WAYE ANGON CHAPTER 9 BY MARYAM JAFAR KADUNA

WAYE ANGON CHAPTER 9 BY MARYAM JAFAR KADUNA

 

 

Soyayyar da yake nuna miki tsakani da Allah ne, zaki fi walawa a gidansa kiyi abin da ki ke so, ba ki da

kokwanto a kanshi. Kuma zan fi farin ciki da nutsuwa

idan ki ka aure shi, nasan ba ki da sauran damuva ko

matsala a rayuwarki.”

Idanunta suka sauya, kwalla ta taru ta dubeta da kyau

ta ce,

‘”Kin kuwa san Kiyayya Rafi’a? kin san zafinta da dacinta?”

Ta ce,

; “Na sani, abu ce mai sauQi ba mai wahalarwa

ba, idan ki ka fahimceta zuciyarki tana fin karfinki ne, in

ki ka zama ke ke iko da ita wallahi za ki nemi Kiyayyarsa

ki rasa, ko kuma ta ragu kashi sittin cikin dari.

Ni ina Kiyayata a inda ta dace a inda naga illa ko aibu,

amman taki Kiyayyar in da kike yinta bata da illa, illa

kin sawa ranki hakanne, shi yasa kike Kara zafafa.

Amman ki dan rage ki gani sai Imran ya zamo shi ne

masoyinki ba Sulaiman da auransa ke da matsaloli cikinsa dankare ba.

Tasa hannu ta goge hawayen idonta ta ce,

“Ya isa

haka Rafi’atu, ba na son shawararki, na gode ku bar ni da

Sulaiman shi nake so, kar ki kuma min maganar Imran

don Allah.”

Ta jinjina kai alamar gamsuwa ta ce, “Shi kenan zan

miki maganarshi nan gaba idan shine mijinki. Na bari,

Allah ya baki hakuri ya za6a miki mafi alkhairi cikinsu

zuwa jibin.

Ba ta ce komai ba, ta sauko daga kan gadon ta shige

bandakin da ke cikin dakin.

Karfe takwas na dare, don haka ta shirya don

wucewa gida, lokacin da ta fito ta ganta tsaye tana yafa gyalanta, ta ce “Ina za ki?”

Ta ce,Gida, dare yana yi.”

Ta karaso tana cewa

“Gida kuma? Na sha a nan za ki kwana?!”

Ta ce,A’a,

Mama bà ta san hakan ba, sai gobe zan dawo.”Jikinta ya yi sanyi, ta marairaice ta ce,

“Kasancewata

tare da ke yasa nake jin sauki da walwala, idan ki ka tafi

wallahi zuciyata zata yi kunci Rafia, don Allah ki kwana Ta ce,

“Mabaruka Mama fa bata sani ba.” Ta ce “Zan

mata waya in sanar mata, nasan Mama ba za ta hana ba,

tasan muna tare.”

Ta ce, “A’a Mabaruka, na fada miki wallahi gobe zan

dawo a nan zan kwana, amman yau kin ga ban z0 da

shirin hakan ba.”

Tayi, jim! Ta zauna gefen gadon tsawon dakiku ta

kasa cewa komai, sai can ta numfasa ta ce, *Ok, kije

daman ke ce matsalata. Wallahi kina tafiya ni ma zan

kama gabana, sai dai a daura auran da wata.

” Ta hade

rai,

Da sauri ita ma ta zauna a tsorace ta ce, “Kada ki fara

Mabaruka, don son Annabi ki zauna gaban iyayenki, ki

musu biyayya a kan abin da suke so da ke, ya fi miki

alkairi a kan ki shiga duniya, sai ki ga Allah ya kawo

miki mafita a cikin al’amurranki, ya yaye miki

damuwarki, tafiyarki ba alkairi ba ce.

Tace,

“To in har ba ki son na tafi sai dai ki zauna tare

da ni har a daura auren.” Tayi jim! Sannan ta ce,Shi kenan na amince tayi murmushi ta ce,

“Na gode kawata,

ba zan iya biyanki ba.

Ba ta ce komai ba, sai ta canza zancen

“Anya ba

muyi kuskure ba da ba mu gayyaci kowa ba bikinnan?”

Ta ce, “Na fada miki bana farin ciki da aurannan bare

a zo a taya ni murna, kowa tayi zamanta gidansu

abokanan taya ni jaje nake nema.

Ta ce,

“Har yanzu kin kasa ganewa Mabaruka,

amman Allah kai mu muga ya abin zai kasance.”

Haka dai suka kasance.

Sun yi wa Mama waya ta ce,

“Ai daman tunda naga

kun yi dare na ce me yiwuwa a can za ku kwana.”

A ka shigo musu da nau’ikan abinci kala-kala,

Rafiatu ta zauna ta take tumbinta, hankalinta kwance

yayin da mutuniyar kallo ma bai isheta ba.

Ganin Rafi’ar ta matsa mata ne yasa ta fita ta hado tea

ta dawo tana shan shi bayan shi bata ci komai ba.

Sun dade suna hira daga baya Sulaiman ya kirata. Ta

dauka ba yabo ba fallasa, ya ce

“Me ya same ki naji

muryarki haka?” Ta ce a shagwabe,

“Kai ma kasan dole muryata ta

kasance a haka, ina cikin tashin hankali fa. Ban san

wane matsyain nake ba shin kai ne ANGON ko ko IMRANne?

Gobe kawai ya rage min amman har zuwa yanzu

babu wanda ya janye kudurinsa tsakanin Momyna da

Imran din. Ta karbi sadaki da duk kayan aurensa

jere anyo a gidansa, shi ma yana shirye-shiryensa gobe à

ke partyn da abokansa suka shirya.

Me yasa to hankalina ba zai tashi ba? Da gaske suke

sun yi shirinsu, ‘yan biki duk sun hallara wasu daga

garuruwa wasu kuma daga was kasashen, hankalina

yana Kara tashi idan naga shirin da suke.”

Ya yi jim! Sannan ya ce, “‘Aure tsakanina da ke shi ne

tabbas, amman nasa gaibu ne NI NE ANGON, duk abin

da suke zai tashi a banzà ne, ni ne kadai mai auranki, don

ba a aure biyu. Sadakinki na bayar yau sun zo sun yi jere,

don haka biki ba fashi.”

Hankalinta ya kasa kwanciya, abin da yake fada shi

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE