YAR SHUGABA CHAPTER 1

YAR SHUGABA 
CHAPTER 1
Mototaci ne guda uku suke tafe bisa hanya aguje, dukansu gilas d’in motocin masu duhu ne, mota ta farko dake gaba bodyguard ne a ciki. Sai na tsakiya motar d’auke yake da tsadaddun ‘yan mata su uku wanda ba zasu wuce shekaru Ashirin da biyu (22yrs) ba a duniya. 
“Yar Shugaban k’asa ce‘ Queen Basma, ta hakimce a seat d’in baya ita kad’ai, sai Meena ‘yar Governor Kaduna ce ita ke driving, sai Leema ‘yar Sarkin Kano wacce take gefen Meena. 
K‘aran wak’ar Music na Larabawa ke tashi a motan, dukkan su suna bin wak’artamkar sune suka rerata, sunayi suna rawa da kad’a kai, kana ganin su kaga ‘ya’yan gata, cike suke da farin ciki fal da nishad’i, domin ba suda wata damuwa k0 matsala a rayuwansu. Motan baya itama na bodyguard ne, suke marawa motan Queen baya. 
Wani Matashin Saurayi wanda bai wuce shekara Talatin ba (30yrs), yake taflya cikin sauri domin ya amso wa Ummansa nik’an masara da k’anwarsa Khadija ta kai ta aje, saboda zata wuce tallan kwai, hankalinsa yayi nisa sosai cikin tunani, baisan yahau kan titi ba. Meena taja birki ji kake  keeeee kadan ya rage ta bigeshi Aryan tsayawa yayi ya runtse ido yana fad’in ‘Innalillahi wa inna ilaihir rajuun’ jira yake motan ta bigeshi domin ya riga ya sadak’ar motan zata kad’eshi, Cikin b’acin rai Queen Basma, Leema, Meena duk suka fitO a motan, haka bodyguard suka yi parking akan hanya suka fito rik’e da bindigogi, cikin k’ank’anin lokaci suka had’a gosilo, mutane suka fara taruwa, ganin bindiga ne yasa kowa ya kama kansa, Queen Basma ta k’arasa kusa da Aryan bodyguard suka take mata baya, tsadadden k’amshin turarenta ne ya dawo da hankalin Aryan jikinsa, domin ji yayi wani k’amshi na ratsashi, bud’e ido yayi a hankali yayi tozali da kyakkyawar fuskan Queen wanda saida gabansa ya fad’i, nan take tsoro ya ziyarce shi, kallon k’asa da sama Queen Basma ta bisa dashi cike da jin haushinsa, kyamansa taji saboda wani irin warin zufa dake tashi a jikinsa, tattaro miyon bakinta tayi ta tofa masa a jikinsa tare da toshe hancinta da hankacif, juyawa tayi ta kalli d’aya daga cikin bodyguard d’inta, cikin sauri ya k’araso, Aryan baiyi aune ba bodyguard d’in ya kifa masa 
kyakkyawan mari guda biyu, Leema ce ta k’araso cikin isa tace “Hee, Marin ma kad’ai ya ishe shi” sai tajuya tana kallonsu Meena tana murmushi, ta kuma cewa 
“babies mu wuce kar mu b‘atawa kanmu lokaci akan wannan mahaukacin, kunsan duk muna da abinyi a gabanmu”.Dakyar Aryan yaja k’afansa zuwa gefen hanya, zuciyansa cike da k’unci, su kuma su Meenal suka shiga mota suka wuce. 
Tsananin damuwa ne Aryan ya tsinci kansa a ciki, sai ya fara zancen zuci yace, 
“shi dai talaka kullun shi wulak’antacce ne a idon jama’a, Allah kai ka haliccemu kayi mana banbancin njinsi, kaine mai girma, ka saka mini da kyakkyawan sakayya” wani guntun hawayen ya sauka a kuncin sa, ba abinda yake k’ara masa bak’in ciki sai irin yanda Queen Basma ta tofa masa miyau, murmushi yayi na k’arfin hali ya girgiza kai a flli ya furta “Rayuwa ce” sai ya wuce inda zashi. Sai gabda Magrib ya kaiwa Umma nik’an masaran, ya sameta ta rafka tagumi, sallaman da yayi shine ya dawo da ita daga duniyar tunani data fad’a, nisawa tayi ta amsa tace Aryan ya akayi ka dad’e ga ruwan sanwan ya tausa harya fara k’onewa” zama yayi a tabarma dake tsakar gidan yace “Umma kiyi hakuri naje basu nik’a ba saida najira suka nik’a shiyasa na dad’e” Umma tace “Allah sarki, ba damuwa tunda mun samu nik’an yanzu zan gama insha Allah” Nan ya zauna yana mata hira tana aikinta har aka kira sallan Magrib ya wuce masallaci. 
Ta b’angaren su Queen Basma kuwa gidan hutawanta suka wuce, musamma tasa aka gina mata shi dan hutuwa. K’aton gida ne babban flat wanda ya k’unci kayan alatu a ciki, ginin zamani aka yi shi a tsakiyar babban fili, filin gidan za a iya pakin mota goma, sai daga can gefe ruffa ne mai d’auke da kujeru da table a tsakiya, an tanaji wannan wurin ne dan hutuwa, wurin zagaye yake da shukokin furenni masu fidda k’amshi mai dad’i, sai kuma daga bayan gidan katon swimming pool ne wanda aka sanya masa ruwa mai kyau da tsafta, in ka kalli ruwan har kashe ido yake dan haske, lokaci-lokaci akejenye ruwan ana sauya wani. Daga gaban swimming pool d’in akwai wata yar k’aramar k’ofa wanda zai sadaka da cikin garden(lanbu), ya k’unshi bishiyoyi na kayan marmari (fruits) da kuma kujeru na hutu dan shawakatawa, wurin ya had’u matuk’a. 
Suna shiga cikin gidan suka shiga babban falo, basu zauna ba sai k0 wacce ta nufi d’akinta kamar yanda suka saba, falo ne mai d’auke da d’akuna guda biyar ko wanne da ban d’aki a ciki (toilet), d’akin farko shine na Leemat wanda aka k‘awata shi da kayan Sarauta a matsayinta na gimbiyar ‘yar Sarkin Kano. 
D’aki na biyu shine na Queen Basma wanda aka kawatashi da kayan more rayuwa, an kashe mak’udan kud’i sosai, a matsayinta na ‘yar shugaban k’asa. 
Sai d’aki na uku na Meena ce, wanda shima aka k‘awata shi da dukiya, amma bai kai na Queen ba, a matsayinta na ‘yar gomna. D’aki na hud’u kuma an sanya masa kaya dai-dai misali, sun bard’akin na masaukin bak’insu. 
Sai kuma d’aki na biyar, tsadaddun kayan motsa jiki ne a ciki, wanda k0 wani lokaci sukan mota jikinsu a ciki. Sai katon kitchen dake gefe yaji kayan amfani. 
Wannan gidan musamnan Basma tasa mahaifinta President ya gina mata shi, bayan dawowarta daga k’asar England karatu, kasan tuwar sunyi karatu tare da Leema da Meena yasa ta sanya ko wacce aka shirya mata d’akinta dan soboda tsananin shak’uwar su kullun suna tare. 
Queen ce ta fito daga ita sai best da pant ta d’aura towel a k’ugunta, hanyar k’ofar baya tabi ta bud’e, direct wurin swimming pool ta wuce, tana isa ta cire towel d’in ta fad’a cikin ruwan ta soma iyo, suma su Meena haka suka fito cikin shigarda Basma tayi, cikin ruwan suka shiga suma suka fara wanka, k0 wacce na abinda ya shafeta. Sun kai misalin Rabin awa a ciki kana Meena ta flta a ruwan, ta zauna a kujeran hutawa dake bakin swimming pool d’in, wani jaka naga ta d’auka ta zage zip d’insa, sigari ta ciro tare da leta, sai ta kunna mata wuta ta hure, kana ta kwanta a bayanta tana zuk’ar sigarin tare da fidda hayak’i sosai ta hanci da baki. Leema ma fita tayi ta zauna a kujeran hutuwa nesa da Meena kad’an, wayarta ta d’auka ta fara chart da abokin harkanta, murmushi take zubawa ita kad’ai da alama tanajin dad’in hiran. Queen Basma tana cikin ruwan ta tsaya da wankan cikin fad’a tace ma Meena “Malama kinsan na hanaki wannan shirman muddun ina wuri ko, ya zaki kunna sigari ya rik’a cutar damu, kuma kinsan bana son warinta” cike da d’aure fuska Meena tace To maida damuwarki zan kashe shikenan?” sai ta kashe ta jefar, bud’ejakanta ta kuma yi ta d’auko kwalban syrup tace cikin gatsali, in kin hanani shan sigarin to ba zaki hanani shan wannan ba, don ita ba hayaki .
Basma take ta fito cikin ruwan ta d‘auki towel d’inta tare da gallawa Meena harara tace ” kanki kike cutarwa” taja tsaki ta wuce cikin falo. Meena itama ta bita da harara bata ce komai ba, Leema ta kalleta ta kwashe da dariya tace 
“wow ina son fad’anki da Basma, domin kullun sai kinyi abinda bata so a wurin nan, ita kuma kullun sai ta tanka miki”. Tsaki Meena taja tace “Ke kuma ‘yar sa ido, to ya isheki, kije ki cigaba da iskancin ki, gwara ni bana bin maza” ran Leema ne ya sosu, ta d’aure fuska, nan take sarauta ya motsa mata, tashi tayi tabi bayan Basma. Meena ta bita da dariya tace “na dai gama”. 
Leema ta samu Basma sanye cikin riga iya cinya ya kamata, ta sanya wakar music sai tikar rawa takeyi tana motsa duk sassan jikinta, tsaki Leema tayi tace 
“zaki damu mutane da wannan wak’ok’in shirme” cikin fad’a Basma tace 
“ina ruwanki, naga kowa yanayin abinda ya dameshi ne, ki shiga d’akinki kiyi chart da samarinki ban takuraki ba, nima ki barni inyi rawata”, hararanta Leema tayi bata tanka mata ba, Meena ce ta shigo falon idunanunta sunyi jawur saboda ta shawu, joining d’in 
Basma tayi suka cigaba da rawa ba tare da ta canza shigar dakejikinta ba. 
Saida aka kira sallan magrib kana Basma ta kashe wak’ar, duk suka wuce d’aki, wanka ta fara yi tare da d’auro alwala,jallabiya ta sanya wacce take sallah dashi ta sanya hijab ta tayar da sallah, bayan ta idar tayi duk azkar da ake karantawa da yamma, ta d’aura da Addu’a, Al’Qur’ani ta shiga karantawa cikin muryanta mai zak’i, tana zaune a haka har aka kira sallan Isha’i, sai ta rufe Al’Qur’ani ta gabatar da Sallan Isha’i. Bayan ta idar ta mik’e ta sauya shiga cikin doguwar riga har k’asa yar kanti, ta kamata sosai 
tun daga samanta har k’ugu, daga gwiwa ya bud’e kad’an har k’asa an masa tsagu. Ta busar da gashinta da hand dryer, ta sanya mai ta kamashi da ribon a tsakiyan kai, ta bar jelan gashin yana reto a bayanta, ta d’auko hular mulki na Queen ta aza a saman gashinta, turare ta fesa masu dad’in k’amshi, ta sanya siririn sark’an goal a wuyanta tare da d’an kunne, a gogon hannu ta sanya da zobe, tayi kyau sosai, sai ta sanya takalmi dogo mai igiya, haka ta d‘aureshi har k’auri, saida ta k’arewa kanta kallo a madubi sosai kana tayi wani murmushi wanda yake k’ara fidda kyanta, sai ta nufi falo cike da takun k’asaita. 
Kallon-kallon su Meena da Leema suka yi saboda I’rin had’uwar da Basma tayi, sai suka ga tasu wankan ba komai bane saboda Queen ta lashe duka wankansu. D’aukarta photo suka farayi kala-kala, suna mata kirayi tare da kurantata, a kullun Basma in dai zasu fita zuwa club irin wannan shigan takeyi, amma fa ko wani shiga da kalarsa domin sai afl watanni bata maimaita wani shigan da tayi ba, ko wace rigan daban. Bayan sun gama d’aukarta photo, nan suka had’u suka yita selfee, suma su Meena sunyi kyau ba laifi, shigan dogayen riguna sukayi tare da barin sumarsu ya zuba a bayan su, kansu ba d’ankwali, dogayen cover shoe suka sanya sunyi kyau sosai amma fa basu kai Basma ba. Fita sukayi suka shiga mota dukansu a seat d’in baya suka zauna suka sanya Basma a tsakiya, driver yajasu, tare da bodyguard suna gaba, da kuma masu rufa musu baya sai club. 
Aryan ya dawo daga sallan Isha’i, ya samu su Umma a tsakar gida kan tabarma suna cin abinci, shima zama yayi a shinfid’ar da yake mai girma ne, Khadija ta mik’e ta isa kitchen ta kawo masa abincinsa, bud’ewa yayi tare da cewa “nagode Dija”, sun kammla cin abinci dukansu sai Aryan ya kai dubansa inda Dija ta zauna yace”Khadija meyasa in kika fita tallan kwai bakya dawowa gida da wuri” marai raicewa tayi tace 
“Yaya Aryan wallahi ba kasuwa ne shiyasa nace bari na k’ara lokaci ko zan saida duka, ka gafa tun shekaran jiya Umma ta dafa min amma har yau bai k’are ba” shuru yayi na ‘yan dak’ik’a kana yace 
“ai Dija mutum baya wuce rabonsa, ni dai dan Allah ki rik’a dawowa da wuri kuma duk inda kike ki tuna matsayinki da rik’e mutuncinki” 
“tom Yaya Aryan insha Allah zan kiyaye” Umma na jinsu tace “Aryan gwara ka rik’a mata fad’a, d’azu ma sai bayan magriba ta dawo” yace 
“ai Umma wallahi ni da ina da hali da Dija ta daina tallan nan sam bana sonta” Umma tace “to Aryan ya zamuyi, haka Allah ya rubuta mana, ya zancen rumfanka an gyara kuwa?” gyara zama yayi yace 
“Umma ba kud’in gyara shiyasa na koma gefe ina aikina inna samun kud’in zan gyara, gashi yanzu cinikin sai Addu’a tunda Lawal ya dawo kusa dani ya kwashemin customers d’ina” Umma tace 
“karka damu insha Allah in kud’in kwai ya taru zan baka ka gyara runfar, batun kuma Lawal ka rabu dashi kowa rabonsa zai ci, muyi ta Addu’a Allah ya kawo mana karshen wannan 
hali da muke ciki”. Duk suka amsa da Ameen kana suka cigaba da hiran duniya. 
Hmm

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE