YAR ALMAJIRA CHAPTER C
YAR ALMAJIRA CHAPTER C
Kwanaki sun shud’e watanni sun tafi kullun suna waya da Dr Affan da kuma Hajiya kuma kusan ko wani sati tana zuwa gidan domin duba su karshen zuwan da tayi kaya ta kawo musu kowa seti biyu atamfa da leshi dan suyi amfani dashi a salla tabbas basuda wani abun cewa a wannan mata se dai adduar fatan alkairi da ita da zuri’arta gaba d’aya domin kusan abunda mahaifiyar su zata musu kenan idan tana raye tabbas sun godewa ubangiji da wannan rahamar da yayi agaresu.
Wahala dai babu irin wanda Innarsu bata sanya su kullun burinta ita da y’arta shine suga cewar sun tagayyara ayyuka dai ba sauki se abunda yayi gaba sedai sun yarda cewa wahala bata kisa domin ba yanzu suka fara sha ba kuma sun yarda cewa komai yanada lokaci da yardan Allah wata rana se labari.
2
Kamar kullun yauma bayan sun gama aiki suka d’iba abun bude bakinsu suka wuce dashi 6angarensu bayan ansha ruwa sukayi hira sosai kafin suka tafi sallar asham a masallacin unguwarsu suna dawo wa motar mahaifinsu na shigowa saurin d’auke kai sukayi sannan suka shige 6angarensu sosai tayi mamakin ganin irin razanar da yayi sanda suka hada ido se dai kawai ta share sukayi kwanciyarsu.
Suna wuce wa kanshi ya fara sarawa tunani ne fal acikin kwakwalwarsa shin wad’annan ba ‘yayan sa bane shine abunda ya yita tambayar kansa da ker ua iya fitowa ya shiga gida yana tafiya yana bin bango saboda yanda kan shi ke matukar sarawa tabbas Akwai abunda yake faruwa.
Achan 6angaren Innarsu Mardiyya kuwa ashe duk taga komai daya faru hakan yasa hankalinta ya tashi d’aki ta shiga tayi ta neme-neme daga baya naga tayi wani murmushi alamar ta samu abunda take nema saurin had’a gaushi tayi amma bata zuba garin maganin ba tanajin motsin shigowar nasa ta zuba maganin duka sannan ta nufeshi tanayi mishi sannu da zuwa cikin mintinan da ba sufi biyu ba ya manta da abunda yake tunani harma ya denajin ciwon kan rungune ta yayi yana mata ya gida murmushi tayi ganin abunda ya faru tabbas Bokanta ya cika Hatsabibi.
Taimaka mishi tayi ya cire kayansa sannan ya shiga danyin wanka kafin kuma ta fito mishi da kayan barci mara nauyi sannan ta sauka ta nufi 6angarensu Noor dan yau ba se gobe ba dole ne subar mata gidanta kafin su lalata mata aiki, suna kwance dukansu har sun fara barci sukaji saukan bulala ta kowani 6angare da sauri suka tashi Noor ta janyosu zuwa bayanta ta tsaya agaba dan karesu sosai tayi mata duka sannan tace su kwashe kayansu subar gidan kuma karsu kara dawowa inba haka ba zata hallaka su subi uwarsu inda taje.
Tsoro ne ya kamasu da sukaji abunda tace kuma tabbas sun sani cewar zata aikata ba shiri suka fara tattara kayansu se da suka kwashe komai dai-dai yanda zasu iya kafin suka fita sunata kuka tabbas Innarsu batada imani amma basu ta6a sanin cewa rashin imanin nata yakai tayi musu haka ba.
Tafiya sukayi me nisa sannan suka nemi guri suka zauna dan hutawa seda suka gaji da zaman sannan suka cigaba da tafiya tasha suka nufa Allah yasosu har zuwa lokacin akwai motoci ba’a gama tafiya ba motar Chibok suka shiga ba tare da wani tunani ba duk da sunsan yanayin yanda garin yake da irin matsalolinsa amma sun gwammacu suje chan idan yaso suma subi mahaifiyarsu kawai, kudi ta biya musu suka shiga suna zubda hawaya na rabuwa da mahaifarsu.
Tafiya sukayi me nisan gaske se daf da azuba suka isa suna zuwa suka sauka a tasha ruwa suka saya da bredi cikin kudin da hajiyar Affan ta basu da kuma wanda shima ya basu suke adanawa bayan sunyi sahur sukayi alwayi sukayi nafila kafin suka jira kiran sallah har zuwa safiya suna zaune suna gyengyedi babu madafa sun rungume kayansu, suna cikin haka sukaji wani irin kara alamar harbin bindiga da sauri suka tashi hankali tashe sukabi ayarin da suka gani agabansu suna zabga gudu, gudu sukeyi sosai ba sassautawa kowa kawai wulla kafa yakeyi ba tare da sanin inda suka dosa ba seda sukayi tafiya me nisan gaske sannan suka ya da zango awani daji me cike da bishiyoyi da abubuwa daban-daban na shuke shuke.
♣🌹♣☘♣🌻♣
*🌻уσвє ѕтαтє*
*♣gαι∂αм ℓ/g*
Bayan sun koma gida aka tambayesu inda sukaje ba tare da shakka ba Hajja Hadiza ta sanar dasu dalilin rashin dawowarsu da wuri sosai Ghaji tayi mamakinta domin bata ta6a tsammanin cewa zata aikata hakanta shin da gaske Hajja Hadiza hauka tayi ko kuma soyayyace ta sauya mata tunani ta zama tamkar karamar mahaukaciya harda zata dubi idanun iyayensu ta gaya musu wannan zancen banzan sosai kowa ma yayi mamakin Hajja Hadiza domin basuyi tsammanin zata iya fada musu irin wannan maganar banzan ba wai taje neman saurayi.
Mamanta tsaban takaici seda tayi mata dukan tsiya amma ko hawaye batayu ba dan tariga da tayi nisa acikin soyayyar Affan kullun yanzu bata da aiki se kuka da fatan Allah ya bayyana mata shi dan itakam harga Allah inba Dr Affan ba se rigiya dan bazata iya rayuwa bashi ba sosai ta dage da addua acikin wannan wata me falala dan kawai ta samu Affan amatsayin mijinta koda ace baze sota va ita dai yanzu kawai ya aureta ya ajiyeta amatsayin baiwa.
Tun suna shareta har dai suka fara bata baki akan tayu hakuri ta fitar dashi daga ranta Ghaji ma tayi iya kokarinta amma abu yakici yaki cinyewa sosai ta chanja ta zama wata iri kamar ba ita ba duk wanda ya santa ada yanzu idan ya ganta seya tambayi ko lafiya take.
Musayar wutar sosai akayi tsakanin yan Boko Haram da sojoji hakan kuwa yayi sanadiyyar rasa rayuka da dama wasu kuma sunji rauni me muni yayinda wasu suka nausa cikin daji ba tare da sunsan inda zasuje ba dan ceton rayukansu tabbas an cutar da mutane da dama acikin garin Chibok.
+
Bayan komai ya lafa aka kwashi gawarwakin aka mik’asu ga danginsu wasu kuma da ba’a samu dangin nasu ba se kawai aka binnesu wadanda sukaji rauni kuma aka kaisu babban asibiti dake cikin garin Chibok se asannan kuma aka samu report din yan matan da aka kwashe sama da mutun saba’in da kuma samarin sama sa mutun talatin sosai sukayi bakin ciki da takaicin abunda ya faru amma sun bawa mutanen hakuri tare da alkawarin binciko musu yaransu aduk inda suke da yardan ubangiji hakan be haka mutane dayawa kuka ba domin basa tunanin cewa abune wanda ze iya yiyuwa.
Haka garin ya kasance tamkar anyi shara dan babu abunda zaka gani se bishiyoyi da dabbobi da suke shawagi akan hanya se kuma jefi-jefi motocin dake wucewa ta cikin garin, haka rayuwa ya kasance musu agarin Chibok kowa tsoron fita yakeyi alamura dayawa sun samu durkushewa saboda fargaba da yayi musu yawa kullun fatan da sukeyi shine ubangiji ya bayyanar musu da yaransu da kuma danginsu da suka gudu.
Yau kumanin satinsu biyu kenan acikin daji kullun sedai susha ruwan rafin dake cikin dajin sannan kuma suci ganyayyakin bishiyoyin dake kewaye dasu barci ma da ido d’aya sukeyi acikin ciyayi domin fargaban da suke ciki ahaka har aka gama azumi akayi bikin sallah, yau sun yanke shawaran komawa cikin gari domin sunsan komai ya lafa zuwa yanzun yayinda, kayansu suka kwashe sukabi hanya yayinda su Noor suka tsoro ta da wannan garin hakan yasa suka chanja hanya suka nufi Kudu dan zuwa wani garin daban.
STORY CONTINUES BELOW

Tafiya sukayi me nisan gaske tun sunayi suna hutawa harde suka yada zango awani dajin washe gari suka shiga cikin gari suna dardar saboda yanayin yanda sukaga garin shuru babu mutane, kowa hanyar gidansa ya nufa seda suka isa mutane suka fito dan tarbansu sosai sukayi murnan ganin juna daganan kowa ya bada labarin abunda ya faru kuka suka hadu sukayi domin tausayin kansu seda komai ya lafa sannan sukayi addua ga mamatan da kuma fatan Allah ya bawa marasa lafiya karfin jiki su kuma wadanda aka sace Allah ya bayyanar dasu.
A6angaren su Noor kuwa tafiyar kwana biyu sukayi kafin suka isa garin Biu sosai suka jigata saboda rashin abinci da kuma ruwa Mimi kuka kawai takeyi dan azaban da tasha ga kura yayi yawa ahanya kasancewar tana da asthma daker suka shawo kanta ta fara numfashi tare da ajiyar zuciya, cikin gari suka karasa inda Noor ta ciro kudin da tayi musu guziri dashi ta saya musu abinci da ruwan sha chan gefe suka zauna sunaci kamar wasu zakuna sau biyu Noor tana karo musu abincin kafin sukayi gyatsa alamar sun koshi hamdala sukayi sannan tace su zauna su jirata kar su tashi harse ta dawo, tafiya takeyi iska na kad’ata saboda wani irin rama da tayi dama ba auki bane da ita wasu mutane ta hango wanda take saran dillalai ne zuwa tayi suka gaisa sannan ta sanar dasu cewar ita bakuwace tana tare da kannenta suna bukatan gida dan karami me saukin kudi, kasancewar mutumin na Allah ne seyace taje tazo da kannen nata, bata dad’e ba ta dawo tare dasu bayan ya gama da abokan harkallar nasa seyace musu su biyoshi, tafiyar minti talatin sukayi kafin suka shiga wani karamin anguwa wanda daga yaninsa kasan cewa anguwar talakawa ne sosai wana suke matukar wahala, wani gida suka shiga me d’akuna uku ko wanne da karamin falo acikinsa se bandaki awaje da rumfar girki ako wani k’ofa, d’akin farko na wata mata ce da ita da mijinta se yaransu biyu k’anana se d’aki na biyu na wani mutun ne bashida mata shi kadai yake rayuwarsa baya shiga sabgar kowa d’akin karshe ya kaisu yace su zauna aciki ko wani wata zasu dinga bada dubu uku amma banda wannan watan se wani wata zasu fara biya sosai sukayi murna suka mishi godiya tambayarsa sukayi inda zasu samu katifa su saya da tabarma kwatance ya musu anan bayan layin nasu sannan ya musu sallama ya tafi, yana fita Noor ta nufi shagon daya kwatanta musu ta saya karamin katifa guda uku se tabarma babba guda daya se kuma shinkafa mudu hudu da taliyar murji mudu hudu se taliyar yara katan guda, ganyen zobo da aya mudu uku uku se kayan miya da kayan d’and’ano se kuma bokiti da tsinsiya duk dai wani abun bukata seda ta saya musu wanda ze musu wata kafin ya kare koma fiye da haka abun mamaki duka sayayyar da tayi dubu biyar kawa ta kashe dadi taji sosai dan akalla kudin jikinta ze dad’e musu kafin su fara sabawa da garin su san abunyi nan gaba, wani ke kwashe kaya ne ya diba mata ya kai mata gida sannan ta bashi naira dari se murna yake yana godiya, kannenta ta kira suka tayata shiga da kayan bayan sun share ko ina sun goge suka jera komai yanda ya kamata kafin suka nufi rijiya suka diba ruwa danyin wanka seda ko wacce tayi sannan Noor tayi nata kafin ta girka musu taliyar yara sukaci suka koshi sukayi ramakon sallama sannan suka kwanta.
♣🌹♣☘♣🌻♣
*🌻уσвє ѕтαтє*
*♣gαι∂αм ℓ/g*
Yau dadi gobe ba dadi wasu sun mutu wasu suna gadon asibiti wasu kuwa suna cikin koshin lafiya yayinda Hajja Hadiza ita sam-sam batasan wani matsayi take ciki ba ita dai ba mutuwa tayi ba amma batajin dadin duniyar ba rashin lafiya takeyi ba amma batajin dadin yanayin jikinta ba lafiya ne da itaba domin ta riga ta zube duk tayi zuru-zuru ido kawai kake gani babu wani kumari atare da ita kullun kwanan duniya setayi kuka kullun setayi sallar dare dan samun Dr Affan amatsayin mijinta haka zalika kullun tana zaune guri daya ba um ba a’a abinci ma se idan taga zata margaya shine take kokari taci dan burinta ta rayu da burin ranta har aka gama azumi bata dena sallar dare ba saboda kawai soyayya sosai iyayenta suke mamaki tabbas d’iyarsu ta sauya suma yanzu adduar samun dacewa kawai suke mata domin ta zama abun tausayi..
Kamar kullun yau ma bayan ta idar da sallar magriba ta zauna tana lazimi bayan ta idar ta kwanta tana hawayen tausayin rayuwarta tun tanayi ahankali har ta fara shesheke tana jan numfashi, Ghaji ce ta rungume ta tana tayata kuka seda sukayi me isarsu sannan suka fara ajiyar zuciya hakuri da kuma nasiha ta shiga yimata seda ta tabbatar ta natsu sannan ta dibo musu abinci sunaci tana kwantar mata da hankali tare da mata kirarin matar likita, hakan ya sanyaya ranta har ta fara murmushi shiyasa kullun se Ghaji tayi mata ahaka har suka gama cin abincin.
Ghaji da kanta ta hada mata ruwan wanka seda ta tabbatar ta shiga sannan ta gyara musu dakin ta tattare komai daya dace ta fito mata da kayanta me kyau dinkin riga da skirt me koren ganye bayan ta fito Ghaji da kanta ta shiyata harda mata kwalliya sosai tayi kyau duk da ramar da tayi kallon kanta tayi a madubi tayi murmushi tana ayyanawa aranta inama da ace Dr Affan dinta tayiwa kwalliya ganin zata shiga wani yanayi yasa Ghaji ta jata suka fita yau dai ba musu ta bita dan itama ta gaji da zaman guri d’aya kusan wata guda kullun tana daki in tafito se dai idan alwala zatayi sau biyu take wanka a sati ranar litinin da juma’a ita kanta yau taji sakat acikin ranta data shaki iska me dadi sun dade suna kewaye garin kafin suka koma gida iyayenta sunji dadi matuka sun kuma sanyawa Ghaji albarka domin y’ar halas ce kullun kokarinta shine ta sanya kawarta cikin farin-ciki tabbas ta cika kawa ta gari.
Satinsu hudu da kwanaki acikin garin Biu idan aka lissafa wata d’aya kenan cif da kwanaki, komai na tafiya dai-dai sedai kewar gida daya addabesu tabbas babu inda yafi gida dadi duk wanda yabar gida gida ya barshi musanman ma idan suka tuno mahaifiyarsu data tafi tabarsu cikin rayuwa mara dadi kullun se sunyi kuka da dare saboda tunanin rayuwa ita kanta Noor din kuka takeyi balle asamu me rarrashi.
Yau Habiba ta tashi da wani irin zazza6i me zafin gaske, chemist Noor taje ta sayo mata magani amma abun ba sauki hakan yasa suka yanke shawaran zuwa asibiti, koda sukaje emergency ward aka kaita dan abun yayi tsanani har sumewa takeyi.
Kusan awa uku suka d’auka azaune suna jinami daga wannan se wannan sukam sun rasa sukuni da walwala me tsawo acikin rayuwarsu abubuwa daban-daban suke 6ullowa yayin annashuwarsu, suna zaune sun zuba tagumi wani likita ya fito sannan ya musu alamar cewa su biyoshi, bayan sun shiga ofis din ya basu guri dan su zauna kafin ya fara musu bayanin cewa tana da hawan jini saboda yanda tasa damuwa a ranta har yayi kokarin haifar mata da zazza6i me zafin gaske dan haka zasu riketa zuwa wani lokaci harse sunga yanayin jikin nata.
Su Mimi dai ido kawai suka zuba mishi suna tunani kaka-kala Noor kuwa damuwarta yansa zata biya abubuwan da zasu bukata har zuwa sanda Habiba zata warke bayan ya gana koro bayanansa suka mishi godiya sannan Noor ta hada kansu suka koma gida, sauran kudinsu ta duba taga akalla ze kai dubu hamsin sabbin kayansu ta d’auki guda d’add’aya nata kuma guda biyu sannan ta fita dan kaiwa dillaliya wacce take bayan layinsu kaya ne masu kyau da tsada wanda Hajiyar Affan tayi musu akalla kowanne ze kai duba goma sha biyar amma haka dillaliya tayi musu tayin walakanci ta bada dubu talatin da biyar badan Noor taso ba ta kar6a dan dai batason musu da manya kuma ita ta kawo kanta bayan ta koma gida ta hada ya zama dubu tamanin dubu goma ta dauka ta kara musu wani sayayyar me yawan gaske kafin suka hada kayansu a cikin karamin ghana must go suka rufe kofansu da kwad’o sannan suka nufi asibiti da sauran kudin hannunsu.
Bayan sun isa suka nufi d’akin da aka basu me dauke da bandaki aciki se kuma karamin fridge dake gefen bango se doguwar kujeru guda biyu da karamin carpet ta gefe guda d’akin me kyau dashi tamkar ba asibiti ba, zama sukayi bayan sun ajiye kayansu agefe ita kuma Noor taje wajen likita dan sanar dashi dawowarsu bayan ta shiga ofis din suka gaisa sannan ta sanar mishi cewar sun dawo, kallon ta yayi na wasu mintina kafin yayi murmushi yace “Noor ko” kai ta girgiza alamar eh “shikenan zaki iya tafiya amma zuwa yamma ina son ganinki domin akwai abunda nakeson sani game daku” ya fada yana murmushi, ita dai toh kawai ta iya cewa sannan ta wuce zuwa dakinsu.
Bayan fitanta ya jima yana kallon kofar kafin yayi ajiyar zuciya yana me ayyana abubuwa daban-daban acikin zuciyarsa.
♣🌹♣☘♣🌻♣
*🌻вσяиσ ѕтαтє*
*♣вαмα ℓ/g*
Tun bayan tafiyansu mahaifinsu ya manta da babinsu acikin rayuwar sa saboda sabon aikin da Innarsu tasa akayi mata akansa sosai suke harka cikin kwanciyar hankali basuda wani damuwa kud’i kuwa se abunda ya karu kullun arzikinsu yana k’ara bunk’asa ta ko wani 6angare na cikin ahalinsu.
Bayan sati uku da tafiyan nasu Hajiya tazo ganinsu anan ta samu mumunar labarin cewa ai an neme su sama da kasa babusu babu labarinsu daga bakin me gadin gidansu, sosai Hajiya ta shiga damuwa dan har seda ta kwanta ciwo saboda yanda tasa abun aranta bashiri Affan ya dawo bayan Auta ta kira ta sanar dashi abunda yake faruwa shima dai tunda ya dawp ba shida lafiya kawai dauriya yakeyi bayan an sallamo Hajiya daga asibiti shima ya kwanta nashi ciwon kamar baze tashi ba seda aka hada da addua sannan ya dawo cikin hankalinsa daganan suka dukufa rokon Allah ya bayyanar dasu kuma ya karesu aduk inda suke.
♣🌹♣☘♣🌻♣
*🌻f¢т αвυʝα*
*♣gωαяιмρα*
Kamar a mafarki ta ganshi zaune saman mota yana doka murmushi tsaki tayi aranta kafin ta karasa ta bude bayan motar ta shiga ba tare data kulashi ba dan ita duk duniya babu wanda ta tsana sama dashi acikin rayuwarta, inda sabo ya riga ya saba da hali irin na Yasmeen shiyasa kawai shima ya shareta ya shiga motar ya tuka zuwa gidan, suna isa bata bari ya gama parking ba ta bude motar ta fita tana guna guni, dariya ne ya kufce mishi saboda yanda yaga ta tsuke fuska daga ganin shi, shikam ya rasa dalilin tsanar da Yasmeen take mishi key din motar ya cire ya shige 6angarensa yana tunani kala-kala gameda abubuwan dake faruwa dashi akan karamar yarinya irin Yasmeen.
A6angaren Yasmeen kuwa tana shiga ta nufi dakin Mammy as usual seda ta gaisheta ta wuce 6angarensu da twins ta fara haduwa suka gaishe da ita ta amsa ba yabo ba fallasa kafin ta nufi dakinta kayam jikinta ta cire ta shiga wanka bayan ta fito ta shirya cikin doguwar riga na atamfa me kalar kore da ratsin fari sosai kayan yayi mata kyau turare ta fesa kala daban-daban seda ta gamsu dan kanta ta fita ta nufi dinning bayan ta gamacin abinci ta koma d’akinta ta d’auki doguwar hijibi me hannu ta saka sannan ta d’au purse dinta da wayanta ta nufi d’akin Mammy zama tayi kusa da ita kafin tace “Mammy please inason zuwa shopping” shafa kanta Mammy tayi kafin tace shikenan ba damuwa ta dauki kudi a safe sannan idan taje karta dade saboda yau jumm’a karamar rana yanzu se yamma yayi, godiya tayi kafin ta fita ta aika a kira mata Moses, shi kuwa tunda yaji kiranta yasan ta shirya mishi wani abun shiyasa murmushi yayi ya dau key sannan ya fita yaje ya sameta bayan ya tada mortar ya bude mata gidan baya sannan ya shiga mazaunin dreba ya fita daga cikin gidan tafiya sukayi me nisa sannan tace mishi ya kaita Shoprite na hanyar Airport ba tare daya tanka mata ba yayi reverse suka d’auki hanyar Airports din, murmushin mugunta tayi sannan tasa earpiece ta kwanta.
Kamar yanda yace ta sameshi da yamma hakan akayi bayan an idar da sallar magriba ta nufi ofis dinshi sallama tayi kafin tashiga, zaune ta sameshi akan kujeran ofishin yana daddanna na’ura me kwakwalwa seda ya karasa aikin da yakeyi sannan ya rufe ya juyo gareta, gaisheshi tayi ya amsa da fara’arsa kafin ya shigs tambayar ta ko shin Habiba ta farka ta amsa da a’a shiru ne ya biyo baya kafin daga bisani yace “shin bakuda iyaye ne ko wani babba ko wasu yan uwa acikin gidanku da zasu zauna da Habiba se ku yaran gidan” kamar bazata amsashi ba se daga bisani tace “bamuda kowa kuma bamuda komai iya mu biyar muke rayuwa acikin duniyar mu” tana gama fada ta tashi ta fita tana share hawaye seda ta tabbatar babu wani d’an guntun hawaye atattare da fuskarta sannan ta nufi cikin d’akinsu.
+
A6angaren Dr Aliyu kuwa ya kasance cikin damuwa bisa kalmomin data furta gareshi sannan ta fita cikin wani irin yanayi tabbas ko batace komai ba akwai alamar rashin kwanciyar hankali da natsuwar zuciya atare dasu afili ya furta “inason saninki Noor da duk wani abunda ya danganci rayuwarki” wani irin abu yakeji game da yarinyar da har yakejin cewa baze iya rabuwa da ita ba tabbas wannan alamarin ba komai bane face ‘SO’ “SO” ya sake fada afili saboda yanda kalmar ta bugi zuciyarsa gumi ya sharce dan ganin kamar bazeyi nasara ba kafin ya kwashi kayan aikinsa dan zuwa duba patient dinsa.
D’akinsu Noor shine d’aki na karshe daya shiga bayan sallar isha’i lokacin duk sunyi barci illa Noor data zabga tagumi tana tunanin rayuwarsu har ya gama abunda zeyi ma batasan ya shigo ba hakan yasa daze fita ya d’auki hoton ta, flash din daya shiga idonta ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi murmushi ya sakar mata sannan ya fita ita kuma ta bishi da kallon mamaki kafin ta tashi ta tofe kannenta da addua kamar yanda ta saba sannan ta kwanta.
Satinsu biyu cif a asibiti sannan Habiba ta samu sauki sosai duk tsawon kwanakinnan wasan 6uya Noor takeyi dan batason abunda ze had’ata da Dr Aliyu shi kuwa sam bayajin dadin hakan shiyasa ma koda aka basu sallama yaji ba dadi dan yasan baze ringa ganinsu kamar da ba saboda koda ace yana zuwa gidansu akai akai ba lallai ne ya ringa ganinsu sanda yaso ba kamar acikin asibiti yaso ya maidasu gida amma Noor taki yarda saboda ba address din gaskiya ta bashi ba shiyasa bataso ya kaisu gida shi kuma be kawo komai acikin ranshi ba yayi musu fatan alkairi tare da alkawarin zuwa dubadu da yardan ubangiji.
Kwanaki sunja watanni sun shud’e yau kimanin watansu shida kenan acikin garin Biu ba laifi sunji dadin zaman garin saboda kowa harkarsa yakeyi babu ruwan wani da wani musanman cikin gidansu da kuma cikin unguwarsu, Ayau sun tashi basuda ko kwayar shinkafa acikin gidan Noor tasha gwada sana’a amma abun yaki yiyuwa domin babu wani riba hakan yasa ta hakura da sana’ar badan taso ba abubuwa sun hadu sun mats yawa ga tunanin inda zasu samu abinci da kuma inda zasu samu kud’in magani saboda ciwon Habiba daya tashi kasancewar tana d’auke da ciwon zuciya kamar mahaifiyarsu tun abun baya wahalar da ita har ya kai munzalin da bata iya tashi sedai komai ayi mata gabaki d’aya yaran suna cikin damuwa duk sun k’ara ramewa sun lalace tamkar k’ashi da rai na yau kam abun ba’a cewa komai domin aman jini kawai takeyi tun safe ganin dai babu wani mafita yasa Noor fita dan neman taimako.
Tunda ta fita take yawo a gari babu wani taimako data samu karshe dai ta yanke shawaran bin layin almajirai hakan kuwa akayi se kusan bayan awa uku ta samu taimako na naira dari biyar daganan tayi sauri ta nufi shago ta shayi garin kwaki na dari da sugar na hamsin sauri-sauri gudu-gudu ta nufi hanyar gida sedai me tana zuwa ta samu mutane cike akofar gidan kamar gidan kallon kwallon k’afa daker ta samu ta kusa cikin mutanen gabanta na tsananta fad’uwa tana zuwa ta samu Mimi da Aminatu zaune agaban gawawwaki guda biyar zuciyarta ne ya buga da karfin gaske daganan kuma ta fad’i agurin bata ko motsi.
♣🌹♣☘♣🌻♣
*🌻f¢т αвυʝα*
*♣gωαяιмρα*
Tunda suka fita suke yawo acikin gari domin duk inda tace yaje se sun kusan isa zatace ta fasa daman yasan za’ayi haka shiyasa be nuna damuwa ba ko kadan domin shi dadi ma yaji aransa saboda ya samu damar kallon sahibarsa cikin kwanciyar hankali, se daf da magriba ta shiga Oasis ta sayi snacks masu yawa sannan tace yabi ta Sahad store anan ta sayi inner wears da kuma wasu kayan make up nata danasu twins.
Ana kiran sallar isha’i suka shiga gida dama ta kashe wayanta dan kar Mammy ta isheta da kira akan ta dawo gida amota ta bar kayan seda ta shiga ta aiki me aikinsu taje ta kwaso kayan daga cikin motar, koda ta shiga direct d’akinta ta nufa tayi sallah seda ta idar sannan taje dinning taci abinci kafin ta kwashi kayan ta nufi d’akin Mammy dasu, sosai Mammy tayi mata fada akan dad’ewar da tayi awaje amatsayinta na d’iya mace kuma musulma hakuri ta bawa Mammy kafin ta nuna mata kayan sosai Mammy taji dadin abunda tayi na sayawa kannenta daganan tayita sa musu albarka, kwashe kayan tayi ta nufi 6angarensu seda ta bawa twins nasu kafin ta nufi d’akinta sosai sukaji dadin sayayyar da tayi musu domin basuyi tsammani ba duk da madai yanzu ta sauya hali sosai ta zama wata sabuwar Yasmeen din.
Moses ma d’aki ya nufa yayi alwala yayi salla yayi wanka sannan yaci abinci kafin ya kira yaranshi sukasha hira kowa na bashi labarin abunda ya faru bayan tafiyarsa sosai yaji dadin magana dasu daga bisani ya musu adduo’i sannan sukayi sallama ya kwanta yana tunanin rayuwarsa ada da yanda aka samu sauyi me yawa acikinta har ila yau baze dena addua ga bayin Allah da suka taimaka wa rayuwarsa ba tabbas sud’in daban suke acikin mutane domin sanda wasu suke kyamatarsa su kuma sukayi na’am dashi tare da bashi kyakyawar rayuwa.
Bata tashi farkawa ba sai bayan da aka idar da sallar ishai a lokacin an riga an kai mamatan gidansu na gaskiya, tana farkawa taga mutane da yawa acikin d’akin nasu kowa nayi musu kallon tausayi fatanta ace mafarki takeyi amma ganin yawan mutanen dake zagaye dasu ya tabbatar mata da cewa ba mafarki bane gefenta ta kalla taga Mimi na barci Aminatu kuma hawaye take sharewa akai-akai ajiyar zuciya tayi kafin ta fara nata kukan mecin rai babu wanda tayi kokarin hanata a cikin mutanen dake kewaye dasu sai da taji nauyin dake zuciyarta ya yaye sannan ta tsagaita ta tashi ta wanko fuskarta tare da d’auro alwala.
Bayan ta idar da salla tayiwa mamatan addua duk da cewa batasan ko suwaye sauran mutanen da aka rasa ba, wata mata ce ta fara mata gaisuwa kafin sauran suka mara mata baya ita dai kawai d’auriya takeyi amma batason taji ana mata gaisuwar rasuwa domin abubuwa da yawa ke dawowa cikin kwakwalwarta, bayan sun gama gaisuwan suka musu sallama suka tafi sai a sannan ta samu natsuwa.
Kallon Aminatu tayi wacce tayi zuru tana kallonta kafin tace “shin Aminatu menene ya faru bayan tafiya ta?” Sai da ta d’auki kusan mintina biyar kafin tace “Bayan fitan ki ciwon Ya Habiba ya sake tashi kafin awa biyu da tafiyar ki Allah ya k’ar6i ranta” shuru ta sakeyi na wasu mintina sannan ta cigaba da cewa “Shine Ya Nusaiba ta aike mu akan muje mu nemoki dan ayi mata sutura seda mukayi kuka muka godewa Allah sannan muka fita dan zuwa sanar dake bayan awa d’aya da fitan mu muka dawo gida dan sanarda ita cewa bamu ganki ba, muna zuwa mukaci karo da mutane a kofar gidan wasu kuma a cikin gidan suna kokarin 6alla k’ofar d’akin Mama Silifa d’akin mu muka shiga muka taras da Ya Habiba a rufe yanda muka barta ita kuma Ya Nusaiba bata d’akin hakan yasa muka fito dan duba ta band’aki muka kwankwasa amma shuru da muka bud’e mu kaga ba kowa a ciki chan kuma da aka samu bud’e d’akin Mama Silifa aka fito da gawawwaki anan muka tsinci nata, tunanin mu shine taya hakan ta faru meya kaita d’akin su?” ta fad’a hawaye na tsere a fuskar ta.
STORY CONTINUES BELOW

Ajiyar zuciya Noor tayi cike da alajabi sai dai bata da ja akan hukuncin ubangiji janyo Aminatu tayi zuwa jikinta tana rarrashinta kukan da takeyi ne ya tashi Mimi daga barci ganin su a hakan yasa itama ta fashe da nata kukan tare da fadawa jikin Noor sai da sukayi me isarsu kafin sukayi shuru sai a sannan Mimi take sanar dasu abunda Malam Iliya me shagon jikin gidan su yake cewa “Ya Noor ashe taje taimakonsu ne abun ya ritsa da ita a k’ofan falonsu” kallon ta Noor tayi sannan tace “kamar ya taimakon su tajeyi abun ya ritsa da ita?”.
“Lokacin da kika suma aka kai ki d’aki na fito waje dan inyi alwala shine naji yana cewa ai ya shigo bahaya ya fara jiyo ihu sai dai beyi tunanin wani abu bane sai da yaji ihun ya fara yawa shine yayi saurin fitowa daga band’akin a lokacin ita kuma Ya Nusaiba tana kokarin shiga k’ofan falon su da yake bud’e ga hayaki kuma na fitowa daga cikin 6angaren nasu da sauri ya fita dan sanar da jama’a ana bukatar taimako kafin ya dawo itama k’ofar ya rufe da ita sabofa wutan daya fara kewaye d’akin sunyi iya kokarinsu dan 6alla k’ofar amma haka Allah yaso” ta kareshe da hawaye masu zafi akan fuskarta.
Rungume su tayi suka sake fashewa da kuka Mimi ta sake cewa “mu kuma haka zamu rinka mutawa cikin garari ba cikin dangin mu ba Ya Noor?” da sauri Noor ta rufe mata baki sannan tace “duk abunda ya faru da bawa Allah yana sane da shi kuma tun rangini ran zane dan haka karki sake fad’in irin wannan maganar domin kamar kina jayayya da hukuncin ubangiji ne duk abunda ya samu bawa anaso ya kasance me hakuri da juriya da kuma tawakkali Allah baya barin wani dan wani yaji dadi kowa da yanda Allah ya tsara mishi rayuwar sa dan haka mu cigaba da hakuri mu kuma gode wa Allah da irin ni’imar da yayiwa rayuwar mu ai ada ba haka muke ba dan yanzu Allah ya jarabce mu semu butunce mishi a’a kannena ba’a haka kuma Umma kafin ta rasu kullun nasihar da take mana kenan dan haka mu rinka kiyaye harshen mu Allah kuma ya ganar da mahaifin mu da sauran dangin mu” Amin su kace a tare suna farin cikin samu yar uwa kamar Noor a cikin rayuwar su wani 6angare kuma suna alajabin adduar da tayiwa mahaifin su ayau domin bata ta6a furta makamancin hakan ba, sake lafewa sukayi ajikinta har barci ya kwashesu
Tun ranar da suka koma gida ya shirya zuwa kai musu ziyara sayayya yayi musu na kayan kwad’ayi sosai yaci kwalliya dan kawai ya burge Noor sai dai kash yana zuwa ya samu ashe adireshin bana gaskiya bane sosai ranshi ya 6aci domin bai jidadin abunda suka mishi ba yasha yawo harya gaji kafin ya koma gida tun daga ranar kullun sai yabi hanya dan nemansu amma har zuwa yanzu babu labarin su har kuka yayi a 6oye saboda damuwa da yayi mishi yawa tabbas yana son Noor kuma baze so ya rasata ba har abada.
Dr Aliyu d’a ne ga wani hamshakin me kud’i a cikin garin biu, yayi karatun sa a madina inda ya karanci fannin kula da lafiya su hudu iyayensu suka haifa shine babba sannan Alisha da Azizah tagwaye sai kuma auta Ashraf Dr Aliyu sun tashi cikin gata da kuma tarbiyya domin iyayen su nagartattun mutane ne babu wasa a cikin lamarin su komai suna kokarin ginawa bisa tafarkin addinin islama hakan yasa mutane dayawa ke sha’awar zuri’arsu.
♣🌹♣☘♣🌻♣
*🌻уσвє ѕтαтє*
*♣gαι∂αм ℓ/g*
Zuwa yanzu Hajja Hadiza ta sake sosai har ta fara shiga cikin mutane sai dai ta kasa zama yanda take ada saboda yanayin data tsinci kanta, yau garin ruwa akayi sosai ko ina iska ke kad’awa gwanin ban sha’awa zama tayi a bakin rijiya tana shan iska yayinda kowa ke cikin d’aki kusan awa d’aya kenan take zaune ba tada alamun tashi, Ghaji ce ta shigo ta tsaya daga bakin k’ofa tana kallon ta murmushi tayi dan jindadin yanayin dats samu kawarta cikin nishad’i karasawa tayi kusa da ita sannan tace “albishirinki kawata ta kaina matar likita” dariya ne ya kufce mata saboda abunda Ghaji ta fad’a duk da cewa taji dadin hakan amma kuma ai wannan ta riga ta maida shi mafarki domin baze ta6a yiyuwa ba.
“Goro kuma fari kal sosai sosai” Ta fada tana murmushi “Matar yayan Umma zata taho hutu daga Bama kinsan ai wannan kawun nawa daya rasu da dad’ewa sai dai dake bama zumunci bamu san juna sosai ba har gwara matar tana yawan kawo mana ziyara amma yaranta bamu ta6a haduwa dasu ba kuma tace idan tazo tare zamu koma da ita” ta fada tana taka rawa “kamanya tare zaku koma kina nufin zaki tafi ki barni a garin Gaidam kenan duk amincin dake tsakanin mu Ghaji” ta karashe kamar zatayi kuka zungurin ta tayi sannan tace “ba kiji nace zamu koma tare ma’ana nida ke ba na fada mata in dai tanaso in bita sai dai muje dake kuma ta amince tace zata samu a boko wayyo Allah dadi kawata”.
Dadi ne ya kama Hajja Hadiza da taji cewa tare zasu koma kila ma ta sake had’uwa da masoyinta daganan su fara soyayya se kuma wani zuciya yace mata gwara ta fitar da shi daga ranta domin ba lailai ne ya sota ba kuma ba lailai ne ta kasance cikin jerin matan da yake so ba dan haka gwara ta saukaka wa ranta ta hanyar cire shi baki d’aya duk da cewa abune me matukar wahala tashi tayi ta rungumi Ghaji suka hau tsalle dan murna seda Malam ya fito wato mahaifin Hajja Hadiza ya tsawatar musu kafin suka tsagaita tare da bashi labarin abunda ya faru shima ya taya su murna domin rashin kud’i yasa karatunsu ya tsaya.
Basu kara sati biyu a cikin garin Biu ba suka sake tattare kayansu bayan Noor ta saida na saidawa sukayi guzirin kud’in mota zuwa garin Kano acikin Rigiyar Lemo sukayi masauki.
Kwanansu biyu suna gararamba a cikin unguwa babu madafa daganan suka samu wani uncompleted building inda wasu marabata sukayi mafaka suma suka zauna.
Bayan sati biyu da zuwansu kudin hannun Noor ya kare hakan yasa ta fara zuwa bara gida gida kamar yanda taga wasu yan mata sunayi, wataran su samu wataran kuma haka suke kwana su yini suna shan ruwa daga wani famfo dake cikin masallacin bayan layinsu.
Sosai sukayi kuka saboda yanayin da Noor ta jefa kanta dan kawai taga cewar basu rasa komai ba sunci sun sha koda kuwa ita zata kwana tana shan ruwa hakan yana matukar ta6a zuciyarsu sai dai ba daman musu da ita, a kullun adduarsu shine Allah ya kawo musu mafita kuma ya karesu daga dukkan sharri.
Yau watansu d’aya kenan a cikin garin Kano a sosai suke cikin damuwa saboda wahalhalun da suke sha ga sauro ga rashin makwanci mai kyau, suna zaune tare da wata mata wacce ake kira baba Azumi dattijuwa ce me matukar kirki tana da ciwon ido hakan yasa take cikin harkar bara dan ta taimaki kanta da kanta domin bata da kowa sai Allah mijinta ya dade da rasuwa kuma Allah bai azurtasu da samun haihuwa ba.
Zaune suke suna dan ta6a hira jefi jefi kasancewar ranar lahadi Noor bata fita ko ina tana zama tare da kannenta dan suyi hira ta sanyasu farin-ciki saboda batason ganin damuwa a tare dasu “Noor nace ba, ko zaki zaga wajen tasi’u me garuwa kice ya taimaka yazo inason ganinshi?” ba tare da wani jinkiri ba ta tashi tana cewa “bari in duba Allah yasa yana nan din” Tana zuwa kuwa tayi sa’ar samunshi dan kuwa yana kokarin rufe shagon da alama fita zeyi “Malam Tasi’u barka da rana ya ayyuka, dama baba azumi ce tace idan baka komai dan Allah in kira ka” washe hakora yayi sannan yace “lafiya kalau Fadimatu ai kuwa kinyi sa’a dan ina shirin komawa gida ne ya kokari kuma?” ya fada sanda suka jere zuwa mafakarsu Noor din “lafiya mun gode Allah” ta fada daidai sanda suka karasa cikin 6angaren da suke kwana.
“Sannu da hutawa barka da yamma Baba Azumi” ya fada yana kokarin zama a gefen ginin daya fara kakka6ewa, “Yauwa Tasi’u sannu ya kokari yi hakuri na tasoka daga gun sana’a” murmushi me sauti yayi kafin yace “babu komai Baba Azumi ai ke uwace matsayinki ya kai” sosai taji dadin kalamansa kafin ta daura da cewa “dama so nake ka sama mana dangun zama koda karamar d’aki ne nida yan yarana dan gurinnan yana da hatsari gaskiya koya ka gani” farin ciki yaji aransa da tayi wannan maganar dan shima ya rasa ta inda ze farane shiyasa tunda shima dan shagon nashi karami ne kuma a ciki yake kwana inba haka ba daya taimaka musu “gaskiya naji dadin wannan batu Baba Azumi kuma insha Allah zanyi kokarin bincikawa zuwa yamma zakiji yanda ake ciki” godiya tayi mishi sannan ya musu sallama ya tafi.
Kamar yanda yace da yamma zai dawo hakan kuwa akayi sai gashi ya dawo da kyakyawar labari akan cewan ya samu wani gidan haya a cikin unguwar sai dai kuma bandakin nasu na gidan yawa ne “bakomai in dai mun samu gurin kwana ai shikenan Tasi’u” shine abunda Baba Azumi ta fada sanda ya sanar da ita cewar ya samu gidan, kud’i ta bashi naira dubu goma wanda ta dad’e tana tarawa bayan ya biya kud’in dubu shida sai ya saya musu tabarma babba guda d’aya da kuma katifa wanda zai d’auki mutane biyu guda biyu kafin ya kara da kud’insa gurin saya musu filo da kuma wasu sayayya dan kadan dai dai karfinsa sannan ya rakasu har gidan cikin jindadi domin gimbiyarsa zata samu gurin kwana mai kyau.
Sosai suka yaba da tsarin yanda ya gyara musu d’akin komai dai-dai ga kuma dan kayan abinci daua saya musu godiya sukayi mishi kafin ya musu sallama ya tafi bayan sunyi sallan magriba suka shiga d’akunan cikin gidan dan sauke hakk’in makwabtaka wasu sun musu kar6a mai kyau wasu kuma sunyi kamar basu gansu ba yayinda wasu suka musu rashin mutunci hakan yasa ba shiri suka koma d’akinsu bayan sunyi alwala dan gabatar da sallan isha’i.
Bredi da shayi suka sha wanda Noor ta sayo musu a gurin Mai shayi bayan sunci sun koshi sukayi godiya a Baba Azumi na taimakon da tayi musu da kuma kokarin da takeyi a kansu har kuka sai da suka mata daker ta samu ta rarrashe su sannan suka dasa babin hira sun dad’e suna ta labari kafin Baba tace su kwanta addua sukayi sannan suka kwanta.
♣🌹♣☘♣🌻♣
*🌻вσяиσ ѕтαтє*
*♣вαмα ℓ/g*
“Hadiza wai sai yaushe zaki fito mu tafi ne kinga fa lokaci na kurewa dan Allah kiyi sauri” Ghaji ta fada tana kallon agogo.
Tsaki Auta tayi sannan tace “komai dai sai ta 6ata mana lokaci yanzu yaushe zamu tafi har mu dawo tabbas yanzu sai bayan magriba zamu dawo dan Biyar saura yan mintina”.
Sai da ta gama shafe shafenta sannan ta fito tana had’e hannayenta guri d’aya alamar ban hakuri harara kawai suka aika mata sannan sukayi ficewarsu tare da yiwa Hajiya sallama, bayansu tabi ta rumgumesu tare tana basu hakuri daker ta samu suka hakura kafin suka shiga mota Auta ta d’auki hanyar Bint Beauty salon dasu inda zasuyi gyaran gashi da lalle saboda bikin kawar Hajiya da za’ayi.
Tafiyan minti talatin ya kaisu Bint Beauty Salon inda akayi wani babban signboard me dauke da BB Salon sosai gurin ya k’awatu da abubuwa masu kyau da tsada da gani kasan cewa ba gurin k’ananan mutane bane na manyan yara ne.
K’inanin watansu d’aya kenan a cikin garin Bama a gidan Hajiya mamansu Dr Affan da Afnan wato Autar Hajiya bayan zuwansu hutu garin Gaidam suka taho dasu kamar yanda Hajiya tayi alkawari ai kuwa iyayen su sunji dadin abunda Hajiyar tayi.
Tun bayan zuwansu suka saba da Autar Hajiya sai ya zamana itama ta samu yan uwa wadanda zata iya nunawa tace nata ne, lokacin da sukazo Dr Affan yana kasar london dan wani aiki da aka turashi kuma har zuwa yanzu bai dawo ba sai dai ya shaida musu kila zuwa sati mai zuwa zai dira a kasar Nigeria a garin Gaidam kafin ya karaso Bama.
Haka rayuwa ya cigaba da gudana yau dadi gobe ak’asin hakan wataran su samu mai kyau wataran ak’asinsa yanzu ba kullun Noor take fita bara ba sai bayan kwana bibbiyu saboda duk randa ta fita tana samun abunda zai musu kwana biyu kuma shima Tasi’u yana musu kokari sosai dai-dai karfinsa.
+
Tsakaninsu da mutanen gidan kuwa gaisuwa ne kawai shima sai idan sunzo daf da juna, shiyasa suke zaune lafiya agefensu saboda basu nuna sun damu da mutanen dake zaune a cikin gidan ba balle su walakantasu, Ayanzu Noor ta fara fahimtar manufar Tasi’u akanta sai dai bata bada fuska ba saboda tana son kara fahimtar ko shi din waye.
Sosai sukejin dadin garin kuma suka samu natsuwa a cikin ransu musanman kasancewar Baba Azumi a tare dasu tabbas sun samu wani 6angare da suka rasa a cikin rayuwarsu domin duk wani kulawa tana kokarin basu tamkar y’ay’an cikinta, a yanzu Noor ta haddace Izifi goma su Mimi kuma sunyi Izifi Biyar daga cikin littafi me tsarki wanda Baba Azumi ke yawan biya musu kasancewarta mahaddaciyar alkurani.
Watansu takwas cif acikin garin Kanon dabo kullun suna kara fahimtar rayuwa a kullun wani darasi suke d’auka na musanman saboda yanda rayuwa tazo musu, zuwa yanzu Tasi’u ya kasa hakuri da barin soyayyar Noor a cikin ransa hakan yasa yaje har gida ya samu Baba Azumi akan yana son ya fara zuwa zance gurin Noor idan har ta amince ba tare da wani damuwa ba tayi murmushi dan dama tasan za’a rina kafin tace mishi zai iya zuwa bayan kwana biyu idan tayi magana da d’iyar nata domin baza ta tauye mata hakkin ba.
Bayan tafiyan shi da yamma Baba Azumi ta kira Noor sannan ta shaida mata yanda sukayi da Tasi’u, Noor ba tayi mamaki ba dan dama ta dade da sanin cewa yana ra’ayinta “Baba na bar miki za6i duk abunda kika yanke dai-dai ne nasan ba zaki za6amin abunda zai cutar dani ba” wannan amsar shi ya kara wata sabuwar kaunar yaran a cikin zuciyar Baba Azumi tabbas tasan ko wacece mahaifiyarsu mutuniyar kirki ce kuma ta musu tarbiyya mai kyau ta kuma d’aura su a hanya madaidaiciya “Allah ya miki albarka ya kuma baki y’ay’a da zasu miki fiyeda abunda kikamin” dadi ne ya kama Noor da taji irin adduo’in da Baba take zuba mata domin bata da wani buri daya wuce taji ana sanya mata albarka ita da kannenta.
Washe gari Baba Azumi ta tara su baki d’aya ta shaida musu cewar ta amince da tarayyan Noor da Tasi’u saboda sanin ko shi din waye da kuma sanin cewa ko bayan ranta zai rikesu da amana tamkar ita din tana raye, sunji dadin wannan bayanin da tayi kuma suka mata godiya bisa jajircewa da takeyi na ganin cewan sun samu rayuwa me inganci, Noor ma taji dadi da Baba Azumi ta amince dan kuwa ko ba komai Tasi’u yayi musu abunda ya dace su saka mishi da duk wani alkairi idan har suna da hali.
Bayan kwana biyi Tasi’u ya dawo kuma ya samu kyakyawar labarin da bai ta6a tsammani ba domin shi a tunaninsa Noor ba zata amince dashi ba “inaso ka turo iyayenka bayan sati biyu domin ayi muku baiko saboda bana son abun ya d’auki lokaci me tsawo domin nima in samu natsuwa a raina” sosai yaji dadin hakan da Baba Azumi ta fad’a kuma ya shaida mata cewan dama ya riga ya sanar da kawunsa akan yana neman wata yarinya idan aka dace zai sanar dasu sannan kuma yana neman alfarma Noor ta dena zuwa gurin bara insha Allahu ba za’a rasa abunda za’aci ba da yardan ubangiji, hakan daya fad’a ya kara tabbatar mata da cewa da gaske yake babu wasa a cikin lamarin, bayan tafiyarsa Baba Azumi ta sanar dasu yanda sukayi suma kuma sunji dadi sosai.
Tasi’u maraya ne ya taso a hannun kanin mahaifin sa mutun mai matukar kirki da dattako kuma Allah bai azurta shi da samun haihuwa ba hakan yasa suka dauki duk wani soyayya shida mai dakinsa suka daura mishi, tun yana karami suke kula dashi har zuwa yanzu daya girma basu fasa dawainiya dashi ba shiyasa ya bude dan karamin shago na saida kayan bukatu na yau da kullun dan taimakonsu baki daya sannan wani lokaci yana aikin garuwa shiyasa ake kiran shi da dan garuwa.
♣🌹♣☘♣🌻♣
*🌻f¢т αвυʝα*
*♣gωαяιмρα*
A kullin kwanan duniya soyayyar Yasmeen ke kara azalzalar zuciyarsa ko wani second ko wani minti ko wani awa sosai yakejin kaunarta a ransa ya rasa hayyar da zaiyi ya samu soyayyarta domin bata bada fuska balle ya samu damar sanin hanyar da zai fara tunkarar ta tabbas wannan soyayyar 6angare d’aya ya fara karya mishi zuciya ada yayi tunanin cewa zata fad’a soyayyarsa cikin kankanin lokaci sai dai kuma abun ashe ba zai tafi mishi yanda yake so ba dole sai ya kara hakuri kafin ya samu biyan bukata hakan yasa duk da cewa kwanakin aikin sa a gidan ya kare hakan bai sa yayi yunkurin tafiya gida ba fatan shi Allah ya ba shi nasara kafin lokacin da zai kara tafiya wani aikin.
A fannin Yasmeen kuwa babu wani halittar data tsana a duniya sama da shi kullun kara tsanarsa takeyi musanman yanda yake mata shishigi cikin lamarinta balle yanzu da ya zama cewa ko ina za taje dole ne sai taje da shi sam-sam babu kwanciyar hankali da natsuwa a tare da ita sai dai kuma tayi damaran yi mishin rashin mutunci kala daban-daban har zuwa lokacin da zai gaji ya kwashi kayan shi ya gudu daga gidan.
“Aure nufin Allah ne kuma insha Allah idan lokacin kara auren nawa yayi tabbas zanyi koda ace ban shirya ba wallahi nima nagaji da zama hakan sai dai kuma akwai wani abunda nakeyi shiyasa amma kiyi hakuri da yardan ubangiji nan bada dad’ewa ba zan kawo miki kyakyawar labari”
“Idan hakan ya kasance zanfi kowa jindadi domin aure shine cikar kamalar ko wani dan adam zaka iya tafiya shikenan na baka lokaci amma da zaran ya wuce babu wani zance naka da zan kar6a sai dai kaga zahiri, Allah ya maka albarka yasa ka gama da duniya lafiya”.
Maganganun da sukayi da Gamboji kenan watanni biyar da suka wuce cewa ya kamata ace yayi aure ko dan yaransa su samu uwa a tare dasu kuma su samu natsuwa a cikin zuciyoyin su hatta itama za tafi samun natsuwa akan ace kullun yana zama haka tabbas hakan shi ya kara mishi damuwa domin yasan bata magana biyu tabbas zata aikata abunda ta fada din.
Tsaftatacciyar soyayya ke guda na a tsakanin Noor da Tasi’u sosai suke kaunar junansu kuma suke kulawa da juna tamkar yanda ake kula da kwai, a yanzu manya sun shiga cikin lamarin domin har an sanya ranar aurensu saboda Baba Azumi ta nuna cewa bata son a d’auki lokaci mai tsawo, yanzu haka saura wata d’aya da sati biyu kullun Tasi’u yana cikin d’awainiya dasu ba dare ba rana duk da yanda Baaba Azumi ta tsawatar mishi ta nuna cewa shima ba wani karfi ne dashi ba kuma bayan haka ga hidimar biki amma shi ko d’ar ba yayi shi dai kawai burin sa Noor ta kasance cikin farin ciki da kuma kwanciyar hankali.+
Kwance take akan katifa tana karatun littafin ‘kawa’idi “Ya Noor Baaba na kiranki” Mimi ta fada tana kokarin zama akan tabarma, ajiye littafin tayi sannan ta fita dan amsa kiran Baaba.
Tsugunawa tayi kusa da ita kafin tace “Baaba ashe aiki kikeyi shine tun d’azu baki aika nazo ba, Aminatu kuna ganin tana aiki kuma baku kirani ba” murmushi tayi sannan tace “y’ar albarka naga kina karatu ne ai kuma tun safe kike aiki baki zauna ba shiyasa nace su barki ki huta”.
Murmushi kawai tayi ta k’ar6i waken ta cigaba da gyarawa ita kam mamaki takeyi yanda Baaba batason hutawa kullun tana cikin aiki gashi yanzu wani k’adaranta ta saida dan kawai ta mata kayan d’aki tabbas Baaba y’ar aljanna ce domin kuwa ta kasance mutun ta gari mace ta gari kuma uwa ta gari babu abunda zata iya saka mata da shi illa tayi mata biyayya tamkar mahaifiyarta.
Bayan ta gama gyarawa ta d’aura musu abinci farin shikafa da wake da mai da yaji, bayan sun gama cin abinci Baaba ta k’ara musu abinci kamar yanda ta saba sai daf da sallar la’asar suka kammala bayan sun idar da salla suka dasa babin hira inda suke bawa Baaba labarin irin rayuwar da sukayi tun mahaifiyar su tana raye har zuwa sanadin zuwan su kano, sosai Baaba ta tausaya musu dan har sai da tayi musu kuka saboda tausayin daya
cika zuciyarta.
Nasiha tayi musu akan maganar da suka fad’a cewa sun tsani mahaifin su, sosai ta nuna musu kuskuren hakan da suka sa cikin ransu domin basu san abunda ya faru ko yake faruwa ba kila yana cikin wani yanayi da Allah kawai zai iya yaye mishi sai da ta tabbatar jikinsu yayi sanyi sannan ta janyo su jikinta ta rungume su tanajin kaunar su a cikin zuciyarta, tabbas sunga rayuwa shine abunda tayi ta tunani a cikin ranta yanzu inda ace ba’a hannun ta suka fad’a ba Allah yasan wani hali zasu shiga godiya tayiwa Allah daya kawo su hannun ta domin ko ba komai zata kula da tarbiyan su.
♣🌹♣☘♣🌻♣
*🌻вσяиσ ѕтαтє*
*♣вαмα ℓ/g*
Fitowarta kenan daga wanka ta zauna gaban dressing mirrow ta janyo hand dryer ta fara gyara
gashin ta, tana gamawa ta goge jikin ta sannan ta shafa mai kafin ta bude wordrobe ta d’auko bak’in jeans da pink top mai d’an tsawo wanda aka rubuta (feeling blessed) da bak’in ink kafin ta sake d’auko pink bracelet da bak’in agogo sannan tasa pink d’an kunne ta kama gashin ta da bak’in ribon guda hudu masu kyau.
Shigowa tayi ba sallama balle kuma knocking tana cewa “Anty an gama breakfast kuma anyi miki setting dinning din cikin falon ki, ga chan emeka har ya gama gyaran motan” a takaice tace “are u stupid baki san ya kamata kiyi knocking ko sallama ba kafin ki shigo d’akin mutane ke wata irin bagidajiya ce, have you not been taught manners in your home?”
da sauri tace “sorry ma kiyi hakuri mistake ne kuma sauri ne yasa banyi ba” ta fada kamar zatayi kuka “sorry for yourself comon get out before i descend on you” da sauri ta fita ta fara knocking sannan tayi sallama ta shigo haushi ne ya kama Nafisa tace “will you get out of my sight before i do something stupid” sumui sumui ta fita kamar wanda kwai ya fashe mata a ciki.
Tsaki taja sannan ta cigaba da kimtsawa, tana gamawa ta fice ta nufi side dinsu Inna Mardiyya wacce take kira da Mom sallama tayi inna ta amsa sannan ta bud’e k’ofar a hankali ta shiga kwanciya tayi akan gado ta fara yiwa Inna shagwa6a tana cewa “Ina kwana momy” da murmushi ta amsa mata da cewa “lafiya kalau ya naga ranki a 6ace? tabe baki tayi sannan tace “ba dakikiyar sabuwar house help dinnan bace debora,
kwata kwata bata da hankali she just bagged into someone’s room without saying excuse” tsaki Inna tayi kafin tace “haba daughter d’an wannan abun ne ya 6ata miki rai” Nafisa tace “eh mana mom” shafa kanta tayi tace “toh kiyi hakuri zan mata magana anjima shin kinci abinci ne?” gyara kwanciya tayi tana cewa “aa ni yau ba zanci komai ba banajin yunwa”.
Kallon ta Inna tayi na wasu mintina kafin tace “haba dear why will you go out wit an empty stomach ko dai yau ba zakije school din bane?” ta6e baki tayi tana cewa “no mom ni ba zanci abincin da wannan wawiyar tayi ba” Inna tace “toh bari ladi tayi miki wani ko kuma tashi muje dinning kici namu tunda ladi ce tayi” murmushi Nafisa tayi sannan ta mik’e tana cewa “why is dad still sleeping by this hour ko dai ko dai” hararanta Inna tayi tana cewa “ke dai yarinyan nan bakijin magana ba kiga jiya bai dawo daga office da wuri ba so ya gaji he deserve to rest.
Dariyan shekiyanci tayi sannan ta wuce dinning taja kujera ta zauna “mom i know that Dad baya barci har zuwa karfe takwas sai dai idan sleeping pills kika bashi Allah Mom ki rage irin haka kar wataran asiri ya tonu” neman guri tayi ta zauna sannan tace “in ban bashi ba bani da wani alternative” murmushitayi kawai tayi sannan suka fara breakfast.
Nafisa kenan y’ar Inna Mardiyya mata ga Baban su Noor kuma kanwa ga Mamansu Noor, yanzu haka Nafisa tana aji uku a secondary sosai take fachaka da dukiyar mahaifinsu Noor da ita da uwarta duniya kam yayi musu dadi yanda suke so har basa tuna cewa akwai mutuwa ko kuma akwai ranar da asirin su zai tonu sosai suke watayawa cikin kwanciyar hankali komai yi musu akeyi basu da matsala, su Noor kuwa ba’a ma tuna su a cikin gidan an riga ab shafe kwakwalwar mahaifinsu game da lamarinsu babu wanda zai shiga gidan ya ambaci sunan su domin kowa ya manta dasu Nafisa kawai aka sani a matsayin y’ar masu gida masu aiki kala daban daban suke dashi tamkar haka zasu dawwama a cikin duniyarsu.
So da kauna ke kara wanzuwa cikin zukatan masoyan Shirye shiryen biki akeyi ta ko wani 6angare kowa yana kokarin ganin cewa ya fita kunya duk da cewa dukansu ba masu hali bane amma kuma sosai suka bada himma gurin kyatata niyyarsu.
A6angaren su Noor sun riga sun kammala kusan komai daya kamata ayi Baaba Azumi ta fitar da 6oyayyen ajiyarta da kuma wasu kadarorinta ta sayar ta bawa aminan ta kud’in su Yaana da Iya domin su sayo kayan d’aki, kujeru da kuma kayan kitchen sosai sukayi kokari gurin sarrafa kud’in suka saya kaya masu kyau da kuma amfani sannan suka kara da sayan kayan gara da za’a kaiwa amarya daga nan suka kara daga cikin kud’insu gurin sayan kayan abincin da za’a dafa ranar biki sannan kuma abunda zasu bawa masu kawo kayan lefe.
Bayan sun dawo aka sauke kayan a gidan Yaana kasancewar tana da d’aki babba a tsakar gida inda babu komai a ciki, setin gado ne mai kyau dai dai talaka kalar baki da ratsin ruwan toka sai kuma kujeru guda biyu dan k’awata d’akin masu kalar ruwan toka da ratsin bak’i sannan sai labule ruwan toka mai dan duhu sai kuma kayan kitchen dai dai misali sosai kayan sukayi kyau komai anyi shi dai dai talaka gwanin bayarda sha’awa bayan sun ajiye suka rufe k’ofan sannan suka d’auki kayan da zasuyi amfani dasu ranar biki da wanda za’a bawa masu kawo lefe suka nufi gidan Baaba Azumi, lissafin komai suka mata kan abunda suka sayo sosai taji dadin kokarin da sukayi gurin tallafa mata daganan suka cigaba da tattauna yanda abubuwa zasu kasance.
A6angaren Ango shima ya gama komai na daga kayan lefe da kuma inda zasu zauna domin ya dad’e da fara karamin d’akin sa a cikin gidan kawun sa kasancewar akwai babban fili a cikin gidan hakan yasa kawu ya ba shi shawaran fara gini d’aki d’aya yayi mai girma sosai sai kuma wani k’aramin kitchen ta gefe guda sannan yasa kara ya zagaye gefen nashi ta ciki kuma yayi yan shuke shuke wanda ya k’awata gurin sosai sannan yayi fentin sa ruwan kasa da feshi feshin ruwan toka.
Washe gari da safe kuma aka kai kayan lefe, matar kawu da wasu aminanta su biyu suka kai akwati guda uku masu kyau da tsari, bayan sun dan ta6a hira da raha suka nemi ganin amarya kafin suka musu sallama suka tafi tare da abun alherin da suka basu na nuna godiyar su duk wadan da su kaga kayan sai da suka yaba mishi domin tabbas yayi matukar kokari gurin hada lefe mai kyau da ma’ana, atamfa ne kala goma da kuma dogayen riguna guda uku sai hijabi uku da gyale uku sannan inner wears ko wanne guda hudu hudu sai kuma kayan kwalliya dai-dai misali masu kyau da quality.
STORY CONTINUES BELOW

Washe gari suka nufi gidan amarya domin suyi jere, sosai suka mata jere mai kyau sannan suka sa turaren wuta bayan sun gama suka nufi kitchen dan had’a kayan kitchen din gefe guda suka sanya mata risho dinta da turmi da ta6arya d’ayan gefen kuma ta cikin drawer suka jera mata tukwane, robobi da tray sai ta saman kuma suka sanya mata kwanuka da kofuna da chokula ta cikin wani abun jere na zamani ta chan bayan k’ofa kuma suka jera mata kayan abincin ta komai chas dashi a cikin kitchen din sai da suka tabbatar sun gama komai babu wani mishkila sannan suka rufe k’ofofin sukaci abinci ta chan gefen matar kawu kafin suka bata makullin d’akin tare da mata sallama suka tafi suna masu yabawa da halin kirki irin na matar da k’awayenta.
Washe gari ya kama ranar juma’a ranar da yafi ko wani rana albarka rana mafi daraja a cikin ranaku kuma ranar da wad’annan ma’aurata baza su ta6a mantawa da shi ba, a kace rana bata karya sai dai uwar d’iya taji kunya, a yau al’umman annabi suka halarci d’aurin Auren Fatima Noor Muhammad Nura da angonta Tasi’u Muhammad Bala a cikin babban masallacin juma’a dake cikin garin Kanon dabo akan sadaki naira dubu ishirin, tsaban murna sai da ango yayi hawaye kowa ya taya shi murna musanman abokansa na nesa dana kusa domin shi mutumin mutane ne kasancewar sa ma’abocin son jama’a da barkonci, bayan an tashi daga gurin d’aurin aure ango da abokan sa suka nufi gidansu Noor inda sukayi gaisuwa tare da d’aukan hotuna kafin suka nufi gurin da za’ayi reception inda wani abokin sa ya kama musu a matsayin gudunmawar sa sosai Tasi’u yaji dadin karan da abokan sa suka masa domin sun bashi mamaki iya mamaki dan anci an sha a wadace tamkar bikin wani mai kud’i sai dai fatan Allah ya basu zaman lafiya da zuri’a dayyiba kamar yanda kowa ke mishi adduo’i da fatan alkairi.
A6angaren Noor kuwa daker ma ta fito sukayi hotuna da angonta da kuma sauran jama’an Baaba Azumi wadan da suka halarci shagalin bikin domin kuwa kuka suka sha ita da k’annen ta saboda tunawa da mahaifiyar su da kuma sauran yan uwansu, babban bak’in cikinta ma ace mahaifinta na raye yana cikin duniyar da take amma ace bai san abunda ke faruwa cikin rayuwar su ba yayi watsi dasu bai rike amanar da mahalicci ya bar mishi ba tabbas ya cutar da rayuwar su ba zata dai na fad’in cewa ya cuce su ba domin sun cutu iya cutuwa duk da yanda Baaba Azumi kan nusar da su akan cewa kila akwai wata makarkashiya amma zuk’atan su yaki aminta da hakan, sosai suka sha kukan su suka gode Allah har sai da Baaba Azumi ta nuna 6acin ranta sannan suka tsagaita tare da bata hakuri.
Karfe biyar na yamma amarya ta sake wanka aka mata kwalliya cikin kayan da Baaba Azumi ta d’inka mata sosai tayi kyau ta kara haske saboda gyaran data sha, bayan an gama gyara ta ska kaita gurin Baaba Azumi domin tayi mata nasiha bayan mutane sun d’an watse a cikin d’akin Baaba Azumi ta rike hannunta tana mai cewa “Fatima inaso ki bud’e kunnuwanki ki saurare ni, inaso kiyi amfani da wannan nasihar da zanyi miki inaso ki kasance mace ta gari agurin mijinki shin kinsan wacece mace ta gari? An tambayi wani Mai Hikima Shin wacece Mafi alkhairi a cikin Mata?? (Wato Mace tagari) Sai yace Ita ce mai kokarin neman yardar Ubangijinta ta hanyar sauke wajibabbun hakkokin dake kanta, Mai shiryar da Mijinta (idan ya ‘bata) Kuma tana taimaka masa wajen bin Allah da Manzonsa da Iyayensa da sadar da zumuncin sa, Bata barin gidanta (don yaji, ko kuma yawon banza sai dai babban uzuri idan ya kama), Ita ce mai tsananin kulawa da sallolinta biyar (Tana yinsu akan lokaci, kuma tare da tsoron Allah), Ita ce mai ‘boye sirrinta da sirrin Mijinta (Ko sun ‘bata da Miji ko abokiyar zama, babu wanda zai sani), Ba’a ganin takalminta ko Kayan adonta idan tana tafiya (wato ta rufe jikinta baki daya), Ba’a jin sautin muryarta ako ina, Ba’a sanin kamannin siffar Jikinta (Ko yaushe tana sanye da tufafin kamala), Abar girmamawa ce a cikin Mutanenta, (saboda karamcinta da kyawun halayenta), Mai kaskantar da kai ne a cikin zuciyar ta(Bata ganin cewa ita tafi Qarfin kowa) Mai tausayi ce ga ‘ya’yanta, kuma tana kulawa da ciyar dasu da shayar dasu, Gidanta tamkar wata Aljannah ce makusanciya (saboda soyayya da sakin fuska da wadatuwar Zuci), Idan ta samu abin alkhairi daga Maigidanta sai ta gode masa afili da boye (Ko yaushe tana yi masa addu’a), Idan ta riski wanni sharri daga gare shi, Takan yi hakuri (Ba wai tayi masa masifa ko haya-gaga ba), Idan ya shigo gareta sai tayi farin ciki tare shi da murmushi (Bata Qullatar kowa a zuciyarta), Idan ya fito daga gidanta (zai tafi wajen aiki) zata nuna damuwarta, kuma tana ‘dokin dawowarsa, Idan yana fushi da ita takan yi hakuri ta jure, har sai ta bashi hakuri ya huce, Ko yaushe idan ta matso gareshi sai ta burgeshi (saboda kyawun ado da tsafta da kyawawan kalamai), Idan ba ya nan, takan kiyaye masa amanar jikinta (ita kanta) da sirrinsa da gidansa, da dukiyarsa, Idan taga wani laifinsa sai ta boye, ta suturceshi,Idan ya gaya mata uzurinsa, takan karba ta yafe masa Mai tsananin Kunyar Allah ne da bayin sa Hatta Maigidanta tana jin nauyinsa Mai gaskiya ce da rikon amana (Bata yin Qarya don burge wani, ko kuma don tada husuma) Mai girmama iyayen Mijinta ne da danginsa (Bata raina iyayen Miji, ko wulakanta ‘yan uwan sa)Mai rufa asirin Mijinta ce yayin da talauci ya sameshi (takan taimaka masa idan tana da iko) Bata yi masa gori ko habaici ko cin fuska, Ta runtse idanunta da Zuciyarta, Bata kallon kowanne Namiji sai Mijinta, kuma bata tunanin kowanne Namiji sai shi, Tana kwantar da hankalin Maigidanta duk lokacin da yake cikin wani yanayi Bata zame masa baya. (Koda an bata masa rai akasuwa ko awajen aiki) Tana nuna ma ‘Ya’yanta da danginta yadda zasu ga Mutuncin mahaifinsu. Tana kuma kula da tarbiyyarsu Fatima inaso ki kasance mace ta gari mai d’auke da wad’an nan kyawawan halayyar ki kasance mai koyi da irin wannan hali insha Allahu ba zaki ta6a ta6ewa ba kuma zaki kasance abun koyi ga yan baya sannan zaki zama tauraruwa a idon mijinki da danginsa, Fatima ki rike amanar mijinki ki rike amanar aurenki ki sani cewa Allah yana kallonki kuma yana sauraron duk abunda zai wakana tsakaninki da mijinki, Allah ya miki albarka yasa ki gama da duniya lafiya Allah ya kare ki daga duk wani sharri ya kuma haskaka rayuwar ki”. Sosai Noor take kuka harda shesheke saboda yanda nasihar Baaba Azumi ya ratsa cikin jikinta da jininta tabbas Baaba Azumi Uwace kuma mace ta gari domin ko mahaifiyarta iya abunda za tace kenen rumgume Baaba Axumi tayi tana kuka mai cin rai wanda hakan yasa itama ta fara kuka dak’er aka cire Noor a jikinta aka sanya ta a mota domin k’annen ta sun shiga d’aki sun rufe sunk’i bud’ewa dan basa son ganin tafiyar yar uwarsu tafiya da ba ta har abada ba amma tafiya irin wanda ya dace.
Satin Dr Affan Uku a garin Gaidam ya koma Bama, har ya gama iya kwanakin sa bai tuna da wata mai suna Hajja Hadiza ba abokinsa yaso ya tunkaresa da maganar amma kuma sai ya share tunda yaga Dr Affan din bai damu da lamarinta ba, yana isa direct office ya tafi yayi reporting kafin ya kama hanyar gida dan yau ba zai iya aiki ba saboda yanda yakejin babu dadi a jikinsa ga kuma wani sabon yanayi na yanda zuciyarsa ke bugawa da k’arfi.
Zaune suke a falo suna hiran wani malami daya nacewa Hajja Hadiza ita kuma har yanzu Dr Affan na ranta shiyasa taki kula malamin amma ba karua malamin ya had’u iya had’uwa ga iya d’aukan wanka yan mata da yawa suna kaunarsa shiyasa dasu kaga yana son Hajja Hadiza ita kuma tana walakanta shi sukaji haushi matuka, yanzu haka suna jss1 a Bama Girls seconday school dake hanyar Sharia Court sosai suke karatu suke kuma maida hankali dan ganin cewa sun faranta ran Hajiya kamar yanda iyayen su suka musu nasiha kafin zuwansu ga iya aiki da kuma tsafta shiyasa Hajiya take matukar kaunarsu.
Ghaji ne tace “Y’ar uwa dan Allah ki bawa Malam Handsome chance mana kinga mutumin kirki ne ga ilimi ga kyau ga kuma naira yarinya idan kika aure shi kin huta baki ba wani tension tunda kinga ya kamu da yawa kuma kila a dace kinga da mun gama jss3 sai aure idan yaso sai ki karasa sauran karatun a gidansa, dan Allah kiyi tunani a kai kinji”.
Auta ce ta amshe zancen da cewa “gaskiya kuwa kinga sai mu sha biki mu rautsaya kuma magana ta gaskiya idan zan baki shawara a matsayin y’ar uwa zan iya cewa ki dai jaraba ki gani a sannu zaki iya fad’awa kogin son sa domin nima na shaida Malam Muktar mutumin kirki ne uwa uba ga asali domin mahaifinsa hamshakin mai kud’i ne ni namayi mamaki daya zauna harkan koyarwa Domin da yawa irinsu sai dai business ko kuma irin manyan harka masu saurin kawo Kudi sannan kuma babban abun shine mahaddacin alkur’ani ne kina ganin shi haka zaki iya cewa baiyi zaman islamiya ba toh ya wuce duk inda kike zato kuma wallahi da ace ni yake so da tuni an wuce gurin dan bazan miki karya ba na dad’e da fad’awa tarkon malam Muktar.
STORY CONTINUES BELOW

Dariya duk sukayi banda Hajja Hadiza ita dai kallon su kawai takeyi domin abunda ya dameta dabanne yau tun safe takejin faduwar gaba ta rasa kona menene gashi har zuwa yanzu bata daina jiba addu’a kawai takeyi akan Allah yasa alkairi ne ba a’kasin hakan ba ajiyar zuciya tayi kafin tace “ba zaki gane ba y’ar uwa Tabbas nasan malam Muktar ya kai matsayin a so shi sai dai fa ni bazan so in yaudare shi in kuma yaudari kaina ba domin dafin dake cikin raina ba dafin da zaiyi saurin fita bane kuma ba wanda zaiyi saurin gushewa bane da ace ina da yanda zanyi da nayi saurin cire wannan dafin na sanya mai sona a cikin raina amma abune mai matukar wahala sai a sannu zan iya samun sukunin zuciya amma kuma insha Allahu zanyi miki addu’ar Allah ya karkata zuciyar malam Handsome zuwa sonki da kaunarki ta malam Muktar” dariya sukayi a tare saboda abunda ta fad’a saida sukayi mai isarsu sannan sukayi haraman alwala dan gabatar da sallar magriba amma har zuwa lokacin jikinta asanyaye yake.
Dariyarsu ne ya mishi sallama yana sanya kafa a cikin falon su kuma suna kokarin hayewa sama dan gabatar da sallan magriba, komawa yayi da baya ya wuce 6angarensa yana mai mamakin ko suwa Hajiya ta samu saraken surutu, bayan ya idar da salla ya nufi cikin gidan dan gaida Hajiya, a stair case ya had’u da Auta da sauri ta wuce d’akin Hajiya dan sanar da ita dawowansa, murmushi kawai yayi ganin yanda ta koma da gudu ita dai kullun kara zama yarinya takeyi, sallama yayi a k’ofan d’akin sai da yaji ance ya shiga sannan ya tura k’ofan a hankali ya shiga.
A saman darduma ya ganta tana karatun al kur’ani, murmushi yayi ya k’arasa kusa da ita ya zauna yana hararan Auta sai da takai karshen ayar sannan ta rufe kur’anin tare dayin addu’a, ta dade tana adduo’i kafin suka shafa a tare hugging dinta yayi yana cewa “i really really miss you Hajiya ta (nayi matukar kewarki sosai Hajiyata)” murmushi tayi ta shafa kansa tana cewa “muma munyi kewarka sosai sannu da dawowa likita bokan turai, da fatan ka dawo lafiya ya hanya?” sake makalkale ta yayi kafin yace “lafiya kalau Hajiya da fatan na same ku lafiya kuma cikin koshin lafiya?” kallon Auta tayi kafin tace “lafiya kalau mun gode Allah, ita kuma wannan mai ya had’a ku daga dawowarka” d’agowa yayi ya kalleta sannan yace “wai fa tana gani na ta koma da gudu dan sanar dake dawowa na toh kuma sai Allah yasa har na shigo bata samu damar isar da gulman nata ba shine nayi mata gwalo toh fa hakan yasa ta had’a rai take wani min gani gani kamar hadarin kaji” dariya duk sukayi har da Auta kafin suka rumgumi junansu suna masu farin cikin kasancewa zuri’a d’aya sun dade a haka kafin Hajiya tace “Auta jeki kira Aisha (Ghaji) da Hadiza suzo su gaisa” har ta tashi zata fita kuma saita tuna cewa suna karatu “Hajiya na manta ashe suna karatu bari zuwa anjima sai su gaisa” ta fada tana kokarin zama, hajiya tace “okay toh ai shikenan Allah ya kaimu anjiman tunda suna gidan” kallon su yayi kafin yace “su waye kuka samu kuma hajiya?” tunawa tayi ashe bata sanar da shi ba nan ta bashi labarin komai kafin suka shiga wani hiran daban ita kuma Auta ta koma d’aki gurin su Hadiza.
♣🌹♣☘♣🌻♣
*🌻f¢т αвυʝα*
*♣gωαяιмρα*
Tunda ya tashi da safe yakejin zuciyarsa na bugawa da k’arfi kamar wani ganga har abun ya fara bashi tsoro tun yana addua a ransa harya fito fili saboda yanda bugun zuciyarsa ke k’aruwa ganin cewa babu sauki yasa ya tashi ya d’auro alwala ya fara nafila sai da yayi doguwar tsayuwa kafin yayi ruku’u sannan yayi sujjada a haka harya idar da sallan dai-dai lokacin aka kira sallan la’asar hakan yasa bai nad’e sallayar ba yayi sallah yayi karatun littafi mai tsarki cikin muryan sa mai dadin sauraro kafin yayi adduo’i ya kwanta dan ba zai iya ma cin abinci ba yanda yakejin jikinsa babu wani kuzari kamar an raba shi da wani 6angare dake cikin jikinsa.
Dariya su Twins suke mata saboda yanda take wani buga k’afa a k’asa ga Al-Hussain a bayanta da bulala a hannunsa “Daddy kaga Yasmeen koh wallahi zan zaneta idan bata fita harka ta ba” kallon su Daddy yayi kafin yace ” Yasmeen sai na fara zaneki a gaban kannenki koh yarinya kamar mai aljanu yanzu ki zama natsatsiya zuwa anjima kuma ki sake rikid’ewa” Yasmeen tace “Daddy shine fa kawai dan nace ya bani aron laptop yaki sai na d’auka yana barci shine kuma dana mayar na bashi hakuri kuma sai yace sai ya dakeni” hararanta yayi kafin yace “toh keh ina naki da ba zaki d’auka ba sai nawa?” itama hararan sa tayi kafin tace “ai nawa yana chaji shiyasa” Dady yace “nikam wai Al-Husain ba yayanki bane eh Yasmeen? Baki ta tura tana cewa “ayya Daddy shine fa ya fara dana ajiye sweet na birthday party na zan kai School shine kuma ya bude sacket d’aya bayan shima yana da nashi” Daddy yace “ashe ma kaine me laifi kai ka fara neman tsokala” Al-Husain yace “Daddy kayi hakuri amma ai nata sweet ne zata iya aikawa a sayo mata wani a lokacin ni kuma inada assignment da zanyi printing kuma gobe karfe bakwai zan kai saboda lecturer din baya son delay yanzu kuma laptop din yayi shoot down kafin yayi chaji inyi editing lokaci ya tafi dan bana son aiki da laptop yana chaji saboda yana saurin lalatawa” Mamy dake kokarin zama kusa da Daddy tace “toh alhaji meke faruwa anan kuma yau kullun dai yanzu sai anyi case daku ko Yasmeen” Yasmeen tace
“ni mummy wlh gidansu Hanaan zan koma na k’arasa karatuna sai na yi rabin hutuna a chan zan dawo dan anfara takurani a gidannan” Mamy tace “gaskya kam ni gwarama ki tafi ko zamu huta da rigima” dariya Daddy yayi kafin yace “ok wato da mamana kika gaji koh” tashi Mamy tayi tana cewa “yi hakuri Daddy kai kuma Al-Hussain ka kama girmanka banson irin abunda kakeyi” hakuri ya bayar kafin ya wuce 6angarensu twins kuwa dariya kawai suke musu saboda yanzu kullun sai sunyi drama a gidan.
Hararan da Yasmeen ta musu ne yasa duk suka tsuke bakin su tare da mik’ewa suka wuce sama sumui sumui dan sun santa yanzu sai ta make su babu abunda ya dame ta balle kuma yanzu da take cikin fushi ai kuma sai ta sauke komai akan su Daddy ne ya kalleta yace “ya zaki koramin yara ina ruwanki dasu toh maza tashi kije da kanki ki kira su sannan kuma kar in sake ganin kinyi wa Al-Hussain rashin kunya hakan ba dai-dai bane idan ya miki wani abu ki sanar dani ko ki sanar da Mamy kinji koh” da kai ta amsa sannan ta wuce sama dan kiran twin