicin da rai duk da ba jinsu take ba, amman don taji an ce
shi ya kira. Ta numfasa sannan ta ce “Shi kenan ba
matsala ka ba su muyi maganar.
Ya ce,Ok! Na gode Rafi’a.Tayi murmushi
“Bakomai.
Tsawon lokaci suna magana ta tsakanin abokanan
ango da babbar kawar amarya, sun tattauna komai
yadda zai kasance, daga bisani suka yi sallama a kan sai
goben.Ta juyo tana kallon Mabarukan, ta ce
“Kin ji yanda
muka yi da Imran, a kan partyn nan. Ni wallahi na manta
“da maganar nan, wa muka gayyata da zai zo? kar fa ayi
abin kunya amarya ba kawaye daga ni saike?”
Wani dogon tsaki taja tare da kwanciyarta taci gaba
da kallonta, ta ce “Da ke fa nake kin ja tsaki kin juya min
baya, nice Imran din da za ki ji haushina?”
Ta tashi zaune a kufule ta dubeta “Me yasa ki ka saurare su? Ni nace ki dauka bare kuyi magana? Partyn
banza ina ruwana, kije kuyi ni dai ba in da za ni wallahi.”
Ta dube ta cikin mamaki ta ce,
“Mabaruka kin san
me kike fada kuwa? Kina son ki ba shi kunya ki nunawa Jama’a ba kya sonsa?
Wai meye laifinsa? Me ya miki? Bawan Allah mai hakuri da saukin kai tunda ki ke kin taba ganin abokin fadansa koda a cacar baki ne?
Komai nashi cikin nutsuwa da hankali yake yi,
mutane suna ganin girmansa, me yasa ki ke son wulakanta shi? Me yasa
ki ke son tozarta
shi Mabaruka?”
Ta ce,Saboda ya shigo rayuwata shi ya fara takuramin yasa aka tursasa ni a kan abin da ba ni da ra’ayi,
Wallahi bana sonsa bana sonsa ko kadan ko muryarsa
naji sai raina ya baci, na rasa me ke min dadi.
Kunci ya baibaye ni, har zuciyata tashi take bare naganshi, ko gidannan ya shigo sai naji ni a kuntace, na
rasa walwalata. Na fada muku na fada na Kara fada don
me ba za ku fahimta ba?
Idan ku ka yi wasa da shi da ku sai na baku kunya, saiya yi kuka da idonsa wallahi.”
Zuwa yanzu Mabaruka ta daina bata mamaki, lallai ta yarda bata sonshi, don taga kiyayyarsa a cikin idonta
Kàrara, amman ta dubeta ta ce mata.
‘”A’a Mabaruka, kar ki tsananta Kiyayyarsa har haka,
wallahi ba ki fahimce shi ba, Imran ba shi da kuskure, ba
shi da aibu wallahi in ki ka aure shi za ki sami kulawa
fiye da kowanne gidan in kikaje.
Saboda yafi kowa sonki, duk cikin wadanda suka
nuna suna sonki ban ga me sonki ba kamar Imran. Ba
wai ina duba abin hannunsa ba, ko gidansu, wallahi sai
don kyakkyawan halinsa da kirkinsa.
HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe