YAR ALMAJIRA CHAPTER B

 YAR ALMAJIRA CHAPTER B

Washe gari da safe ta kira wayar sa taji akashe, haka tayi ta kira har yamma amma baya zuwa duk dai zance da yace wai swtchoff, karshe dai bayan sallar magriba ta kira Hajja Ghaji akan tazo ta raka ta gurin saurayin yayarta ko zata samu information akan inda zata sameshi.

+

6angaren Dr Affan kuwa hankali kwance har yama manta da cewa wata ta kirashi jiya harta 6ata mishi rai don kuwa tunda ya tashi ya cire sim din data kira dashi yasa wani a cikin wayar yaji damuwarsa ta tafi.

  

Meanwhile a 6angaren su Hajja Hadiza har sun tari dan adaidaita don shigowa anguwarsu Sule,sun koyi dace domin suna sauka suka hango shi a bakin masallaci, ba tare da tunanin komi ba suka karasa inda yake cike da jindadin ganinsa, shi kuwa mamaki ne ya kamashi akan meya kawo su a wannan lokaci kusan ishai, ganin cewa gunsa suka nufo yasa ya tashi yaje ya same su.

“Hadiza lafiya na ganki a wannan lokacin kusan goshin ishai?” ya tambaya yana nazarinta

“Lafiya ba lafiya ba yaya, dama munzo ne akan ko zaka nuna mana gidan su abokinka!” ta fada kai tsaye.

“Abokina kuma, wanne toh a ciki, ince dai ba wani abun ne ya faru ba?” yana magana yana tunani kala kala.

Hajja Ghaji tayi saurin cewa”eh toh abokinka wanda ka bamu lambarsa jiya da kazo dama mun kira shi yau ne wayar akashe tun safe kuma muna da wani muhinmin business dashi shiyasa muke nemansa”.

“Au okay wai Dr Affan kuke nufi,inaga kila ya cire layin awayarsa amma barin baku sauran layikan sa guda biyu, amma samun shi a gida yanzu zaiyi wuya kila ma yana majalisa ta chan gangaren babban masallaci”. ya fada yana lalibo numbern.

yana gama fada musu sukayi mishi godiya suka kama hanyar majalisan da ya kwatanta musu, shikuma ya fada ne ba tare da tunanin ko zasu iya zuwa ba.

STORY CONTINUES BELOW

bayan sun wuce ya tsaya tunanin hali irin na yaran zamani toh koma wani irin abune ai sai su bari zuwa gobe tunda bagun mace yar uwarsu bane, gashi sai wani rawar kafa Hadiza keyi “Allah dai yasa ba wata akasa”. ya fada tare da komawa bakin masallacin

Su kuma anasu 6angaren har wajen majalisan su kaje, ai kuwa sunyi saa yana gurin,dialing dayan layin da aka basu sukayi ai kuwa ba jimawa ya shiga amma dai baa dauka ba saida su kayi kira sau kusan uku ana hudun ya dauka.

“Hello waye ne naga anata kirana lafiya koh?” ya tambaya cikin jin haushin su domin ya hango su kuma ya gane Hadizan saboda kasancewa inda suka tsaya akwai haske sai dai ba sosai ake ganin fuskarta su ba.

“Lafiya kalau, dan Allah ko zamu iya ganinka minti biyu,muna daga gefen inda kuke zaune”. ta fada cikin lumana

Sai da yadan jinkirta kadan kafin yace “okay gani nan zuwa”. Kashe wayar tayi murna fal ranta “kawata kinga wai yana zuwa fa”.

“Amma dai wallahi ya cika dan rainin wayo sai da ma tayi tunani kafin ya amsa da zaizo din mtsss”. ta fada cikin jin haushin sa.

Hadiza ce tayi charaf tace “A’a kar ma ki fara aibanta min shi ehe ni duk abunda zaiyi bazai dameni ba indai zai na kulani” Tana gama rufe bakin ta sai gashi ya iso yana wani ya mutsa fuska kamar yaga kashi ita dai Hajja Hadiza bata ji haushi ba amma Hajja Ghaji kam kamar ta rufe shi da duka aranta tace “dan rainin wayo wato ma irin ga matsiyata nan sunzo  neman sa mtss”.

Sannu Dr yanzu muka hadu da Sule abokin ka ya bamu numbrnka, nayi ta kiran dayan layin naka baya shiga dama shine mukazo muji ko lafiya dai koh”. tafada ba ko kunya

Shikam abun ma mamaki ya koma bashi lailai kuwa wannan yarinyar da alama dai bahuwa ce babba ma kuwa ya fada a cikin ransa kafin yace “eh lafiya kawai bana son yawan yin wayar ne shiyasa na kashe don kar adameni dayawa kinsan wasu matar ba hankali ne dasu ba sai suringa kai kansu inda ba’asan suna yiba ma”. yafada cikin gatse yana murmushin mugunta

Ba tare da takawo komai aranta ba tace “eh wallahi a wasu matan ba suda kunya gaskiya, toh tunda kana lafiya mu zamu koma gida amma zan kiraka anjima, wannan kawata ce Hajja Ghaji” tafada tana nuna masa Ghaji wacce mamakin maganar da ya ya6a musu kadai ya cika zuciyarta ga karin abun haushin ma wato ita hadizan bata fahimci hausar ba harda tayashi zagin..

Dr Affan na zaune yana gyara kayansa domin komawa Bama yaji wayar sa ta fara ringing, da kamar baze kula ba se kuma ya duba dan ganin waye, ganin cewa hajiya ce yasa yayi saurin dauka, seda suka gaisa sannan ya tambaye ta yaushe ta dawo yaga numbern kasar ne bata saudiyya ba, sannan ai sunyi akan cewa zata biyo ta Gaidam sannan su koma tare, murmushi tayi sannan tace ta fada mishi hakanne saboda tanaso ya dan kwana biyu achan dan tasan inda ba haka ba da ya dade da dawowa, dariya ma maganar ta bashi amma kawai ya share yace mata shima yagama shiryawa washe gari ze dawo, fatan alkairi tayi mishi sannan ta ajiye wayar..

Tunanin su Noor ne ya fado mata amma ganin cewa dare yayi shiyasa kawai ta bari akan washe gari zataje ta duba su dan tasan kila kayan abincinsu ya kare, addua tayi sannan ta kwanta..

Dr Affan kuwa farinciki ne ya cikashi tunda hajiya ta dawo ze samu komawa dan yaga Noor dinsa rabin ransa domin yasan kila suna cikin wani hali tunda tafiyar yazo mishi abazata kuma beyi tunanin kara musu kudi ba, yana gama hada kayansa ya kira Sule ya shaida mishi cewa tafiyarsa gobe ne sannan ya kwanta barci…

♣🌹♣☘♣🌻♣

*🌻вσяиσ ѕтαтє*

*♣вαмα ℓ/g*

Addua kawai ta keyi acikin zuciyar ta domin bata da wani ma fita da ya wuce ambaton Allah saboda yanda suka za gaye ta, kudin hannunta suka fara kar6a kafin su kayi yunkurin cire mata kaya, kuka takeyi tana rokonsu akan suyi hakuri kome suke nema zata basu amma karsu ta6a mutuncinta, murmushi ogan yayi sannan ya tambaye ta akan me take dashi da har zata basu, kudin cikin jikinta ta ciro gaba daya sannan ta mika musu cikin rawan jiki, kar6an kudin su kayi kafin ogan nasu yace “tashi kije kawai, kinci sa’a ki nada sauran chanji ajiki da yau kin yaba wa aya zak’in ta amma ba komai zamu sake hadewa” cikin rawar jiki ta tashi tayi musu godiya sannan ta fara gudu ba sausautawa, seda ta iso shagon kusa da gidansu sannan ta samu guri ta zauna tafara shar6an kukan ta, mai shagon ne ya leko dan ganin abunda ke faru saboda yaji kamar shesheken kuka.

Ganin Noor yasa yayi saurin fitowa yana cewa “subhanallahi lafiya kuwa kike irin wannan kuka haka Fatima”? Goge hawayenta tayi kafin ta sanar dashi duk abunda ya faru daga fitan ta har zuwa gurin dillaliya da kuma haduwarta da wadannan mutane, sosai mutumin ya tausaya mata seda ya mata nasiha sosai kafin ya ciro taliya guda biyar manya da shinkafa mudu daya ya bata akan suje suyi maneji, godiya tayi mishi sannan ta dauki hanyar gidansu.

Bayan tafiyar dr Affan  kuwa Hajja Ghaji ta kulu iya kuluwa don kuwa ya bala’in ci musu mutunci sosai da sosai,bata ma jira Hajja Hadiza ba ta tari mai adaidaita tayi tafiyarta zuwa gida,ita kuwa Hadiza juyawar da zatayi taga har me a daidaitan yayi wucewar sa, bata kawo komai aranta ba ta tari nata ta wuce gida itama zuciyar ta fari kal dan samun sahibinta cikin koshin lafiya.

+

Sule kuwa be koma gida da wuri ba yana isa ya taras da Dr Affan har ya kwanta, ai kuwa ya dage ya daga hannu yayi masa dundu da karfi har sai da shima yaji zafi a hannun nasa.

A firgice ya tashi yana cewa”Kai baka da hankali ne meye haka dan Allah fisa bilillahi,ai zakasamin ciwon kirji, bama wannan ba harda ciwon zuciya, yanzu saboda Allah karasa wadan da zaka bawa number ta sai wadannan kidahuman yaran?”

“Bangane ba nifa cemin su kayi kuna da muhinmin abu dasu shiyasa ma na basu”nan ya kwashe komai daga basu number zuwa yau da sukazo gurin sa suka kara karban numbern wai akan wanchan baya shiga.

“Tabdijam nima kuma munyi drama daga daren jiya zuwa yau”nan shima ya zayyana masa abunda ya faru daga jiya data kirasa zuwa dazu da suka rabu.

Zaro ido Sule yayi yana mamaki “ashe se da suka je gurinka, lailai yarannan basu da hankali, kaima fa dan rainin wayo ne haka ka zagesu hankali kwance su kuma dake garori ne basu gane ba kai Dr”. yafada yana ta kyelkyale dariya.

“A’a toh mai zance musu wai harda fa anzo duba lafiya ta ne sai kace wani kaninsu ko kuma yaronsu”ya fada yana tuna yanda wawiyar take ta zaro zance.

“A’a dai Dr kaga fa yarinyar tana sonka ka dai daure ka bata lokaci koda kadanne kaga irin nata jarumtar”. ya fada da iya gaskiyarsa,sannan ya gyara filonsa ya kwanta.

“Haba abokina wannan gaular me zanyi da ita, amma dai shikenan zan jaraba tunda kasa baki”. yafada cikin zolaya.. kafin shima ya kwanta yana tir da hada iri da Hajja Hadiza.

6angaren Hajja Hadiza kam tana isa gida tayi wanka ta yi sallah sannan tayi shirin barci ta dauko wayarta ta fara neman layinsa, seda yayi ringing sau biyar kafin aka dauka cikin muryar barci yace “Hello dan Allah na fara barci kibari gobe mayi magana nagode”be jira cewarta ba ya katse wayar, itama kuma taji dadi dahar ya dauka ya mata magana kuma ai yana da uzuri bakomai goben zata kirashi.

Washe gari da safe ta shirya taje gidansu Ghaji dan bata hakuri dan kuwa taga alama fushi tayi sosai, ai kuwa ba jimawa ta sakko suka fara hiransu dama basu iya fada da juna ba ko sunji haushin juna ma na dan lokaci ne, sai kusan azahar ta koma gida..

♣🌹♣☘♣🌻♣

*🌻∂υвαι*

*♣αℓ-qυσχ*

Yau da farinciki ta tafi makaranta saboda tasan babu yanda za’ayi mayenta yaje d’auko ta, kowa mamakin Shiryawanta da wuri yake saboda kullun itace last din tafiya makaranta.

Wajajen karfe hudu suka tashi, da fara’arta ta fito daga cikin makaranta, sedai me, tana fara tafiya taji karan horn alamun da ita akeyi, kamar bazata kula ba se kuma ta juya dan ganin wani dan rainin hankalinne, abun haushi abun takaicin kawai taga yayanta alamar ita yazo d’auka, bakin ciki ne ya cika zuciyarta kamar taje ta shakeshi amma ba damar yin hakan, tsaki taja sannan ta karasa kusa da motar ta bude gidan gaba ta shiga ta zauna ba tare data kulashi ba, shima kuma be kulata ba saboda yan miskilancin suna kusa.

Suna isa yayi parking a bakin gate sannan ya mata alama da tafita, ba tace dashi kala ba ta sauka sannan tayi shigewarta cikin gida, shi kuma figar motarsa yayi, yayi gaba abunsa, dama ya biyo ta hanyar school dinsu ne shiyasa ya tsaya d’aukanta in ba haka ba shi ba shida lokacinta itama ta sani.

Moses dake tsaye a bakin window yana ganin shigowarta ya fashe da dariya yanajin dadin dawowarta gida, dama yanzu yake tunanin zuwa d’aukanta se kuma akayi sa’a ta dawo, seda yayi dariya me isarsa sannan ya koma ya kwanta yana me tunanin abubuwa kala-kala gameda Yasmeen yarinyar na bukatan gyara acikin lamuranta…

“Assalamu alaikum warahmatullahi taala wa barakatuh, Hajiya danki ya dawo nasan kinyi kewata fiye da fitinanniyar chan koh”? Ya fada yana kokarin shiga cikin falon.

+

Murmushi hajiya tayi kafin ta amsa sallamar tasa tana cewa”Dr ka kiyayeni ka fita a harkan auta, irin wannan shigowa gari ba notice, ai ka bugo ka sanar da tashinka saboda ayi maka abun tarba” ta fada tana murmushi.

“Wato atakaice dai ana kokarin nunamin ceaa matsayin auta ya zarce nawa koh Hajiya, shikenan bari in koma inda nafi wayo tunda ba’a maraba da zuwana” ya fada yana kokarin fita daga cikin falon.

Dariya auta tayi sannan tayi saurin zuwa ta riko hannunshi ta dawo dashi cikin falon tana cewa “haba sweet bro, kaima kasan babu kamarka ai, kuma kasan munyi farincikin dawowarka gida, yanzu ma ba wannan ba tashi zakayi muje muga halinda su  Noor suke ciki tunda kaga tafiyar tamu yazo a kurerren time so bamu samu yi musu sallama ba, nasa kuma ayanzu kila suna cikin wani hali dan haka kaje kayi wanka kaci abinci seka shirya mu fita”.

Farinciki ne ya bayyana akan fuskarsa wanda ke nuna alamun tsantsan kaunar da yake yiwa Noor din, murmushi yayi sannan yace “aini kanwata akoshe nake kawai ki tashi muje mu dubasu”.

Hajiyace ta dakatar dashi ta hanyar cewa “bazaka fita agidannan ba sekaci abinci tukunna so gwara ma kaje kayi wanka”.

Marairaicewa yayi yanason rokonta akan tabarsu suje su dawo amma ganin yanda fuskarta ya nuna ba alamar wasa atare da maganarta shiyasa yaja akwatinsa ya nufi 6angarensa dan cika umarninta.

Kallon Hajiya tayi sannan tace “Hajiya kin gani koh, dama na fada miki ya Affan yana son wannan Noor din kawai de boyewa yakeyi, nima inason yarinyar sosai Hajiya saboda bata da matsala sedai tayi kankanta da yawa a ya Affan”.

Murmushi Hajiya tayi sannan tace “Nima abunda nayi tunani kenan akwai rata me yawa tsakanin Noor da Affan amma dai babu abunda zance se Allah  ya za6a mana abunda yafi alkairi”.

♣🌹♣☘♣🌻♣

*🌻∂υвαι*

*♣αℓ-qυσχ*

D’aki ta wuce direct ba tare data kula kowa agidan ba, suma cikinsu babu wanda ya kulata kowa na harkar gabansa, tana shiga ta jefar da jakar akasa sannan ta cire uniform ta shiga wanka, seda ta 6ata lokaci me tsawo kafin ta fito tana goge gashinta da wani karamin towel, dryer ta dauka ta jona shi da wuta sannan ta fara drying gashinta, tana gamawa ta shafa mai ajikinta ta dauko na gashi ta shafa se humra data lafta se kace tana bikin turare sannan ta sake dauko arabian perfume kala kala ta saka sannan ta saka inner wears ta dauko wondo da riga as usual ta saka, kasa ta sauka dan samawa cikinta abinci, seda taci takoshi sannan ta haura sama dakin Ummie, da sallama ta shiga kamar abun arziki, zama tayi kusa da Ummie sannan ta gaisheta, kallonta Ummie tayi daga sama har kasa, kamar zatayi magana kuma seta fasa, amsa gaisuwar tayi sannan ta cigaba da aikin dake gabanta, itama yasmeen ganin haka seta kwanta a 3seater tana danne-dannen waya.

Horn sukaji na motoci alamar dawowar Abby, da gudu Yasmeen ta sauka dan murna, dama Allah-Allah take ya dawo dan ya kori Moses, batasan cewa shima Moses yana chan ya shirya mata wata *gadar zaren* ba, tana zuwa tasamu yan biyu har sun rigata tarban Abby, 6atarai tayi tafara bubbuga kafa akasa akan meyasa zasu rigata zuwa wajen Abby, kallonta suka tsaya yi shi kuma Abby an ta6a yar lelensa da sauri ya isa gurinta ya rungumeta yana bubbuga bayanta halamar rarrashi, daga nan yaja hannun sauran yaran suka shiga ciki.

Wani irin bugawa taji zuciyarta keyi tabbas akwai abunda ke shirin faruwa da ita ko kuma har ya riga ya faru wani irin dumi taji afuskarta tana dubawa taga ashe hawaye mamakine ya kamata dan batasan meye dalilin hakan ba adduo’i kawai take ta karantawa acikin zuciyarta.

+

Tana isa kofar gidan motocinsa na kokarin shiga baki bud’e take kallon motar zuciyarta cike da tunani kala-kala wani hawayenne yafara sauka akan kuncinta da sauri ta shige 6angaren nasu dan bata kaunar abunda ze sake had’a ta da azzalumin uba irinsa duk da cewa Umma kafin ta rasu kullun zancenta shine karsu tsaneshi dan abunda yake d’awainiya dashi ya wuce gaban tunaninsu, ajiyar zuciya tayi sannan ta k’arasa shiga cikin akurkin d’akin nasu.

Sautin kukan da taji a cikin kitchen d’insu shiya sake dawo da fad’uwar gaban da take ciki ada da sauri tayi wulli da kayan hannun nata komai ya tarwatse akasa da gudu ta k’arasa kitchen din tana haki, a zaune ta samesu rike da hannun hawwa’u suna dirzan kuka bakinta ta kalla yanda yake fitar da kumfa idanunta sun kakkafe “innalillahi wa inna ilaihi rajiun” shine abunda kawai ta fad’a kafin tayi kansu da sauri ta d’au kanwar nata ta fita waje da ita suma da sauri suka mara mata baya sa’arsu d’aya suna fita suka samu adaidaita.

Minti goma sha biyar ya kaisu asibitin gomnati dake kusa dasu, suna isa suka nufi emergency da ita da sauri likitoti suka kar6e ta suka shiga da ita se alokacin Noor ta tuna cewa bata biya me adaidaita ba da sauri ta fita dan biyansa kudinsa koda ta fita bata sameshi ba ashema harya tafi saboda ganin halinda suke ciki wani napep din ta tara zuwa gida “dan Allah malam ka jirani yanzu zaka mai dani” tana gama fada ta sauka ta shiga gida.

D’aki ta shiga ta tattare shinkafar ta saka a leda sannan ta d’auki taliyar duka ta fito, napep din ta shiga suka juya zuwa asibitin suna isa ta kunce kud’in data d’aura a bakin zaninta ta biyashi kud’in shi sannan ta tsallaka zuwa wani d’an karamin shago data hango kayan hannunta ta bashi tace dan Allah ya taimaka ya saya saboda tanason ta biya kud’in asibitin kanwarta.

Kallonta mutumin yayi na d’an wani lokaci yana nazarinta seda ya gama kare mata kallo sannan ya kar6i kayan ya fara duba yanayinsu seda ya tabbatar cewan basuda wani nak’asa sannan ya ciro kud’i acikin aljuhun sa naira duba d’aya da dari biyar ya bata godiya tayi mishi kamar ta mishi sujjada sannan ta mishi sallama ta tafi.

Tana zuwa cikin asibitin ta wuce direct inda ta bar sauran kannenta azaune ta samesu sun takure a guri d’aya suna kuka se kace ance musu ta mutu zuwa tayi ta janyosu jikin ta tana kokarin rarrashin su sukuwa wani irin tsoro ne ya kamasu da suka tuno da Ummansu se kuma a sannan ta tuna cewa ashe bata tambaye su abunda ya faru ba, tana kokarin tambayarsu wani likita ya fito daga d’akin yana sarce gumi “ke kika kawo mara lafiya ko” wani tunani ta farayi acikin zuciyarta da sauri kuma ta kawar da hakan ta fara addua kafin tace “eh nice na kawota tare da kanne na” to ki biyoni zuwa office” tsorone ya fara kamata amma ta dake ta rarrashesu kafin ta bi bayansa.

♣🌹♣☘♣🌻♣

*🌻∂υвαι*

*♣αℓ-qυσχ*

Bayan Abby yayi wanka ya shirya suka fito dancin abinci adinning suka had’u da uwarci tanata faman loma dama ita kam bata basa da cikinta ko kad’an bata iya komai ma se cikinta ya cika, zama sukayi kowa ya d’iba abunda yakeso Umee da Abby a plate d’aya sukaci nasu dan dama haka sukeyi duk sanda yake gida.

Bayan sun kammala cin abincin suka nufi palo hira sukeyi sama-sama saboda kusan duka hankalinsu naga wani qur’anic competition da akeyi akasar saudi sosai yaran dake musabaqan suka burgesu daman wannan karan Abby yace dukansu matan zasuyi tunda mazan sunyi yafi akirga dukda cewar ita Yasmeen bataso hakan ba amma kuma saboda kar kannenta su rainata shiyasa ta amince.

“Duk ku bani hankalinku” shine abunda Abby ya fad’a bayan sun kashe T.V din suka zazzauna a kasa suka bada hankulan su gabaki d’aya dan sun san cewa magane me mahinmanci “kamar yanda kuka sani aiki ne ya kawoni kasarnar kuma na kammala shi tun wancan shekaran yanzu lokaci yayi da zamu koma kasar mu wato Nigeria kuma baya ga hakama Hajiya tace lalle-lalle in dawo tana son ganina dan haka na riga nayi mana visa gobe insha Allahu zamu dira akasar Nigeria kuma a garin Borno kafin mu koma Abuja sannan yan makaranta na riga na nema muku transfer dan haka ba kuda matsala inafatan kun gane”.

Atare mazan sukace “mun gane Abby Allah ya kara arziki daman muna son zuwa muga Hajiya” matan kuma sukace “eh Abby mungode sosai Allah ya barmana kai da Ummy kuma dama muna son zuwa muga yanayin kasarmu da irin cigaban da akasamu mun mafi sha’awar zaman chan fiyeda kasarnan”.

Se alokacin ta dawo daga sumar zaunen da tayi sannan tace “What Abby you mean Nigeria ( Abby mekenan kana nufin kasar nigeria) oh no it cant be i just cant please Abby dont do this to me (a’a baze yiyu ba dan Allah Abby karka min haka).

Murmushi yayi daman yasan za’ayi haka ko kowa ze yarda itakam se anyi da gaske zata kona amma ya zama dole ma su koma saboda furucin mahaifiyarsa akansa “look Yasmeen is not a matter of choice umarni ne daga nawa mahaifiyar so i dont wana hear any single no just do as i said other wise you will face the consequences alone and i mean you alone ( Yasmeen baki da za6i anan kawai kiyi abunda nace ko kuma ki fuskanci hukuncinki ke kadai) yana gama magana ya haura sama.

Madubin dake idanunsa ya cire sannan yace “ya akayi kuka barta tasha kalanzir kuma baku bata taimakon gaggawa ba sannan baku kawota asibiti da wuri ba?”.

+

“Likita kalanzir fa kace to taya tasha kalanzir d’in” da gudu-gudu ta fita waje gurinsu Mimi har tana tuntu6e tambayarsu tayi akan shin menene ya faru da batanan Habiba ce tace “Wallahi yaya muna zaune muna jiran dawowarki shine tace bari taje tasha ruwa bayan ta fito se na kece mata ya nakejin warin Kalanzir da sauri ta koma kitchen din shine mukabi bayanta se alokacin taga ashe kalanzir tasha har kofi biyu ba ruwa ba, na duba ko ina kuma bamu da zuma ko madara shine muka zauna akitchen din muna kuka har dai ta farayi kamar zata suma har kuma idanunta suka rufe se kunfa dake fita daga bakinta”.

Zamewa tayi ta zauna a k’asa tana maimaita duk wani adduar da yazo bakinta tabbas suna cikin gagarin rayuwa wani irin damuwa ne haka y’ar kanwar nata take ciki da har zata sha kalanzir ba tare data iya banbance ko ruwane ko ak’asinsa ba “Allahumma Ajirnifi Musibati Wa Kallifli Kairan Minha, Innalillahi Wa Inna Ilaihi Rajun” shine kawai abunda take ta maimaita wa kafin ta tashi tabi bango zuwa office din likita sannan ta mishi bayanin komai tanajiran taji result ko lafiya ko ak’asinsa.

Tausayi ta bashi yanda yaga tana hawaye amma ya zama dole ya fad’a mata gaskiya dan kuwa yarinyar jikinta is allegic to irin abubuwa masu karfi haka kuma jininta babu karfi da wata kila zata iya rayuwa “am sorry to say” da sauri ta d’ago kai ta kalleshi dan jin kalmar data ruguza rayuwa da dama kalmar “am sorry” kalmar daya sata shiga maraicin uwa me hakan ke nufi kenan kallonshi tayi ido cikin ido tace “inajinka ya kayi shuru kuma likita kawai fad’amin kalmar da zata k’ara tarwatsa rayuwarta kalmar daya dad’e da sanyi zuciyata cikin garari”.

Ajiyar zuciya yayi yana me tunanin yama zeyine wai shin mezece mata ne kawai kallonta ya tsayayi yana nazarin abubuwa da dama “ina iyayenku suke ko kuma danginku”.

Wannan tambaya daya mata shiyasa ta mishi wani mugun kallo kafin tace “ina ruwanka damu ina ruwanka da rayuwar mu malam dan Allah kayi mana maganar abunda ya had’amu da kai bawai abunda be shafeka ba na had’aka da Allah domin mu musulmai ne zamu kar6i kaddaran rayuwa duk yanda yazo mana”.

Ganin yanda ta d’au zafi kawai ya yanke shawaran gaya mata abunda ke faruwa koshi ma zesamu sukuni acikin ransa da zuciyarsa idan ya sauke nauyin dake kansa “Am sorry once more sedai kuyi hakuri Allah yayi mata cikawa”.

Murmushi yaga tayi kafin tace “hmmm biyu kenan ko waye kuma agaba bari dai mu zuba ido Allah ya jikanki Hauwa’u kin huta da rayuwar garari rayuwar kunci” kafin ta tashi ta fita gurin kannenta.

♣🌹♣☘♣🌻♣

*🌻∂υвαι*

*♣αℓ-qυσχ*

D’akin Abby taje ta same shi yana karatun jarida zama tayi kusa da kafarsa kafin tace “yanzu shikenan bazamu sake dawowa Dubai ba Abby idan mun tafi mun tafi kenan?”.

D’agota yayi ta zauna akan kujera sannan yace “duk kasar da kukeson zuwa hutu zakuje amma ayanzu abar batun cewa baza’aje Nigeria ba saboda shine tushenmu kuma asalinmu dashi muke tunkaho muke kuri dan haka kiyi hakuri kinji babyna”.

Hawayen idonta ta share tace “shikenan Abby amma dai bazamu tafi da Moses bako danni bana sonshi ya fiye takuramin”.

Yau dai tanaji da rigima ne kawai shi kuwa Abby yaji dadi da har akwai wanda take tsoro dan yana takura mata amma saboda bayason ta sake kawo wani abun shiyasa kawai yace mata “shikenan babyna baze biyomu ba kinji ko”.

Farinciki taji acikin ranta da Abby ya amince dan itakam duk wani d’an Nigeria ta tsanesu balle kuma shida yake takura rayuwarta Hakan yasa ta shiga d’akin tana kokarin had’a kayanta cikin farin ciki tunda zata rabu da mayen arne me takurawa rayuwarta sosai take cikin nishad’i saboda haka, hakan yasa kowa agidan yake mamakin abunda ya sata nishadi.

Moses dai ba kowa bane illa Mustapha aiki ne ya kawoshi gidan Alhaji Ibrahim Nura amatsayin secret agent tun sanda yayi sanadin bayyanar gawartattun yan mafiya agarin Kano aka d’auke shi aiki afannin binciken sirri agidajen manyan masu kud’in kasa  wad’an da suke zama a cikin k’asan da kuma wad’an da suke zama a wata k’asa daban acikin shekaru hud’u da suka wuce yayi kokarin fito da ainihin fuskar mutanen kirki dana banza acikin k’asar Nigeria inda aka samu raguwar cases ta fannin yan mafiya da kuma masu safaran kayan maye da wasu abubuwan da basu dace ba ya samu award da yawa saboda kwazonsa da kuma kokarinsa yanzu haka yaranshi biyar a duniya Hafiz me Sunan Malam shekarunsa goma, yan biyu Aisha me sunan Ummi, Hafsa me sunan Gamboji shekarunsu Bakwai se Isa me sunan mahaifinshi shekarunsa biyar se auta Halima me sunan Mammy wanda gurin haihuwarta Zahra ta rasu yanzu haka tana da shekara uku a duniya kuma tun daga lokacin be sake sha’awar aure ba se yanzu daya had’u da Yasmeen sedai ya san cewa zesha fama kafin ta amince dashi.

Bata gaya musu abunda yafaru ba kuma bata bari sunga gawar ba ta kaisu gida sannan ta dawo, se asannan tayi settling bill din aka samata gawar a mota suka kama hanyar gida suna isa motarsu Dr Affan na shigowa cikin sauri suka fito shida Auta ganin motar asibiti kallon Noor yayi sannan ya kalli gawar da aka lullu6e da zani ahankali ya matsa kusa dasu sannan yakai hannunsa kai ya yaye lullu6in dai-dai lokacin da su Mimi suka fito cikin sauri suka karasa kusa da gawar suna kuka suna kallon yayartasu.

Hawayen idonshi ya share kafin yace “Ku shiga mota mu tafi gida se ayi mata salla achan” ba musu duk suka shiga banda Noor data tsaya tana kallon gawar kallon dreban yayi yace mishi amaidata ciki se subi bayansu saboda ba’anan za’ayi janaizar ba, se a sannan itama ta shiga motar da aka mai da gawar shima Affan ya juya ya shiga nashi ya tayar ya fita dreban yabi bayanshi.

Mamaki ne ya kama Hajiya ganin cewa ko minti biyar basuyi ba suka dawo to kila kuma basunan amma da dare haka ina zasuje ganin sun jima basu shigo ba yasa ta tashi ta fita dan ganin ko lafiya k’amewa tayi aguri d’aya ganin suna kokarin shigowa da gawa, kallonsu tayi d’aya bayan d’aya amma bata ga mutun d’aya ba hakan yasa ta gane wacece aka lullu6e tausayin yaranne ya kamata tabbas suna ganin rayuwa Allah dai ya sassauta musu wannan lamari.

Har akayi mata wanka akayi mata salla Noor ta kasa ta6uka komai dan koda aka kirata dan tayi mata addu’ar bankwana ba tace musu komai ba tayi zamanta hakan yasa kawai aka tafi da ita se a sannan tayi ajiyar zuciya ta kwanta a kasa tana tunanin duniya.

Mahaifin mu d’ane ga Malam Nura Ibrahim da kuma Hajiya Falmata, su hudu iyayensu suka haifa Ibrahim Nura, Juwairiyya Nura, Muhammad Nura se auta Nabeela Nura.

Mahaifinmu sun taso cikin gata da tarbiyya domin iyayensu mutane ne masu kiyaye dokokin Allah sunyi karatun boko dana addini kuma duk sunyi haddar alkurani mahaifinsu babban malamine kuma attajirin d’an kasuwa wanda babu kamarsa acikin garin Bama, hakan yasa yaransa maza duka biyu suka biyo sahunsa kuma cikin izinin Allah suma suka shahara fiyeda mahaifin nasu harma mutane sun rasa gane wanda yafi wani kud’i tsakanin Ibrahim Nura da Muhammad Nura, Ibrahim Nura ne ya fara aure inda ya auri wata Baboliya yar asalin garin Damaturu akarkashin jihar yobe, Allah ya azurtasu da yara shida uku maza uku mata se Muhammad Nura wanda ya auri wata y’ar Hakimin garin potiskum kuma jikar sarki ta gurin uwa shima Allah ya azurtashi da yara shida duk mata  se Juwairiyya wanda tayi aure agarin Bama ta auri d’an abokin babansu se Nabeela da akayi mata auren zumunci da d’an yayan Hajiya.

Kiran Sallar magriba ne ya dawo da ita daga duniyar tunann data fad’a tashi tayi ta alwala tayi salla bayan ta idar tayiwa mahaifiyarta addu’a sannan tayiwa kanwarta da kuma sauran yan uwa musulmai da suka riga mu gidan gaskiya sake kishingid’a tayi tana kallon sauran kannenta babu abunda take fad’a acikin ranta se Allah ya saka musu akan abunda mahaifinsu yayi musu.

Akwana atashi asaran me rai yau akayi sadakan bakwai kuma har zuwa yanzu Noor ba um ba a’a sedai tayita bin mutane da ido ita burintama shine taga tayi kuka ko zata samu sanyi acikin ranta lailai hawaye ma rahama ne domin ita kadai tasan me takeji acikin zuciyarta ita daya dace ace tana rarrashin kannenta wai su suke ma rarrashinta kuma duk da haka sedai ta bisu da ido baza tace dasu komai ba Hajiyasu Affan ma tayi magana harta gaji sedai kawai ta zuba mata ido shima Dr Affan yayi rarrashin amma abu yaki yiyuwa kamar kullun yau tana zaune tana aikin tunani Dr Affan tazo ya zauna kusa da ita juyar da kanta tayi tana tsaki kasa kasa dan batason magana ko kad’an sake dawowa yayi 6angaren data juya hakan yasa ta d’aga ido ta kalleshi “dan Allah Dr ka kyaleni inji da abunda yake damuna na rokeka dan Allah” dad’i ne ya kamashi ganin cewa yau tayi mishi magana duk da cewa bataso ba amma ba komai zata fara sakewa ne, tashi yayi yana cewa “Allah ya baki hakuri my Noor” jin abunda yace yasa tayi murmushin da bata shirya ba shima sautin murmushinne yasa ya mayar da martani sannan yayi wucewarsa.

♣🌹♣☘♣🌻♣

*🌻уσвє ѕтαтє*

*♣gαι∂αм ℓ/g*

Ghajiiii!!! Shine abunda take ta ambata tana kokarin shiga d’akin kawarta, da sauri ta fito tana dube-dube “Hajja Hadiza lafiya kike kuwa wannan kiran ai nazata biyoki akayi?”.

“Inafa lafiya kawata ai dole ki ganni haka cikin tashin hankali wai yanzu nakejin labarin cewa Dr Affan ya koma ba tare daya sanar dani ba kuma kullun ina kiran wayarsa amma baya d’auka wayyo nashiga uku ni Hadiza Allah kuwa binsa zanyi Ghaji bazan iya ba gaskiya nagaji da dakon soyayyar tasa gwara ayita ta kare kawai” ta fada tana share hawaye.

Kallonta gaji ta tsayayi tana nazarinta toh gata dai tsaf da ita balle tace ko dai tayi gamo ne ikon Allah shin lafiyarta kuwa “wai in tambayeki naji kina cewa kawai binsa zakiyi bangane kalmar binsa ba ki kara yimin bayani dakyau”.

Hararanta tayi kafin tace “hausa dai nayi miki balle kice yare nayi da bazaki iya ganewa ba nace bin shi zanyi zanje Bama dan inganshi saboda mu kak’are magana kowa ya huta dan ni bazan iya zama ina gadin soyayyarsa ba shi kuma kila wata yakeso achan kisan ance abari ya huce shikw kawo rabon wani kuma garin kallon ruwa kwado yayi maka k’afa dan haka idan zaki rakani gwarabki shirya idan kuna bazaki ba se ki sanar dani ki barki kiyi tunani zuwa yamma zan dawo” tana gama magana ta figi jiki tayi gaba abunta tana ta banbamin matsifa.

Ghaji kuwa zaman dirsham tayi akasa tana saka da warwara tabbas akwai abunda yake damun kwakwalwar kawarta inba haka ba wani irin magana ne zatace wani wai abishi se kace mahaukata eh lailai dole akira masu rukiyya domin su warware komai.Yau kwanaki arba’in kenan da rasuwar Hauwa kuma yan uwanta sunyi kokarin cire damuwa a ransu sun fawwala wa Allah lamuransu sedai suna matukar kewarta saboda kasancewarta mace me barkwanci duk sa’adda suke cikin damuwa ita take kokarin kwantar musu da hankali kuma ta sanyasu dariya amma yanzu ta zama tarihi.

+

Kamar kullun suna zaune a falo tare da Hajiya tana karayi musu nasiha game da rayuwa bayan ta gama Noor ta fada mata cewar sunaso su koma gida tambayarsu tayi shin mutanen gidan sun dawo ne sukace a’a basu dawo ba dan Noor ce kawai tasan da dawowarsu kuma bata bari kannenta sun sani ba.

Hajiya ta sake cewa “ni aganina tunda babu wani abunda kukeyi agidan ai se ku zauna anan kawai dan banga amfanin zamanku ku kad’ai ba alhali kuma masu gidan basa gari sedai idan ba kwason zaman gidan nawa ne”.

Da sauri Noor tace “a’a Hajiya kiyi hakuri Wallahi munason zama daku se dai kuma masu gidan zasu dawo cikin satinnan idan kuma har suka dawo basu taras damu ba toh tabbas baza muji dadi ba shiyasa gwara kawai mu koma idan yaso insun tafi semu dawo”.

Nazarinta Hajiya ta farayi kafin daga bisani tace “shikenan tunda kin kawo hujja me k’arfi amma dan Allah idan har suka koma ki sanar dani Affan zezo ya kawoku kinji ko, ungo wannan waya ce da shi zan dinga kira inajin  lafiyarku” ta fad’a tare da mik’a mata wayar.

K’ar6a tayi tare dayi mata godiya sannan suka tashi dan komawa gida Autace zata kaisu gida saboda Dr Affan yana gurin aiki kuma baze dawo da wuri ba, seda ta biya ta wani store kamar yanda dai Hajiya ta umurce ta akan ta saya musu kayayyakin abinci da kayan sakawa wadacecce, bayan data gama saya se aka loda musu a mota sannan suka kama hanyar gida.

Tare suka dinga kwasan kayan suna kaiwa cikin d’an karamin kitchen din nasu bayan sun gama kwashewa suka mata godiya tare da bada wani sakon godiya zuwa ga Hajiya, bayan ta tafi suka shiga ciki dan hutawa.

STORY CONTINUES BELOW

Bayan sallar Magriba Dr Affan yazo tare da kawo musu kayan itatuwa da kuma gasheshen kaza seda suka d’anyi hira sannan ya tafi duk da cewa Noor din taki ma sakewa dashi, kitchen ta kai kayan itatuwan ta ajiye sannan ta juye musu kazar acikin karamin tray ta kawo musu d’aki, suna zaune suna buga loma aka sheka musu ruwa me d’an karen sanyi ko ba’a fada ba sunsan cewa ba kowa bace zata musu wannan aikin se Innansu Mardiyya sunan da suke kiranta dashi kenan ita kuwa ta tsani Innan da suka lak’aba mata hakan yasa suke kara k’aimi gurin kiranta dan sunan da suka lura cewa bataso  “yan iska dangin tsiya ba uba ba uwa gashi wai naji cewa kun kara wani rashin toh ba dole ba abu da masu farar k’afafu duk kanwar jace Allah dai ya raba bawa da wahala wajen had’a iri da mayu irinku abu na farko daya kawo ni shine inason inja muku kunne karku kuskura koda wasa ku bari kuyi ido hud’u da mahaifinku domin idan hakan ya faru zaku bi tsinanniyar uwarku inda taje abu na biyu shine kar in sake ganin k’afar wannan d’an iskan acikin gidannan idan ba haka ba kun dai sanni sarai kunsan halina gwara tun da wuri ku tsayar dashi daga zuwa dan ba karamin aikina bane insa a aikashi barzahu ina fatan kun gane sannan daga yanzu mun dawo kenan babu wani tafiya me tsawo da zamu sakeyi dan haka ga wannan kayan ko wacce ta d’auki kala uku uku daga gobe zaku fara mana aiki acikin gida domin munada ku baza mu d’auki masu aiki muna biyan kud’i abanza ba ina fatan kun gane dan haka gobe da sassafe inganku acikin 6angarena kuma ku tsaya akitchen zanzo in sameku” tana gama fad’a musu ta kara gaba tana ta tsine kusu albarka.

♣🌹♣☘♣🌻♣

Nura Family House gidane wanda yake cikin jerin gidajen dake manya manyan housing estate dake cikin garin bama baban gidane me d’auke da 6angare uku na farko 6angaren Ibrahim Nura tare da iyalinsa na biyu 6angaren iyayensu shine atsakiya sena karshe 6angaren Muhammad Nura tare da iyalinsa duka yaran Nura mazan acikin wannan 6angaren suka zauna kafin sukayi gininsu na alfarma inda Ibrahim ya gina gidansa a garin Abuja shi kuma Muhammad yayi nashi a cikin garin bama sukan zauna agidansu na cikin family house idan wani abun ya taso Ko meeting atsakanin family gabaki d’aya.

Ayau su Yasmeen sukayi wata d’aya da dawowa cikin garin Nigeria kuma har zuwa yanzu ta kasa sakewa da kowa twins kam babu ruwansu da kowama suna mu’amala dan basuda damuwa ko kadan haka sauran yaran duk sun sake da dangi se ita kadai dan ko magana batayiwa kowa sedai ta bisu da harara ko kuma tsaki kasa-kasa ita dai kawai Allah Allah takeyi su koma Abuja ko zata samu natsuwa dama gashi yan makaranta da suka tafi hutu anan sun kusan komawa dan bai wuce saura sati guda ba hakan yasa take murna dan tasan sun kusan barin garin.

Kamat koda yaushe yau ma tana zaune a garden tana hutawa d’an Anty Juwairiyya yazo shi ya zauna kusa da ita duk da cewar yasan hakan da yayi zesa ranta ya 6aci amma kawai yanajin dad’in masifarta ne “toh masu gani har hanji ya da kallo haka ko akwai abunda na tare makane acikin gidannan dan na lura sa take-takenka na kuma ga alamar cewa kana neman in yanke maka rigar mutunci ne dan haka idan kanason kanka da arziki ka tashi kawai ka barnan” ta fada cikin isa da takama ita ta fiti daga kasar waje an haifeta akasar waje tayi karatu achan tafishi wayewa.

Dariya ya kwashe dashi saboda ganin yanda ta dage tana ta wani masifa kamar dai wani laifin yayi mata harda wani harare harare da murgude baki kamar ak’auye “haba y’ar kanwata nida nazo dan muyi hira shine kuma zaki faramin fad’a haba babyn Abby da kanta toh kiyi hakuri bazan sake ba kinji amma nidai ki ringa kulani ko zan danji dadi araina kuma sannan ki fad’amin abunda kikeso yanzu zan miki kinji y’ar kanwata”.

Har zata sake balbaleshi se kuma ta tuna cewa tana neman me tayata maganin Moses dan dole ne atayata maganinshi tunda taga alamar Abby ba korarsa zeyi ba “tam shikenan nidai abu d’aya nakeso daga gurinka inaso ka tayani fitar da wani munafiki daga gidanmu idan har kayi min haka toh zamu shirya bama kad’an ba” daga nan ta bashi labarin Moses da irin zaman da takeyi dashi da yanda yake takurawa rayuwarta.

Murmushi yayi aranshi yace anzo gurin kafin yace “ai wannan karamin abune agurina kawai ki fadamin abunda kikeso da kuma yanda kikeso tuni zan aiwatar dashi ranki ya dade babyn Abby”.

Wani dadi taji aranta da yace ze taimaketa hakan yasa ta fara gaya mishi tsarin da takeso ayi wa Moses din shi dai kawai jinta yakeyi yanata mamakin yanda tasan kan mugunta amma tunda har ya samu abunda yakeso wato ta kulashi shikenan ba komai asannu ze zama mata k’arfen k’afa.

♣🌹♣☘♣🌻♣

*🌻уσвє ѕтαтє*

*♣gαι∂αм ℓ/g*

Zaune take a d’aki ta rasa madafa gashi ita batasan ta inda zata fara nemanshi idan taje garin Bama ba daman tunanin ta shine idan har Ghaji ta yarda ta rakata shikenan se suyita yawi tare suna nemansa har Allah yasa su dace seta fada mishi abunda yake ranta idan ma shi baze iya turawa ba se ita ta tura anema mata aurenshi hakan ma shine kawai abunda ya dace tayi.

Tana cikin tunani taji an dafata tana d’agowa taga Ghaji tsaki taja ta d’auke kai murmushi Ghaji tayi dan tasan tayi laifi shiyasa baza’a kulata ba “kiyi hakuri Hajja Hadiza kawai dai inaganin kamar zubar da ajine zuwa neman saurayi har wani gari amma tunda kina ganin hakan shine dai-dai yanzu dai seki fadamin shin idan har zamuje din gurinwa zamuce zamuje idan aka tambayemu agida”.

Murmushin jindadi Hajja Hadiza tayi “yanzu naji batu kawata amma ana nuna miki annabi kina rintsa idanu waya sani ko kema ki hadu da naki likitan achan kinga shikenan mukam mun samu gurin zama se mu zama manyan gaske matan likitoti, batun cewa ina zamuje kawai base muce za’ayi bikin kawarmu Karime ba kinga shikenan semu samu damar zuwa dama kuma kinga bikinta sati me zuwane kuma chan Bama za’a kaita kuma yauwa ashema likita zata aura kinga ankwana gidan sauki dolema nasan zezo bikin tunda ai likita abokin likita ne ko mekikace”.

Haushine ya kama Ghaji ita dama tayi mata maganar ne atunaninta kila batada mafita inyaso se tace mata tayita tunanin mafita kafin lokacin zatasan yanda zata shawo kanta ta hakura ashe dai dagaske take wai bib saurayi zatayi da sunan soyayya “shikenan bari inje gida zamy k’arasa maganar daga baya dama nazo baki hakuri ne kuma tunda kin hakura madalla semun sake haduwaç ta fada tare da gyara zamsn hijabinta tana kokarin fita, da sauri itama Hajja Hadiza ta sako nata danyi mata rakiya.

Auren soyayya iyayenmu sukayi tabbas Umma taga gata iya gata daga dangin mahaifinta dashi kanshi mahaifinnata  zuwa dangin mahaifiyar ta sosai sukayi bajinta suka cika mata d’akuna guda uku da kayan more rayuwa haka falonta biyu da kuma kitchen dinta duk seda suka tabbatar sun sanya mata dukkan wani abun bukata sosai masoyanta suka tayata murna yayinda makiyan nata suka kasa 6oye irin bak’in-cikin da suke ciki anyi taro lafiya aka watse lafiya cikin annashuwa.

Iyayen mahaifinmu suna matukar son mahaifiyar mu tamkar su suka haife ta haka cikin dangi kowa na kaunarta sosai take samun kulawa daga gun mahaifinmu dan haka itama take ta kokarin kyautata musu dai-dai gwargwado.

Shekara d’aya bayan aurensu aka Haifeni sosai akayi bidiri aka kashe kud’i ta ko wani 6angare kasancewar nice mace ta farko da aka fara haifa acikin jikokin gidan Uncle Ibrahim ma lokacin yazo shida yaran shi guda uku itama Anty Halima tana d’auke da ciki haihuwa yau ko gobe, Ranar suna naci sunan kakata ta gurin uwa wato Fateema ana kirana da Noor bayan suna da sati d’aya anty Halima ta haihu ta samu baby girl sosai akayi bidiri a sunan dan duka yaranta uku maza ne ranar suna aka sawa baby sunan kakarmu wato Falmata ana kiranta da Yasmeen.

Nida Nusaiba aka haifa a family house su Hauwa’u Habiba Aminatu da kuma Khadija duk acikin gidan mu na New Housing Estate Bama aka haifesu sosai muka samu gata fiyeda tunanin me karatu kullun muna cikin ziyaran park kala daban-daban ko makarantar da muka fara ma k’adai babban makarantar kud’i ne wanda babu na biyunshi agarin bama mahaifiyar mu macece me saukin kai da son jama’a dan haka ko yan aikin gidan mu cikin gata suke, babu wani abunda yaran masu kudi zasu nuna mana domin mahaifinmu ya zance duk inda ake tunani, ina jss3 Nusaiba na jss1 Hauwa’u da Habiba kuma na pri6 kasancewar kusan kansu d’aya Aminatu na pri4 se auta tana pri2 alokacin rayuwa ta juya ta sauya ak’ala.

Bazan iya cewa ga wani abunda ya faru ba domin nima kaina bansani ba haka bazan iya cewa ga dalilin sakin da yayiwa mahaifiyarmu ba kuma bansan dalilin da yasa yace mu koma d’akin da ake kiwo da zama ba ni dai naga an chanja wa dabbobin muhalli me kyau mu kuma an wurga mana katifa d’aya me d’an girma da tabarma se kayan abunci wanda da gani awu akayi aka bamu tun daga ranar mahaifin mu, danginshi da kuma dangin mahaifiyarmu da mahaifinta duk suka juya mana baya.

Kwasam aka wayi gari wai mahaifin mu ya kara aure da wata bazawara wacce ba kowa bace illa Innarmu Mardiyya wacce kuma take kanwa agurin mahaifiyarmu Uba d’aya domin daga Umma se ita ajerin haihuwar gidansu, Innar mu tayi aure sedai auren be wani d’aure ba alokacin da aka haifi Nusaiba lokacin itama ta haifi d’iyarta me suna Nafisa wacce yanzu haka take gidanmu amatsayin y’ar gidan tana haihuwar Nafisa da wata biyu suka rabu da mijinnata kuma tun lokacin bata sakeyin wani aure ba se sanda ta shigo gidanmu matsayin matar mahaifinmu, sosai mukayi kuka nida kanne na Umma ma nasan tayi kuka amma bata ta6a bari mungani ba kuma duk sanda muka fad’i abu mara kyau kan mahaifin namu ko kanwarta ranar ranmu duk ze 6aci hakan yasa muka dena kumaja bakinmu kukayi shuru.

Tun sanda akayi auren kuma suna siri barin kasar mudai kawai muna matsayin madu gadin gida ne dan ko ainihin masu aikinmu duk an koresu wasu sabbi aka kawo masu munin gaske dagani kasan babu imani atare dasu, duk sanda suka dawo daga tafiya se Innanmu ta shigo taciwa mahaifiyarmu mutunci muma kuma tayi mana duk abunda taso amma Umma sedai kawai tayi murmushi ni banajin na taya ganin kukan Umma indai akan walakancin da muke ganine har abun yana bani mamaki.

Bayan shekara biyu da faruwan lamarin mukaji labarin rasuwar mahaifin Umma bayan anyi arbain sosai Umma tayi kukan bakin-ciki da bata samu damar ganawa da kakan mi ba hakan yasa kullun take cikin rashin lafiya da mukaje asibiti aka sanar damu cewa ta kamu da ciwon zuciya haka muka dawo gida muna jinyarta tare da maganin da aka bamu, kuma tun lokacin muka dena ganinsu kwata-kwata se aranar da muka dawo tare da Umma daga asibiti shine bayan shekara d’aya da tafiyar nasu abun kuma ya dawo harda Nafisa ake zuba mana rashin mutunci kuma bamu isa muyi magana ba tunda bamuda wani matsayi acikin gidan, har zuwa sanda mahaifiyarmu ta rasu babu abunda ya sauya dan ko ta’aziyya babu wanda ya mana daga danginta har danginmu hakan yasa muma muka tattara lamarin dangi muka watsar saboda tunaninsu ma bashida wani amfani atare damu.

Marin da tasha shiya dawo da ita daga duniyar tunanin data fad’a rike kuncinta tayi tana zubar da hawaye saboda ganin sa’ar kanwarta na zuba mata mari acikin gidan ubanta “Yar iska shine har zaki zauna hutawa ko bayan kinsan cewa inajin yunwa bazaki tashi kiyi abinci da wuri ba, toh bari kiji in fad’a miki daga yau duk inda sha biyu yayi ki tabbatar kin kusa gama girkin da kika d’aura kuma anjima zan aiko miki da time table din girke-girken da zaki dingayi shashasha kawai kwad’ayayyun banza” ba tace komai ba ta tashi ta shiga kitchen dan d’aura girki kamar yanda Innar su tace dan yanzu ko wani girki ita zata dingayi Nusaiba kuma ita zata dinga gyara d’akin Nafisa dana Innar tasu se Habiba da zata dinga share katon falon sama dana kasa Aminatu kuma nata aikin shine mopping falo biyun idan an share Khadija wacce ake kira da Mimi kuma aikinta shine wanke wanke idan anci abinci.

♣🌹♣☘♣🌻♣

Yau abun nata yayi matukar basu mamaki saboda duk suna zaune ne afalo ana hira ita kuma sunata aikin kus-kus tare da Adam d’an Anty Juwairiyya sosai yake bata labarin irin muguntar da ya shirya a daren jiya dariya takeyi babu sausauci kamar yayi mata albishir da gidan Aljanna kowa dai afalon mamaki yakeyi saboda sanin halin yar gwal din.

Kamar daga sama Hajiya taji ta kira sunanta tana cewa “Granny zamu tafi tare da bro Adam zuwa Abuja kinji dan Allah” wani dadi ne ya kama hajiya hakan yasa tace “babu komai yar jikalle zaku iya tafiya dashi tunda kinason hakan” ita atunaninta ta fara sakewa ne da jama’a shiyasa batayi wani korafi ba ta amince da hakan duk da yanda duk cikin jikokinta maza tafi kaunar Adam din kuma batason yayi nisa da ita shiyasa ma aka dawo dashi cikin family house.

Da gudu ta fad’a jikinta tana cewa “thank you Granny love you” kafin ta tashi da gudu tayi 6angarensu ta shiga cikin d’akinta tanajin dad’i wannan yanayi.

Hajiya kuwa wani irin dadi taji aranta wai yau ita Yasmeen tayi hugging ai abun alfaharine agurinta Mustapha dake zaune agurin mamakine ya kamashi dan shikam be yarda da ita ba tabbas akwai abunda take shiryawa dan bayajin ko iyayenta sunfishi sanin halinta shima tashi yayi ya fita ya koma chan 6angaren bak’i yana tunanin abunda ya dace yayiwa wannan yarinyar.

Adam kuwa murmushin jindadi yayi da kuma nasara saboda ya kusan samun abunda yakeso cikin ruwan sanyi dan ya riga ya gano lagonta shine wannan Moses din indai zaka tayata yimishi  mugunta tabbas kai nata ne hakan yasa ya cigaba da tunanin hanyoyin da zebi dan cimma burinshi akanta.

Tana gama ayyukanta ta gyara kitchen din kafin ta nufi 6angarensu dan gabatar da sallar azahar achan ta taras da kannen ta har sun idar suna d’an hutawa “Nusaiba dafa mana abu me d’an sauki kafin in idar” ta fada tana kokarin shiga ban d’aki danyin alwala.

Bayan ta idar da salla Nusaiba ta shigo rike da tray me d’an fad’i wanda ta zuba musu indomie a ciki, babban ledar cin abinci Mimi ta shimfid’a sannan Nusaiba ta ajiye musu, seda ya d’an fara hucewa sannan suka fara ci bayan sun gama Aminatu ta gyara gurin Habiba kuma ta fita da kwanon.

Hira sukeyi sosai suna tuna Umma da Hauwa’u suna masu musu adduar samun rahamar Ubangiji tare da fatan Allah yasa suna su cika da imani Nusaiba ce tace “wallahi Ya Noor ba karamin dace mukayi da innar mu bata ga kayan abincin dake cikin kitchen dinmu ba dan nasan da tuni ta tafi dasu ko kuma ta bawa masu tsaron gidannan kyauta”.

Murmushi Noor tayi kafin tace “nima sosai nayi mamaki da batayi mana bincike ba har addua nayi akan Allah karya bata ikon ganin kayan ni yanzu babban matsalata shine yanda zan kalli ya Affan ince karya sake zuwa gidannan” ta fada cikin yanayi na damuwa.

Nusaiba tace “karki damu insha Allahu Allah ze mana maganin komai ze sama mana mafita” suna gama hiran suka sake komawa 6angaren Innarsu dan cigaba da aikin data raba musu dan yanzu har kayanta ita da Nafisa duk su zasu rika wankewa dan mugunta kuma bawai babu injin wanki ba kawai saboda bata kaunarsu.

Se bayan isha’i suka samu hutawa gabaki d’aya dambun gari sukayi sukaci sannan suka kora ruwa suna gamawa kiran Dr Affan ya shigo d’auka tayi sannan tayi sallama bayan ya amsa ya sanar da ita cewar yana waje tsoro ne ya kamata amma kawai ta fuske ta fita, sun dade suna hira yau kam ta d’an saki jiki dashi sedai tanata addua acikin ranta akan Allah yasa kar Innar su ta fito ta kuwa taki sa’a dan harya tafi babu wanda ya leko.

Waahe gari da safe tun asuba da suka tashi yin Salla basu koma barci ba suka nufi 6angaren Innar su kamar jiya yauma sun dizga aiki ba sauki seda suka sha panadol bayan sallar isha’i, har taja pilo zata kwanta sega kiran Dr Affan yauma cikin d’ari-d’ari ta fita sun d’anyi hira kadan kafin yayi mata sallama ya tafi dan yanason zuwa gida ya had’a kayansa saboda wani aiki da aka turashi zuwa garin Abuja, sosai tayi murna saboda zata samu lokacin tunanin mafita kafin ya dawo.

Bayan sati biyu babu abunda ya chanja daga cikin wahalar da Innar su take zabga musu sosai sukayi duhu suka kara ramewa gashi azumi ya kusa abun ba sauki se godiyan Allah, kullun suna waya da Dr Affan haka Hajiya ma kusan bayan kwana bibbiyu take kiransu, sosai take son yaran shiyasa ma ta damu da lamarinsu.

♣🌹♣☘♣🌻♣

Yau kusan satinsu d’aya agarin Bama bayan sun kawo kawarsu Karime gidan mijinta suka samu wani d’an rumfa suna kwana saboda neman Dr Affan.

Tun ranar da aka fara shagalin biki take zuba ido dan ganin zuwansa amma shuru kakeji kamar an shuka dusa bayan kwana biyar da zuwansu mijin Karime ya sallame su akan su koma gida anan kuma ta dage cewa ita kam seta hadu da rabin ranta zata iya tafiya gida, tun Ghaji na zuba mata ido har dai ta fara mata fada dan taga abun nata hauka ne ita kam ta gaji dan haka so take ta koma gida se dai tana tsoron barin kawar nata agarin da basu da dangi uwa bare na uba.

Yau dai ta riga ta kawo wuya gashi kud’in hannunsu na mota kawai ya rage musu yanzu kam ta yarda da abunda zuciyarta ke raya mata game da Hajja Hadiza tabbas ta haukace akan son wanda besan da zamanta ba domin wannan makauniyar soyayyar bata mata adalci ba, sedai tana tunani kila kuma akwai aljanu atare da ita dan haka suna komawa zata sanar da yayarta dan tasan abunda ya dace suyi in zasu fadawa iyayensu ne toh idan kuma zasu fara nema mata taimakon addua ne toh duk dai wanda yayar ta bada shawara akai shi zasuyi.

Kallonta ta sakeyi yanda ta rame ta wani yi duhu wai duk saboda soyayyar wani chan wai Affan da kila yama manta da ya ta6a haduwa da wata wai Hadiza “A gaskiya kinga kiyi hakuri mu koma gida idan yaso daga baya se mudawo idan mun samu dabaran daza muyiwa abokinsa kinga in mun samu address dinsa ai shikenan koh”.

Tunani ta farayi tabbas Ghaji ta kawo shawara kawai hakan zasuyi idan yaso daga baya sesu dawo “shikenan tunda haka kikace kuma wannan shawaran yamin dadi kinga se in dinga shigewa mjin yaya daga nan har mu samu biyan bukata kai gaskiya kanki naja kawata” ta fada tana rumgumeta dan murna.

Ita dai Ghaji dadi taji a cikin ranta dan zata samu biyan bukata tunda dai ta yarda zasu koma ai shikenan dama tayi tunanin cewa zatayi mata gardama amma tunda ta yarda cikin sauki komai ma zezo da sauki insha Allahu.

Satin Affan biyu da tafiya ya kirata ya sanar da ita cewan an turashi k’arin karatu achan k’asar saudiyya sosai taji ba dadi dan tanason ganin shi amma kuma seta mishi fatan alkairi, sosai yaji dadin adduar da tayi mishi harma da nuna cewa zatayi kewarsa ranar sunyi hira sosai ta kuma sake dashi kafin ta kwanta.

Sosai suke aiki ba hutu bare sassauci wataran had’uwa sukeyi su sha kukansu su godewa Allah suna masu yiwa Umma addu’a domin dama itace gatansu Allah gatansu to yanzu kuma basuda kowa daze jik’ansu se Allah wani lokaci har tunani sukeyi inama da sunw Hauwa’u domin ita kam ta huta da rayuwar kunci da garari.

A yau akatashi da azumi tun k’arfe uku Innarsu tace su tashi su gyara mata gida tare dayi musu abincin sahur kamar yanda tace haka sukayi kafin k’arfe hud’u har sun gama komai yau kam se da Noor ta d’iba musu abincin dan baza su iya zuwa su dafa wani ba Allah kuwa ya taimakesu har suka gama kwasan nasu Innarsu bata sauko ba seda suka isa chan 6angaren nasu sukaga an kunna wutan dinning halamin sun fito kenan shiga d’akinsu sukayi sukayi brush sukaci abinci sannan suka fara haraman sallah.

Bayan sun idar sukayi karatun alkur’ani kafin suka koma suka gyara inda su Inna suka 6ata seda Noor ta tabbatar sun gama komai kafin suka koma 6angarensu sukayi wanka sannan suka kwanta dan huta gajiya.

Karfe uku suka koma dan had’a abun bud’e baki se daf da sallar magriba suka kammala komai saku d’iba nasu kamar na d’azu yanzu ma sunyi sa’a domin har suka tafi bata fito ba se bayan isha’i suka dawo suka tattare gurin suka gyara sannan suka koma nasu 6angaren.

Kullun dai ba sauki haka rayuwa ya cigaba da tafiya da dadi da ba dadi kuma har zuwa lokacin babu aikin da aka rage musu kullun da salon abunda ake kara musu sa’a d’aya kawai sukayi sunacin me kyau su sha me kyau ba tare da sanin Innarsu ba dan ko kad’an  bata ta6a sanin cewa duk abunda suka dafa musu shi sukeci ba itadai tasan bazasu d’iba ba shiyasa ma bata damu da lura da suba.

♣🌹♣☘♣🌻♣

*🌻f¢т αвυʝα*

*♣gωαяιмρα*

Yau kinanin satinsu d’aya kenan da komawa Abuja sosai Yasmeen takejin dadin yanayin garin dan kuwa yayi matukar burge ta tunda aka haifeta sau d’aya ta ta6a zuwa kasar Nigeria kuma ko alokacin tana primary school ko kad’an yanayin k’asar be ta6a burgeta ba shiyasa bata sake sha’awar ace sunzo koda hutu bane se gashi yanzu sun dawo zaman har abada.

Zaune take acikin garden tana sauraron wak’ar 2pc na (Love wind) tana kada kai kamar kadangarewa k’aran wayar nata ne ya dawo da ita daga shaukin data shiga tsaki ta d’anja ganin cewa Ummy ce ke kiranta kome zata musu oho murmushi tayi data tuna da mayenta ko ina yake da be biyosu Abuja ba tashi tayi tashiga dan amsa kiran Ummy.

Tana shiga ta taras dasu duka acikin falo karasa wa tayi kusa da Ummy sannan ta zauna akusa da ita tana wani shigewa jikinta kamar mage, tsaki Ummy taja kafin ta m’ika mata makullin mota “gashi makullin motarki kafin Moses ya dawo se kifara kai kanki da kanki makaranta dama abunda kike so kenan ba” ta fada cike da takaici dan bata so ambata makullin mota ba saboda Yasmeen bata da hankali har yanzu.

Kallon Ummy tayi taga yanda ta 6ata rai kamar ance wani laifi ta aikata mara kyau murmushi tayi kafin tace aranta yau dai d’aya bari ta gwada faranta ran Ummy taga ya zatayi “Ummy ki ajiye kawai agurinki zan dinga bin driver dinsu Twinsis tunda duk hanya d’aya ne se ajiye ni idan yaso in Moses din ya dawo seya dinga kaini” ta fad’a tare da mikawa Ummy key din motar sosai Ummy ta kasa 6oye farin-cikinta akan abunda Yasmeen din tayi tabbas yanzu kam tanaga kila yarintar ta fara hankali ne dan inda ace ada ne bazata ta6a bata ba balke taso faranta mata, su kansu yayyin da kuma kannen nata sunyi matukar mamaki sosai domin basu tsammaci jin haka daga gurinta ba, farin-cikin data gani akan fuskar kowa shiya sanya ta nishad’i itama kuma jikinta yayi sanyi domin bata ta6a sanin cewa farin-cikin yan uwanta shine nata ba musanman ma Ummy tabbas tayi kuskure abaya kuma zatayi kokari gurin gyarawa.

Yau abun mamaki harda Yasmeen agurin had’a abun bud’e baki sosai kowa ya cika da mamaki kuma suna fatan Allah yasa ta dore a haka dan suna matukar son y’ar uwar tasu, bayan sun gama ita da Twinsis suka gyara kitchen din tsab sannan suka koma d’aki dan hutawa se da aka kira sallar magrib sannan tayi salla ta sauko danyin bude baki alokacin kowa ya hallara ita kawai ake jira yau kam sunyi komai cikin farin-ciki da nishadi wanda suke fata ya dore har abada shi kanshi Abby sosai yaji dadin sauyawar Yasmeen din yana fatan Allah ya kara hada kan iyalansa Adam kak yafi kowa jindadin lamarin dan ta haka ze samu abunda yake kwadayi da muradin samu da yardan Allah.

Mustapha kuwa ya koma gurin yaransa ne saboda yaji damuwarsu da kuma bukatarsu saboda baya son abunda ze takurawa musu ko kad’an saboda tausayinsu da yakeyi na rashin mahaifiyarsu a irin wannan shekarun domin yafi kowa sanin zafin rabuwa da iyaye dan ya dandana haka kafin ya samu farinciki a cikin rayuwarsa dan haka yake kokarin kyautata musu, har zuwa yanzu yanajin Yasmeen a cikin ransa kuma insha Allahu bayan azumi yake son komawa domin ya aiwatar da sauran abunda yake shirya mata. 

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE