YAR ALMAJIRA CHAPTER D KARSHE
YAR ALMAJIRA CHAPTER D KARSHE
Tunda suka shiga mota Noor take kuka har suka isa gidan bata dena ba sunyi rarrashin har sun gaji kafin suka kaita d’akin Inna Kubra matar kawu dan bata amanar d’iyarsu sosai aka musu kar6a mai kyau kafin suka kaita d’akinta, basu dad’e a gidan ba suka juya zuwa gida aka barta tare da k’awarta d’aya da kuma y’ar mak’otansu duk da cewa zata girmi Noor din sosai amma kuma suna shiri na ban mamaki.
+
Bayan shigowan Tasi’u ya nufi d’akin kawu dan amsa kiran da yake mishi, bayan sun gaisa kawu yace “dama ba wani abu bane face d’an k’aramin nasiha gareka d’ana, kasani cewa akwai wasu siffofin nagari dake tattare da kowani namiji wanda kowace macce ke so, Mijin dake son matar sa bayan aurensu fiyeda yadda yake sonta a layi, Miji mai kishin matarsa domin Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace “duk wanda baya kishin matarsa bazai shiga Aljannah ba” sai kuma Mijin da ya dauki aure a matsayin Ibadah, ba wai abin wasa ba ko kuma abin jindadin rayuwa kawai ba, wanda ya dauki matarsa a matsayin abokiyarsa, kanwarsa, almajirarsa, kuma abokiyar shawararsa wanda baya zagin matar sa, baya cin mutuncinta, baya cin zalinta, baya ha’intarta koda a bayan idonta ne, wanda yake zaune da iyalinsa cikin amana da gaskiya da kyautatawa ba cuta ba cutarwa, wanda idan ya fahimci halayen matarsa yake hakurin zama da ita tare da kyautatawa domin neman rahamar Allah Ta’ala, shine mijin da idan zai yi magana da matarsa, zai fadi gaskiya babu yaudara ko karya acikin zancensa, shine wanda ya dauka a zuciyarsa cewa Iyayen matarsa, Iyayensa ne. ‘Yan uwanta ma ‘yan uwansa ne, kuma dangin matarsa danginsa ne shine wanda yake daukar cewa farin cikin matarsa shine farin cikinsa kuma matsalar ta, itama tasa ce shine wanda yake kokarin kiyaye sirrin matarsa, kuma yake kokarin kare mata mutuncinta koda a wajen ‘yan uwansa ne, tare da hikima da fahimtarwa shine wanda baya fifita matarsa akan ‘yan uwansa, kuma baya tauye mata darajarta yana bawa kowanne gefe nasa hakkin kamar yarda shari’ah ta tanadar shine wanda ya tanadi ruwan afuwa da hakuri a cikin zuciyarsa domin kashe wutar tashin hankali da bacin rai a duk lokacin da hakan ta faru tsakaninsa da matarsa shine wanda a kullum yake kokarin tarbiyyantar da iyalinsa akan rayuwar addinin Islama ba rayuwa irin ta yahudu da nasara ba shine wanda yake zaune da matarsa komai dadi komai wuya ba zai dena nuna mata soyayya ba wai don tafara yankwanewa ko kuma karfinta yafara raguwa shine wanda yake bawa matarsa yabo a duk lokacin da tayi kwalliya ko kuma tayi girki komai rashin dadinshi Miji nagari baya raki baya ihu don yaji abinci yayi yaji ko gishiri yayi yawa. Sai dai yace: “uwargida abincin nan yayi dadi iyaka, sai dai gishiri yayi mana shisshigi a ciki” ina fatan zaka d’auki wannan nasiha kayi amfani dashi gwargwadan iyawarka, Allah yasa mazaje su gane su kuma sauke hakkinsu yanda ya dace, Allah kuma ya albarkaci rayuwar aurenku” Kuka Tasi’u ya fashe dashi dan tunawa da iyayensa tabbas wannan nasiha ya ratsa zuciyarsa sai da yayi mai isarsa sannan yayiwa kawu godiya yana mai alfaharin kasancewa cikin zuri’arsa domin ba kowa bane zai iya 6ata lokacinsa gurin nunawa mutun irin wannan abun.
STORY CONTINUES BELOW

D’akin Inna Kubra ya shiga itama nasihar tayi mishi dai-dai gwargwado kafin yayi mata sallama ya nufi 6angarensa inda abokansa biyu ke jiransa a waje, sallama sukayi a k’ofar d’akin, sai da aka basu izinin shiga sannan suka shiga bayan yan gaishe gaishe da raha tsakanin abokan ango da kawayen amarya, abokan suka d’an musu nasiha mai ratsa zuciya kafin sukayi addua sannan suka musu sallama, rakiya Tasi’u ya musu zuwa k’ofar gida kafin k’awayen amarya suka fito shi kuma ya koma cikin gida.
Har ya dawo tana zaune inda ya barta sai faman shar6an kuka takeyi, zama yayi a kusa da ita ya rungumo ta yana cewa “haba Noor d’ita hasken rayuwata ya isa haka mana ko anyi miki wani abunne?” d’ago kanta tayi ta kalle shi har zatayi magana sai kuma tayi shuru a haka dai yaci gaba da rarashin ta har aka kira sallah ya wuce masallaci, gyaran gidan ta k’ara yi ta shiga wanka tare da yin alwala duk da cewa ba sallah zatayi ba amma ta saba kwanciya da alwalarta domin tun a gida haka Umma ta koyar dasu, kwalliya ta d’anyi yanda Baaba Azumi ta koyar da ita rigar bacci ta saka mai laushi wando da riga ta daura hijab mai hannu har k’asa a kai, turaren wuta ta kunna wanda ta gani a cikin kayanta kafin ta samu gefe guda ta kwanta a takure tana tunanin kannenta da kuma Baaba Azumi duk kewarsu ya addabeta ganin cewa ta kasa samun barci ta janyo wayarta wanda Tasi’u ya saya mata ta bud’e app na alkur’ani kasancewar bata da tsarki babu yanda za’ayi ta ta6a cikekken Qur’ani.
Bayan ya fito daga masallaci ya biya k’asan layin su ya sayo kaza gasheshe guda d’aya da kuma hollandia yoghurt kafin ya koma gida da sallama ya shigo tun daga k’ofa yakejin kamshi mai dadi harya shiga cikin d’akin da yaji karatun Qur’ani na tashi nan ya shiga ya sameta a kan gado rik’e da wayar daya saya mata tana karatun Qur’ani, hamdala ya k’ara yi cikin zuciyar shi, sai da ta kai aya ta ajiye sannan ta juyo tana mishi sannu da shigo wa murmushi yayi kafin yace “yauwa Noor na barki ke d’aya ko? Ba tace komai ba ta k’ar6a abun hannunshi, shi kuma ya cigaba da cewa ‘Kamshin turaren nan ya min dad’i sosai gaskiya Noory” murmushi ta sakeyi kafin ta fita zuwa kitchen ta d’auko plate da cups, a saman center table ta ajiye shi kuma yace tayi serving dinsu babu musu ta cire kazar ta saka a saman plate tare da yanyankawa kafin ta bud’e yogurt din ta zuba a cups “ki cire hijab din mana uztaziya Noor” cikin jin kunya ta cire sai binta da kallo yakeyi, kusa da ita ya koma kamshi mai sanyi tare da saka nutsuwa ke fita daga jikinta, haka sukayi ciyar da juna har suka k’oshi ta kwashe kayan ta wankesu kafin ta shiga band’aki “ruwa ta had’a mashi na wanka yanda ya bukata, bayan ya fito ya zira jalabiya ya dawo cikin d’aki a nan ya sameta zaune shiru “ya dai ko kina kewar Baaba Azumi ne da sauran kannen mu?” d’aga ido tayi ta kalle shi kafin tace “kaman ka shiga zuciyata ya Tasi’u” zama yayi kusa da ita ya janyo ta jikinshi yana cewa “sai dai kiyi hakuri haka aure yake hira yake ta janta dashi tana kwance a jikin shi har suka fara jin bacci ya kashe komai tare da rufe k’ofa, sallaya ya umurce data shimfid’a suyi nafila cikin jin kunya ta sanar dashi cewar bata sallah duk da haka shi sai da yayi raka’a biyu bayan ya idar ya kwararo addu’oi na neman tsari da zaman lafiya ita kuma tana mai amsawa da ‘ameen’ bayan ya gama ya haye yago ya jawota jikin shi tare da kashe wuta.
Cikin kwanaki ukun da sukayi tare haka suke gudanar da rayuwar aurensu cikin natsuwa da kwanciyar hankali, duk basu da matsalar komai sai dan abunda ba’a rasa ba har mijinta ya koma bakin aikin shi.
Satin aurensu hud’u ya kama wata d’aya kenan Tasi’u ya fara wani rashin lafiya mai ban tsaro ,tin yana daure wa har ciwon ya kwantar dashi, sosai Noor ta tsinci kanta cikin k’unci su kawu sunyi iya kokarinsu na ganin sun mishi maganin gargajiya jinya yayi mai tsawo dan kuwa watan shi biyar yana fama da abu d’aya k’arshe dai da suka ga abun yak’i ci yak’i cinye wa sai suka tattara suka koma asibiti a can sukaci gaba da jinyan shi, bayan wani lokaci suka had’u da wani babban likita wanda aka maida case din agun shi wannan likitan ne ke sheda musu cewa Tasi’u na d’auke da cutar *BLOOD CANCER* ya kuma shaida musu akwai buk’atar a fita dashi waje dan zaifi samun kulawa a chan.
Awannan lokacin ko ba’a fad’a ba kunsansu Noor na cikin matsanancin tashin hankali, a yanzu kam basu da wata mafita daya wuce su maida shi gida su cigaba da jinyar shi sai dai ina kafin su tattara su koma Tasi’u kwana sun k’are Allah baya barin wani dan wani ana gobe zasu koma da shi gida Allah yayi masa rasuwa..
A wannan ga6ar kukan ma kasa zuwa yayi haka ta koma tamkar mutun mutumi ba um ba a’a sai dai kallo a haka aka had’a gawarsa aka kaishi gida, bayan anyi mishi wanka aka mishi salla daker ta iya zuwa gaba gawar tana kallonsa amma ta kasa cewa komai tamkar an datse harshenta babu wani kalma da takejin cewa akwai a saman la66anta haka ta sha zamanta har aka d’auke shi bayan anyi sallan la’asar aka sallace shi sannan aka kaishi makwancinsa har zuwa lokacin Noor na zaune a gurin ta kasa motsi kowa tausayinta yakeyi saboda k’ank’antar shekarunta su Aminatu ma sunzo sai kuka sukeyi amma ita ta rasa gane ainihin duniyar da take ciki.
Bayan kwana uku da rasuwan mijin nata sai a sannan tayi kukanta har ta gode Allah, babu wanda ya hanata kuka har sai da ta fara ajiyar zuciya sannan aka fara rarrashinta ita dai kawai da kai take iya amsa gaisuwarsu domin bakin ta yayi mata nauyi sosai hawaye kawai ke zuba daga idonta Allah Sarkin dad’i inji b’arawon takand’a, Allah baya barin wani dan wani yaji dad’i Tasi’u ya tafi ya bar ta a lokacin da tafi buk’atar shi tabbas tayi rashin miji mai qauna ta miji wanda ko wace mace take burin aure duk da kasancewar sa talaka amma shi din mutun ne jajirtacce kuma tsayayye akan gidansa tsakanin ta da shi a yanzu sai dai addu’an Allah ya biya shi da gidan aljannah bisa d’awainiyar da yayi da ita da kuma yan uwanta harma da Baaba Azumi Allah kuma ya kai masa ladar abunda yayi na alkhairi makwancin sa.
Ayau Tasi’u ya cika wata Shida da rasuwa Noor kuma harta fita takaba duk ta rame ta zama ba kyaun gani.
+
Tana zaune a d’aki su Baaba Azumi suka shigo tare da Kawu da kuma Inna Kubra daker ta iya d’ago kanta ta kalle su saboda yanda kirjinta ke matsanancin ciwo, bayan sun gama gaisawa suka k’arayi mata nasiha tare da adduo’i ga mamacin sannan Baaba Azumi ta bukaci ta shirya domin zasu koma gida Kawu ne yace su d’an dakata yana zuwa bayan ya fita Noor ta tashi ta fara kokarin had’a kayanta bayan ta kammala ta nemi guri ta kwanta dan wani irin jiri takeji.
Kawu bai dade ba ya dawo tare da wasu manyan malamai, bayan an gaigaisa suka bud’e taro da addua kafin Kawu yace “dama na kira sune akan batun raba gadon mamacin domin ya dace ace kafin ta bar gidannan ta tafi da kasonta”.
Gaban Noor ne ya fad’i saboda jin abunda Kawu yace saboda ita tama manta da zancen raba gado “innalillahi wa inna ilaihi rajiun” shine kawai abunda tayi ta maimaita wa acikin ranta.
Malamin ne ya tambayi adadin dukiyar mamacin sai Kawu yace “wannan ginin da yayi sai kuma k’aramin shago da abun garuwa” nisawa malamin yayi kafin ya sake cewa “Shin mahaifiyarsa ko mahaifinsa suna raye ko kuma wasu yan uwansa” Kawu yace mishi bashida kowa sama da shi sai kuma matarsa Noor.
Noor wacce kanta ke k’asa tana ta tunanin hiransu da Tasi’u a lokacin daya fara rashin lafiya “Noory fatana ace munyi rayuwa mai dadi cikin kwanciyar hankali da tattalin juna sai dai abun da kamar wuya, babban abunda yake damuna shine matsalar daya addabemu wanda na kasa maganceta sai dai fatana idan da ace Allah zai tashi kafad’a na sai in sanar da Kawu ko kuma muje gurin malami domin ya bamu irin shawaran daya dace amma duk da haka d’auko takarda da biro ina fad’a kina rubuta wa saboda halin rayuwa” a lokacin bata ta6a kawo cewa mutuwa zaiyi musu yankar k’auna a d’an k’ank’anin lokaci ba sai gashi har mijinta abun k’aunarta yayi wata shida a k’ark’ashin k’asa.
Tashi tayi kowa ya bita da kallo a ranta tana cewa “ba zata bari a karo na biyu ta aikata ba dai dai ba tunda idan har wancan girman laifinta ba mai yawa bane toh wannan karan kam laifin da zata aikata mai muni ne” akwatinta ta bud’e ta ciro wannan takardan sannan ta rufe ta koma mazauninta tare da mik’a wa malamin wasiyyar mijinta.
Ganin ‘WASIYYA’ da manyan harufa a jikin takardan yasa malamin yayi bismillah sannan ya bud’e bayan ya warware ya fara karantawa kamar haka “Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta’ala wa Barakatuh, na sani cewa alokacin da wasiyya ta zata isa gareku na riga nayi muku nisar da babu waiwaye a cikinta kuma na riga na zama tarihi a gareku, bayan d’inbin gaisuwa da fatan kuna lafiya, Ina mai kara bawa matata Noor hakurin rashina da tayi tare daku iyayena abun alfaharina babban abunda yasa na rubuta wannan wasiyya shine dan na saukaka muku zaman da zakuyi ayau Ni Tasi’u ban d’aurawa Noor idda ba dan kuwa harna koma ga mahalicci na aurenmu bai gama cika cikkenken aure ba dan bamu ta6a had’a shimfid’a a matsayin mu na ma’aurata ba saboda wasu dalilai masu k’arfi wanda da farko naso ace idan na samu lafiya mu ziyarci malami amma kuma sai naga yanayin da nake ciki zaiyi wuya in tashi shiyasa na umurce ta data rubuta domin rana irin haka, kar kuga laifin Noor domin kuwa matsalar ba daga gurinta bane daga gurina ne, abu na gaba shine inason abata shagona halak malak idan ma saidawa zatayi duk ba damuwa bane gida kuma dana gina na barwa kawuna ya rike tunda bani da iyaye a raye kuma bani d’a acikin fad’in duniya, sai kuma kud’i dana bari a cikin asusun banki a ginamin k’aramin masallaci ko kuma a hak’a rijiya a inda ruwa ke wahalar samu daga k’arshe ina neman yafiyarku akan abunda nayi ina sane da wanda nayi bisa rashin sani Allah ya had’a fuskokin mu a cikin Aljanna” malam yana gama karantawa kowa yayi kabbara Noor kuwa ta fashe da kuka domin mutuwar sabuwa ya dawo a gareta.
Kowa a gurin ya jinjina wannan lamarin sai dai kuma sun sani cewan haka Allah ya tsara shiyasa dan haka basu da ja akan abunda ya faru sai dai fatan Allah ya bawa Noor hakuri a cikin zuciyarta, sai da tayi kuka har ta gode Allah kafin malamin yayi y’ar nasihar sa game da rashin sanarwan da tayi tun afari dan da ace an sani da baza tayi zaman da tayi a gidan har zuwa wannan lokacin ba sai dai ya danganta hakan da kuruciya sannan yayi nasiha mai ratsa zuciya da jiki ya kuma karayiwa mamacin addua sannan suka musu sallama tare da fatan alkairi.
Bayan tafiyarsu Kawu ya kara yiwa Noor fad’a akan shurun da tayi sannan ya tambaye ta shin ko tana son a sayar da shagon ta amsa da eh saboda ba zata kara sati acikin garin kano ba dan garin ya fita aranta tunda ta rasa mijinta madubin rayuwarta, fita kawu yayi ya samu dillalai aka saya akan farashi mai nauyi fiyeda zaton Kawun daga nan ya nufi banki tare da cire kud’in da tasi’u ya bari sannan ya dawo gida, kud’in shagon ya bawa Noor sannan ya sanar dasu cewa ya ciro kud’in zuwa gobe zai bincika inda ake bukatan masallaci sai a gina da yardan Allah sosai sukaji dadin abunda Kawun yace sannan suka mishi sallah suka tafi akan cewa zasu aiko a kwashe kayan Noor din zuwa yamma.
Bayan sun koma gida su Mimi sunyi murnar ganin ‘yar uwarsu kuma uwa a garesu sai da suka gama ihun murnan sannan kuma suka shiga gaishe ta da kara kwantar mata da hankali, kamar yanda Baaba Azumi ta fad’a haka kuwa akayi da yamma ta tura dillalai suka kwaso kayan tare da yiwa kayan kud’i yanda ya dace kuma ta samu mutanen kirki domin abu kad’anne kawai ya rage akan farashin data sayi komai godiya tayi musu ta amshi kud’inta suka shiga cikin gida ita da Aminatu.
A zaune ta samu Noor din ta zuba tagumi da alama tunanin mijinta takeyi ita kuma Mimi sai daman hira take mata ba tare data lura cewa Noor din tayi zurfi a tunani ba zama Baaba Azumi tayi kusa da ita kafin ta cire mata hannu da tayi tagumin “haba d’iya ta gari mai yasa ba zaki sanyawa zuciyarki hakuri ba wannan abu dai ya riga ya faru babu yanda zamuyi sai dai mu kara yiwa Allah godiya, shin kina son ki nunawa duniya cewa ba zaki iya kar6an kaddaranki hannu bibbiyu ba shin kina jayayya da hukuncin ubangiji ne haba Noor dan Allah ki sanyawa zuciyarki hakuri hakanan kinji koh”.
Hawaye Noor ta share kafin tace “Baaba ina neman alfarma a gurinki idan har zan iya samu, tunda kince bakida kowa a cikin garinnan mai zai hana mubar cikin garin Kano mu koma wani gari daban mu fara sabuwar rayuwa?”.
Ajiyar zuciya Baaba tayi kafin tace “tabbas haka yake bani da kowa sai k’awaye na gari da kuma ku da Allah ya azurtani da samu, tunda har kina ganin cewa zaki samu natsuwa idan mukabar garin shikenan nima na amince ko zuwa gobe ma mu tafi sai dai shin wani wani gari ya kamat mu tafi?”.
Cikin farin-ciki Noor tace “Baaba mai zai hana mu tafi garin Gombe ko kuma garin Bauchi”.
Murmushi Baaba Azumi tayi kafin tace “shikenan sai muje Gomben zuwa gobe in Allah ya yarda dama gobe kud’in hayan mu zai kare kinga komai ya tafi a daidai kenan ko, yanzu ku kiramin Yusufu almajirin gidannan yazo ya kwashi kayan da baza mu buk’ata ba idan yaso zuwa gobe sai ya k’arasa kwashe sauran”.
Da sauri Mimi ta fita dan kiran Yusufu Noor kuma suka cigaba da tattauna wa akan tafiyar tasu.
Har zuwa washe garin dawowan Dr Affan basu had’u da Hajja Hadiza ba saboda aikin dare daya sake fita bai koma gida ba sai washe gari da safe lokacin kowa na barci shima kuma ya kwanta dan huta gajiya, ko da suka tashi breakfast bai fito ba hakan yasa Auta ta sanya nashi a tray ta kai 6angarensa.
Karfe sha d’aya ya tashi daga barcin gajiya bayan yayi wanka yayi brush sannan ya nufi 6angaren Hajiya dan ya gaisheta ko da ya shiga bai taras da kowa a falon ba hakan yasa ya nufi d’akinta, da sallama ya shiga bayan ta amsa ya samu guri ya zauna sannan ya gaishe ta sai da suka d’an ta6a hira sannan yake tambayan su Auta da bak’in Hajiya anan take cewa ai sun fita ta aike su gidan kawarta okay kawai yace sannan ya mata sallama akan zai tafi yaci abinci.
Kusan atare suka shigo gidan dashi lokacin ya dawo daga sallar azahar su kuka sun dawo daga gidan kawar Hajiya d’aga musu hannu kawai yayi sannan ya wuce baki bud’e Ghaji take kallonsa har zatayi magana sai kuma tace kila idonta ne kuma batason tayi magana ta tayar da hankalin kawarta daga haka suka shiga cikin gida a lokacin Hadiza batasan abunda ke faruwa ba dan idonta na kan waya.
A falo suka yada zango Auta ta dhiga da sakon Hajiya zuwa d’aki sai da suka huta sannan suka zuba abinci dafeffen doya da sauce wanda yaji kifi a cikinsa sai kuma lemon gwanda wanda Hajiya tayi da kanta, bayan sun gama Auta tace su tashi suje su gaida Dr Affan babban abunda yasa basu gane gidansu Dr Affan bane shine basu ga hotonsa ko kuma sunji an ambaci sunansa ba dan Auta yayana kawai take cewa ko tace Dr.
Da sallamasuka shiga falonsa zama sukayi a k’asa ita kuma Auta ta mishi knocking k’ofa sannan ta dawo ta zauna, kallon falon sukeyi yanda yayi kyau kamar gidan wata amarya komai na ciki blue da golden ne babu wani tarakuce daga kujeru set d’aya mai kyau royal design sai dinning table me kujera uku sai babban plasma Tv da Dstv decorder a ko wani kusurwa akwai flower vase wanda ya k’awata falon a tsakiyan falon kuma akwai wani carpet babba mai laushi irin masu gashinnan sosai suka bada hankali gurin kallon falon da yabawa da tsarin Auta kuma hankalinta na kan Dadin kowa da ake gabatarwa a arewa24.
STORY CONTINUES BELOW

Fitowa yayi sanye da dogon wando baki da kuma farin shirt sosai kayan ya mishi kyau kasancewarsa fari kamar Hajiyarsa ba kamar Auta da take wankar tarwad’a kamar Abbansu ba haka Ghaji ma take wankan tarwad’a kamar Babanta Hadiza ce kawai mai haske sosai har taso tafi Dr Affan ma musanman yanzu da fatanta ya kara samun gyara na amfani da takeyi da mai masu tsada sannan ga cima mai kyau fiyeda wanda take samu a gidansu hakan ya kara gyara mata fata da jiki baki d’aya.
Kamshin turarensa ne ya sanar dasu zuwansa cikin falon domin Dr Affan akwai son kamshi duk wani turare masu tsada yakan 6ata kud’in sa gurin saya saboda yafi son a ko wani lokaci kamshinsa ya fita daban shiyasa komai nasa yake unique.
D’ago kansu sukayi dan amsa sallamarsa wanda tunda ya shigo falon da kamshinsa ya ziyarci hancin Hajja Hadiza ta fara saka da warwara akan son tuno inda ta ta6ajin wannan kanshin kafin ta gama tunani yayi sallama inda tayi saurin d’ago idanunta gabanta na fad’uwa saboda jin muryan masoyinta abun kaunarta wanda take dakon kauna wanda ta cire rai da tsammanin sake had’a hanya da shi sai dai wannan karon tayi alkawarin koda ace sun had’u zatayi kokarin kau da kai ta nuna itama bata gane shiba sai dai kuma yanzu zuciyarta na son ruguza mata tsari yana azalzalarta son shi na kokarin kara dawowa sabo a cikin ranta harma takejin kamar yafi nada zugi.
Tsaf Ghaji ta gane shi sai yanzu taga wautanta na kasa gane cewa d’an uwan ta nema ashe dan kuwa kamannin shi da Hajiya ba k’aramin kama bane sosai yake yanayi da ita kasancewar ta ita ma doguwa ce kuma bata cika jiki ba shima haka yake kamarta tsaki taja aranta tana ayyana irin rashin mutuncin daya dace Hadiza tayi mishi domin a yanzu duk wanda ya ganta dole ne yaji ta kwanta a ransa basarwa kawai tayi dan kunsan mutuniyar taku bata son raina balle yanzu da ta shigo birni ta k’ara wayewa ta6e baki tayi kafin tayi murmushin mugunta tana mintsinin Hadiza data zuba mishi ido kamar mayya ajiyar zuciya tayi sannan suka gaisheshi a tare ya amsa da fara’arsa Ghaji ta kara da cewa “yau dai yayan mu Allah yayi zamu had’u da fatan ka dawo lafiya ya aiki?”.
Kallonsu yakeyi yana kokarin son tuno inda ya ta6a ganinsu amma ya kasa tunawa karshe dai ya bari kawai akan cewa kamace tunda kuma ai ance d’aya y’ar uwarsa ce kila ya ta6a ganinsu tare ko kuma kamace kawai shiyasa yake ganin kamar ya ta6a ganinsu murmushi yayi yace mata “lafiya lau yau Allah yayi naga kannen nawa da fatan dai kunajin dadin zaman gari Bama kuma kuna karatu sosai?” ya fad’a hankalin sa nakan Hadiza data sunkuyar da kanta cikin jin haushin bai ganeta ba.
Dad’i Ghaji taji da taga cewa bai gane su ba hakan ya k’ara bata damar cigaba da hiran cikin kwanciyar hankali da natsuwa Hadiza kuwa haushi ne ya k’ara kamata sosai dan ba hakan taso ba hakan yasa kawai ta kara maida hankali kan kallon Tv duk da ba wani ganewa za’a ce takeyi ba saboda gaba daya hankalinta na kan masoyin nata Auta kuwa batasan wainar da ake toyawa ba tunda ta gaishe shi ta maida hankali kan kallonta bata sake kulasu ba.
♣🌹♣☘♣🌻♣
*🌻f¢т αвυʝα*
*♣gωαяιмρα*
Har zuwa wannan lokacin ya kasa samun soyayyarta sai dai koba komai ta rage hararansa da kuma yi mishi abunda taga dama sosai ta mai da hankali kan karatunta dadin shi d’aya shine ita ba mai kule kulen samari bace shiyasa ma yake ganin abun zai zo mishi sa sauki.
2
Zaune yake a branda yana tunanin rayuwa yanda abubuwa suke tun farko har zuwa wannan lokacin da Allah ya dauka ka shi ada ya kasance cikin duhu a yanzu kuma Allah ya mai dashi cikin haske tabba ba shida abun cewa sai dai yayita hailala ga ubangiji domin Allsh ya soshi da rahama shiyasa ya kyautata rayuwarsa.
2
Karan wayarsa ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya tafi ganin sunan dake yawo a jikin wayan yasa hankalinsa ya tashi domin kuwa yasan wannan lokacin babu makawa dole ne ya bar gidansu Yasmeen ko yanaso ko bayaso har wayan ya tsinke bai iya d’agawa ba sai da aka kira a karo na uku sannan ya daidaita natsuwarsa ya d’auka tare dayin sallama.
Ajiyar zuciya na cikin wayar yayi kafin yace “ina ka shiga ne haka Mustapha inata kiranka shuru baka d’auka ba kasan cewa wa’adin daka d’auka sun riga sun cika dan haka dole kayi hakuri ka dawo bakin aiki idan har Allah yayi yarinyar rabonka ce toh fa babu makawa sai ka aureta dan haka ka sanyawa zuciyarka salama kayi hakuri ka kwantar da hankakinka komai ya faru da bawa rubutacce ne kuma Allah baya barin wani dan wani yaji dadi sannan matar mutun kabarinsa”.
2
Mamakine ya kama shi yanda akayi Ogan nasa yasan dalilin zamansa a gidan koda yake bai dace yayi mamaki ba tunda aikinsu kenan bincike da bin diddigi murmushi mai ciwo yayi duk da cewa yaji dadin abunda Ogan yace na kokarin ganin ya kwantar masa da hankali kafin yace “insha Allahu gobe zan dawo kuma nayi alkawarin komawa bakin aikina gwargwadon iyawa na sannan kuma idan ban samu shigowa a goben ba ayimin afuwa domin saina bi ta gida na duba yara da kuma mahaifiyata”.
Dadi Ogan yaji akan abunda Moses din yave domin bai yi tsammanin cewa abun zai zo mishi da sauki ba dan Moses akwai kafiya da taurin kai “Babu komai ai bukatan mu shine muga ka dawo an cigaba da aiki yanda aka saba dan kuwa a yanzu haka mun samu gidan Muhammad Nur din kuma shi k’ani ne ga mahaifin Yasmeen din bincike ya biyo ta kansa dan haka nextweek muke so kayi reporting a gida”.
2
Chakwakiya ya fad’a a ransa fatansa Allah yasa shima bashi da matsala kamar Abban Yasmeen “Insha Allahu zanyi iya kokari na inyi aiki na bisa k’aida kuma baza asamu matsala ba kamar yanda aka saba samun nasara wannan karan ma zamu samu da yardan ubangiji sai na shigo goben yallabai”.
Murmushi Ogan nasa yayi sannan ya ajiye wayan bayan ya mishi adduar Allah ya kawo shi lafiya cikin koshin lafiya kuma Allah ya biya mishi bukatun nasa idan har alkairi ne agareshi, sosai yaji dadin adduar kuma ya sake samun natsuwa shiyasa yake matukar daraja Ogan nasa domin mutunne mai saukin kai da sanin yakamata.
2
Charles ya kira wani yaronsa da yake aiki a karkashinsa ya bashi umarnin ya gyara mishi kayan shi baki d’aya sannan ya kira layin Al-Hussain domin ya mishi iso zuwa gurin mahaifin su idan yana gida saboda tattaunawar da zasuyi mai mahinmanci ne bayan ya ajiye wayan ya shiga ya chanja kaya zuwa Suit mai kyau sannan ya kira sauran yaransa suka shigo kowa sanye da suit ajikinsa.
Sallama sukayi a babban falon gidan sannan suka shiga baki d’aya yaran gidan suna falo amma ta wani 6arayi daban Abbi kuma yana tare da Ummi suna zaune a guri d’aya sosai kowa a gurin yayi mamakin ganin Moses da kuma shigarsa da mutanen dake biye dashi bayan sun zauna Moses ya fayyace mishi komai game da shi da kuma aikin da yakeyi sannan ya sanar mishi cewan ya kammala aikinsa dan haka gobe insha Allahu zai bar garin dan akwai wasu aikin a gabansa yanzu ma sallama yazo musu tare da neman yafiya idan ya musu ba daidai ba.
Sosai Abbi yayi mamaki bama shi ba dukansu yan gidan musanman mutuniyarsa wanda take tsananin mamakin cewa Moses din musulmi ne kuma sannan shi din jinin sarauta ne wannan abun shine yafi k’ara bata mamaki ido kawai ta zuba mishi sai yanzu ma ta ta6a kare mishi kallo saboda ada k’ank’aminsa takeyi kasancewarsa ba musulmi ba amma ahalin yanzu wani abu ta faraji game da shi wanda ta kasa tantancewa.
2
Handala abbi yayi da ya kasance mutumin kwarai kuma yake aiki da zuciya daya ba tare da ya cuci al umma ba inba haka ba da ya zaiyi da ransa a irin wannan rana da tabbas ya kunyartar da kansa da iyalinsa baki d’aya godiya yayiwa Moses din tare da adduar fatan alkairi kuma ya nemi alfarman ya rika kawo musu ziyara idan ya samu lokaci shi ma godiya yayiwa Abbi daya fahimce shi kuma yayi alkawarin idan ya samu lokaci zasu ganshi aransa yace ai ko dan ya zo yaga Yasmeen ai dole su ganshi ma.
Sallama suka musu tare da fatan alkairi suka bar su cike da al’ajabin wannan rayuwa mai cike da rud’ani da abubuwan mamaki sannan suka kwashe kayansu suka zuba a booth suka bar gidan zuwa Area11 masaukinsu na asali kafin su bar garin washe gari idan Allah ya nufa.
Hira sukayi sosai kafin suka mishi sallama suka koma cikin gida danyin sallar la’asar, sai da Hadiza ta bari Auta ta shiga band’aki sannan ta kalli Ghaji wacce ta nuna kamar babu wani abu da ta gani a yau kuka kawai Hadiza ta fashe da shi wanda Ghaji tayi saurin toshe mata baki sannan tace “kina hauka ne meye haka kuma yanzu idan Hajiya ta shigo sai kice d’anta kike so kuma baya sonki shiyasa kike kuka ko kuwa dai mai zaki ce da ita dan wannan kukan duk wanda ya gani yasan ba kalau kike ba”.
Daurewa tayi ta tsayar da kukan iya k’arfinta dan kuwa Ghaji ta fita gaskiya yanzu idan Hajiya ta shigo mai zata ce mata da girmanta dai ba zata ce kewan gida ne ya sata fashewa da kuka ba dan haka kokarin daidaita natsuwarta tayi sannan ta tashi ta fita zuwa toilet din falo dan kar Auta ta fito ta ganta taja kuka ta santa da iya bin diddigi bayan tayi alwala sai ta koma d’aki lokacin har Auta ta fito ta fara salla.
2
Harara Ghaji ta mata sannan ta shige band’ajin tana fatan kar Allah yasa Hadiza ta kwafsa mata dan so take Dr Affan ya tsunduma cikin soyayyar aminiyarta yanda ba zai iya ba ita ba kafinnan ta bayyana kanta amma da alama Hadiza bazata iya daurewa ba kwafa tayi sannan ta fara alwala.
2
Bayan sun idar da salla suka fara karatun kur’ani kamar yanda suka saba bayan ko wani salla sai sunyi kamar izfi d’aya ko rabin izfi kafin su tashi daga kan sallaya wannan shine tarbiyyan Hajiya.
Sai da suka karanta daga nasi zuwa sabbi sannan sukayi addua suka nad’e sallayan tare da ajiye al kuranin a mazauninsa musabaha sukayi da juna yanda Hajiya ta koyar dasu bayan ko wani salla ayi musabaha da juna dan kore shaidan a tsakani kafin suka fita suka nufi d’akin Hajiya dan taya ta hira.
Da sallama suka shiga cikin d’akin bayan ta amsa musu suka zauna saman carpet tare da mata barka da hutawa sannan suka shiga hira kamar yanda suka saba labarin yan uwa da kuma tarihin maganata suna cikin haka sai Dr Affan shima ya shigo tare da zama kusa da Hajiya tun da ya shigo idonsa na kan Hajja Hadiza har sai da Hajiya itama ta lura da hakan murmushi kawai tayi suka cigaba da tattaunawarsu shima ya jona su duk da haka ako wani lokaci yana satan kallonta kuma ko wata magana yana kokarin sanya ta a ciki ita kuwa tunda ya shigo ta rasa natsuwara wayoyin jikinta suka daina aiki gaba d’aya jikinta yayi sanyi jefi jefi take d’anyin magana har sai da abun ya basu mamaki Hajiya ta tambaya ko lafiya take tace kanta ke ciwo Ghaji ce kawai tasan ainihin abunda ke damunta.
STORY CONTINUES BELOW

Sai kusan biyar suka cewa Hajiya zasu kitchen domin d’aura abincin dare shi kuma Dr yayi zaman sa suka cigaba da hiransu irin na uwa da d’a inda take tambayansa ko akwai wani cigaba akan inda Noor suke yace har yanzu shuru, nasiha ta mishi mai ratsa zuciya inda ta nuna mishi mahinmancin hakuri da kuma yarda da kaddara sannan ta kara da cewa ya kamata ya samu mata yayi aure idan har Noor rabonsa ce nan gaba zasu sake had’uwa domin ita kanta tana kaunar Noor din kuma zataso had’a zuri’a ita duk da cewa batasan ainihin tarihin rayuwarsu ba.
2
Godiya yayiwa Hajiya tare da alkawarin neman mata da yardan ubangiji, sosai taji dadin amsarsa agareta danta k’osa yayi aure itama taga jikokinta dagana suka cigaba da hiransu har zuwa sanda aka kira sallan magriba sannan ya tashi ya tafi masallaci ita kuma Hajiya ta shiga band’aki tayi alwala.
A6angaren su Auta kuwa tuwon alkama suka tuka da miyar kuka wanda yaji naman saniya da man shanu sannan suka had’a kunun aya dayaji kwakwa bayan sun kammala su ka jera abincin a dinning kafin suka gyara kitchen din tsaf ya zama kamar ba’ayi aiki a ciki ba.
D’aki suka koma sukayi alwala sukayi salla kafin suka nufi dinning Hajiya da Dr Affan suka samu a zaune suna jiransu bayan sun zauna Hadiza ta zubawa Hajiya Ghaji ta Zubawa Dr Affan sannan Auta ta zuba musu nasu bismillah sukayi sai da Hajiya ta faraci Affan ma ya faraci sannan suma suka faracin nasu babu abunda kakeji a cikin falon sai karan Tv da kuka kamshin turaren wuta.
Kusan minti ishirin sukayi kafin sukayi hamdala ga ubangijinsu daya basu abinda zasu sanya acikinsu ba wai dan yafi sonsu ba sai dan hakan ya tsarawa musu kuma sunyi imanin cewa idan yaso ya jarabe su zai iya jarabtansu ta ko wani hanya musanman ta fannin rashin abubuwa kaman na more rayuwa irin wanda suke dashi a yanzu sai da sukayi addua sannan suka tattare kwanikan suka kai kitchen.
2
Haka rayuwa ya cigaba da tafiya musu cikin annashuwa da lumana komai sunayin shi cikin natsuwa da kwanciyar hankali basu da wani matsala da zaman gidan Hajiya saboda gidanta ko masu aiki ne suna cikin kwanciyar hankali ba tare da wani damuwa ba balle kuma suda suke yan gida wanda babu banbanci a tsakaninsu da Auta a garera kullun godiya suke da Allah ya basu ikon zuwa gidan Hajiya a matsayin y’ay’anta shirye shiryen komawa school sukeyi dan kwanaki kadan ya rage musu a hutun da aka bada sosai suka dage gurin karatu dan ganin sun cimma burinsu kuma sun saka wa Hajiya ta hanyar sata farin ciki, Hadiza tayi matukar dauriya gurin kai zuciyarta nesa akan Dr Affan duk da cewa ko wani lokaci soyayyarsa karuwa yake aranra sai dai ta dage da adduar Allah ya sanya sonta da kaunarta a ransa fiyeda yanda ita take kaunarsa, sosai Ghaji taji dadin hakan kuma ta cigaba da bata shawarwarin daya dace.
6angaren Dr Affan kuwa ya fara shiga wani yanayi akan Hadiza ya farajinta aransa sosai fiyeda k’ima kuma fiyeda yanda yayi tunani sai dai baya fatan hakan ya kasance wani abu makamancin K’auna ko Soyayya domin Noor dinsa na nan mak’ale a cikin ransa kuma yana matukar sonta da kaunar ta, a kullun yanzu idan bai ga Hadiza ba bayajin dadin rayuwarsa sai dai har tanzu ya kasa yadda da cewa zuciyarsa na tare da ita kuma ya kasa yadda cewan sonta ne ya kamashi kawai yana ganin hakan a matsayin wani abu wai kusanci da suke samu da juna shine take burgeshi dan bata kasance mai yawan surutu ba kuma tana da kunya duk sanda suke tare ana hira sai dai tayi murmushi ko tayi amfani da kai gurin bada amsar.
♣🌹♣☘♣🌻♣
*🌻gσмвє ѕтαтє*
*♣мαѕαяαυтα*
Su Mustapha sun isa garin Gombe cikin koshin lafiya direct Masarauta suka nufa suna zuwa ya fara tsayawa a fada dan ya gaisa da dan uwanasa kuma sarki a yanzu wato mai martaba sarki Aliyu Hydar miji agurin Fatima Human Tansy shekaran sa hud’u kenan akan karagar mulki tun bayan rasuwan mahaifinsa sarki Abdurrahman bayan sun gaisa ya nufi cikin gida chan 6angaren mahaifiyarsa wato Gamboji.
Sosai tayi farin cikin ganin shi a lokacin da ba tayi tsammani ba dan bai sanar mata da zuwansa ba haka yaransa suma sai murnan ganin shi sukeyi shima kuwa yaji dadin ganinsu cikin koshin lafiya zama yayi suka gaisa kafin suma yaran suka gaishe shi daganan suka bude babin hira sai da aka kira sallan la’asar sannan suka tashi dan gabatar da ibada.
Bayan ya dawo daga salla ya nufi 6angaren shi dake cikin gidan yayi wanka sannan ya sanya k’ananan kaya, abincin da aka kawo mishi ya d’an ta6a kad’an dan baya wani jin yunwa saboda sunci abinci a mota bayan ya gama ya d’auki makullin motarsa ya nufi gurin Gamboji.
Ita kad’ai ya taras a falon tana kishingid’e a jikin tum-tum tana lazumi sai daya bari ta gama sannan ya kara gaisheta tare da sanar mata dalilin dawowarsa da kuma aikin da aka sanya shi fatan alkairi tayi mishi kafin ta sake d’auko zancen aure tana cewa wannan karan yana gama aikin matukar bata ji wani labari mai dadi ba wallahi aure zata mishi da wanda taso kuma kar yayi tunanin cewa zata k’ara d’aga mishi k’afa domin wannan shine damarsa ta karshe idan ya sama wa kansa to ya kyauta idan kuka baiyi ba tabbas zai samu amarya yana dawowa da sati guda kuma babu fashi, sosai maganar Gamboji ya chaki zuciyarsa kuma wannan karan yasan babu zancen d’aga k’afa yanzu kam babu abunda ya saura mishi daya wuce adduan neman za6in Allah domin ya gama sarewa da lamarin Yasmeen kuma gashi aiki ne agaban shi balle ya kara samun daman tunanin mafita “insha Allah zanyi biyayya a duk hukucin da kika yanke idan lokaci yayi ba tare da na samu mafita ba” wannan shine abunda ya fada kafin ya kira yaran sa domin suzo su zaga gari.
15
Ogan shi ya kira ya sanar dashi isowarsu tuntuni da kuma uzuri sa ayanzu akan cewa washe gari da sassafe zai shiga office din, fatan alkairi Ogan ya mishi tare da cewa ya gaida yaran, gurin wasan yara suka nufa sai da su kayi wasa har suka gaji sannan suka nufi Zoo dan ganin namun daji daganan sukaje gurin shan ice cream sai yamma suka dawo gida daf da kiran sallan magriba matan suka sauke su kuma suka tafi masallacin masarauta.
Su Noor basu taso da wuri ba sai da akayi azahar saboda gidajen kawayen Baaba Azumi da suka shiga danyi musu sallama da kuma wasu makwabta inda sai da suka dad’e kafin suka nufi gidansu Tasi’u bayan sun fito suka garzaya tasha inda suka hau motar Gombe.
7
Karfe shida suka shiga cikin garin lokacin gari har ya fara duhu abinci suka saya a cikin tashan bayan sunci sun koshi sukayi alwala da ruwan bakin masallacin dake a cikin tashan kafin sukayi sallah daganan sukaga gwara kawai su kwana a cikin masallacin tunda akwai 6angaren mata kafin washe gari su nemi gida madaidaici dai-dai talaka tunda suna da kud’in da zai ishesu haka kuwa akayi bayan sallan isha’i sukayi kwanciyarsu dan huta gajiya.
Sad’af sad’af ya shiga cikin masallacin da d’an karamin tocinsa sai daya chaje jakan kowa ya samu na d’auka sannan ya fita a hankali ya shiga 6angaren mata nan ma Allah ya bashi sa’an samun kud’i masu yawa daga ciki harda kud’in Baaba Azumi da kuma na Noor hankali kwance yayi ficewarsa yana mai farin cikin samun kud’i masu yawa fiyeda yanda yake samu kullun sai dai dake Allah yayi ba zaici kud’in ba shima wasu 6arayi suka yashe shi suka barshi da dana sanin d’auko kud’in a hanyarsa ta komawa gida kuma mota ta kad’e shi har lahira (duniyan kenan kana naka Allah na nashi shiyasa yake da kyau mu yawaita aikin aikairi domin bamu san ranar tafiya ba).
7
Washe gari mutane suka tashi babu ko sisi a jikin su saboda yashesu da akayi kowa yayi ta jan Allah ya isa domin wani shikenan gare shi wani ma kud’in ajiya ne wai a masallaci ma baza’a bar mutun ba sai anyi mishi aikin da zai rasa ina ya dace ya fake dan samun tsira daga miyagun mutane, sosai su Noor sukayi kuka domin yanzu shikenan basu da komai a jikinsu sai yan kayansu Baaba Azumi ce tace su d’an zauna zuwa wani lokaci har suga yanda Allah zaiyi.
Sai bayan sallan ishai ya koma cikin gida yaransa ya sake kira dan yaji ko suna da matsala sai da ya tabbatar ya musu duk abunda ya dace kafin ya ce duk suje su kwanta har sun tashi zasu tafi sai Auta Zahra ta dawo tace “Abba ba kace zaka kawo mana Momy ba” da sauri Halima tace “yauwa Abba har yanzu fa baka kawo mana sabuwar uwa ba kuma kowa a school yana da Momy” tausayin yaranne ya kama shi ba kamar Auta da bata tashi taga mahaifiyarta araye ba, Hafsa tace “dan Allah Abba muma fa muna son Momy din” ita dai Aisha sarkin miskilanci kallon su kawai takeyi dan kuwa tana kishin mahaifiyarsu kuma babu wata mace da zataso ta zauna tare da Abbansu Hafiz ma dai duk kanwar jace shima bayason Abba ya kara aure shuru yayi yana mai jin haushin kannensa, sai da Mustapha yayi ajiyar zuciya kafin ya d’ago ido yana mai kallon manyan yaran nasa yana nazarin su tabbas ya hango wani 6acin rai atattare dasu sai dai dake miskilai ne ai dama yasan baza suce komi ba shi babban dalili auren da yake sonyi ma saboda yaransa k’anana ne tausayinsu yakeji dan yasan zafin rashin tashi da iyaye, rarrashin su yayi tare da alkawarin yana dawowa za’a kawo musu Momy da haka ya samu suka tafi d’akunan su bayan sun tafi zama yayi yana tunanin mafita kafin daga baya ya tafi gurin Gamboji suka d’an ta6a hira zuwa tara yayi mata sallama ya koma 6angarensa dan huta gajiya sai dai tunanin yaransa shine a cikin ransa har barci 6arawo yayi awun gaba da shi.
2
Washe gari da sassafe ya shirya cikin english wears riga da wando ya d’aura coat akai, abinci ya zauna yaci tare da yaransa bayan ya gama ya musu sallama ya tafi dan amsa kiran Ogansa bayan fitan sa su Hafiz suka sa ‘yan kannensu a gaba akan su ajiye batun new Momy in ba haka ba zasu daina kulasu sosai hankalin yaran ya tashi dan suna matukar aunar yayyinsu saboda suna sonsu sosai suna basu kulawa dai-dai k’arfinsu hakuri suka bawa yayyin tare da alk’awarin dena maganar new Momy dadi su Hafiz sukaji daganan suka koma 6angarensu gurin Gamboji.
2
CID office ya nufa tunda ya shiga ake gaishe shi daga kan securities din kananan ma’aikata har zuwa kan manyan domin suna matukar daraja shi saboda yanda yake aikin nasa cikin kwarewa da burgewa cikin kankanin lokaci ya samu d’aukaka fiyeda wad’anda ya samu akan aikin domin sai da aka turashi makarantar horo na musanman daga nan ya samu certificate na tabbatar da zamansa cikekken ma’aikaci tunda hakan ya kasance kuwa ya kulla d’amaran aikinsa cikin gaskiya, jajircewa, da rikon amana, salonsa da kwarewarsa ta fannin aikinsa ya janyo mishi d’aukaka da karin girma cikin lokaci kad’an ya shahara a ma’aikatan nasu kowa so yake ace yana mu’amala dashi sai kuma cikin sauki suka samu yanda suke so din kasancewarsa mutun mai sanyin hali da kuma son jama’a mahassada ma dai sun buga sun bari domin duk ya wuce karfin tunaninsu hakan ya saka suka ajiye makaman yaki suka bishi cikin k’unan rai dan kuwa da yawan masu aiki a k’arlashinsa duk manyan ma’aikata ne wad’anda suka dad’e a cikin aikin a yanzu haka ya zama d’aya daga cikin shugabannin masu bada horon aikin CID a k’asa baki d’aya.
2
STORY CONTINUES BELOW

Tun yana amsa gaisuwar da baki har ya gaji da amsa wa ya koma d’aga musu hannu tare dayin murmushi, da sallama ya shiga office din bayan an amsa aka ba shi izinin zama, zama yayi cikin natsuwa sannan ya gaida Ogan bayan ya amsa ya d’ago kai ya kalleshi tare da ajiye biron da yake rubutu “barka da dawowa lover boy dafatan kun iso lafiya kuma kun samu kowa lafiya?”.
Murmushi yayi da yaji abunda Ogan nashi ya kirashi dashi “lafiya kalau kuma kowa lafiya, Sir da fatan kuma mun sameku lafiya cikin koshin lafiya?”.
“Lafiya kalau sai aiki daya taru yayi mana yawa sai dai tunda ka dawo yanzu d’aya zai ragu kuma na bawa Yusuf na shi gobe zai wuce garin Adamawa akan wannan mutumin da ake zargi da safaran miyagun kwayoyi sannan ‘yan mata da k’ananun yara da suke kaiwa chan k’asar waje da naso in baka wancan d’in amma dana bincika naga suna da alak’a dasu Yasmeen yasa na yanke shawaran baka wannan aikin kuma da fatan zaka bada kaifi akai?” ya fad’a yana kallonsa.
Ajiyar zuciya ya sauke yana mai adduar Allah yasa shima ya kasance mutumin kwarai kamar d’an uwansa domin ba zai so ace ya kulle kawun Yasmeen ba “insha Allah zanyi iya kokarina dan ganin cewa babu miskila idan har da hannunsa cikin 6ata k’asar mu nayi alkawarin rage iri kamar sa idan kuma yana cikin mutane na gari shima nayi alkawarin wanke shi agaban hukuma”.
“Hakan yana da kyau nayi farin ciki kuma na yarda da kai nasan baza ka bari azzalumai suyi ta yawo a gari ba kuma na sani cewa baza ka bari a cuci mai gaskiya ba, ga wannan (ya mik’a mishi wani file mai dan girma) report din da muka samu kenan akan Muhammad Nur da duk wani shige da fitansa babban abun ma shine anfi zargin matarsa akansa sai dai lokaci zai mana bayanin komai”.
Kar6a yayi ya bud’e wasu hotuna guda hud’u suka fad’o d’aya hoton wata kyakyawar mace ce da yara shida duk yan mata sai kuma wani daban duk dai iri d’aya dana farkon amma akwai wani dattijo aciki alamun cewa baban sune sai kuma a d’ayan hoton dattijonne da yaran ba matar a ciki sai dayan kuma dattijonne da wata mata sai ‘yarta a ransa yace kenan matansa biyu ne sai dai abun mamaki duka mata biyun suna dan yanayi daga fuska har jikin sai dai na farkon tafi haske kuma karamin jiki gareta ta biyun kuma wankan tarwad’a kuma tafi na farkon girman jiki kaman ma itace babba kallon su yakeyi yana wani nazari wanda ba shida abun kamawa sai dai nan gaba kadan idan ya shiga gidan zai san gaskiyan lamarin.
Wani karamin takarda ya sake ciro wa wanda aka rubuta sunan mutumin ajikinsa da manyan baki wato Muhammad Nura sai kuma sunan matarsa Maheeda Aliyu Bomai da Mardiyya Aliyu Bomai sai sunan yaran Fatima Noor Nusaiba, Nafisa, Habiba, Hauwau, Aminatu sai ta karshen Khadija mimi sosai ya tsurawa yaran ido saboda dagani hoton ya jima dan ta karshen ma bazata wuce shekara hudu ba abun mamakin ma shine surname din matan daya kasance iri d’aya kuma Aliyu Bomai indai wanda ya sani ne tabbas shahararren mai kudi ne kuma malami a cikin garin Yobe amma kuma mutumin kaman ya d’an jima da rasuwa sai dai asannu zai san alakar matan da juna da kuma alakarsu da Aliyu Bomai din daya sani numfasa wa yayi kafin ya tattara abubuwan ya maida cikin file din.
“Sir nagani sannan gobe da sassafe nake tunanin zan wuce amma ta jirgi zanbi sai in sauka a cikin maiduguri zanfiso in tafi ni kad’ai idan har ina da bukatansu Danial zan sanar maka ko kuma in kirasu sai su sameni a chan din sannan inaso ayi min booking hotel domin in sauka a ciki in kara binciken gidan da kyau yanda zan samu damar shiga cikin sauki kuma in kama aikina ba tare da an zargeni ba” abunda ya fad’a kenan yana kokarin tashi daga kan kujeran.
Hannu Ogan ya mik’a mishi sukayi musabaha yana cewa “shiyasa kake burgeni saboda kaifin basira da iya nazari mai kyau da ma’ana Allah ya kai ka lafiya kuma ya bada sa’an abunda akaje nema gobe zasu zo su kaika airport din”.
Godiya yayi sannan ya fita sai da ya biya office dinshi ya d’auki wasu abubuwan da zai bukata sannan ya musu sallama ya tafi, a wani masallaci ya tsaya yayi sallah sai daya dad’e yana adduar samun nasara kafin ya biya gurin saida gasasun kaji bayan a saya ya kara da fura da nono sannan ya tada motar ya kama hanyar gida.
Kiiiiiiiiiiiiiiii… Kakeji ya taka burki amma duk da haka sai da yayi sama da ita ta dawo k’asa tare da buguwa a jikin karfen da ke ajikin motan wani irin salati yayi kafin ya fito a cikin motan a rud’e ya nufi inda take yana fadin duk wani adduar da yazo bakinsa tunani ma yake ta yanda akayi bai lura da ita ba tun daga nesa har sai da ya kusan isowa in da take dama yasan dole a yanda sukayi kusa sai ya bigeta d’agota yayi yana kallon gabas da yamma kudu da arewa yama rasa ta ina zai fara ga jini sai ambaliya yake daga kanta da kuma jikin ta kafin yayi wani yunkuri ya jiyo ihun su hango su yayi suna zuwa da gudu suna kokarin tsallakewa mota ya bude ya sanyata sannan ya tsallaka gurin su dan ya tsallako dasu saboda hanyan babban hanya ne bayan ya tsalla ko dasu yace su shiga mota dan a kaita asibiti kuka kawai sukeyi babu mai rarrashin wani shima duk a rud’e yake daker ya iya gane inda ya dace ya nufi dan samun asibiti mafi kusa dasu.
Gudu yake tsalawa akan titi domin ganin an samu ceton ran wannan baiwar Allah cikin ikon Allah su ka isa cikin wani private hospital dake cikin garin gombe da sauri nurses din suka fito ganin irin yanda motar ta shigo sun san cewa emergency ne hakan yasa suka kar6eta cikin gaggawa suka san ya ta kan gadon marasa lafiya sannan suka nufi emergency unit da ita.
2
Likitoci hudu ne akanta d’aya na sanya mata OG oxygen wani na kokarin gyara mata raunin jikinta wani kuma na kokarin sayarda jinin dake zuba daga kanta na karshen kuma nurse ne wanda ke mik’a musu duk abunda suka buk’ata, sosai suka duk’ufa gurin ganin sunyi kokarin ceto ranta amma har zuwa wannan lokacin babu numfashi a tare da ita zufa kawai sukeyi duk da nauran sanyi dake aiki acikin d’akin domin yana yin karan da sukaji naura mai kwakwalwa yake ta badawa alamun cewa zai iyayin wuya ta tashi dan lokaci k’alilan ya rage mata acikin duniyar tamu.
2
Achan waje kuwa kuka kawai su Mimi keyi an rasa wanda zai rarrashi wani a cikinsu Noor kuwa tagumi tayi tana adduar Allah yasa Baaba Azumi ta tashi domin itace komi nasu itace garkuwarsu itace komai ma a duniyar su ta riga ta zama inuwa agaresu kuka sosai take mara sauti tana fatan kar Allah yasa wani kaddara ya sake giftawa tsakanin su da marikiyarsu domin a wannan gab’ar zuciyar ta ba zata iya d’auka ba abubuwa sun riga sunyi mata yawa tun tana ‘yar shekara sha uku take ta fuskantar matsaloli da dama har zuwa yanzu da take kusan sha takwas tabbas idan wani abun ya faru zata iya rasa komai wato ciki kuwa harda rayuwarta.
5
Safa da marwa kawai Mustapha yakeyi ya rasa madafa tun dazu suke ta zaman jiran tsammani har la’asar ya kusa waya ya ciro yayi dailing wayar Gamgoji domin karta ji shuru ta sanya damuwa aranta “assalamu alykum dan albarka da yanzu fa wai zan kira inji ko lafiya shuru baka dawo ba sai kuma ga kiranka ” ajiyar zuciya yayi wanda har sai da taji hakan yasa tayi mamaki kafin tayi magana kuma yace “Um Umma wallahi a hanyar dawowa na buge wata tsohuwa yanzu haka ma muna IB Private Hospital shine nace bari in sanar dake kar kiji shurun yayi yawa”.
STORY CONTINUES BELOW

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, Allahumma ajirni fi musibati wa khallifli khairan min ha, ya ilahi yanzu kai da waye achan din toh” ta fad’a cike da tashin hankali domin ita kam akwaita da tsoro ba laifi abu kad’an ke firgita ta.
Ganin yanda hankalinta ya tashi yasa yace “karki damu Umma kisa driver dina ya kawoki sai a taho musu da abinci amma ba mai yawa ba dan su uku ne sai kuma kayan itatu nasan shine zaifi kyau ga mara lafiya”.
Toh kawai Gamboji ta iya cewa sannan ta kashe wayan Salame mai aikin ta takira akan ta had’o abinci da kayan itatuwa da za’a kai asibiti gurin mara lafiya, yan uwanta ta samarwa abunda ke faruwa duk hankalinsu suma ya tashi matan yan uwanta ne suka shirya dan su mata rakiya itama shiryawa tayi cikin dogon riga ta atamfa sannan ta yafa babban mayafi daga ban suka shiga mota sai asibiti.
Yana zaune a bakin kofar shiga masallaci ya idar da salla kenan ya fito dan komawa ciki sai kuma ya ga gwara ya tsaya kawai a wajen dan yasan yanzu Gamboji zata iso kafin ya gama tunani kuwa saiga su sun iso ita da ayarin ta murmushi yayi kad’an dama yasan za’ayi haka ahakinsu ba dai had’in kai da tausayi ba shiyasa suke matukar burgeshi kuma yake alfahari dasu a koda yaushe tashi yayu ya k’arasa gunsu sannan ya gaishesu suka amsa tare da tambayan ya mai jikin “toh har yanzu dai shuru bata farka ba muna dai jiran tsammani”.
Addua sukayi mata akan Allah ya tashi kafad’unta sannan suka shiga cikin asibitin suna zuwa suka taras da likitocin sun fito da sauri ya nufi gurinsu yana cewa “Dr karkace min akwai wata matsala please”.
Likita d’aya ne ya tsaya sauran kuma suka nufi office din dake jikin dakin “toh yanzu dai mun samu mun shawo kan matsalar kuma zata iya farkawa a ko wani lokaci da yardan ubangiji she is totally safe and out of danger”.
1
Murmushi ne ya bayyana afuskarsa ya rungumi Dr cikin nuna godiya da kuma farincikin samun kyakyawar labari yanzu kenan zai iya tafiyarsa cikin kwanciyar hankali sai su Gamboji su kula da ita harta warkewa “nagode sosai Dr” ya fad’a tare da amsan bill din da Dr ke mik’a masa da kuma maganin daza ta sha, kyakyawar labari ya bawa su Gamboji da kuma su Noor da sukayi tsuru tsuru kamar an tsare mage a kitchen kafin ya wuce bank din cikin asibitin sai da ya biya komai sannan ya nufi gurin magunguna ya saya duk wadanda aka bukata sannan ya koma gurinsu cikin annashuwa da natsuwar zuciya.
Wani d’aki likita ya kaisu suka zauna saboda fahimtar da yayi akan ko su d’in su waye bayan sun shiga Gamboji tasa su Noor agaba sai da ta tabbar sunci abincin sun kosho sannan ta barsu suma d’in kawai rashin k’arfin jiki ke damunsu in ba haka ba ai yunwa kam tunna safiyar yau kuma hakan shine dalilin fitan Baaba Azumi dan kawai tayi bara ta sama musu abunda zasuci sunyi iya kokarinsu dan ganin cewa sun hanata amma taki sauraransu fitan da tayi kenan ya had’u da tsautsayi amma yanzu sun d’anji dama dama tunda dai tana raye kuma zata farka da yardan Allah.
Bayan sallan magriba suna zaune likita ya shigo yake sanar musu cewa an sake mata wani allura dan haka zasu iya komawa gida su dawo washe gari saboda abun ba zau saketa yanzu ba sai washe gari godiya suka mishi sannan Gamboji ta tasa kye’yar su Noor suka wuce gida dan sunce su sai dai su kwana da Baaba Azumi ganin ran Gamboji ya 6aci shiyasa suka yanda akan zasu bita dan basu son ganin 6acin ran babba musanman ma ita da take mai kud’i ai bai dace su wulakanta ta ba tunda ita ta nuna musu soyayya.
Suna isa gida suka fara ajiye matan kawun kafin suka kai Gamboji koda suka isa 6angarenta da gudu su Zahra suka fito dan tarbanta suna cewa sunyi kewarta cikin gida suka shiga Gamboji ta basu d’aki guda mai cike da abubuwan morewa domin babu ne kawai babu a cikin d’akin na bukatan yau da kullun bayan sunyi wanka suka sanya kayan da salame ta kawo musu sosai yayi musu kyau abunka da fararen mutane dan ma wahala yasa sunyi duhu bayan sun shirya suka nufi falo kamar yanda Gamboji tace musu anan suka taras da yaran suna hira da kakarta su zama sukayi gefe guda sai da Gamboji ta nuna 6acin ranta sannan suka saki jikinsu har ma idan anyi abun dariya sai su dan murmusa a haka har tara yayi kowa ya shiga d’aki danyin barci.
Washe gari da sassafe bayan anyi karyawa suka nufi asibiti harda yaran da kuma shi Mustapha kasancewar ba jirgin safe zaibi ba shiyasa ya bisu cikin ikon Allah suka samu ta tashi har tana iya magana farinciki a gurinsu Noor ba magana domin har saida suka ba Gamboji mamaki yanda taga sunata yiwa Baaba Azumi surutu harda kuka had’e da dariya dan dadi kusa da gadon Mustapha yaje ya gaisheta tare da bata hakuri akan abunda ya faru da kuma adduar Allah ya bata lafiya “babu komai yaron kirki domin da wani ne ko tsayawa ba zaiyi ba saboda yanda rayuwar takala ta zama ba abakin komai ba mai kud’i shike rayuwa cikin jin dadi yayi laifi a kasa hukuntashi sai dai ma a hukunta wanda baiji ba kuma bai gani ba Allah ya maka albarka kuma ya saka maka da alkairi ya baka duk abunda kake so ya kuma baka sa’a a cikin lamuranka sannan karka damu nayafe maka duniya da lahira” ta fad’a tana murmushi dan jin dadin yanda d’an masu kud’i ke amsa laifinsa da kuma bada hakuri cikin ladabi harda neman yafiyarta.
Sosai yaji dadin adduar Baaba Azumi har wani washe hakora yakeyi dan kawai an mishi adduar samun Yasmeen se kace haka yaji tace ya dade a asibitij sosai kafin ya musi sallama ya tafi gida dan kimtsawa kafin lokaci yayi kuma yace wa Gamboji ta tafi dasu gida idan an sallamesu har Mamansu ta samu sauki kafin sai su tafi inda zasuje, sosai Baaba Azumi taji dadin sallahun daya bari ko ba komai zuwa lokacin ta warke sai su k’ara gaba godiya tayi mishi tare da fatan alkairi.
Akwana atashi asaran mai rai su Hadiza har sun koma makaranta cikin ikon Allah komai na tafiya musu dai-dai basu da matsala gurin fahimta domin sunsa himma har zuwa wannan lokacin Dr Affan na mak’ale cikin zuciyarta amma tana iya kokarinta gurin kawarda tunaninsa acikin ranta dan saboda kar hakan ya shafi karatunta.
Zuwa yanzu Dr Affan ya fahimci cewan soyayyar Hadiza ke d’awainiya da zuciyarsa kullun kaunar ta k’ara huruwa yakeyi a cikin ransa kuma a yanzu ya ganesu Hajja Hadiza shiyasa har kunyan kan sa yakeji, ranar ya dawo daga office dan d’aukan wasu files daya manta direct ya nufi 6angaren Hajiya zai shiga yaji suna maganarsa inda Ghaji take cewa Hadiza “duk walakancin daya miki abaya baki daddara ba kike neman k’ara kai kanki garesa toh gwara ma ki sanya wa ranki hakuri domin bazan zuba ido wannan karan in barki kiyi wani haukan ba haba mutun ya nuna shi bayayin ka toh ba sai ka hakura ba kin manta irin cin zarafin daya mana ranar da mukaje garesu toh gwara ki sake tunani” kuka Hadiza ta fashe da shi tana cewa “Ghaji ina son Dr Affan ina kaunar Dr Affan kiyi wa zuciyata adalci mana Haba Ghaji kema kinsan bayin kaina bane ba So hana ganin laifi” tausayi taba Ghaji hakan yasa ta sassauto ta fara rarrashinta amma tace lailai ta kara hakuri zuwa wani lokaci a haka dai har tayi shuru daga nan tace bari ta kwanta saboda matsanancin ciwon kan dake damunta, yana gama sauraronsu ya dafe kai asibitin da bai koma ba kenan ranar yayi nadamar abunda ya aikata na walakanta dan adam wanda baya cikin tarbiyyar Hajiya daganan ya fara tunanin mafita akan yanda zai had’asu ya basu hakuri kuma ya fallasa sirrin zuciyarsa.
Yau da wuri ya fita aiki saboda tiyatan da zai shiga addua yayi akan Allah ya basu ikon yin tiyatan lafiya su fito lafiya, awa d’aya suka d’auka kafin suka fito cikin nasara sai washe hakora sukeyi bayan ya koka office ya taras da wani tsohon abokinsa na jiransa wato Dr Aliyu (ina fatan kun tuna Dr Aliyu masoyin Noor na garin Biu wanda ta address din karya yayi ta nemansu ya rasa har suka bar garin) mamakin ganin abokin nasa yayi dan sun dad’e sosai basu had’u ba yana ga kaman zai kai shekaru kusan biyar rabonsu da ganin juna rungume juna sukayi cikin jindadi da farin cikin k’ara had’uwa “Dan uwa yaushe kazo ina fatan kuma zaka dad’e mana agarin bama ya ayyuka yasu Mom da sauran ahali?” ya fad’a yana kokarin zama akan kujera “lafiyansu kalau nazo wani aiki ne kuma zan kai wata guda cikin asibitin naku dan haka kaga kullun zamu na ganin juna” Dr Aliyu ya fad’a.
STORY CONTINUES BELOW

Hararansa Dr Affan yayi yana cewa “kana hauka ne ga gidanmu a garin sai ka wani cemin zamu ke had’uwa kenan a hotel zaka sauka lailai ma ai baka isa ba kaga yanzu ma kawai tashi mu tafi dan zanje in huta sai yamma zan k’ara shigo wa” ya fad’a yana kokarin sanya coat dinsa tare da tattare wasu takardi da kuma wayoyinsa, shima Dr Aliyi murmushi yayi ya tashi daman yasan dole ne yace agidansu zai sauka bayan sun fito kowa ya shiga motarsa suka kama hanyar gidan su Dr Affan.
Horn sukayi aka bud’e musu, parking motar sukayi sannan suka fito suka nufi 6angaren Affan d’aki d’aya ya bawa Dr Ali shima ya shiga nashi sai da suka ajiye kayan su sannan suka d’an watsa ruwa atare suka fito ko wanne sanye da dogon jallabiya mai karamin hannu fita sukayi dan zuwa gaida Hajiya, a cikin falon suka taras da yan matan suna hira cike da natsuwa da kwanciyar hankali, tunda Ghaji ta d’aura ido akan Dr Aliyu ya tafi da natsuwarta abun farin cikin shima sai satan kallonta yakeyi bayan sun gaisa dasu suka nufi d’akin Hajiya.
2
Sallama sukayi sai da ta basu izinin shiga sannan suka shiga, zaune take a k’asa saman carpet tana daddanna computer tana ganin Dr Aliyu tace ‘lale maraba da mutanen Biu yau dai an lek’o ku ina fatan ba yanzu zaka tafi ba?”.
Murmushi yayi kafin yace “eh Hajiya sai nan da wata d’aya saboda aikin da zanyi a office dinsu Affan, dafatan na sameku lafiya Hajiyata”.
Murmushi itama tayi tace “alhamdulillah kuma naji dadi da ba yanzu zaka tafi ba gashi duk kuna nan a gauraye kun kasa kawo katar aure”.
Da sauri Aliyu yace “A’a Hajiya wannan ya zama da yanzu kuma na samu mata a cikin gidanki na ganta tare da Autanki tana yanayi ma da auta ni dai in kin bani izini zan tunkare ta mu daidaita”.
2
Da farko zuciyar Affan sai da ya buga amma da yaji cewa ba Hadiza bane shine yayi murmushi yana cewa “nima Hajiya y’arki Hadiza nakeso idan kin bani damu sai inje mu daidaita kan mu”.
Dadine ya kama Hajiya har ta kasa 6oye hakan tana cewa “Alhamdulillah Alhamdulillah Allah na gode maka daka sanya wannan tunani acikin zukatan ‘ya’yana kuma naji dadin wannan batu domin duk na gida ne nasan halinku duk kuma duk na yaba da tarbiyyar da muka baku Allah ya za6a maku abunda yafi aikairi kuje na baku izini kuma na baku amanar yarana”.
Sosai sukaji dadin yanda Hajiya ta sanyawa batun albarka hakan ya kara musu k’arfin gwiwa tashi sukayi suka fita suna zuwa falon suka cewa Auta Hajiya na kiranta dan kawai ta basu guri bayan tafiyanta Dr Affan ya kira Hadiza ita kuma Ghaji Dr Aliyu ya zauna dan su daidaita, ba tare da wani 6ata lokaci ba ya sanar mata abunda yake ransa farin ciki ne ya mamiye zuciyarta jin cewa ba ita kad’ai ta kamu da love at first sight ba murmushi kawai tayi ba tace komai ba hakan ya bashi damar cigaba da zuba kalamai.
6angaren Dr Affan ma hakane sai da ya fara da bada hakurin laifinsa da kuma sanar mata cewa ranar duk yaji zancen su shiyasa ma ya gane cewa sune duk da cewa farkon ganinsu yaso ya gane amma ya kasa fahimta hakuri ya bata sosai kafin ya daura da sanar mata abunda ke cikin ransa sosai tayi mamakin hakan kuma tayi godiya ga ubangiji daya kawo mata dauki a cikin rayuwarta, cikin kankanin lokaci suka dai daita kansu Hadiza sai wsni blushing takeyi ta samu abunda takeso.
Suma Ghaji cikin lokaci kadan suka gama daidai tawa daganan sukayi musayar number kafin ya mata sallama ya tafi yana fita itama Hadiza ta shigo cikin farin ciki da annashuwa jikin Ghaji ta fad’a tana sanar mata duk abunda ya faru sosai Ghaji taji dadin lamarin duk da taso ace Hadiza taja aji amma hakam ba daidai bane tunda duk suna son juna itama Ghaji ta bata labarin Dr Aliyu da yanda sukayi ranar kam sunyi kwanan farin ciki Auta da taji labari sosai tayi murna da adduar Allah ya sanya alkairi ya kad’e fitina a cikin lamarin tun kafin dare ya gamayi taje d’akin Hajiya ta sanar mata komai itama Hajiya taji dadi da yan matan suka bada hadin kai ranar kowa yayi kwanan farin ciki a cikin gidan Hajiya.
Koda sukaje makaranta washe gari kowa yayi mamakin ganin farin cikin daya gaza 6oyuwa a fuskar Hajja Hadiza har sai da Malam Handsome ya kirata ya tambaya ko lafiya ai kuwa ba tare da 6ata lokaci ba ta sanar mishi kodan ya barta da shegen nacinsa sosai ya tayata murna duk da yaji ba dadi a ransa amma ya zaiyi fatan alkairi yayi mata sannan ya nemi alfarman ta had’ashi da Auta tunda ita ta samu wani ai kuwa kaman ta rungume shi haka taji saboda wani farin cikin daya sake mamiye ranta akan Auta itama zata samu za6in ranta tasan tabbas Auta zatayi farin ciki kwatancen gidansu tayi mishi akan yazo sai su daidaita godiya yayi mata cire da zumud’in samun za6in ransa ta farko, mamaki ne ya kamani akan hakan shin dama yana sonta ne amma ya gaza sanar da ita tabbas akwai wata a k’asa.
Kamar yanda yayi alkawari da yamma sai gashi ya aika mai gadi ayi mishi sallama da Auta koda taji sakon sallama tayi mamaki amma su Hadiza ko tankawa basuyi ba dan dama sun san da zuwan bakon Hajiya ce tace mata taje mana ta gani kila alkairi ke nemanta bata sani ba ai kuwa tana zuwa data ganshi a cikin ranta tace lailai Hajiya tayi gaskiya alkairi ke nemanta, bayan sun gaisa tace mishi ya shigo direct falon bak’i ta kaisa sannan ta shiga kitchen ta had’o mishi kayan motsa baki bayan ta ajiye ta nemi guri nesa dashi ta zauna ba zato ba tsammani taji yace “My Queen yau dai gani a gidanku kuma nayi farin cikin sake sanyaki a cikin idanuna daman a rashin ki nayi kokarin sanya wata a zuciyata toh da Allah ya kaddara itan na wani ne sai Allah ya sake had’amu nazo da kokon barata akan ki taimaka ki amshi soyayyata domin kece first love dina tsoro da fargaban kada ki k’i amincewa yasa nakasa sanar miki dan Allah ki yiwa zuciyata adalci ki amince dani”.
Farin ciki da rud’ani ta shiga a lokaci d’aya wai dana ya dad’e yana sonta amma gaskiya bai kyauta ba da yaki sanar mata ai da yanzu kila har sunyi aure sun haifi yara biyu ko uku (kuji auta da iya tsari) ajiyar zuciya tayi amma bata ce komai ba kawai ta zuba mishi ido sai da yayi magiya har da durkusawa akan gwiwowinsa sannan ta amince mishi cikin lokaci kadan suka gama daidai tawa kafin sukayi musayar number daga nan ya nemi gaisawa da Hajiya bayan sun gaisa ta sanyawa lamarin albarka sannan ya musu sallama ya tafi Auta kuma ta shiga d’aki gurin su Hadiza tana tsalle ta sanar musu haka suka shiga murna baji ba gani sai sa Hajiya ta lek’o d’akin sannan sukayi shuru.
Cikin wata d’ayan da Dr Aliyu yayi a garin Bama sosai suka fahinci juna shida Ghaji haka shima Dr Affan sun gama hada kansu da Hadizarsa ita ma Auta sun fahimci juna da Handsome dinta hakan yasa Hajiya tace duk su turo ayi musu baiko idan yaso da zaran su Hadiza sun gana makarantar secondary lokacin Auta itama ta gama jami’a sai asa ranar Aure hakan kuwa akayi cikin kankanin lokaci akayi engagement dinsu achan garin Gaidam tun daga lokacin wadannan masoyan suka k’ara shimfida sabon babin tsaftataccen soyayya da nuna wa juna kauna cikin natsuwa da kwanciyar hankali.
Satin Mustapha biyu a garin Bama ya gama sanin shige da ficen ahalin gidan da kuma duk wani lungu da sako na gida sannan acikin binciken ya gano cewa wannan matar mai yara shida ta rasu su kuma yaran basa gidan sun dade da barin garin baki d’aya sai dai ya kasa samun hujjan da zaiyi amfani dashi gurin sanin dalilin barin gidan da yaran sukayi hakan yasa ya sake tunanin wani mafita.
Ayau ya fara aiki acikin gidan Dr Muhammad Nur a matsayin mai gadinsu kuma lura cewa mace ta biyun jikin hoton itace kawai a cikin gidan tare da wata mara kunyar yarinya kuma a yanzu Muhammad Nur bai cika fita waje gurin hidimar aikinsa ba ya riga ya d’aura d’an kanwarsa Adam akan dukiyarsa ta chan shikuma yana lura dana gida Nigeria.
Yau satinsa d’aya a cikin gidan Dr Muhammad Nur babban abunda ya lura shine matar gidan tana yawan fitan dare yarinyar ta kuma tana yawanyin bak’i maza da dare sai dai wani abin mamakin tare da k’ananun yara mazan ke shiga gidan idan zasu tafi kuma babu yaran atare dasu shi kuma mai gidan kullun baya fita sallar isha’i da asuba kuma idan sun dawo daga masallaci sai ya tsaya a gurin wani karamin building na cikin gidan wanda yayi kura sosai kamar ba a gidan yake ba sai ya d’auki kusan minti talatin yana kallon gurin kafin ya rike kai ya shiga cikin gida a iya karatun da yayi na addini da kuma baiwar da Allah yayi masa na gane wanda akayi wa sihiri tabbas yaga hakan a jikin Dr Muhammad Nur sai dai kuma sai ya samu wasu hujjoji zaiyi kokarin taimaka mishi.
Yau ce ranar daya za6a dan fara gudanar da aikin sa bayan an dawo daga sallar jumma’a ya wuce hotel din daya sauka ya chanja kaya yayi kyau ya fito a Mustapha dinsa sannan ya d’auki key din motarsa wanda Oga ya aiko mishi daga Gombe wani shopping mall ya nufa ya jidi kaya na mata masu yawa sannan ya kama hanyar gidan Dr Muhammad Nur horn yayi abokin aikinsa Sani ya bud’e mishi gate ya shiga bayan yayi parking ya kwashi kayan zuwa gurin da sani yake yace gashi ya kaiwa yarinyar gidan yace mata tana da bak’o cikin rawar jiki Sani ya k’ar6a ya shigar da kayan ciki tare da sanar da sakon bakon.
STORY CONTINUES BELOW

Ba tare da 6ata lokaci ba Nusaiba ta fito dan ganin irin Kayan da aka lodo mata tun daga nesa ta hango shi jingine da jikin motarsa kirar benz cikin mintinan da basu wuce uku ba ta fad’a tarkon son shi saboda yanda yayi matukar burgeta ga Kyau ga naira tabbas ya cika irin mijin da take buk’ata kuma irin wanda Inna zatayi murnan gani murmushi tayi sannan ta sake daidaita tafiyarta tana wani kad’a jiki harta isa gurinsa.
Sallama tayi mishi ya amsa da fara’arsa yana cewa “ga Gimbiya ta fito Allah dai yasa zan samu k’ar6uwa a gurinki farko dai sunana Saif ni d’an garin Kebbi ne amma ina zama agarin Abuja kuma ayyukana mostly a kasar waje nakeyi sana’ata dai kasuwanci ne kuma duk wani kasuwanci daya ke kawo kud’i bana wasa dashi kinsan Naira shine mutun ayanzu haka ina da biliyoyin kud’i cikin account dina kuma ni marayane bani da kowa sai ke da nake fatan ki zama matata ki kula da dukiyata ko bayan raina sannan kuma ni mutunne da nake son komai za’ayi dani afad’amin gaskiya”.
Murmushi tayi ganin cewa itama zata zama matar mai kud’i ta zama hamshakiya kamar Inna Mardiyya dadi ne ya sake kamata da yace shidin ba shida kowa shi maraya ne kenan dukiyarsu daga su sai yaransu kai abu yayi daidai yayi mata dadi sannan da alama yana irin business dinsu tunda yake duk wani abu mai kawo kud’i yana yi amma bari ta gwada shi “toh Saif naji bayananka kuma kamar yanda kace kai aikinka kasuwanci ne toh nima haka kasuwanci nakeyi zuwa kasashe da dama amma naji kace duk wani aikin dake kawo kudi kanayi kenan har safaran yara zuwa kasar waje da safaran miyagun kwayoyi kanayi?”.
Murmushi Mustapha yayi yana cewa aransa anzo gurin gyara hullarsa yayi sannan yace “mai zai hana inyi ai kud’i kamar yanda na gaya miki sune mutun ni babu irin aikin ba banayi indai zan samu kud’i shikenan komai fa lafiya lau dan haka su din ma muna d’an ta6awa ko kema kinayi ne?”.
Sosai taji dadin batunsa hakan ma nufin zatayi aikinta cikin kwanciyar hankali tunda shima yana irin wannan aikin “kwarai kuwa ni sana’ata shine safaran yara da kuma yan mata domin abun yana matukar kawo kud’i sosai akwai abokan harkallata su suke kawo min yan matan da kuma yaran amma kasan dai yanda mutane suke dan haka da dare ake kawo wa ni kuma sai na gama had’a su nake fitar dasu da dare karshen ko wani wata ita kuma Inna nata shine safaran miyagun kwayoyi tare da abokin aikinta Mamman yola dan garin Adamawa ni ma kuma wani lokacin muna d’an harkalla dashi saboda shina yana cikin harkan safaran yara da yan mata”.
Wani irin annashuwa yakeji acikin ransa dan ganin wannan dabaran daya samu akan aikinsa yana tafiya yanda yakeso “masha Allah gaskiya hakan yana da kyau ai gwara ace kana da kud’i akan ace maula kakeyi ko kuwa Gimbiya sannan baki bani dan labarinki bafa”.
Murmushi tayi dan dama haka takeson namiji wayayye kuma wanda ya san kan duniya “tabbas hakane nawan, sunana Nafisa Muhammad Nur ni kad’ai ce d’iyarsa ina ss1 yanzu a wani babban makaranta mai suna AY International kuma Allah yayi mishi arziki fiyeda tunanin wanda yasanshi kuma a gaskiya mahaifin nawa aikinsa yakeyi cikin gaskiya da tsoron Allah kuma baya ha’inci a cikin kasuwancinsa, baya cin amana da zalunci yana matukar kokarin kare dukiyarsa daga haram kuma a gaskiya bai san cewa muna aikin safaran mutane ba kuma bai san cewa Inna na safaran miyagun kwayoyi ba” toh kaji iya abunda zan iya cewa.
Sosai bayanan nata suka kammala mishi komai domin zai iya cewa ya gama aikin da aka turo shi sai dai ba zai tafi ba sai ya tabbatar da cewa ya taimaki Muhammad Nur gurin samun lafiya kuma sai ya tabbatar da ya kamasu da kanshi da yardan ubangiji godiya yayi wa Allah daya bashi kwakwalwa mai basira irin hakan domin inda ace bata hakan ya biyo ba da sai ya dade yana abu d’aya kafin ya samu nasaran aiki “lailai ma Gimbiya baku tsoron ya sani wata rana toh amma idan kuka sanar mishi to meye aciki ne ni inaga ai ba komai”.
“Rufa mana asiri ina mu ina sanar mishi ai saiya koremu daga gidansa baki d’aya kuma da zaran ya sani abubuwa dayawa zasu faru bama wannan ba ai sai ya mik’a mu ga hukuma dan shi mutunne mai tsoron Allah da sanin tsoron sanin abunda mukeyi kuma zan iya cewa Inna tayiwa tufkan hanci domin bata barin shi haka ai sannan tana bashi maganin barci da dare saboda karya ringa binciken inda take ko kuma abunda ni nakeyi” ta fad’a tana kallonsa.
Murmushi ya sakeyi kafin yace “gaskiya Inna tayi matukar burgeni ai haka akeson iyaye masu kula da ‘yayansu yanda ya kamata ta hanyar basu yanci kamar yanda kika sanu kinga babi ruwanki da wani sa ido kina da yancinki Inna ta baki ai hakan shi yafi, yanzu dai bani number dinki ni zan koma Abuja yau dama saboda ke nazo kuma gobe zan tafi aiki chan america dan haka ba lailai mu rinka waya kullun ba idan dai na samu time zan kira ki kuma idan na dawo sai ayi batun auren mu ki cigaba da karatu a gida na ko Gimbiya” ya fada yana mik’a mata wani karamin leda da ya ciro daga mota wanda yake cike da kud’i.
Kar6a tayi sannan sukayi musayat number daga nan ta mishi godiya shi kuma ya shiga mota ya wice hotel din daya sauka ita kuma ta shiga cikin gida dan sanar da Inna new catch dinsu kuma bankinsu na yanzu sannan mijinta na nan gaba.
Tana shiga ta nufi d’akin Inna da fara’arta bayan ta zauna ta m’ika mata kud’in Inna na budewa taga tulin kud’in dake ciki ai kuwa fitowa tayi dashi ta hau kirge tana gama wa ta kalli Nafisa tace “ke y’arnan ina kika samo mana sabuwar kifi har ya iya baki kud’i zunzurutun miliyan d’aya lailai kinyi goshi yarinya ai wannan na aure ne kawai” ta fada tana jujjuya kud’in.
Murmushi Nafisa tayi kafin ta tashi taje d’aki ta d’auko sayayyan da yayi mata bayan ta dawo tace “Inna kiga fa kayan daya kawo ai wannan dole ma ya zama mijina koda ace bayaso amma ya kyauta wa kansa tunda dai yana sona kuma yana sakin kudi kinga sai anyi auren zamu kamashi ko kuma idan ya dawo daga tafiyan nashi”
Tattaunawa sukayi akan yansa zasu kama Saif wato Mustapha a hannu idan ya dawo daga tafiya yanda zasu rinka juyashi domin sunga alamun naira na aiki sosai a gurin sa daganan Inna tace gwara kawai ta fara mata gyaran jiki hakan zaifi kafin ya dawo sun kammala yana zuwa sai ayi maganar aure ba tare da 6ata wani dogon lokaci ba kuma shi zai bada kud’in kayan d’aki sai su kar6a daba lefen suje su sayo komai daga dubai sun tattauna sosai kafin Inna ta d’auki rabon ta Nafisa kuma ta kwashi saura ta wuce d’akinta dasu tana ayyana irin daulan da zata shiga kwanan nan.
Watanta d’aya a asibiti aka sallame su direct masarauta suka nufa sai a sannan Baaba Azumi ta kara jinjinawa kirkinsu ashe bama kud’i kawai suke dashi ba nasabarsu ma mukami ne na daban sosai ta jinjinawa Ahalin su saboda saukin kai da son jama’a.
D’aki d’aya aka ware wa Gamboji ita da Mimi dan su wataya Noor kuma na tare da Aminatu sayayya sosai Gamboji tasa aka musu na kayan sawa ko wacce seti goma nasu Noor dogayen riguna yar kanti guda biyar da kuma atamfa biyar wanda aka bayar dinki tare dana Baaba Azumi guda goma sai hijabuna set hudu ko wannensu.
Acikin sati uku aka gama musu dinkunan nasu sai da Gamboji ta tabbatar ta saya musu duk wani abu na buk’ata daga kan inner wears har kayan kwalliya daganan tayi maganar komawa makaranta dan tana matukar tausayinsu saboda Baaba Azumi ta sanar mata da labarin rayuwarsu kamar yanda suka fada mata hakan yasa Gamboji ta d’auki aniyar rikesu har zuwa lokacin da zata gwada maida su ga danginsu idan an dace shikenan idan ba’a dace ba sai ta zauna dasu har ta aurar dasu da yardan ubangiji sosai take kaunar yaran kamar y’ay’anta.
Makarantar masarauta tasa su inda Zahra take primary one Mimi take primary four 4 tare da Halima, Aminatu kuma na jss1 tare da Hafsa sai Noor ss1 tareda Aisha da Hafiz kasancewar kansu kusan d’ayane su biyun amma Noor ta girme su.
Yanzu duk tare suke tafiya makaranta cikin lokaci kad’an duk suka saba amma banda Aisha da Hafiz dan duk cikinsu sunfi tsanar Noor din ko kad’an basa sonta duk da cewa ajinsu d’aya duk science class aka sasu amma koda wasa basa nuna sunsanta itaka bata damuwa saboda ta riga ta saba da halin mutane daban daban mahaifinta ma yak’i ta balle wasu to meye abun damuwa sai dai wani abun na bata dariya idan taga suna kula su Mimi har wasa sukeyi dasu kamar yanda sukeyi da kannensu ita kam ko ahaka zuciyarta wasai tunda kannenta na cikin farinciki.
Baaba Azumi najin dadin kulawar da ake basu ita da yaranta tana matukar farin ciki koba komai su ma yanzu zasu kasance cikin natsuwa da kuma kwanciyar hankali dama burinta kenan taga suna cikin walwala kuma sun samu hutu arayuwarsu cikin hukuncin ubangiji yanzu sun samu saura kuma Allah ya karkato zukatan danginsu zuwa garesu wannan shine adduarta a kullun.
STORY CONTINUES BELOW

Gamboji najin dadin yanda yaran suka sake suke muamala da kowa kamar dama sun saba gashi kuma akwai su da ladabi da biyayya ga son aiki dan kafin masu aiki su shigo har sun kusan kammala komai na cikin gidan musanman Noor wata rana kitchen take shiga tayi musu girki dan kawai farantawa Gamboji sam sam bata da k’iwa mutanenta kuwa tare da su ake santin girki sai dai har zuwa yanzu basu son muamala da ita kuma ko kadan bata nuna tasan sunayi.
Karatu yanzu sukeyi baji ba gani kowa na kokarin ganin ya fito da abu mai kyau yanzu sun rage hira da dare sosai kowa sai dai ya d’auko littafinsa musanman ma Noor da Aisha wani competition sukeyi a fannin karatu gwara Hafiz da bai fiye bawa kansa wani wahala ta fannin karatu ba dan yana da saurin rike abu idan anyi kuma wo wani lokaci shi ke d’aukan na d’aya Aisha kuma ta uku.
♣🌹♣☘♣🌻♣
*🌻f¢т αвυʝα*
*♣gωαяιмρα*
Tun tafiyan Mustapha Yasmen ta dawo shuru shuru bata fiye magana ba wani irin so da kaunar sa ke dawainiya da ita gashi yanzu batasan inda zasu sake had’uwa ba a 6angaren Abby kuwa har anyi baikom Yasmeen da Adam d’an kanwarsa dan kuwa Adams ya d’aureta ta hanyar cewa ai suna soyayya ne kuma kowa ya yarda da batunsa duba da yanda Yasmeen din ta sake dashi lokacin zuwansu Bama da kuma lokacin da yaje musu hutu a Abuja ba tare da 6ata lokaci ba akayi musu baiko kuma Adams din na zawa gurinta akai akai yanda take sakewa dashi yasa babu wanda yayi tunanin cewa ba soyayyace tsakanin su yanzu haka ana jira ta zana weac dinta sai ayi bikinsu idan yaso sai ta cigaba da karatu a gidan ta.
Yanzu Ummi ta tsira yi mata wa’azin aure aduk sanda suke tare ga kuma kayan gyaran jiki da take bata na sha dana wanka dana shafawa kullun sai tayi hayakin turaren wuta kuma bata ta6a kawo komai aranta ba balle yanzu da batason yawan magana ko tambayan dalili batayi ba kawai dai komai tanayi yanda aka umurce ta da tayisu hakan na faranta ran Ummi sosai tunda taga batayi mata musu ba.
A yau tana zaune Abby ya aika akirata tana zuwa ta taras dashi tare da Ummy bayan ta zauna ya tambayeta ko shin akwai soyayya tsakaninta da wannan yaron wato d’an uwanta ita duk tunaninta Mustapha ake nufi (ni dideey kuma ban san sanda Mustapha ya zama dan uwanta ba) ba tare da dogon tunani ba tace eh hakan yasa Abby yace shikenan zata iya tafiya bayan ta tafi yace wa Ummy shikenan ko yanzu hankalin nata ya kwanta tunda ta dage sai lailai an kira Yasmeen din ta amince da bakinta murmushi kawai tayi ba tace mishi komai ba ta cigaba da yanka fruit dinta.
A6angaren Yasmeen ita duk tayi tsammanin su Abby sun fahinci tana son Mustapha shiyasa suka tambayeta farin ciki kawai takeji aranta nan danan ta dawo Yasmeen dinta mai shegen fi’ilin tsiya yanzu kan zuciyar ta wasai hankalinta ya kwanta zata samu zab’in ranta.
2
Bayan watanni shida ta gama zana ssce dinta suka tattara sukayi garin Bama sai ma alokacin ta gane cewa bikinta ne ya taso itakam komai yinshi take cikin farin ciki domin bata san ainihin waye angon nata ba tunaninta dai burin ranta ne wato Mustapha, taso ganinshi amma kuma ta hakura tunda shi bai neme taba sau dai tana mishi uzurin kila aiki ne,bayan sati uku da zuwansu abokan ango suka zo dan tsara komai da suke bukata amma tace ita gaskiya walima kawai take bukata dan haka suyi hakuri hakan kuwa ba karamin daraja ya kara mata ba a idanun su har sai da suka samu Adam suka mishi murna na musanman na samun mata wacce take da sani akan addini.
Haka Yasmeen ta zage tana narkawa cikin ta duk wani tsumin da aka bata kuma zuwa yanzu ta kara sakewa da yan uwanta harda kakarta ma wato Hajiya kowa sai nan nan yake da ita dan jindadin wannan lamari da zai kara dankon zumunci sosai suke mata gyaran jiki irin nasu babu wani gayyata da sukayi na wanda zata gyara ta acewarsu ai sune ma ake gayyata dan gyara wasu dan me kuma zasu nemo wanda zata gyara musu d’iya ai hakan ma abun kunya ne sosai, kullun Adam na zuwa duba ta kuma koda wasa bai nuna mata cewa shine angon ba dan yasan abunda ya kulla kuma idan har ta sani tabbas sai dai afasa shiyasa yaja bakin shi yayi shuru.
Rana bata karya sai dai uwar d’iyar taji kunya a yau dinbin jama’a yan uwa da abokan arziki manya manyan mutane suka halacci d’aurin aure na amarya Yasmeen da angonta Adams akan sadaki naira dubu dari hamdala kowa yakeyi a bisa wannan lamarin ango bakinsa har kunni ya kasa rufewa sai wage hakora yakeyi kamar gonar auduga, achan cikin gidama kowa yana cikin farin ciki Yasmeen banda fad’uwar gaba babu abunda takeji sai ma da taji wai an d’aura haka ta kwanta ta narki kukanta har zuwa sanda ango ya shigo da abokan sa daker ta fito ta d’auki hoto ba tare da ta kalli angon ba har aka gama tana hawaye karshe dai basu samu ke6ewa da ango ba shima kuma hakan yaso.
Tashin hankali wanda ba’asa mishi rana yau Mustapha ya halacci d’aurin aureb sarauniyar sa kuma burin ransa da ace yasan d’aurin auren tane da baiyi gigin amsa gayyatar da mahaifinta yayi mishi ba sai dai yana zuwa ya had’u da tashin hankali wanda da kyar ya iya rike kansa saboda yanda zuciyarsa ta buga adaddafe ya gaida Abby tare da mishi Allah ya sanya alkairi sannan ya koma hotel dan hutawa sosai yake tausaya wa kansa na rashin samun duk wani za6in ransa haka ya rasa Huzna sai dai ba zai ce bai godewa Allah daya musanya masa da Zahra ba gashi yanzu ya rasa Yasmeen kuka yayi sosai har barci ya d’auke shi.
2
Karfe takwas aka fara shirin kai amarya bayan anyi mata nasiha mai ratsa zuciya sosai take kuka na nesanta daga iyayenta da zatayi ga kewan kannenta masu sonsa rungume twins tayi suka sha kukansu daker aka cireta daga jikinsu aka kaita mota saboda anan Bama zata zauna inda yayi gidansa amma ba zasu dad’e ba zasu koma kasar waje da zama dan cigaba da kula da harkokin kasuwancin Abba wato babansu Noor.
Har suka isa gidan tana faman kuka da zata fito a mota ma sai da akayi daru da ita dan zama tayi akan bazata shiga ba sai dai amayar da ita gurin Ummi, da lallashi aka samu ta fito sai da aka bata ruwa tayi alwala sannan ta shiga da k’afar dama tare dayin adduoin da Ummi ta koya mata.
Babban building ne hawa biyu an fenteshi da blue colour hatta burglary din duk blue ne haka manyan atficial flower da akasa shina duk blue ne hatta gate din gidan blue ne daga ciki kuma babban falo ne daya sha royal chairs pink da ratsin blue labule pink inners blue babu wani tarkace a cikin falon sai Tv, Decorder, Show glass, Center table da flower vase duk silver colour amma flower din ciki daya blue daya kuma pink ta ko wani kusurwa sai carpet blue and pink wani k’ofa nagani ta hagu wanda da alamu visitor’s restroom ne ina bud’ewa naga ko mai na ciki blue and pink sai wani a dama shi kuma d’akin bak’i ne set din gadon ciki silver pentin kuma fari labulen silver inner fari sai carpet fari da silver toilet din ciki ma silver da fari.
Ta gefe guda kuma dinning ne me d’auke da babban Table da Kujeru guda shida masu kyau blue and pink sai wani k’aramin flowervase blue da pink flower wanda aka ajiye a tsakiyan table din wani k’ofa na ganin ina bud’ewa naga kitchen ne mai kyau ga girma ga fad’i komai an jerashi in order gurin plates daban cups daban tukunya ma daban komai dai dai ga fridge da kuma frizeer ga gas cooker da hot plate sai microwave komai na kitchen din silver pink da blue.
Sama na haura inda na ga d’akuna uku a jere a tsakiya kuma akwai dan karamin falo wanda bai kai na farkon ba komai na ciki fari,silver da bak’i sai dai wadannan kujerun leather ne masu matukar kyau silver colour, throw pillors da center table da labule duk fari inner din kuma silver show glass, flower vase kayan kallo kuma duk bak’i flower din cikin vase din kuma fari da silver ako wanne ta ko wani kusurwa sai carpet silver da bak’i.
D’akin farko na shiga set din gado mai kyau black and white carpet black and white labule black inner white haka toilet din shima komai black and white, d’aki na biyu shima set mai kyau italian blue and white colour carpet blue da white labule blue inner white haka toilet din komai blue and white sai d’akin k’arshe inda anan na taras da Yasmeen ta kudundune akan gado sai rawan sanyi takeyi kafin in karewa d’akin kallo naji tashin mota alamar yan rakiyan nata ne zasu tafi gida, sake kallonta nayi sannan na kalli d’akin in da komai na ciki pink and silver, labulen pink inner silver sai carpet pink da silver toilet dinta shima pink da silver da alama dai ma’auratan masoyan pink blue da silver ne dan naga kusan komi agidan kalar kenan.
Da sallama ya shiga cikin gidan a falo ya zauna sai da yayi adduar had’uwa da Yasmeen sannan ya haura sama dak’in shi ya shiga mai d’auke da blue furnitures wanka ya fara kafin brush tare da d’auro alwala bayan ya fito sai ya fara da goge jikinshi sannan ya ciro jallabiya daga wardrobe ya sanya direct d’akinta ya shiga tana kwance a gado sai rawar sanyi takeyi ac ya fara kashewa kafin ya k’arasa kusa da ita yana ta6a jikinta yaji wani irin zafi sosai toilet dinta ya shiga ya d’ibo ruwa da towel laffayan ya fara warewa sannan ya cire rigan da skirt din ya rage wani under skirt da vest tana jinshi amma jikinta yayi nauyi ta kasa bud’e ido sai dai kuma ta rasa dalilin da yasa takejin irin kamshin turaren yayanta Adam, sai da ya tabbatar jikinta ba zafi sannan ya dai na sa mata ruwan a lokacin barci ne ya fara d’aukarta kafin ya fito har tayi barci sai wani ajiyar zuciya takeyi a haka ya zauna gadinta har shima barci ya d’auke shi.
Washe gari da safe ana kiran salla ya tashi kafin ya tashe ta yaji alamun motsinta hakan yasa ya fita d’akinshi ya shiga yayi alwala sannan ya tafi masallaci, bayan an idar ya gaisa da mutane tare da introducing kansa sannan ya musu sallama ya tafi gida yana zuwa ya shiga kitchen ya had’a musu breakfast toasted bread da tea sai da yaci nashi sannan ya had’a mata nata a tray ya kai d’aki lokacin tana wanka hakan kuwa ya mishi dad’i.
Ahaka sukayi sati biyu kullun kuma a d’akinta yake kwana amma sai tayi barci kuma kullun yana kai mata breakfast idan ya daidaici lokacin data shiga wanka kuma bata ta6a damuwa ba acewarta ai kila haushi yakeji na abunda ta mishi ada shiyasa baya kulata amma tunda yana kawo mata breakfast shikenan batada damuwa idan ya sauko zasu daidaita.
4
Ayau visa dinsu ya fito na tafiya kasar america inda yake aiki, da zai kirata sai kuma ya fasa message ya tura mata akan driver zaizo ya d’auketa ya kai ta cikin family house dan tayi musu sallama tana ganin message din tayi saurin shiryawa dan tayi kewar yan uwanta suna isa da gudu ta shiga cikin gidan d’akinsu Ummi ta shiga lokacin Abbi na cin abinci ita kuma Ummi na kokarin tattara kayansu dan zasu koma Abuja a cikin satin rungume ta Ummi tayi dan itama tayi kewarta Abby kuma kada kai kawai yayi yana cewa “mamana bazaki chanja ba kinyi aure amma baki girma ba” maganar ma kunya ya bata daker ta saki jiki sukayi hira da iyayen nata haka yayyin ta da kannenta daganan ta nufi 6angaren Hajiya nan ma saida suka sha hira har zuwa lokacin ta kasa gane cewa Adam take aure duk da cewan Hajiya nata mata nasiha akan ta kula mata da jikanta ita duk a tunanin ta ai shima mustapha ya zama jikan gidan a haka ranar ta wuni ziyara har sai dare sannan ta tafi cike da kewar yan uwan ta da danginta.
Washe gari da safe driver ya kaita airport inda ta had’u da Adams bayan sun gaisa take tambayar sa ina jeze yace mata in da zata shiyasa mijinta ya hada su tafiya guri d’aya danshi ya riga ya tafi ba taji dadin hakan ba amma kuma kawai ta basar tace toh ai babu damuwa shi kuwa tausayi ta bashi har yake ga kamar bai kyauta mata ba yanzu ma bai san yanda zasu kare ba.
♣🌹♣☘♣🌻♣
*🌻υѕ αмєяι¢α*
*♣ωαѕнιиgтσи*
Cikin hukuncin ubangiji suka isa Washington lafiya mota ya tara musu suka nufi gida dan driver dinsa bai san zai shigo kasar yau ba, suna zuwa ya sauke kayan masu aiki sai gaisheshi sukeyi nan ya basu izinin shiga da kayan cikin gida ido Yasmeen ta zuba mishi tana kokarin san gano wani abun amma tana karyata kwakwalwarta tana karyata tunaninta bata son ta yarda da wannan abunda ke faruwa.
Bayan sun shiga ta fara karewa gidan kallo komai kusan iri d’aya da gidanta na nigeria sai dai wannan yafi wancan kyau sosai amma yanayin tsarin kayan da akasa achan a nan dinma hakan yake har ta fara taka matakala ta juyo tana kallon Adam dake tsaye yana kallonta murmushi kawai tayi kafin ta wuce sama dan batason dagula wa kanta lissafi tare da wahalar da kwakwalwarta.
Shima murmushi yayi kafin ya kwashe kayanta ya kai mata d’aki tana kallonshi ya shigo ya fita amma batace mishi komai ba ita dai mijinta take jira kuma yau ya zama dole su had’u dan haka ba zatayi barci ba tunda taga alamar cewa a d’akinta yake kwana kaya ta cire sannan ta shiga wanka.
Shima ayau ya sanya wa ransa cewa dole ya nuna mata gaskiya domin ayi wanda zaayi saboda su fara zaman aure yanda ya dace da wannan tunanin yayi wanka yayi alwala bayan ya idar da salla ya fita zuwa wani restaurant ya sayo musu friedrice da gasheshen kaza yana dawowa ya ganta a falo yana waya ajiye mata leda d’aya yayi sannan ya fita zuwa wajen shakatawa na cikin gidan bayan ya kammala ya dawo ciki amma bai ganta a falo ba d’akinshi ya shiga yayi kwanciyarsa.
Akwana a tashi babu wuya gurin Allah yau su Hadiza suka gama final paper dinsu kuma hakan yayi dai-dai da saura sati biyu bikinsu wanda za’ayi a gidan Hajiya dan tace ita zata aurar da yaranta mai son ganinsu ya taho Bama biki.
Wata yar uwar Hajiya ke musu gyaran jiki sosai Hajiya tayi sayayya na gani na fad’a komai iri d’aya ta saya musu sai dai banbancin kala na Auta set din gado coffee brown da milk falonta da d’ayan d’aki kuma purple da milk kayan kitchen din ta milk da silver, Hadiza kuma kayan d’akinta red da black sai dayan black da milk falonta black da red kitchen kuma black da milk sai Ghaji kayan d’akinta golden da brown dayan kuma golden da fari haka falonta golden da fari kitchen dinta ma golden da brown, gabaki d’aya an riga anyi musu jere Auta a federal low coast su Ghaji da Hadiza kuma a staff quarters na specialist hospital Bama dan Dr Aliyu shima anyi mishi transfer zuwa garin Bama, yanzu abunda ya rage kayan lefe ne sai kuma daurin aure dan Hajiya tace babu dinner din da zaayi walima din dai shine abunda yafi dacewa garesu.
3
Bayan sati guda aka kawo lefensu ko wacce akwati biyar da kit dinsa na Auta purple Hadiza red Ghaji kuma golden sosai angwayen sukayi kokari komai awadace amma ba irin wanda ya wuce ka’ida ba kowa ya yaba da tsarin kayan da aka sanya anata sanya alkairi da fatan zaman lafiya ga ma’auratan.
1
Ranar laraba bayan Anty Bilkisu yar uwar Hajiya ta gama musu gyaran jiki suna zaune suna d’an ta6a hira kamar yanda suka saba kullun sai ta dan basu shawarwari yau ma hakanne tace musu bari ta basu wasu yan sirrika na gyaran jiki wanda za su rinkayi dan gyara kan su da kan su hankalinsu suka bada gareta tare da cewa “muna sauraronki anty” tace toh ayau zamu fara da Sabulun gyaran fata nasa laushinta da kuma maganin tabo da farko ki samu sabulun salo,wato ghana soap, ki samu dan madaranki na gari kona ruwa, lemun tsami, krkur haska amarya, sabulun broonze ba shida tsada ana sai dashi a stores haka sai kiyi kokari ki nemi sabulun caramel shima duk acikin kayan hadine, ki had’a sabulun duka ki daddakasu ko kuma ki yanyankasu siri siri saiki hadesu sosai da sosai sannan sai ki kawo kurkur dinki daidai misali ki juye sai ki samu haska amarya daidai misali ki zaba haska amarya da kurkur agidajen gyaran jiki ake samunshi sai ki hadeshi asabulun ki buga sosai sannan wasu suna sa nescafe domin yana sa laushin fata in kinaso ki saka in bakyaso saiki barshi saiki sa madaraki ki buga saiki kawo ruwan lemun tsamin da kika matse shima ki juye, idan ki kai hakan saiki bugesu sosai su hade, za kiga yayi ruwa ruwa amman ba komai bane, saiki juye hadin cikin container mai murfi ki rinka wankanki dashi wannan hadin yana mugun gyara fata, baya bleaching gyaran fata ya keyi yana kuma maganin kujaren fata da kuma na fuska yana gyara sosai kuma yana da kyau ki rinka shafa sabulunnan kamar ana saura awa daya kiyi wanka yana da kyau ma ki samu ganyen magarya bushashshe ki daka ki zuba a sabulun da kika hada ki kara buge wa bakaramin kyau zaisa kiyi ba kuma duk tabon dake jikinki saikin nema kinrasasu mata mu ringa kokari gurin gyara fata dan miji yakalla yaji dadi yanasa santsin fata da kuma laushinta.
2
STORY CONTINUES BELOW

Sai Gyaran Fata zaki tanadi ababe kamar haka
Man Zaitun, Lalle, Kur-kur Madarar ruwa(peak) zaki hade wannan kayan guri guda sai ki kwaba su ki shafe jikinki da fuskar ki, za kiyi hadin kafin shiga wanka idan ya bushe a jikinki sai ki murje kafin shiga wanka ya na sa jiki yayi kyau da sheki zaki iyayin wannan ma wanda ake hada kur-kur, dilka, zuma, kwai, Lemon tsami zaki hade su a guri guda ki samu ruwan ki kwaba kamar yadda ake kwaba lalle, amma ya fi kwabin lallen ruwa, sai ki shafa a fuskanki, idan kuma har da jiki kike so, saiki shafa harda jiki bayan kaman awa d’aya sai ki shiga wanka zaki ga yadda jikinki zai goge das da izinin Allah, Idan kuma gyaran fuska kike so sai ki tanadi dettol, sabulun ghana, garin zogale, farar albasa, saiki hade su guri guda ki kir6a su aturmi ki rinka wanke fusku zakiga yadda fuskarki zatayi kau wannan hadin na sanya fuska yayi haske da kyau da annuri ya kuma kore kurajen fuska za’a tanadi abu kamar haka bawon kankana sai a rinka goge fuska da shi yana gyara fuska yayi sumul ga wani hadin duk na gyaran fatar jiki shi ma wannan hadin na musamman ne wanda yake sanya fatar mace ta zamo tana tare da shauki da laushi kai har ma zaki ji jikinki yana wani santsi wannan hadin yawanci na amare ne, zaki tanadi ababe kamar haka ayaba lemon tsami, tatacciyar madara, kwai daya zaki sami ayaba mai kyau ki bare ki matse da hannu ki koki markada ablenda yayi laushi, sai ki zuba tataciyar madara ki fasa kwai kamar guda daya amma farin zaki zuba sai ki matse lemoun tsami ki gauraye shi ki shafa ajiki ya samu kamar awa daya, sai kiyi wanka da ruwan dumi, idan har kuki lizanci yin hakan kamar kwana uku a ko wani sati zaki sha mamaki.
2
Sai kuma lalle wanda kariya ce daga sihiri, Kariya ce daga aljanu sannan kuma Kariya ce daga cututtuka da dama, yin lalle a kafa na zuqe cutar dake kafa sannan yana maintaining dumin mace, bi maana yana inganta ni’imar mace ba tare da ya gushe ba, ga duk mace mai infection, ta tafasa lalle in ya dan huce sai ta yi sit bath da shi na sati biyu in Allah ya yarda zata warke, ana iya sha ruwan lalle cokali 1 don wankin dattin ciki amma banda masu ciki, a bangaren gyaran fuska, tana sa fuska tayi kyalli, laushi, da haske in an kwaba da ruwan Kwai amma banda kwaiduwar kwan, ki kwaba shi ruwa ruwa amma ba sosai ba ki lizimci shafa shi kullu yaumin 30 mins kafin ki shiga wanka sai kinga banbanci a cikin sati biyu Insha Allahu, ga masu son hasken fata, kwaba lalle da ruwa, ki shafe a jikinki inya bushe ki dirje da man zaitun za kiga canji, ga masu fama da pimples, yar’ uwa ki hada lemon tsami da lallenki kwabi mai dan karfi bafa sosai ba kina shafa wa a fuskar ki bayan watanni kuraje zasu mutu sannan tabo bazai zauna ba ga hasken fuska da laushi sannan mai son kamshin fata, ki kwaba lalle da turarenki mai kyau na ruwa wanda ake durawa ki zuba isasshen ruwa a bucket ki sa garin lalle ta jika tai jazir sai ki tsiyaye ruwan ki diga turaren ki mai kamshi ciki Bayan kinyi wankan sabulunki sai ki dauraye jikinki da shi inkin lizimci haka to bake ba rabo da kamshin jiki in sha Allahu, lalle dai karamin tasiri yake dashi wajen gyara fata ba da jiki baki d’aya dan haka ku dage dayinshi, sosai ta basu sirrika masu yawa game da gyaran jiki da fata da kuma kula da tsaftar gida da girki sosai sukaji dadin shawarwari data basu godiya suka mata tare da fatan alkairi gareta da ahalinta.
Ranar alhamis akayi walima inda aka kira shahararriyar malama ta african tv wato malama zuwaira sosai tayi wa’azi ga ma’auratan wa’azi ne mai ratsa jiki da zuciya kowa sai da jikinta yayi sanya wasu kishiyoyi a gurin suka shirya kansu tare sa neman yafiyar juna haka aka tashi cikin farin ciki da walwala akan karuwar da aka samu mai dinbin yawa kowa yaji dadin waazinta tasha adduo’i kala kala daga masu sauraro har da mazajen data gyara wa aure.
Rana bata karya duk abunda aka sawa lokaci indai da rai da lafiya sai yazo haka zalika wannan rana ta farinciki ya riske mutane shida wadanda ke matukar kyaunar juna an d’aura aure lafiya kowa yaci yasha ya koshi Hajiya tayi bajinta tayi matukar kokari domin tayi wa amare komai yanda zatayiwa d’iyarta kowa sai son barka da fatan alkairi da dare aka kai amare gidajensu tare da guzurin nasiha daga iyayensu sosai sukayi kuka suka gode Allah sai dai muce Allah ya basu zaman lafiya da zuria dayyiba.
1
♣🌹♣☘♣🌻♣
*🌻υѕ αмєяι¢α*
*♣ωαѕнιиgтσи*
1
Bayan taci abincin daya kawo tayi wanka ta huta sai daf da sallar magriba ta tashi bayan ta idar da salla ta sauka k’asa tayi musu jollof rice wanda yaji kayan lambu, lemon kwakwa da fruit salad ta had’a ta jera a dinning kafin ta wuce d’aki danyin sallar isha’i koda ta idar Ummi ta kira suka gaisa ta sanar musu isowarsu tun d’azu sai da sukayi magana da twins sannan ta sauko dancin abinci har ta gama cin abincinta bai dawo daga masallaci ba bayan ya dawo shima ya zauna ya cika cikinshi yana shiga d’akinsa ita kuma tana fitowa bata bi ta kanshi ba kawai tayi tafiyarta ta sauka k’asa kwanonin ta kwashe ta kai kitchen saida ta gyara komai sannan ta koma d’aki wanka tayi ta sanya rigar barci tayi zaman jiran mutumin nata.
Yana fitowa daga wanka ya sauke ajiyar zuciya na tunanin yanda zasu kare da mutuniyar tasa kaya ya saka sannan ya fesa turare ya fito daga d’akin tana jinsa lokacin daya shigo d’akinta shuru tayi dan tanason ganin mai zaiyi zama yayi a kusa da ita yana tunanin mai zai fara fad’a mata chan dai yace “Yasmeen dan Allah kiyi hakuri ki tashi muyi magana nasan ba barci kikeyi ba”.
Muryanshi ne ya k’ara tabbatar mata da cewa Adams ta aura ba zabin ranta ba sai yanzu ma ta fara tuna abunda Abbi ya fada mata “soyayya kike da wannan yaro ne wato d’an uwanki” amsar data bashi ta tuna inda tace “eh” tabbas ba Adams ne kawai mai laifi ba harda ita da soyayyar ya rufe mata ido har take kasa banbance magana idan anyi amma tambayan a nan shine “shin meyasa Adams zaiyi mata haka bayan yafi kowa sanin cewa Mustapha ne za6in ranta” tambayar kanta tayi “shin meya kamata tayi? amsar data baiwa kanta shine “kuka” yes tabbas “kuka” ta sake mamaitawa a ranta kafin ta fashe da wani irin kuka mai matukar ban tausayi shi dai ido kawai ya zuba mata ya kasa motsi balle ya aikata abunda zuciyar sa ke kokarin fada mashi wato ya rarrasheta ya bata hakuri.
Kusan minti goma ta d’auka tana kuka kafin ya daure ya karasa kusa da ita ya janyota zuwa jikin shi “kiyi hakuri Yasmeen dan Allah ki yafemin son da nake miki shiya tilasta min na aikata abunda nayi saboda banason in rasaki dan Allah kiyimin hakuri Yasmeen ki yafeni domin kece rayuwata ke kadai nakeso kuma nake kauna dan Allah ki yafeni Yasmeen”.
Janye jikinta tayi daga nashi tashi take kokarin yi yayi saurin rikota wani irin kallo ta jefa mishi wanda ya tilasta mishi sakinta babu zato babu tsammani yaji saukan wani irin bahagon mari wanda ya ratsashi ya ratsa cikin jikinshi da sauri ya d’ago idanu ya kalleta kugu ta rike ta wurga mishi wani mugun kallo “kace nice rayuwar ka to ka sani cewa ni din nan Mustapha shine dai rayuwata shine komai nawa shi nake kauna ko wani numfashina da so da kaunarsa yake fitowa inaso ka sanyawa kanta da kwakwakwarka cewa ni Yasmeen ba taka bace ni matar Mustapha ce kuma ya zama dole ka sakeni dole ne ka sakeni domin ni ban sonka ban kaunarka na tsaneka Adamu na tsaneka Adamu na tsaneka Adamu!”.
2
Tamkar saukan garwashi haka yakejin kalamata suna sauka a cikin jikin shi har zuwa sanda ta bude kofa ta fita sannan ya dago idanu jikinshi a sanyaye bai ta6a tunanin cewa zata furta mishi irin wannan abubuwan na duk da yasan cewa bata sonshi zaiyi hakuri yayi kokarin daure zuciyarsa tunda shiya jawo komai kuma tabbas bai kauta mata ba amma saki dai atsakaninsu bazai ta6a yiyuwa ba sai dai idan zata kashe shi wannan shinr kawai maslaha a gareta amma shi Adams bazai ta6a sakin Yasmeen dinsa ba.
Tana fita ta nufi d’akin dake kallon nata kuka kawai takeyi baji ba gani itama tasan cewa Adam ba zai ta6a sakinta ba kuma itama ba zataso ace hakan ya faru ba domin Ummi za’a daura ma laifin rashin basu tarbiyya wanda abun ba haka yake ba Ummi mace ce ta gari kuma tana iya kokarinta gurin sanya su a hanya nagari sosai tayi kuka har sai da kanta ya fara ciwo dakinta ta koma har zuwa lokacin yana zaune a inda ta barshi jakanta ta bude ta dauki magani sannan ta fita abunta ba tare da ta kuma kallonsa ba.
Anyi biki lafiya kowa ya koma gida lafiya cikin k’oshin lafiya sun bar Hajiya da kewarsu.
Amare suna chan gidajen su cikin natsuwar zuciya buri ya cika duk sun auri wanda suke so da kauna zamansu gwanin ban sha’awa sai son barka ko wacce tana iya kokarinta gurin kyautatawa mijinta haka suma angwayen ko wannensu na kokarin farantawa matarsa zama sukeyi na fahimtar juna da girmama junansu sai dai muce Allah ya kara dankon kauna.
Hajiya Yasmeen babu fa abunda ya ragu sai ma abunda ya dad’a karuwa kullun da salon muguntar da take b’ulowa da kuma kalar rigimar da takeyi a gareshi, abinci ma bai isa yaci wanda ta dafa ba sai dai yayi da kansa kuma ya wanke duk wani abun daya 6ata komai tanayi a gidan amma banda aikin Adam ko kallo bai isheta ba batun gaisuwa ma bai taso ba dan koda tafiya takeyi yazo ta gefenta sai dai ya jira ta wuce shi dai yaga ta kansa dan shiya janyo rigimar da yafi karfinsa, rayuwarsu babu armashi ko kad’an kuma babban abun shine bata so ya kulata shi kuma ya kasa hakuri da wannan hukuncin idan kuma yayi ranar sai ya gwammace bai ce mata komai ba.
A6angaren Mustapha har ya kammala aikinsa an sake turashi chan kasar saudiyya inda zai binciki wani lecturer d’an naija ko sallama bai samuyi da Gamboji ba sai awaya ya sanar mata inda ta kara mishi tunin alk’awarinsu bai iya ce mata komai ba dan yanzu ba shida wani mafita shi abunda yafiso shine ya gama wannan aikin idan ya dawo kuma sai aje a kama su Inna da sauran yan uwansu kafin nan Abban su Noor ya gama warkewa danya bawa wata amintacciyar mai aikinsu ruwan addua da kuma wasu maganin karya sihiri yanzu da shi take yiwa Abba abinci da kuma had’a lemonsha na gargajiya dan Abba bai cika son abun kwali ba.
Kwana uku da zuwansa ya fara aikinsa tare da yardan manyan jami’an madina inda ya shiga ya fara da zaman aji kamar wani d’alibi guri ya samu kusa da wata y’ar nigeria ya zauna da ganinta kaga fulanin usul kyakyawace son kowa kin wanda ya rasa duk da cewa fuskar ta kawai yake gani dan duk jikinta arufe yake ta sanya hijab har kasa da safan hannu dana kafa ko kad’an bata kalli inda yake ba har aka tashi ba wanda ta kula, takardun ta tattare komai nata ta k’ara gaba, a maimakon Mustapha yayi aikin dake gabansa sai ya buge da son sanin ko wacece ita.
2
STORY CONTINUES BELOW

Hauwa’u Sa’ad Sulaiman Yola wacce akafi sani da Gimbiya Jidda d’iyace ga sarkin yola itace ta hudu a d’akinsu kuma ta goma a yaran mai martaba duk cikin yaran gidan itace ta gaban goshi mahaifanta saboda natsuwarta da sanyin halinta mahaifiyar ta itace ta biyu agurin me martaba bayan rasuwan matarsa ta farko wacce ta bar yara shida dukan su mata Fulani maman su Gimbiya Jidda ce ta samun sa’ar samun d’a namiji agidan wanda yaci sunan kakansa na gurin uba wato Aliyu Saad, ana kiransa da Yarima Haidar Saad Sulaiman Yola duk sauran yaran gidan mata ne, Jidda tayi karatunta na jami’a akasar saudiya inda ta karanci first degre dinta afannin Islamic ta kuma haddace alkur’ani mai girma daganan ta fara second degree inda harta gama take masters afannin Gynecologist a yanzu haka tana shekara na karshe a cikin jami’ar madina tunda tafara bata da kawa balle aboki idan kaga tana magana acikin aji toh tambaya takeyi a lecturer bayan haka babu abunda yake had’ata da classrep kawai ke samun magana da ita idan zaije kar6i assignment ko wani project hakanan takeyin rayuwarta cikin natsuwa dasanin ciwon kanta tare da kare martabanta na d’iya mace mutane da yawa suna sonta amma koda wasa bata ta6a tankawa ba iyayenta naso tayi aure amma kuma taki bada hadin kai ga kannenta da yawa sun yi aure wannann karan kam sun yanke shawaran aurar da ita ga wanda ya dace dan sun san Zatayi biyayya.
1
Wannan tarihin da yaji na Jidda shi ya kara sa shi farajinta a ransa amma kuma baya fatan ya kara soyayya a rayuwarsa ya barwa Gamboji za6in ya kuma san zata mishi za6in matar auren wanda ta dace, a kullun ya shiga Aji a kusa da ita yake zama kuma ko rantsuwa zai iyayi akan bata ta6a kallon inda yake ba har ta gama duk bincikensa a iya cikin makarantar ya tafi babu mai kula wani gwara shima yana yawan kallonta amma ita koda wasa baya gabanta.
Cikin watanni ukun da yayi ko wani sati sai ya shiga dan ganin Jidda acewarsa kawai tana burgeshi ita kuwa bata san ma yanayi ba dan karatu shine abunda ya kaita ba kalle kalle da 6ata lokaci ba.
Acikin watanshi na biyar ya gama tattara duk wani bayanai akan SAS Sanusi Audu Suni lecturer acikin jami’ar Madina wanda ya kasance d’an Nigeria dan asalin garin Yola, karatu ya kaishi Madina kuma yayi matukar kokari gurin karatunsa afannin kula da lafiyar mata ya samu kyautar yabo da dama a jami’ar Madina daganan suka rikeshi a matsayin lecturer wanda hakan da sukayi yana matukar yin wuya amma chanchanta yayi shiyasa ya samu.
Cikin aminci Dr Sanusi yayi karatunsa ya kuma kama aikinsa ba tare da wata matsala ba sun ba shi gida harda mota inda yake zaune da matarsa yar kasar Niger da kuma yaransa, sosai ya maida hankalinsa gurin aikinsa suma kuma suna biyan shi albashi mai tsoka, ana cikin hakan kuma ya hadu da tsohon abokinsa wanda ake kira Mamman Yola, Mamman mutun ne mai tsananin son kudi in dai zai samu toh zai iya aikata koma menene da farko yak’i amincewa da shawaran da abokinsa ya zo mishi dashi sai daga baya shima son kud’i da hudubar shaidan yasa ya amince da buk’atarsa in da suke safaran miyagun kwayoyi a ko wata k’asa da suke da abokan harka duk cikinsu shine kawai ba za’a yarda yana aikata hakan ba yanzu haka an kama Mamman Yola da wasu abokanan harkallar su aciki akwai Isa Lawal Zaria wanda yake aiki tare dasu kusan duk dai an kamasu shi kadai ne ma yanzu ya rage kuma shima sun samu hujjoji kwarara da zaiyi musu amfani gurin kamashi sai kuma su Inna Mardiyya shima suna saka ran da zaran Mustapha ya dawo zasu wuce garin Bama dan kamosu tare da sauran mutanensu.
♣🌹♣☘♣🌻♣
Cikin ikon Allah Abbansu Noor ya fara warkewa ya fara dawowa hayyacinsa har yana tunanin yaransa babban abunda yake dan bashi mamaki shine wani mafarkin da yakeyi akan mutuwar Mahida da bai yarda ba har yanzu yafi tunanin cewa tafiya tayi ita da yaran amma ba zai iya yarda da cewa ta tafi ta barshi ba ga kuma wai Mardiyya da yake gani a gidan shi dai bai gane takamanman matsayinta ba kawai dai ya zuba mata idone.
Yana zaune a falo kamar kullun yana duba jarida Inna Mardiyya ta shigo ko kallonsa batayi ba ta wuce sama abunta shi dai hakan bai dameshi ba babban damuwarsa shine yaga matarsa da yaransa amma ba wai Mardiyya da Nafisa ba.
Ajiye news paper din yayi sannan ya fita masallaci yana dawowa ya aika me gadi ya kira mishi Ladidi wacce suke kira da Ladi bayan tazo yayi gyaran murya sannan yace “ina da tambayoyi da yawa a cikin kwakwalwata kuma kece kawai zaki iya bani amsar tambaya ta, ba wani abu bane illa inason sanin inda Mahida take da kuma yarana dan inaji kamar barci nayi na farka daga shekaran jiya zuwa yau duk na duba bangan suba sai wannan kanwar Mahidan wato Mardiyya da yarta Nafisa sa’ar Nusaiba”.
Murmushi Ladidi tayi dama irin wannan rana take jira kuma gashi cikin hukuncin ubangiji Allah yasa ita zata amsa mishi tambayoyinsa “toh Alhaji da farko dai zan fara dayi maka ta’aziyyan rashin matarka shekaru shida da suka wuce da kuma d’iyarka hauwa’u shekara biyar da suka wuce Allah ya jikansu ya kuma rahama musu”.
Kallon Alhajin tayi da yayi tsuru yana kallonta alamar cewa kanshi ya kulle hakan yasa ta fara bashi labari tun daga koran Mahida da yayi har zuwa komawarsu dakin awaki da duk walakancin da ya ringa yiwa matarsa da yaransa kafin ya kore su da sakinta da yayi da auren Mardiyya duk dai wani abunda ya faru tun daga farkon har karshe bata rage ba har izuwa rasuwan Hauwa’u da koransu da Mardiyya tayi daga gidan.
Wasu gani yakeyi kamar amafarki wasu kuma ba zai ce gashi yasan anyi ba iya dai abunda zai iya tunawa shine dan fad’an da suka farayi da kuma matsalolin da suka fara samu da matarsa amma harga Allah bai saketa ba kuma bai san ya koresu ba sannan babban abun shine bai san fa ya auri Mardiyya ba, sallamarta yayi sannan ya fita dan yin sallar magriba daga nan ya shiga d’aki yasha kukansa yana tunanin ko wani hali yaransa suke ciki tare da adduar Allah ya karesu ya kuma yiwa matarsa addua da yarsa akan Allah ya jikansu ya rahama musu sosai yayi kuka har ya gode Allah waya ya d’auka ya kira Hajiya abunda ya dad’e baiyi ba.
Hajiya tana zaune taga kiransa batasan sanda hawaye ya zubo mata ba rabonta da d’anta harta manta ga kuma rashin jikokinta da tayi wanda aka nema aka rasa ita ma lokacin bikinsu Adam da Yasmeen ta warke daga duk abubuwan da suka same ta gabaki d’aya ahalin gidan anyi musu mugun abu da yasa suka manta komai dangane da yaran d’anta abu d’aya suka sani shine rasuwar Mahida bayan wannan duk basu tashi farkawa daga mumunar aika aikar da aka musu ba sai lokacin zuwan wani abokin mijin ta daf da bikin Yasmeen babban Malami ne kuma shahararre lokacinne ya fara basu magungunar karya sihiri da kuma adduoin da zasu rinkayi cikin ikon Allah duk suka warke kowa yanzu tunaninsa yanda za’ayi Nura ya dawo cikin hayyacinsa dan ko gidansa ba’a bari su shiga sai kuma inda za’a samu su Noor sai gashi cikin ikon Allah yau ya kirata kasa d’auka tayi saida tayi kukanta ta gode Allah daganan ta dauki waya ta kirashi kuka ya fashe mata da shi daker ta rarrashe shi daganan ya nemi yafiyar ta tare da bata labarin abunda Ladidi ta sanar masa itama ta kara da iya abunda ta sani jimami sukayi akan abun kafin suka yanke shawaran had’a family meeting ranar jumma’a ya kama nanda kwana biyu kenan.
Acikin satin Mustapha ya dawo kasancewa tafiyar dare sukayi ma’ana da yamma suka tashi hakan yasa suka iso da sassafe yana isowa basu tsaya jiran komai ba dan sunyi booking jirgin da zasu wuce Borno da shi hakan yasa basu 6ata lokaci ba suka kama hanyar Borno.
Suna isa suka sauka a hotel dan sai da dare suka shirya kai musu hari bayan sun d’an huta sukayi order din abinci sukaci suka koshi shi kuma Mustapha ya d’an kwanta dan huta gajiyar hanya.
Kamar kullun yau ma ta kai mishi coffee dinshi da take saka maganin barci abune wanda tasan baya fashin sha koda batayi ba zai tuna mata amma kwana biyu ko magana ya dena mata bayan ta ajiye harya d’auka zai sha kuma sai ya tuna da maganar Hajiyarsa inda tace inba Ladidi ce tayi abinci ba karya kuskura yaci duk abunda za’a kai mishi domin basu san ko meye acikinsa ba hakan daya tuna yasa yaje toilet ya zubar sannan ya dawo ya ajiye kofin yayi adduar kwanciya barci.
Harya fara Barci yaji an bud’e gate kafin shigowar motoci dan ak’alla yaji kara sau uku tashi yayi a hankali ya leka ta window wasu maza uku ya gani sun fito daga motar ko wanne ya tasa k’eyar yara biyar, mamaki ne ya kamashi ‘su kuma daga ina haka” shine abunda ya tambayi kansa harya koma ya kwanta sai kuma ya dawo ya bud’e cctv camera da ya dade baiyi amfani dashi ba.
Falon k’asa na farko ya fara bud’ewa ba kowa a ciki hakan yasa ya bud’e na biyu wadannan maza ukun ya gani zaune tare da Nafisa abunda ta fada shiyaja hankalinsa “gobe wata zai cika dan haka bayan sallar asuba sai kuzo mu tafi dan an riga an mana booking komai da komai kuma zamu fita dasu ne amatsayin yaran makaranta wadanda za suje yawan k’aro ilimi”.
Murmushi d’aya daga cikin su yayi kafin yace “gaskiya kanki naja hakan shine daidai ta yanda babu wanda zai zargemu” Na biyun ma yace “tabbas hakanne tunda an kaka su Alhaji Mamman mu kuma sai muyi takatsantsan” na karshen yace “toh kinyi mana ID ne a matsayin malaman makaranta ko kuma ya abun yake?”.
STORY CONTINUES BELOW

Murmushi tayi sannan tace “haba ai dole inyi maganin abun tuntuni nasa an gama mana komai akarkashin wani private school wanda na cika principal da kud’i da farko yaki yarda da yaga naira shine harda bamu damar amfani da sunan makarantar da kuma uniform dinsu sai dai wani kala daban” dariya duk suka sheke dashi suka cigaba da tattaunawa.
Abba dai yayi mutuwar zaune wato ackin gidan nasa ake aikata wannan mumunar aikin idan dai zai fahimta trafficking fa kenan Addua kawai yake Allah yasa karsu fita da wuri dan dole ya sanar da jami’an tsaro tunanin inda Inna Mardiyya take yasa ya koma bud’e falon sama inda ya ganta tare da wani bak’in mutumi suna tattaunawa akan kama y’an uwansu da akayi da kuma yanda zasu bawa su Nafisa Miyagun Kwayoyin su tafi dashi ba tare da an gane ba sun d’an dad’e suna magana daganan kuma suka shiga aikata sa6on Allah da sauri ya rufe computer din baki daya kanshi na wani irin sara mishi ya rasa shin ko da wasu irin mutane yayi rayuwa tsawon shekaru shidan da yayi baya hayyacinsa.
A chan waje kuwa manya ma’aikatan sojoji da yan sanda sun kewaye gidan Mustapha da ogansu da wasu mutane hud’u suka shiga bayan sun gargadi mai gadi akan kar yayi wani motsi, suna shiga suka tsaya a k’ofa suna dan kuskus da juna kafin suka tura kofan ahankali babu kowa a ciki rufewa sukayi da key sannan suka haye sama d’akin Abba suka fara shiga a d’an tsorace ya tashi duk da cewa jikinshi a mace yake abunda sukace ne yasa yaji hankalinsa ya kwanta “karka damu ba kai muke nema ba” sai dai daya tuna halindasu Mardiyya ke cika yasa ya musu bayanin cewa ga abunda yake faruwa dan Allah karsu bud’e k’ofan su bari harsu fito tunda basuyi tsammaninsu ba kawai su fara da Nafisa da mutanenta bayanin abunda yaji suke cewa yayi musu sannan suka fita zuwa falon k’asa na biyun.
Suna zaune suna sun cikinsu ga kayan ciye ciye kala daban daban ba zato ba tsammani sukaji ance “you are under arrest” wani irin zabura sukayi atare duk jikinsu 6ari yakeyi Mustapha ne ya fara isa kusa da ita yana cewa “nagode miki bisa taimako na da kikayi a farkon had’uwarmu dan kinsa aikina yamin sauki” yana gama fad’an haka ya fara bubbud’e k’ofofin da suke cikin falon sai da ya bud’e kusan guda uku ana hud’u yaga yara sun kai k’imanin hansin suna zauzaune duk kowannen su na cikin koshin lafiya kuma hankali kwance da alama basu san ainihin inda za’a kaisu ba shiga yayi ya taso k’eyarsu baki d’aya mamaki ne ya kara mana jami’an tsaron tare da Abba da kuma Ogan nasa dan basuyi zaton har suna iya kwasan yara masu yawa haka ba lailai abun nasu da girma gasu dai duk ba wasu manyan mutane ba barinma ita Nafisan bata wuce sha shida ba su kuma mazan baza su wuce ishirin da wani abu ba, Nafisa kam duk ta gama tsurewa da tagane cewa ashe Saif dinta jami’in tsaro ne yayi mata basaja ga kuma Abbansu Noor da take ganin kamar ya samu lafiya suna cikin haka sai ga Inna Mardiyya sun sauko tare da wannan gardin sai wani manne mishi takeyi basu ma lura da yan falon ba sai da sukazo tsakiyan gurin cikin tsoro ta dafe kirji ganin mijinta da kuma jami’an tsaro ga kuma yaran dake tsaye cirko cirko jiki na rawa ta zube a kasa shi kuma abokin harkallan nata yayi niyar guduwa aka chafkeshi.
Kuka Inna ta farayi tana danasin abunda ta aikata gashi yau asiri ya tonu dama ance rana tara na 6arawo kwana d’aya na mai kaya gashi yanzu ba wan ba kanin zata rasa mijinta kuma zata rasa dukiyarta ni kuwa nace (wannan ihu bayan hari kenan kikeyi Innarsu) duk zubewa sukayi akasa dan wani irin fargaba daya ziyarci zukatansu gashi ba daman guduwa shikenan tasu ta kare komai ya lalace.
Rarrafawa Inna tayi ta isa kusa da Abba tana cewa “shikenan asiri yau ya tonu dama boka yace min duk randa ka dawo cikin hayyacinka komai zai warware nayi kokarin gujewa wannan rana sai dai gashi na makaro dan Allah Abban Noor ka yafe mana duk abunda muka aikata gareku da kai da yaranka da matarka kuma yayata, ayau zan fada maka duk wani abu da ya faru har zuwa wannan rana wanda zai matukar baka mamaki”.
Hawaye ta share sannan tayi wani murmushi mai cike da ma’anoni iri iri kafin tace “kamar yanda ka sani Yaya Mahida ita kadai ce agurin umman ta ahaihuwa kuma daga ita saini mahaifiyarta ta rasu tun bayan data haife ta hakan yasa mahaifin mu ya fifitata akanmu acewarsa dan ita bata da uwa wannan abunda yayi yasa muka tsaneta haka Innarmu itama ta tsane ta ana cikin haka baban mu ya sayarda kayan gadonta na gurin uwa inda ta samu kud’i masu yawan gaske saboda mahaifiyarta diyace a gurin yar sarkin fika a cikin garin yobe kakanta mai kudin gaske ne shi yasa ta samu k’udi masu yawa daga dukiyar mahaifiyarta”.
Shuru tayi na wasu yan mintina kafin ta cigaba da cewa “banki baban namu yakai kud’in akan daga baya zai san meya dace yayi mata wannan abunda yace yasa Innar namu ta shiga tashin hankali dan taso ace a gida ya bari saboda ta sace su, ana haka ka fito neman auren Yaya abunda ya kona zuciyar Innarmu shine kai mai kud’i ne dan haka dan haka baka dace da yar kishiyarta ba ahaka dai akayi aurenku bayan haihuwar Noor da Habiba nima nayi aure inda muka haihu atare ita ta haifi Nusaiba ni kuma na haifi nafisa kafin wani lokaci aurena ya mutu saboda Innarmu kai takeso in aura nanfa ta shiga ta fita har na samu zuwa hutu gidanka daga nan muka fara aikin mu cikin kwanciyar hankali bayan komawa ta gida dama na dasa tsanarta a cikin zuciyarka wannan abun yasa kuka fara samun sa6ani har dai na samu yanda nakeso nayi amfani da kwallin da boka ya bani na sake komawa gidanku daganan ka fara sona har ka saki Yaya Mahida ka aureni lokacin da baban mu ya samu labarin hakan ya shiga tashin hankali dan daga gidanmu har gidanku basu son auren mu daga ni sai Innata muke bidirin mu ganin zasu rusa mana aiki yasa mukaje gurin boka yayi aiki akansu daganan kowa yayi shuru kowa ya fita harkar Yaya Mahida da yaranta kowa ya tsaneta hatta dangin mahaifiyar nata bakin cikin haka yasa Baban mu ya fara addua ba dare ba rana danshi Allah ya taimake shi babu abunda ya sameshi haushin hakan yasa innarmu ta kashe mahaifinmu tare da sace dukiya masu yawa kafin araba gado harda na Mahida daya ajiye yake juya mata” daganan ta cigaba da bashi labarin komai daya faru ciki har da mutuwar Mahida da mutuwar Hauwa’u da duk wani miyagun aiki da sukeyi da koransu Noor da tayi komai dai kamar yanda Ladidi ta sanar masa harda wanda ladidi bata sani ba.
Mamakine ya kama kowa a falon kuka sosai takeyi tsakani da Allah Abba kasa magana yayi kawai ya haura sama ya shiga d’akinsa ya kwanta yana wani irin kuka daya kasa fahimtar kona miye ne a cikin duk labarin data ba yar domin abubuwa da yawa suna bukatan ayi musu kuka tunanin yaransa yayi yanzu shin ta ina zai fara yau dai yasha kuka irin wanda tunda Hajiya ta haifeshi bai ta6a yiba domin wannan irin rayuwa dame yayi kama.
Achan falo kuwa bayan sun gama jimami suka tasa keyarsu zuwa inda suka sauka tsaro sosai aka bada akansu dan kar suyi yunkurin guduwa da sassafe sukayi booking jirgin zuwa birnin tarayya inda head quarters dinsu yake dan mik’asu ga hukuma yaran kuma duk aka tambayesu gidajen su Allah yaso suna da wayonsu daganan kowa aka fara maidashi gida tare da yiwa iyaye nasiha akan su dena bada yaran su yanda sukaga dama dan kawai suna cikin talauci domin basusan inda za’a kaisu ba wasu suna hannu na gari wasu kuma sai dai ajefasu a hanyar karuwanci nasiha sosai akayiwa iyayen inda duk jikinsu yayi sanyi da yawansu sunyi kuka kuma sunyi nadama sai da suka tabbatar sun maida kowa sannan suka koma head quarter’s dan ganin mai ake ciki sabods duk an had’a kan mutanen har SAS shima an kamoshi dafa k’asar saudiyya da sunso suyi mishi hukunci da kansu amma aka basu hakuri tare da tabbatar musu da cewa za’a musu hukuncin daya dace da zaran an dawo nigeria dan suna da yawa.
Kamar yanda aka tsara a yau za’ayi family meeting hatta dangin Umma sun zo daga Yobe daga ciki akwai kakarsu Noor da kuma kakansu kusan duk family dinsu Mahida dai sun k’araso har amarya Yasmeen da angonta su Abbi da wasu family din dangin mahaifin Mahida ne kawai suke hanya.
+
Karfe d’aya da rabi kowa ya hallara acikin babban falon gidan lokacin duk anyi sallah anci abinci da adduo’i aka bud’e taron kafin ko wani 6angare suka fara gabatar da kan su saboda wa’anda basu sansu ba bayan gabatar wa aka farayiwa juna jaje akan abunda ya faru daga nan kowanne ya bada labarin yanda yaji ya tsani Mahida da kuma yanda duk suka manta da ita da yaranta sannan cikin ikon Allah alokaci guda duk suka fara tuna ta musanman yaranta da yandu kowani 6angare suka samu taimako daga gurin yan uwansu wanda abun bai shafa ba irin adduoin da akayi kafin aka samu dacewa daga nan Abbansu Noor ya fara bada iya wanda ya sani da wanda Ladidi ta fad’a mishi da kuma ita kanta Mardiyyan abunda ta fad’a mishi sannan da duk wani abunda suke aikatawa da kamasu da akayi ajiyan.
Manaki da alajabi ya cika zuk’atansu tabbas dan adam ba’a iya mishi kuma duk yanda kake da mutun wani abun zai iya sawa ya manta da alakar ku ya tafka maka abunda bakayi zato ba babban abunda yafi d’aga musu hankali shine mutuwar Mahida da Hauwa’u babu gatan dangin uwa bare na uba babu dangin kusa bare na nesa ga kuma wahalhalun da suka sha kamar basu da gata ga kuma 6atan yaran shin ta ina zasu fara bincikowa kuka sosai masu raunin ciki sukayi sai da suka samu natsuwa sannan abokin babansu Abban Noor ya fara da musu nasiha akan sakaci da addua da sukayi wanda shine babban dalilin da yasa komai yayi tasiri a jikinsu sai dai kuma abun dama kaddararre ne dan haka ba zaiyi jayayya da ubangiji ba sosai yayi ta musu nasiha da nusar dasu illar rashin addua a koda yaushe da neman tsari daga dukkan wani sharri sannan ga rashin zumunci tsakanin junan su tunda an riga an had’a zuri’a hakan bai dace ba sai da yaga jikinsu yayi sanyi sosai sannan ya bar su.
Tabbas maganarsa haka ne kuma gaskiyane suma sun sani cewa tabbas sunyi sakaci da addua da kuma zumuncinsu da kila koma meye ne dole zasu rinka tuno wani abu daya danganci su Noor din har ma kilasu samu maslaha akan hakan yafiyar juna suka nema akan sakaci da zumuncinsu abunda Allah ya riga ya had’a ai babu mai rabawa an riga an zama d’aya bayan sun fahimci juna suka fara da adduo’i ga mamatan sai da suka d’auki lokaci mai tsawo kafin suka koma kan yanda za’a fara neman yaran.
STORY CONTINUES BELOW

Sun dade suna tattauna wa kafin suka yanke shawaran watsa abun a k’afafen yad’a labarai ta tashoshin da yafi tasiri akowani gida irin su NTA AIT TVC CHANNELS da dai sauransu daganan Abbi yace ya d’auki nayin hakan godiya aka mishi tare da sanya albarka sannan taro ya watse cikin aminci wadanda suke nesa sai washe gari zasu koma Abba kuma a gidan Hajiya zai zauna.
D’akunan 6angaren Abba aka bawa duka mazan su kuma matan 6angarensu Abbi, Abba, Abbi da kuma family dinsa da Yasmeen da mijinta duk 6angaren Hajiya suka zauna abun haushi d’aki d’aya aka ba Yasmeen da Adams shi kam dadi yaji amma ita bakin ciki ne ya kamata ai kuwa akasa ya kwana ga sanyin tiles dan ma akwai carpet (asuba ta gari AdYas).
Washe gari da safe ko wannensu ya shirya komawa gida bayan sunyi breakfast sukayi sallama da juna sannan suka tafi Yasmeen gidan su suka koma na cikin Bama Abbi kuma suna nan tukunna sai wani lokaci zasu koma bayan kowa ya tafi suka nufi gidan yad’a labarai sai da suka tabbatar sun fad’a aduk gidajen da zasu samu saurin biyan bukata sannan suka tafi gida tare da adduar samun nasara.
Gidan amaren Bama naje inda naga duk suna nan zaune lafiya sai tattalin juna sukeyi babu wani hayaniya sai tsantsan soyayya da biyayya da sukeyi ga mazaje su dama kiwon Hajiya ai dole su zama masu tarbiyya fatan alkairi nayi musu sannan na lek’a gidan Yasmeen.
Zaune take akan kujera ta d’aura k’afa d’aya akan d’aya tana shan fruits shi kuma bawan Allah aiki kawai yakeyi dan gidan ya danyi kura sai daya gyara ko ina tukunna sannan yayi wanka ya fita ya sayo musu abinci ya d’auki nashi ya nufi d’akinsa bayan yaci yayi salla sannan ya sha magani ya kwanta dan huta gajiya ita kuwa abincinta ta narka ta cigaba da kallo cikin kwanciyar hankali.
♣🌹♣☘♣🌻♣
*🌻gσмвє ѕтαтє*
*♣мαѕαяαυтα*
Cikin nasara Mustapha ya dawo gida kowa ya taya shi murnan hakan harda yar karamar liyafa akayi a gidan, Gamboji tayi matukar alfahari da d’an nata haka sauran yan uwansa da dangin mahaifinsa dan yanzu zaman lafiya sukeyi sosai da dangin mahaifin nasa.
Bayan komai ya lafa ta kirashi dan sanin ko ya samu matar aure cikin jin kunya yace mata a’a d’an nazari tayi akan abunda ta yanke kafin tace “ina fata ka tuna da alkawarin mu kuma kasan bazan fasa abunda nayi niyya ba dan haka kaje ka fara shiri nanda sati biyu za’a d’aura maka aure kuma na sai kasan matar ba idan ranar yayi zaka ganta kawai kai dai kayi duk abunda ya dace daga lefe zuwa gyaran gida kuma inason ka shirya mana tafiya zuwa garin Borno cikin hukumar Bama cikin satinnan dan inason sada yarannan da danginsu idan har yanzu bazasu kar6esu ba sai in rikesu a gurina batun lefe kuma matar kusan kansu d’aya da Noor dan haka zaka iya gwada komai da yanda Noor din take zaka iya tafiya”.
Godiya yayi mata dan hakanne kawai abunda bakinsa zai iya fada kafin ya duba yaransa sannan ya wuce 6angarensa na cikin gidan masu gyara ya kira na masarauta ya sanar musu da duk wani abunda yakeso suyi na gyaran gidan daga k’ara gyara tsarin gidan da kuma pentin da yakeso ayi mishi sai daya gama musu bayanin komai sannan ya kira Huzna Fulani a yanzu matar mai martaba sarki Aliyu ya shaida mata irin kayan lefen da yake buk’ata dab itace besty dinsa har yanzu kuma tana harkan business sosai dan ba sosai take zuwa kula da asibitin ta ba sai dai ta kanje dubawa akai akai bayan ya kammala da batun lefe ya samu guri ya kwanta dan huta gajiya.
Washe gari da safe suna zaune a falo baki d’ayan su aka hasko Abbansu da Abbi a gidan talabijin suna bayani akan 6atan y’ay’ansu sosai hankalin su Noor ya tashi da suka ga yanda Abba yake kuka da yake magana Mimi ne tace “Ammi kinga Abban mu wallahi shine gashi kuma neman mu yakeyi har yaba kuka” da sauri Gamboji ta kalli Noor da Aminatu da suke hawaye hakan ya tabbatar mata da gaskiyan maganar hamdala sukayi ita da Baaba Azumi hatta su Hafiz sun taya su murna a wannan karan suma harda guntun hawayensu waya Gamboji tayiwa Mustapha tace ya shirya tafiyan ayau dinnan ba sai gobe ba hakan kuwa akayi zuwa karfe sha biyu jirginsu ya d’aga zuwa garin borno.
Cikin ikon Allah suka isa lafiya cikn koshin lafiya motocin da Mustapha yayi order suka shiga inda shi yake tuka wanda Gamboji da Baaba Azumi da Aisha da Hafiz suke ciki dayan kuma driver dinsa ke tukawa mamaki ya kamashi da yaga inda suka dosa sai dai baice komai ba har suka shiga gidan shuru ko ina babu alamun mutane sai ga baba sani mai gadi ya fito gaisawa sukayi da alamu bai ganesu ba tambayan mutanen gida sukayi yace suka gidan Hajiya godiya Noor tayi mishi sannan suka shiga mota suka kama gidan Hajiya kowa a motar mamaki yakeyi akan cewa daga irin wannan daulan su Noor suka fito musanman Gamboji da Baaba Azumi da sukasan tarihin rayuwarsu.
Direct gidan Hajiya suka wuce suna zuwa suka samu duk mazan suna masallaci bayan sunyi parking suna mazan suka sauka danyin salla matan kuma suka bi bayan su Noor zuwa 6angaren Hajiya ko da suka shiga ba kowa a falo sai kamshin turaren wuta da sanyin AC dake tashi acikinsa zama sukayi sannan suka aika wata mai aiki data shigo dan ganin ko suwaye suka bud’e kofar koda Gamboji ta tambayi dalilin da yasa su ba zasu shiga ba kawai murmushi sukayi itama ganin haka yasa tayi shuru.
Alokacin data shiga ta taras duk suna salla fitowa tayi ta sanar dasu Noor bayan tafiyanta Noor tace ga band’aki a cikin falon suyi alwala suma suyi sallan, hakan kuwa sukayi kowacce tayi alwala ta gabatar da ibada, bayan sun idar suna zaune suna d’an ta6a hira su Abba suka shigo tare da bak’i mazan lokacin su Hajiya suma suka fito sai a lokacin idonta ya kai kan Noor da Mimi da Aminatu da sauri ta mik’e tana cewa “kai Nuraddini ba yaran naka bane anan?”.
Cikin sauri ya juyo sukayi ido hud’u da yaran ai bai san sanda ya sauka kasa ya k’arisa gurinsu da sauri ba yana zuwa ya rungumesu baki d’aya kawai ya fashe da kuka kowa a falon jikinsa yayi sanyi suma yaran kuka sukeyi wani irin farinciki ne aransu abunda suka dade suna mararin samu abunda suka cire rai da sake samu shine Allah ya amsa musu ta hanyar basu ayau gasu ajikin mahaifinsu yan uwansu suka tuno da suma suke burin ganin irin wannan rana amma Allah baiyi cewa zasu gani ba sosai suke kuka daga su har Abban sai da yaji wani natsuwa acikin ransa sannan ya janye amma duk suna jikinshi kaman zasu sake 6ata ko za’a kwace su, murna ya hana ya tambayi sauran yan uwansu sai dayayi ajiyar zuciya sannan ya fara da cewa “kuyi hakuri ku yafe min yarana nayi muku laifi babba amma ba’a cikin hayyacina nake ba Innarku ta cucemu baki d’aya tayi min asiri tare da dukkan yan uwa haka yasa duk muka janye daga gareku kafin in cigaba da neman yafiyar naku shin inasu Habiba suke?”.
Wani irin bugawa kirjinsu yayi saboda tambayan da Abba yayi musu sai dai ya zasuyi ya zama dole su fad’i gaskiya labari Noor ta fara basu akan rayuwar da sukayi tun daga dena kulasu da Abba da sauran dangi sukayi har zuwa rasuwan Umma da kulawan da Dr Affan da danginsa suka basu da kyautatawan da sukayi musu da rasuwan Hauwa’u da koran da Innarsu tayi musu da zuwansu Chibok da duk wahalar da suka sha da kuma zuwansu Biu da rasuwan Habiba da Nusaiba da barin garin da sukayi suka koma Kano da haduwarsu da Baaba Azumi harda mijinta Tasi’u da aurenta da rasuwan Mijin da barin garin da sukayi zuwa Gombe har kad’e Baba Azumi da zamansu a masarauta babu wani abunda bata fad’a musu ba.
STORY CONTINUES BELOW

Babu abunda akeji sai tashin kuka duk wani mai imani sai ya tausayawa rayuwarsu domin sunga rasuwa sun shiga garari da kunci sun d’and’ani duk wani wahalar dake cikin rayuwa hatta su Aisha yau sunyi kuka da sukaji labarinsu tabbas rayuwar d’an Adam ba abakin komai yake ba duk kud’in ka duk mulkin ka sai Allah ya jarabce ka dan ya gwada imaninka tabbas yaran sunga abu arayuwa kuma sunga jarabawa kala kala sai dai fatan Allah yasa mu cika da imani.
Sai da komai ya lafa sannan Abba yasa driver yaje ya d’auko Hajiya dan ya santa sosai ta dalilin wani aiki da sukayi tare kuma ya gane kwatancen da Noor tayi na gidanta, ba tare da 6ata lokaci ba sai gasu tare da Dr Affan da yakeson jin dalilin irin wannan kira tsayawa yayi chak yana kallon Noor juyawa yayi ya kalli Hajiya da itama su d’in take kallo jiki a sanyaye duk suka zauna bayan an gama gaisawa Abba ya musu bayanin komai tare da godiya mai tarin yawa sai da Dr Affan ya nuna rashin jindadi sannan ya dakata, da gudu su Noor suka fada jikin Hajiya duk suka fara sabon kuka ita ms kasa daurewa tayi haka ta rungumesu suka dinga kuka daga baya kuma ta koma rarrashin su tareda godiyawa Allah da suka sake haduwa da danginsu, Dr Affan kuma auren da Noor din sa tayi harda rasuwan mijin shi yafi tada mishi hankali.
1
Godiya Hajiyar Affan ta shiga yiwa Baaba Azumi da Gamboji akan kokarin da sukayi akansu Noor in dan ita amatsayin yaran data haifa ta d’aukesu ba wai kawai had’uwar jini bane kaunace daga cikin zuciyarta, labarin yanda suka sha wahala gurin nemansu Noor ta basu da kwanciyarta a asibiti harda kwanciyar Dr Affan da duk tashin hankalin da suka shiga, kowa a gurin ya jinjina irin soyayyar da sukeyi wa yaran tabbas sud’in sun chanchanci a yaba musu musanman Dr Affan da yayi zaman jiran Noor duk da ya dan manyanta sai dai sunji dadi da yayi aure a yanzu ita kuwa Noor haushi taji da akace yayi aure dan had’uwarsu ya tada mata tsohon soyayyarsa.
Ba zato ba tsammani Noor tace “Abba innarmu tayi tafiya ne munje chan gida batanan anan dinma kuma batanan?” da sauri Mimi tace “kai ya Noor har wani maganar Inna kikeyi bayan duk azaban data gana mana da kuma kashe mana yar uwa da tayi wato Hauwa’u wanda ni kadai nasan cewa ita ce silar mutuwar nata!” ta fada tana share hawayen dake kwance a fuskarta duk jikinsu yayi sanyi da maganar da tayi da sauri Mustapha yace “wai kina nufin matar mahaifinku da muka kama harma da kisan kai ta aikata kenan ko kuma ba ita kike nufi ba?” cikin rashin fahimta tace “bangane matar da kuka kama ba Innar tamu ce take hannunku?” kafin yayi magana Abba yayi saurin fara basu labarin komai tun daga zuwanta gidan da kuma yanda ta tarwatsa farin cikinsu har zuwa kamata da akayi ita da d’iyarta duk sai da ya basu labarin iya abunda ya sani kuka sosai sukeyi banda Mimi da tace “kai Alhamdulillah ya ubangiji nagode maka daka kawo karshen wannan matar ya Allah ka wulakanta rayuwarta irin yanda ta wulakanta namu kuma ka sanya tayi mumunar cikawa ya Allah ka nuna mana ranar da zamu ga rayuwarta ya tagayyara” kowa agurin kawai zuba mata ido yayi da tayi irin wannan mumunar addua ga kanwar mahaifiyarta sannan kuma musulma yar uwarta.
Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace “kubar ganin cewa dan tana yar uwar mahaifiyata zan saurara mata tabbas da ace za’a bani hukunci a hannuna wallahi sai ta gane cewa ni din na tsane ta tsana kuma bana baki ba kawai ba na gaske wanda yake fitoww daga karkashin zuciyata cutar da Inna tayi mana ba irin wanda zamuyi saurin yafe mata bane Innarmu muguwa ce kuma azzaluma ban ta6a ganin munafuka irin Innarmu ba Innarmu ta cutar da Mahaifiyarmu ta cutar da mahaifinmu ta cutar da ku kanmu yaran yar uwarta koda yake ta cuci yar uwarta ma balle mu ku sani cewa Inna dai da kuke gani ita ta kashe mana uwa da yar uwa!” ta fad’a cikin d’acin rai a yanzu kam kowa acikin rud’ani yake data ambaci kisan mahaifiyarsu.
Murmushi mai ciwo tayi kafin tace “alokacin da muke aiki acikin gidan ni kadai take bari inje cikin falonta bayan haka babu wanda take yarda yayi mata gyaran d’akunan sama sai d’iyarta, aranar da aka d’auki azumi kin aikeni inje in sanar mata cewan gyad’ar da tace za’ayi kunuj gyad’a dashi ya riga ya 6aci dan dama tace ki duba idan yana da kyau in babu sai ayi wani ina shiga na sameta tare da wata kawarta sai dai kasancewar k’ofar abud’e yake shiyasa har na iya shiga basu sani ba kafin inyi magana naji Innarmu na cewa “ai Hajiya Asabe da ace bamu kashe ta ba da yanzu kila Alhaji ya dawo dai dai ni kuma ya koreni” hakan da naji sun fad’a yasa ni la6ewa a bayan kofa, wacce aka kira da Hajiya Asabe tace “tabbas kin kyauta da kikayi amfani da abunda na fada miki sannan ya batun yaran nida naso ace dana dawo zanji kyakyawar labari wato labarin mutuwarsu!”.
STORY CONTINUES BELOW

Tsaki Innarmu tayi kafin tace “ai yanda nasa aka kashe uwarsu haka naso ace duk na kashesu, baki sani ba ai mutuwar yar nan ba haka kawai bane jarkan ruwa na musanya na sanya na kalanzir irin wannan da warinsa baya saurin tashi sai kuma ya kasance Hauwa’u ce dai kawai tasha sauran babu wacce tayi amfani dashi ganin haka yasa kafin su dawo daga kaita asibiti ni kuma na mayarda ruwan a mazauninsa na dauke kalanzir din Allah yaso babu wanda ya ganni a lokacin harna mayar da jarkar kalanzir din, nayi tunanin sake had’a wani abun sai dai kuma kisan zaiyi yawa yanzu inason koransu baki d’aya su fita daga rayuwarmu dan sun isheni wallahi nida d’iyata munason jindadi amma na tsani ganin yarannan sun hanani sukat” dariya kawarta tayi sannan tace “ai ko dai gwara da kowa ya rufawa kansa asiri inda ace wani yayi gigin ganinki da shima mun aikashi barzahu tuni irin na nurse din data sanya guba ajikin uwarsu kafin ta gama karasawa gudun kar wata rana tace zata tona mana asiri shiyasa kawai nace mu kasheta” daganan suka sheke da dariya suka cigaba da hiran yanda zasu lalata rayuwarmu da sunso a yiwa yaya Noor fyad’e sai de kuma suka janye akan kawai gwara su turamu cikin duniya kila mu fada harkar karuwanci aranar da sukace da zasu sanya ayi mata fyad’en ni kuma naji tsoro kar ba fasawa sukayi ba kila su sake yunkurin aiwatar da niyar su shine nasa yaya Noor ta kaimu gidan Hajiya dan mu gaisheta duk da yaya bataso ba amma na dage saboda kawai ina jin tsoro kuma inason in kubutar da ita tunda dai Allah yayi cewa ni zanji zancen nasu a haka na koma gurin Yaya Noor nace mata Innarmu na barci daganan kowa ta cigaba dayin aikinta duk dani jikina asanyaye yake akan cewa wai yar uwar mahaifiyarmu itata kashe mana mahaifiya harma da yar uwa kuma muma tana neman rayuwarmu tundaga lokacin na dinga mata la6e dan ina sonjin duk abunda zata fad’a ko kila zata sake kulla wani munafurcin har dai zuwa sanda ta yanke shawara akan koran mu kuma tayi hakanne wai saboda ta lura Abbanmu zai iya dawowa cikin hayyacinsa.
Jikin kowa a gurin yayi matukar sanyi da abunda Mimi ta fad’a mata masu rauni kuwa kuka sukeyi dan abun yayi matukar ta6a zuciyarsu Aminatu tace “Allah ya isa kuma baza mu ta6a yafewa ba wallahi Inna kin cuce mu kin cuci rayuwarmu kin kashe mana uwa da yar uwa kin sanya rayuwar mu cikin hatsari Allah ka wulakanta Inna Mardiyya yanda ta wulakanta mu” ta fada tana share kwalla ganin yanda duk suke ta maganganu yasa Noor ta riko hannun kannen nata kafin tace “tabbas adduar nan da kukayi mata tama chanchanci fiyeda hakan sai dai kuma inda fa ace muna tare da Ummanmu ayanzu ranta ne zai 6aci kuma abunda zatace bai wuce muyi hakuri kamu yafe mata ba, dan Allah mad’aukakin sarki yana son masu hakuri, yafiya da kuma yadda da duk wani kaddara mai kyau ko mara kyau,ku sani fa cewa komai na duniya mai karewa ne duniya ba madawwama bace kuma ko wani mai rai bai wuce jarabawar ba Allah ne ya jarabce ta da aikata haka kuma Allah yayi lokacin cikawarsu Ummanmu da Hauwa’u ne yazo inba da dan hakan ba babu wani abunda bawa zai iyayiwa wani bawan face abunda Allah ya riga ya kaddara inda ace Umma tananan fushi zatayi damu bama kamarni dan zatace ban daura ku akan irin hanyar data d’aurani ba shin yau kuna son ace Ummanmu ta rasa natsuwarta acikin kabarinta?” atare sukace mata a’a murmushi tayi mai ciwo kafin tace “ban ta6ajin ciwon mutuwar Umma kamar na yau ba saboda jin cewa guba ne silar mutuwarta amma ina farin cikin cewa tayi shahada duk da cewa ita mutuniyar kirki ce kuma uwa ta gari amma kashe ta da akayi ya kankare duk wani zunubanta haka Hauwa’u itama mutuwar shahada tayi, babu wani abunda zamuyi wanda zai sanya farin ciki acikin zuciyar mahaifiyarmu irin ace munyi amfani da duk wata tarbiyya data mana mun kumayi kokarin koyi da kyawawan halayyarta da kuma na magabatan mu ina fatan ayanzu duk zuciyoyin kannena yayi sanyi kuma zakuyi koyi da abunda mahaifiyarmu tayi da wanda ta koyar damu bazan manta ranar da marigayiya Habiba ta fad’i wani magana akan Innarmu ba budan bakin Umma sai tace “shin wai yarana bakusan samun rahamar ubangiji ne” duk mukace munaso sai tace “to kuyi kokarin tsarkake zukatanku kuma kuyi wa kowa kyakyawar zato kar ku kuskura kuce zakuyi zargi akan abunda baku da masaniya akai kuma ku zauna da kowa lafiya ku kyautata wa duk wani wanda kuke zaune dashi kuma kuyi biyayya aduk abunda bai sa6awa Allah madaukakin sarki ba ku kasance salihan bayi ku kuma kasance masu aiki da sunnar manzon tsira sannan ku kasance masu kiyaye harshensu akoda yaushe” wannan shine nasihar da tayi mana a ranar da zan iya cewa yana cikin ranakun duk mukayi ban kwana da farinciki domin rasa jigo na rayuwarmu” atare duk suka fashe da kuka suna cewa “wallahi Yaya Noor munbi Allah kuma munbi annabi kuma mun biki ba zamu sake kwatanta irin abunda mukayi ba ked’in uwace agaremu domin kinyi kokarin sanya mu akan hanyar daya dace ke d’in ta dabance kuma zaki samemu masu yin biyayya agareki duniya da lahira kuma mun yafe wa Innarmu Allah ya yafe mana baki d’aya” wani irin dadi Noor taji acikin ranta tare da rungumesu ajikinta.
Kabbara d’akin ya d’auka kowa yana kallonsu cikin sha’awa da kauna shima mahaifinsu tashi yayi ya rungumesu yana cewa “tabbas Mahida ta tafi ta tafi ta barni amma kuma bata barni ni kadai ba ta barni da abunda zan iya rayuwa ba sai da wani jigo ba ta kuma barni da abunda zan rinka alfari da kasancewarta uwar yayana ta barni da abun da kud’i ba zai iya saya ba ya Allah idan har nine zan d’aga k’afa Mahida ta shiga aljanna ya Allah na d’aga ya Allah ka sanya ta a cikin aljannar firdaus domin ita din macece ta kwarai kuma mumuna ta kwarai” duk gurin hawaye kawai suke zubarwa dan tausayinsu da kuma irin yanda yaran suka burge su tabbas mahaifiyarsu uwace ta gaji sai da aka gama kukan sannan aka jajantawa juna tare dayi wasu Gamboji da Baaba Azumi godiya kafin kuma aka shiga kiran waya ana sanar da yan uwa da duk wasu dangi na kusa dana nesa.
Bayan yaran duk sun watse an basu d’akuna su kuma manyan suka zauna dan tatraunawa Gamboji ta sanar dasu batun Auren Mustapha da kuma na Noor duk da cewa sunso abawa Affan amma kuma halaccin da suka musu na rike musu yara yasa suka sanyawa abun alkairi tare da fatan Allah ya kai musu rai ita kanta Hajiya taso ace su aka bawa Noor amma ai idan tayi hakan tayi son kai dayawa shiyasa bata kuma cewa komai ba sai fatan alkairi anan Hajiyar su Abba tace tana neman alfarma akan ahada aure tsakanin Hajiyar Affan da Baaba Azumi a d’anta Dr Muhammad Nur tunda ai duk basu da aure kuma ba wai sun wuce su sake auren bane idan yaso sai zumunci ya kara karfi sai su rike su Aminatu yanda suke burin basu rayuwa mai inganci kowa agurin yayi na’am da zancenta haka Baaba Azumi itama bata musa ba tayi fatan Allah yasanya alkairi ita dai Hajiya ce saida taga ran Hajiyarsu Abba zai 6aci sannan ta amince itama tare da fatan Allah ya sanya albarka a duka auren da za’ayi sosai duk sukayi farin cikin yardar ta sannan aka cigaba da tattauna yanda komai zai kasance na auren yaran su kuma nasu ana saura sati d’aya za’a daura dan su tare ayi auren Noor a gidan mahaifinta kowa yayi na’am da shawaran da aka yanke kafin duk aka watse cikin farin ciki da annashuwa.
Yau kan sunyi kwanan farin ciki acikin danginsu abunda suka cire rai da kara samu sai dai kuma ba’a cire rai daga samun rahamar ubangiji sannan sun kara godewa Allah da yasa mahaifinsu zai auri mutanen da sukafi kauna bayan mahaifiyar su domin mutane biyun nan sun taka muhinmin rawa acikin rayuwarsu.
Washe gari yan uwa na nesa na kusa da abokan arziki duk suka iso dan taya wannan ahali farin cikin dawowansu Noor nan akayita maida zance ana bada labari kaman yanda ya kasance a jiya kowa yayi mamakin haka kusab kowa kuma agurin saida yayi kuka wasu dai idanunsu ne kawai yayi jawur dan 6acin rai sai dai jin yanda komai ya kasance tsakanin yaran sai duk suma jikinsu yayi sanyi sukayi fatan Allah ya kare gaba kowa na gidan cikin farin ciki ya yini su Yasmeen ma sun zo farin ciki gurin Noor ba’a magana itama sosai ta sake da ita kamar sun dade da sanin juna har take gaya mata bikinta saura sati biyu ita kuma Yasmeen ta bata labarin yanda bikinta ya kasance sa irin zaman da sukeyi da mijinta sosai Noor tayi mata fad’a tare da nasiha duk da cewa itama tana da ilimi harma tafi Noor din amma 6acin rai yake ta sanya ta aikata komai sosai nasihar Noor din ya shiga zuciyarta har suka kwanta tana bata duk irin shawarwari daya dace ta kuma d’auka dan harta fara barci sai kuma ta kira Adam ta fada mishi cewa kwana zatayi yaji dadin kiran sosai duk da cewa idan taso ba zata fada mishi ba amma sai gashi harda kira godiya yayi mata dan sanarda shi datayi ita abunma dariya ya bata shi kuwa yayi matukar farin cikin hakan da tayi, kafin ya koma gida aranar suka had’u da Mustapha har sun gaisa cikin mutunci da girmama juna harma yake sanar mishi da bikin shi da za’ayi nanda sati biyu kuma Adam din yayi alkawarin zuwa.
STORY CONTINUES BELOW

Washe gari da safe kowa ya fara haraman tafiya gida cikin farinciki da natsuwar zuciya tare da alkawarin dawowa satin bikin Noor din kuma duk sunyi farincikin aureb da Muhammad Nur din zaiyi saboda zamanshi haka ba dadi ga yaransa suma lokaci yayi dazasu zauna agidansu su Gamboji ma duk suntafi cikin kewarsu Noor din sai kuma Aisha data tafi cike da tunanin Adams aranta (akwai damuwa fa Yasmeen zata 6allata).
Sati na zagayowa aka d’aura auren Hajiyar Affan da Abbansu Noor da kuma Baaba Azumi da Abbansu Noor kowa yayi farin cikin wannan aure barinma dai Noor da kannenta saboda tsaban farin ciki kasa barci ranar sukayi godiya suka dinga yiwa ubangiji daya nuna musu irin wannan ranar farin cikin Dr Affan da Auta suma duk sunji dadin lamarin sai fatan Allah ya basu zaman lafiya, sosai aka sake gyara gidan inda Hajiya tana sama Baaba Azumi kuma tana k’asa amma komai nasu iri d’aya ne masu aikin Hajiya ne suka cigaba da musu aiki agidan ta fannin gyaran gida da taya Ladidi aikin kitchen wataran Hajiya da Baaba Azumi sukanyi girkin da kansu sunayi suna hira gwanin shaawa Aminatu da Mimi suna chan masarauta sai sun zana Junior waec dinsu zasu koma gida dan sun kusa ma farawa da zaran an koma hutun.
Noor kuwa yanzu ba wani sosai take hira da angonta ba dan dama kullun sai dai suyi hira bata yadda yazo gurinta duk sanda yayi niyar zuwa sai tayi mishi wani karyar haka zai hakura dan kansa tun yanajin haushi har dai ya sanya hakuri acikin zuciyarsa tunda kwanaki kad’an suka rage ta zama matarsa.
A6angaren Mustapha har an gama gyara mishi gidan kuma Huzna ta gama had’a kayan lefe komai yaji acikin akwatin Gamboji taji dadin yanda ya saki jiki ba tare da nuna rashin son auren ba duk da har zuwa lokacin ta hanashi ganin amarya sedai suyi waya shima ba ko yaushe ba itama amaryan ba kaunar zuwansa takeyi ba dan duk sanda yace mata zai zo saita kawo mishi wani uzurinta hakan yasa ya hakura da zuwan har sai an kawo ta saiya ganta.
Yanzu Yasmeen ta d’anyi sanyi ba kamar da ba har gaisheshi tanayi tana musu girki tare kuma tana gyara mishi d’aki ba karamin dadi yaji ba duk da shima ya fara shareta dan yanzu shishige mata da yakeyi ya dena hakan kuwa yana matukar damunta sai dai tana dannewa a cikin ranta kosa taji kabarin auren Mustapha fatan alkairi kawai tayi mishi duk da ta d’anji ba dadi a ranta amma ta share saboda tasan kila kwadata ma yake sonyi dan yaga irin abunda zatayi ai kuwa ta bashi mamaki yanda ta nuna ko akolar rigarta.
♣🌹♣☘♣🌻♣
Rana bata karya sai dai uwar d’iya taji kunya duk abunda aka sanya mishi rana cikin hukuncin Allah zai zo ya wuce kamar ba ayi ba, ayau dai mutane da dama manyan masu kud’i, talakawa, manyan masu muk’ami sarakuna manyan malamai suka shaida daurin auren Noor da angonta Affan acikin babban masallacin garin Bana yayinda aka daura na Mustapha da amaryar sa Jidda cikin aminci a masarautan Yola, anyi daurin aure lafiya cikin kwanciyar hankali ko wani 6angare suna cikin annashuwa Mustapha de bai san koda wata Jiddan aka daura auren ba yayin da Affan ya kasa ta6uka komai daga zuwa d’aurin aure kuma sai a d’aura dashi matarsa ya tuno yanzu shin mai zai ce da ita ai koma meye bazata yarda ba zata ce yasan cewa aurensa ne alhali shi har ga Allah bai san da wani zancen auren ba bazata kawai aka mishi yanda ya lura kuwa duk kowa ya san da cewa d’aurin aurensa ne dan abokan sa duk sunzo sai sanya alkairi sukeyi.
Amarya sun iso cikin masarauta lafiya achan 6angaren Gamboji aka fara ajiyeta kafin aka mai data nata gidan masha Allah abu da jinin sarauta komai yaji sai son barka bayan sunyi sallar ishai aka fara haraman zuwa dinner inda sarki Aliyu da kanshi ya shirya musu an tsara gurin gwanin burge wa komai golden da fari mutane da yawa sun iso ciki harda Amarya Noor da angonta Affan wanda sarki ya tura private jet dinsa suka d’aukosu dan yace harda su aka shirya dinner Husna da Haidar ma sun iso sai manne mishi takeyi saboda kar yan mata su kyasa, Faruk na hango tare da matan nasa Falmata da Amal sun sanyashi a tsakiya ko wacce taci gayu dan burge mijinta abun dai gwanin ban shaawa mutane da dama sunzo dan taya su Mustapha da Affan murna Oganshi da matansa suma duk sun hallara chan na hango yan yar Almajira fans sun cika canopy guda sun sha goggoro bama kaman Ayeesha da juwai da Aishatudarling ga sarkin rawa harta fara motsa k’afa (kunsanta ai ba sau na fad’i suna ba) ga yan Hikima writers Association sunyi ankon leshi kota ina fans din yar almajira sosai sukayi bidiri agurin dinner anci ansha an godewa Allah kowa sai son barka da fatan alkairi haka taro ya watse cikin kwanciyar hankali da annashuwa tare da yiwa amare fatan alkairi.
3
STORY CONTINUES BELOW

Mustapha sai agurin dinner ya gane amaryar sa itama sai a gurin ta ganshi sai dai ta manta insa ta ta6a ganinshi, shi kuwa yaji dadin za6in da mahaifiyarsa tayi mishi ko ba komai yarinyar tun ganin farko ta kwanta a ransa gata kuma da ilimi na addini da halayya masu kyau, 6angaren Noor kuwa tayi matukar mamakin ganin Affan a matsayin mijin aurenta sosai tayi farin ciki har hakan ya gaza 6oyuwa sai dai tayi kokarin seta kanta sanda suka had’u a gurin dinner dan sai a gurin tasan cewa shi aka aura mata.
Washe gari da safe suka yiwa su Gamboji sallama da Mustapha da amaryar sa kafin wanda ya kawo su ya maidasu a gidan Abbansu Noor suka sauka dan Hajiya tace tanason ganinsu koda suka isa yan biki duk sun watse sai daidaiku acikin babban falon gidan suka zauna inda suka samu Hajiya kakarsu Noor da Abbi da kuma Gimbiya Nuraini kakarsu ta wajen uwa, bayan sun gama gaisawa Hajiya da Baaba Azumi da Abba suka fito chan sai ga Auta ita da mijinta sai kuma Ghaji da mijinta sannan Hadiza data shigo duk jikinta a asanyaye idonta jazir halamar tayi kuka sosai bayan sun zauzauna aka bud’e taro da addua kafin Abbi ya shaida musu cewa Gamboji da kanta ta bawa iyayen yaron dake neman Noor hakuri sannan ta gaya musu dalilin fasa auren suma sun goya mata baya sun kuma sanya alkairi yaron ma sun bashi hakuri kuma ya fahimta kuma abunda yasa tayi hakan shine ganin chanchantar auren Noor da Affan sai kuma tayi amanna cewar Dr Affan shi ya dace da Noor kuma zai riketa bisa amana fiyeda yanda wani bare zai iya riketa kuma tazo har gurin Hadiza tayi mata bayanin komai kuma ta fahimta tare da bada goyon baya hakan yasa ma aka d’aura auren ba tare da sake d’aga lokaci ba nasiha Abbi yayi musu sosai kafin yayiwa Affan akan rike matansa bisa amana da kuma kyatata musu ba tare da fifita wata akan wata ba domin idan gidansa yayi kyau koya 6aci toh duk shine dan haka yana da kyau ya gina gidansa cikin aminci da tsoron Allah bayan ya gama nashi Abba ma yayi sai Gimbiya Nuraini da Hajiya Babba sannan Hajiyar Affan da Baaba Azumi kafin aka rufe taro da addua daganan kowa ya watse bayan an raka su motan da zai kaisu gida.
1
Mustapha da direba ne a gaba Noor da Hadiza kuma a baya ko wacce zuciyarta kaman zai fashe sai dai duk suna daurewa bama kaman Hajja Hadiza data riko hannunta tare da mata murmushi tana cewa “amarya kin min kwacen miji koh toh Allah ya bamu zaman lafiya” kasa cewa komai Noor tayi sai murmushin yak’e da tayi wanda yafi kuka ciwo wani irin zafi takeji kaman an watsa mata garwashi dan ita batasan tana da kishi har hakan ba sai a wannan rana sai dai tana fata Allah ya yaye mata karta zama dalilin rushewan farin cikin gidan Dr Affan kuwa mamakin Hajja Hadiza kawai yakeyi bai san cewa hakurinta ya kai haka ba (niko nace ayya tayi sanyi shiyasa amma data dace da yanzu kun kwashi yan kallo) suna isa duk suka sauka har zuwa lokacin Hadiza tana rike da hannunta sai da ta kaita har 6angarenta dan gidan 6angare biyu yake dashi sai dai ta k’ofa d’aya ake shiga ko wani gefe d’aki bibbiyu da falo sai kuma babban falo d’aya da kitchen a tsakiya sai dinning, anyiwa Noor jere na gani na fad’a ba zata nunawa Hadiza kaya ba dan itama kayanta ba daga baya ba sai dai wasu abubuwanta sunfi na Hadiza tsada amma batun quality ko wacce nata mai kyau ne falonta komai na ciki baki da fari dakinta daya komai pink da fari daya kuma konai purple da fari sai babban falo inda akayi musu fari da ruwan madara komai yayi kyau agidan matsala daya kitchen daya suke dashi sai dai babba ne sosai dan ko wacce anyi mata gere ta gefe guda abubuwan da za’a iya sawa a falo kamar fridge da dispenser duk an kai musu falonsu fridger kuma na Noor a dinning na Hadiza a kitchen an sake cabinet d’aya ta gefe guda inda akasa kayan Noor sai kuma store dinsu wadatacce dan wasu kayansu a ciki akasa.
Bayan dreban ya tafi ya tsaya yayi sallar azahar bai shiga gidan ba sai bayan sallan Magriba inda ya fara zuwa 6angaren Hadiza kuma kamar yanda ta saba tarbarsa hakan tayi bata chanja ba shima yaji dadin hakan sosai babban falon suka koma inda ya aika ta kira Noor atare suka shigo sai ya tsaya kare musu kallo sukansu kyawawa ne zainiya ce Noor haske kawai zatafi Hadiza sai dai ita siririya Hadiza kuma tana da dan jikinta dai dai misali dukansu babu na kushewa kuma duk babu wacce zata nuna ma wata wani abun hamdala yayiwa ubangiji daya azurtashi da mata kyawawa son kowa kin nai bakin ciki bayan sun zauna yayi adduar bude taro sannan yayu musu nasiha tsare da nuna musu sukansu d’aya ne agurinshi kuma duk ya auresu ne saboda yana sonsu babu wacce baya so acikinsu kuma bazai yarda da rashin girmama junansu ba sannan wajibi ne aci abinci tare koda kuwa kowa zata girka abunda takeso amma a zauna guri daya aci tare in dai bawai daya tana barci ko batajin dadi ko kuma wani lalura ba toh dole su zauna tare suci abinci suyi hira su hada kansu sannan bazai yarda da raini ba ya gargadi Noor akan karta raina mishi mata dan bawai baya sonta ne ya kara aure ba kuma tana gaba da ita dan haka ta bata girmanta itama Hadiza yayi mata gargadin karta raina mishi mata dan dukansu matsayinsu guda agurinsa kuma duk yana kaunarsu bayan haka ya yanke zai rinka musu kwana bibbiyu idan Noor ta cika sati daya nasiha mai ratsa jiki ya musu Hadiza mai saurin kuka tuni ta fara sai da yayi aikin lallashi sannan ya kaita d’akinta tare da kanainayeta da kalmomi masu dadi ya ajiye mata kazarta kafin ya tafi dakin Noor itama dai tasha kukanta ta koshi daganan kuma na fito tare da musu fatan zaman lafiya da zuria dayyiba.
Su Inna Mardiyya an yanke musu hukuncin daurin rai da rai sosai suka shiga tashin hankali sai alokacin suka fara dana sanin abunda suka aikata dan basu ta6a kawowa aransu cewar duniya zata juya musu baya ba tabbas sun cutar da Noor sun maida ta Yar Almajiran dole gashi yanzu ta samun Juyin Lamari a cikin rayuwarta ta kuma samu soyayyar danginta da kuma gidan hutu tare da miji na gari asanda su kuma suke Ihu Bayan Hari sosai sukayi bakin cikin rayuwarsu tare da nadama mara amfani tabbas sai a yanzu suka fahimci cewa rayuwa Gida Biyu ne dadi da akasinsa mai kyau da mara kyau haske da duhu ahaka aka tasa keyarsu zuwa cikin gidan yari domin su fuskanci hukuncin da aka tanadar musu.
A6angaren Noor zaman lafiya sukeyi da mijinta da kuma abokiyar zaman ta sosai suka had’e kansu suka watsawa mahassada kasa a ido suka kuma bada mamaki musanman da suka samu miji tsayayye wanda bai yarda da cin zarafin dayansu ba ko kuma wulanta daya daga cikinsu ba.
Alokacin da Affan ya fuskanci Noor budurwa ce sosai yayi farin ciki duk da yana danjin saurin haushin Tasi’u daya aure mishi mata amma kuma idan ya tuna cewa shiya fara saninta sai yaji wani natsuwa a cikin ransa sosai yake kokarin faranta ran matan nasa tare da maida ko wacce sarauniya a cikin ransa yana iya kokarin ganin yayi adalci atsakaninsu shiyasa suma suka kwantar da hankalinsu tare dayi mishi biyayya da kuma wanzar da zaman lafiya a tsakaninsu.
Lokacin da Noor taji labarin hukuncin da akayi wasu Inna Mardiyya sam sam bataji dadin hakan ba sai dai babu yanda ta iya yan uwanta ta kira tare da sake tabbatar da sun yafewa Innarsu har cikin ransu sannan ta kira mahaifinta da sauran dangi suma suk saida kowa yafe sannan ta samu kwanciyar hankali kowa sai mamakin irin halinta yakeyi tare da fatan Allah ya basu zuciya mai kyau irin nata.
Zaman Mustapha da Jidda dai sai yar sannu da sannu daga idan sun hadu yace mata sannu sai itama tace mishi yauwa sannu kullun sai dai suyita satan kallon junansu amma agaban mutane basa nuna cewa akwai rashin jituwa a tsakaninsu.
STORY CONTINUES BELOW

dadin sa d’aya bata da son jiki kuma bata da girman kai komai na cikin gidan da kanta takeyi sam-sam batason zama da mai aiki dan ko da Gamboji tace zata aika mata bayi cewa tayi ita kam bataso zata iya aikinta da kanta.
Jidda akwai tsafta da iya daukan wanka gata da son yara shiyasa take matukar kaunarsu little Zahra duk rashin kaunar dasu Aisha suke nuna mata hakan ko a kolar rigarta duk abunda ya dace tayi musu tanayi sai dai bata daukan raini ko kad’an shiyasa ma suke shakkan yin wani abun musanman idan agaban idonta ne saboda kwarjininta.
Kulawar da take basu yana matukar sanyaya ransa kuma hakan ya gina mata wani gurbi acikin ransa.
A6angaren su Yasmeen yanzu sun zama tsintsiya mad’auri daya zaman lafiya sukeyi kamar basu ta6a samun sa6ani ba, tun wani lokaci data ganshi yana wayan karya kamar da mace yakeyi a yanda abokinsa ya bashi shawara sai hankalinta ya tashi bori tayi mishi sosai daker ya samu ta natsu yayi mata bayani sannan ta huce daganan suka shirya kansu cikin kankanin lokaci ba tare da dangi sun fahimci irin zaman nasu ba, alokacin da suka kaiwa Hajiya ziyara tayi murna sosai dan ta riga tasan akwai wata matsala atsakanin su farin cikinta ya kasa 6oyuwa a sanda taga sun had’e kansu sosai ta kara yi musu nasiha tare da adduar zaman lafiya.
Gidan Ghaji da Auta suma sai son barka ko wacce suna zaman lafiya da mijinta cikin natsuwa da kwanciyar hankali su ma mazajen suna iya kokari gurin sauke duk wani nauyi daya rataya a wuyansu duk gidaje ukun sun had’e kansu da Affan da Aliyu da kuma Malam Handsome zumunci suke atsakaninsu fiyeda yanda sukeyi ada.
Hajiya da Baaba Azumi zaman su babu wani matsala sai girmama juna da kuma tsantsan zaman lafiya kwanciyar hankalin yaran nasu shi yake kara sanyaya ransu musanman zaman Noor da Hadiza duk ko wacce na kokarin kawar da shaidan daga ranta tare da danne kishinta da yiwa juna kyakyawar zato hakan ya basu natsuwa a zukatansu da kuma kwanciyar hankali.
♣🌹♣☘♣🌻♣
6years later
Bayan shekaru shida abubuwa da yawa sun faru ciki harda zaman lafiya tsakanin Jidda da su Aisha da kuma mijinta Mustapha sai da sukayi shekaru biyu sannan duk suka fara kyautata mata tare da sakin jiki da ita dan sun fuskanci ita din uwace ta gari shi kuma mijinta sai bayan data shirya da yaran sannan suka shirya suma tare da gina soyayya mai tsafta atsakanin su.
Komai suna gudanarwa cikin natsuwa da kaunar junansu ayanzu yaranta biyu dukansu maza d’aya mai sunan mahaifinta Sulaiman ana kiransa Sudais d’aya mai sunan sarki mai rasuwa wato Abdurrahman ana kiran sa Shureim Hafiz yayi murnan samun kanne maza kullun yana gida mak’ale da yaran suma kuma suna son yayan nasu da sunji muryansa zasu fara tsalle tsalle su fita da gudu dan murna shiyasa daya tafi karatu akasar waje sai da duk sukayi zazza6i zamansu gwanin ban shaawa.
Cikin shekaran nan Hafiz ya kammala karatunsa na masscom akasar waje kowa yayi murnan dawowarsa musanman yan kannensa Sudais da Shureim dan wani irin kauna ne tsakaninsa da su, Aisha kuma achan Abuja a Nile University tana karanta medicine dan Mustapha yace yaransa mata ba zasuyi karatu awaje ba sai mazan, Hafsa kuma tana ss3 Halima jss3 Zahra jss1 Jidda kuma ya bud’e mata babban asibiti acikin Gombe tare da d’aukan kwararrun ma’aikata.
Aisha tun tana dakon son Adams har dai ta hakura bayan Noor ta bata shawaran hakuri da batun dan tasan yanda Adam yake matukar kaunar matarsa zaiyi wahala ya iya kara aure duk da cewa aure nufin ubangiji ne hakan yasa ta hakura tare da sanya wa zuciyar hakuri daga baya ta samu wani malamin makaranta dan jos inda a yanzu har anyi baikonsu tana gamawa za’ayi bikinsu.
Ghaji ta haifi yara uku mata biyu na miji daya sai Auta itama yaranta uku maza biyu mace daya Yasmeen ma yaran ta uku maza biyu mace daya sosai suke zama da mazajensu cikin jindadi da annashuwa tare da kokarin bawa yaransu tarbiyyar data dace ko wacce ta gama jami’a inda Ghaji take aiki a 6angaren jarida ita kuma Auta lawyer ce sai Yasmeen Likitar mata ko wacce tana bana aikinta cikin kwarewa da kuma kiyaye dokokin ubangiji tare da kula da gidanta yanda ya dace.
Gidansu Noor suma zamansu sai son barka Noor ta haifi yaranta uku mata biyu namiji dana ita kuma Hadiza yaranta hudu yan biyu maza da yan biyu mata sosai Affan yayi farin cikin samun yara bakwai a cikin shekara shida Noor da Hadiza duk tare suke aiki da mijinsu acikin babban asibitin Bama kuma ayanzu Affan yana kan gina musu Asibiti inda zasu koma aiki tare dashi baki d’aya zaman su gwanin sha’awa duk sun toshe wani k’ofa da zai kawo musu 6araka a tsakani basu da kawaye bayan Ghaji, Auta, Jidda matar Mustapha da Yasmeen duk sun had’e kansu suna zumunci tare da ilimantuwa da juna hakan kuwa ya sanya natsuwa a zukatan mazajensu.
Wadannan ahali suna cikin kwanciyar hankali kullun suna kara godewa Allah daya jarrabesu kuma ya basu ikon yarda da kaddara gashi a yanzu komai ya wuce kamar ba’ayi ba kullun nasiharsu ga mutane shine su kasance masu hakuri da yarda da kaddara da kuma yiwa kowa kyakyawar zato domin hakan zaisa musu natsuwar zuciya domin duk abunda yayi farko zai yi karshe.
Tammat billah, Alhamdulillah anan zan ajiye alkalamina Allah yasa a amfana da abunda aka karanta ina yiwa kowa fatan alkhairi