YAR SHUGABA CHAPTER 12
YAR SHUGABA
CHAPTER 12
‘Da Dare’
Bayan sallan Isha’i, Yaya Ahmad ya nufi d’akin Momy ya tambaya k0 su Basma sun dawo, Momy ta shaida masa basu dawo ba, da mamakin hakan yabar part d’in Momy, ya kira Yaya Naufal a waya yace masa ya fito ya raka shi wani guri, cikin sauri ya fito suka kama hanya.
Ta b’angaren Basma kuwa sun gama shiri tsaf sunyi hotunan da suka saba, sai suka fito haraban gidan suka shiga mota, mai gadi ya bud’e musu gate, d’aya bayan d’aya suka fice, wanda yayi dai-dai da shigowan Yaya Ahmad layin, ganin motocin su ne, sai Yaya Naufal yace “to ai gasu nan sun fito ina ga gida zasu” Yaya Ahmad yace
“ai kuwa, amma bari mubi bayansu mu tabbatar da gidan zasu” da sauri ya juya akalan motansa yabi bayansu, tafiya suke da gudu kamar zasu bar gari, sunzo dai-dai kan kwanar da zai sadasu da gida, sai Yaya Ahmad yaga sun mik’e, da mamaki yajuya ya kalli Naufal yace
“ka gani ko, ba gida zasu ba, duk yanda akayi akwai inda suke zuwa yaran nan, Amma dai bari muje” sun cigaba da bin bayansu har su Meena suka isa hotel d’in.
Sun shiga ciki sunyi parking motocin, Yaya Ahmad yayi parking motonshi a waje, da sauri ya fito Naufal na biye dashi a baya, da shigansu sai suka hango su Basma cikin wani shegen shiga tamkar zasu gasar kyawawa, tafiya suke tamkar ba zasu taka ba, har suka shiga cikin club d’in, mamaki da tsoro ne ya lullub’e su Yaya Ahmad, binsu su kai a baya, escot na ganin su Naufal duk suka fara b’arin jiki, d’aya daga ciki bakinsa ya d’auki rawa yace,
“sir sannu da zuwa” Yaya Ahmad ya masa wani mugun kallo ya wuce su, har cikin hall d’in suka bi su Basma, suna hangen inda suka zauna, Yaya Ahmad yace
“Naufal ga key je gida da sauri ka d’auko Momy da Ammi, kace kawai suzo, dan bai kamata ace mu kad’ai muka gansu ba” cikin sauri Yaya Naufal ya amsa ya wuce, Yaya Ahmad ya samu wani kujera ya zauna daga baya duk yana hango su, bayan kamar minti ashirin saiga Jalal yazo ya kama hannun Leema suka bi ta wata k’araman k’ofa ta gefe suka fita, da sauri Yaya Ahmad ya bi bayansu, a hankali yake binsu tambayar b’arawo, har suka isa d’akin hotel d’in da Jalal ya kama, suna shiga ya dawo, jikinsa ne ya d’auki rawa saboda tsabar b’acin rai, yana dawowa hall d’in ya hangi Meena cikin wani group maza da mata suna d’aga kwalaben syrup, bai tsinke da lamarin ba saida ya hango Basma kan step tana kwasan rawa iya k’arfinta, da karairaya jiki, ai tuni wasu zafafan hawaye suka cika masa ido bai taba tsammanin haka ba, lamarin ya girgiza shi, wayansa ne ya soma ringing da sauri ya fita hall d’in, ya duba ashe Yaya Naufal ne sai ya d’aga, ya sanar masa sunzo, da sauri ya isa wurin motocin harda escot d‘in su Momy, Ahmad ya kasa magana hannun Momy ya kama suka wuce cikin hotel d’in, haka su Ammi suketa binshi har suka isa d’akin da Leema ke ciki, kwankwa k’ofan yayi, daga ciki Jalal ya bud’e daga shi sai best da gajeran wando, Yaya Ahmad ya runtse ido ya bud’e, Jalal yana musu kallon mamaki yace “lafiya wa kuke nima?” daga ciki ne Leema ke cewa cikin d’aga murya “baby waye ne? kazo mana wlh ina cike da buk’atarka fa” ai da k’arfi Yaya Ahmad ya bangaje Jalal ya kusa kai ciki, su Ammi ma suka rufa masa baya, a razane Leema ta mik’e tana ja da baya harta kai jikin bango, Allah yasa bata cire kayan jikinta ba, idonta ne kamar zasu yo waje saboda tsananin furgici, su Momy da Ammi sai suka hau salati, abin ya girgiza
su, Yaya Naufal saboda fushi baisan sanda ya zaro bel d’insa ba ya shiga jibgar Leema, ai Jalal na ganin haka ya fice a sittin, Leema ta kasa ihu domin tashin hankalin da take ciki ya wuce na jin azabar dukan da Yaya Naufal ke mata, da kyar Ammi ta kwaceta tace su fita, haka suka fIto cikin tashin hankali. Momy tace
“ina su Basma suke” Yaya Ahmad yace
“muje in kaiku” ya musu jagora har cikin hall d’in, saboda dan dazon mumne da kyar suka samu hanyar shiga, Yaya Ahmad ne yace “Momy ga Basma can” yayi mata nuni da inda take kwasan rawa, Ammi ne tace “innalillahi wa inna ilai hir rajiun, mun shiga uku ni Faitima” idon Momy ne ya kawo kwalla, sai tayi saurin shanyewa tace
“ita kuma Meena tana ina?” cikin mutane Yaya Ahmad ya kusa dasu, ya kaisu hargun da take, suka tsaya ta bayanta, Momy ta dafata, Meena tajuya da niyyar kwararo ashar domin ta riga tayi tatil, ganin Momy a bayanta ne yasa ta mik’e zunbur tace cikin maye
“Ke ya kike min kama da Momy ce” wani wawan mari Yaya Naufal ya sakar mata saida taga taurari, a gigice ta kalle shi, ai tuni hanjin cikinta suka hautsine sai taji cikin ta ya murda, nan da nan jikinta ya d’auki b’ari, ta kasa magana sai rufe baki tayi, idonta tamkar zasu fad’o k’asa saboda tsoro, Momy ce ta kama hannunta suka fita waje, a cikin mota suka
sanya ta kusa da Leema, sannan suka k’ara komawa cikin hakl d’in. ‘
Yaya Ahmad yabi ta baya ya hau kan step d‘in, ya kutsa cikin masu rawan yaje ta bayan Basma ya yajawota ta baya, ya rad’a mata magana a kunne “In kin gama rawan ga su Ammi can sunajiranki” sai yayi mata nuni da in da suka tsaya” ai a razane Basma ta juyo, ganin Yaya Ahmad ne yasa tayi luuu zata fad’i k’asa, da sauri ya tallabota ya kamo hannunta suka sauka akan step d’in, mutane suna ta ihu yau Basma ta kula Namiji, a tunaninsu saurayi ne ta samu, suna sauka suka Fita a hall d’in, su Momy suka rufa musu baya, ba wanda yayi magana duk suka shiga mota suka wuce gida. Suna isa gida suka wuce part d’in su Yaya Ahmad, d’aki ya bud’e musu suka shiga, Yaya Naufal ya shiga dukansu saida ya musu lis sannan ya fito ya sanya key ya rufe su, Momy suka wuce part d’in president. Sun zauna dukansu a falon, sai gashi ya sauko ya zauna, Yaya Ahmad suka gaishe shi, sannan suka d’aura da bayanin abinda ya faru, mamaki ne ya ziyarci Abba mik’ewa yayi ya shiga safa da marwa a falon, sunan Basma yaketa ammabato yana girgiza kai, komawa yayi ya zauna, ya d’auki wayarsa ya kira number gomna Ibrahim mahaifin Meena, suka gaisa kana ya sanar masa da
“gobe in Allah ya kai mu suzo akwai family meeting na gaggawa” cikin ladabi ya amsa masa da “to suna nan zuwa” sai suka yi sallama ya kashe wayar, gomna Ibrahim ya kalli mahaiflyar su Meena ya labarta mata abinda president yace masa, duk suka cika da mamaki suna Allah Allah gari ya waye su wuce Abuja d’anjin ko lafiya.
Haka Abba ya kira sarkin kano yayi masa umarnin da suzo suma domin family meeting, cikin kulawa ya amsa da alkawarin suna tafe. Abba ya kalli su Ammi yace “kuna gidan nan ace yaran nan suke fita suna wannan iskancin” cikin damuwa Momy tace “yallabai kayi hak’uri, amma iyaka kulawa munayi, kuskuren da akayi shine yanda aka basu daman flta ko ina da mota ba mai kwab’a musu, an basu escot duk da haka ya zama aikin banza, Allah ya shirya mana su” duk suka amsa da “Ameen” Abba yace “Lallai laifi nane dana nuna musu gata, kanma ace Basma na sakar mata komai, a gani na Yarinya ce mai hankali kuma mun bata tarbiyya ga kuma ilimi na addini, ashe shirme mukayi, amma insha Allah daga yau zan d’auki tsastsauran mataki” yana gama fad’an haka ya haye sama cike da b’acin rai, su Momy suka bishi da kallo yau ran maza ya b’aci, haka suka watse a falon cike da damuwa. Bangaren Yaya Aryan yanata kiran wayan Basma, gata a kunne amma anki d’auka, ya kira ya kai sau ashirin amma ba a d’auka ba, hankalinsa yayi matuk’ar tashi, yanaji ajikinsa akwai abinda ya sameta, dak’ar barci ya d’aukeshi tare da yin mafarkai barkatai marasa tushe. Su Basma kuka suke ba k’auk’autawa, kanma ace maka Meena da Leema tamkar zasu had’iye ransu, yau dai dubunsu ya cika, suna tsoron gamuwansu da iyayensu. ‘ ‘Washe gari‘ Da misalin k’arfe goma na safe, gida ya cika da dangi, an cika babban falon bak’i, abinci kala-kala aka jera, duk suna zazzaune, mai martaba da iyalensa Hajiya Sa’a da Hajiya Murja, sai gomna Ibrahim shima da matarsa Hajiya Sadiya, sai kakansu Ahmad Kaka Ma’u, sai su Momy da Ammi, President yana gefe shima, nan suka bud’e taro da addua, president ya soma bayani akan had’uwansu yace “Mun had’u anan ne domin in sanar maku da cewa, na sanya aurensu Basma nan da wata d’aya, Basma da Shureym, Meena da Naufal, Leema da Jamal, bisa sadaki dubu D’ari, ina so duk sai ku fara shiri daga yau” Cike da mamaki iyayen suke kallon juna, gomna Ibrahim ne yace “Yallabai yaushe muka yi magana da kai akan batun aurensu, kace sai nan da shekara d’aya, amma me ya kawo sauyawan wannan lamarin” cike da fad’a Ammi tace “wannan hukunci shine dai-dai, domin yaranmu suna gab da lalacewa k0 ince summa lalace” falon ne ya hautsine da magana ko wanne yana tambayan meya faru, nan Ammi ta kira Yaya Ahmad yazo ya labarta musu komai, ai mai Martaba yafi kowa shiga tashin hankali, cike da b’acin rai yace “a kira yaran dukansu” cikin k’ank’anin lokaci suka shigo sanye da kayan da suka fltajiya, salati iyayen nasu suka saki kowanne mamaki ya gama cika su, sai suka zauna, nan mai
Martaba ya soma musu fad’a daga k’arshe ya shiga nasihi, ya kuma kafa musu doka.
Daga yau na yanke fitanku waje” ya kai dubanshi ga Momy yace “ke Maryam ina son yaran nan su zauna a part d’inki” ya cigaba da cewa “sannan kuma na haramta muku amfani da waya, kuma koda lanbun gidan nan na hana kuje gun, daga part d’in Mominku sai part d‘in Ammi da president, Ku tashi Ku bani guri mutanen kawai”
President ne ya dakatar dasu, suka koma suka zauna, yace ma Yaya Ahmad daya kira su Yaya Naufal, yaje ya kirasu.
Nan duk su ka shigo da yake duk sun zo da iyayensu, Anty Husnah Autan Ammi wacce take aure d’an senator, Yaya Naufal, Yaya Ahmad, Yaya Jamal. Yaya shureym, Yaya Adam duk suka samu guri suka zauna, Gomna Ibrahim shine ya fara magana yace “Ku yaranmu ne, kuma ba zamu yanke muku hukuncin da zaisa muku damuwa ba, duk yanda kuka kai ga lalacewa baza mu k’iku ba, dan haka mun yanke aurenku nan da wata d’aya mai zuwa za ayi insha Allah, kai Shureym an bada sadakin Basma, kai Jamal kai da Haleema, kai kuma Naufal kai da Ameena, dama tuntuni mun yanke haka domin mun fahimci kuna son junanku, sai dai yanzu saboda wasu dalilai mun dawo da zancen baya, za’a d’aura muku aure nan da wata d’aya mai zuwa, kai Ahmad da Adam kuyi k’ok’arin gabatar mana da wanda kuke so domin a had’a bikin gaba d’aya”.
Yaya Naufal a ransa sam baiji dad’i ba saboda Meena ta gama flta a ransa, Yaya Jamal ma ransa ne ya b’aci dan Gaskiya baya son Leema ya tsani halinta, biyayya kawai zaiwa iyayensa. Basma ita kuma kuka ta fashe dashi tace “Wallahi Abba bana son Yaya Shureym, karku had’a auren nan” wani mari Yaya Naufal ya sakar mata wanda ya k’ara gigitata, kuka ta shiga yi sosai tace “wlh zan mutu bana sonsa, dan Allah karku min haka, na tuba bazan sake ba” Lamarin ba k’aramin mamaki ya bama iyayen nasu ba, domin sun san Basma soyayya suke yi da Shureym, ta b’angaren Shureym baiyi mamaki ba, domin k’ila tana k’inshi ne saboda abinda yake ce mata, tsoronsa karta tona masa asiri. Momy ce ta dakawa Basma tsawa, sai ta shiga natsuwanta, duk suka flto suka bar iyayen nasu, Basma tana flta tayi hanyar waje da gudu, aida gudu su Naufal suka bita suna gargad’in masu gadi karku barta ta fita”.
Kamata sukayi suka kaita d’akin Momy suka rufe, ihu take tana buga k’ofa
“kun daina sona kuna so na mutu, Yaya Aryan kazo ka ceceni zasu rabamu wayyo na shiga uku, wai ba mai Sona ne a gidan nan” surutai take ta yi kamar mahaukaciya, Ammi ce ta shigo falon zata bud’e k’ofar, president na shigowa yace “karki kuskura ki bud’e ta, yau ina so ta nuna mana karshen hauka, kuma wlh na rantse aure tsakaninta da Shureym ba fashi” yana gama fadin haka ya fice. Kaka Ma’u ce ta sanya aka bud’e d’akin ta shiga, Basma ta rungumeta tanata sambatu, Addu’a taketa tofa mata, a tunaninta ko akwai jinnu a lamarin, lallashinta ta shiga yi har ta
samu tayi shuru, tana ajiyan zuciya, da haka barci mai nauyi ya d’auketa. Bayan komai ya lafa, su Meena da Leema an natsu, sun zama kamar kurame, farin cikin su ma za’a aura musu abinda suke so, sai dai zuciyansu na cike da damuwan waye Basma take so haka? sun tausaya mata sosai. Yaya Ahmad ya wuce d’akinsa, damuwa ne ya shigeshi, yasan dole dama za’ayi haka, kira a wayan Basma ne ya shigo, yana dubawa yaga an rubuta my love Aryan, kamar bazai d’aga ba saiya d’auka, Yaya Aryan ya fara magana
“Basma, Basma me ya sameki dan Allah kimin magana, ina cikin damuwa” hawaye ne ya kawo ma Yaya Ahmad na tausayinsu yace ba Basma bace Ahmad ne” cikin sauri ya tari numfashinsa “me ya samu Basma dan Allah karka b’oye min” Yaya Ahmad yace “ka kwantar da hankalinka Basma tana lafiya barci take yi” cikin damuwa yace “Basma batada lafiya, karka b’oyemin akwai abinda ke damunta” kawai saiya fashe masa da kuka….
Hmm ikon Allah wannan soyayyah haka