YAR SHUGABA CHAPTER 15

YAR SHUGABA 
CHAPTER 15
‘Da dare’ 
An shirya kayataccen Dinner a katon hall mai d’aukan mutane dubu, manyan mutane sun halarci wannan Dinner, harda wasu yan k’asashen waje sun halarta,Amare da Angwaye sunsha kyau, ko wanne zaune yake da Amaryansa, Safeena na zaune cikin mutane ranta ya gama b’aci, zuciyarta yana mata zafl dan tsananin kishi, tunani ta shiga yi, ita fa Auren sirri aka mata sam ba’ayi irin wannan shagalin ba, haushi ya k’ara cikata, amma tasan matakin da zata d’auka akan Shureym, dan taga yana ta rawan jiki akan Basma. Kowa ka ganshi a wannan lokacin yana cikin farin ciki, amma banda Basma da take cikin damuwa na rashin ganin Aryan agun, dan batasan yayi taflya ba, sai kuma Safeena da take jin haushi akan mijinta. Anyi taro lafiya an watse lafiya, cikin farin ciki da kwanciyar hankali. ‘Washe gari’ 
An kai ko wace Amarya gidan Mijinta da misalin karfe hud’u na yamma, Deeja an kawota gidan president a side d’in mijinta, haka Meena ma an ajeta acikin gidan president, part d’insu na gefen nasu Yaya Ahmad, Leema kuma an wuce da ita Kaduna zuwa gidan Jamal da Dady ya siya masa, sai Yaya Adam an wuce da matarsa Munayah, an kaita part d’inta dake cikin gidan Sarki, Basma ita ce tayi saura a gida, itama part d’inta yana gidan Sarki kusa dana Yaya Adam, kasantuwar Yaya Shureym bai gama aikin da suka d’aukeshi ba na shekara biyu, yasa zasu wuce America, su cikasa sauran shekara d’ayan daya rage. Sauran baki kuma suna nan basu soma tafiya ba. Sai Washe gari ko wani Ango ya shiga d’akin matansa, suka bud’e faifan sabon rayuwa cike da So da K’auna. Da safe su Basma suka wuce airport, da kyar aka raba Basma da jikin Ammi, tasha kuka kaman ranta zai fita, Shureym kuwa sai wani kamata yake yana lallashi, sun shiga jirgi Basma na d’agawa iyayenta hannu,ji take kamar in ta tafi bazata dawo ba, haka suka zauna wuri guda, sannan aka rufe k’ofar jirgi, ana rufewa Shureym ya tashi kusa da ita ya kona gefen hagunsa, kusa da Safeena ya zauna, ta cika ta batse dan haushi, Basma ta bishi da kallo ganin ya zauna kusa da wata mace cike da mamaki, bata iya cewa komai ba, Safeena ce da taga Basma na kallonsu, sai tayi saurin sakin fushin tajuyo fuskanta tana kallon Shureym, sai ta had’a bakinsu guri guda, ai da sauri Basma ta kauda kai, zuciyarta na dukan uku~uku, bakinta na fad’an “lnalillahi wa inna ilaihir raji’un” kwantar da bayanta tayi jikin kujera, ta runtse ido, tsananin radad‘i zuciyarta yake mata, bawai kishin Yaya Shureym taji ba, tsabar bak’in ciki da irin tsanar hayayyansa take, a tunaninta k’aruwansa ce, Safeena tana ganin Basma ta kauda kai, sai ta janyejikinta ta fara magana k’asa~k’asa tace “Baby wlh ka b’ata min rai cikin kwanakin nan, naga sai wani rawarjiki kake akan wancen yar iskan Yarinya, to wlh ka sani bazan tab’a raba kwana da ita ba, alkwari ka d‘aukan min cewa kai mijin mace d’aya ce, dan haka kai nawa ne ni kad’ai, tunda kace had‘in zumunci ne shiyasa na yarda da auren, dan haka da kanta zata gaji da zaman gidanka, harta nima saki tayi gaba” Gaban Shureym ne ya fad’i, hankalinsa ya tashi, amma sai ya dake ya wayince yace”Love ke kad’ai ce a guna, me zanyi da Basma, had’in zumunci akai mana dan bana sonta” Cike da murmushi tace “yauwa Babyna, kamin alkwara ba raba kwana da ita” murmushi yayi wanda yafl kuka ciwo yace 
“na miki alkawari, ai bana son b’acin ran ki, ko me kike so zan miki domin in saki farin ciki” Safeena farin ciki ya rufeta, take nan ta manta da b’acin rai data shiga. Basma kuwa kuka ta shiga yi mara sauti, a haka har barci ya kwasheta. ‘America” 
Bayan sun kai, mota biyu kejiransu, d’aya wanda zai d’auki kayan su, d’aya kuma wanda zasu shiga, Basma jikinta a mace ta bud’e k’ofan bayan mota zata shiga, sai Yaya Shureym ya daka mata tsawa yace 
“Karki kuskura ki shiga nan, ki shiga gaba ki zauna da driver, k0 baki ga ina tare da matata bace?” cikin tsoro Basma ta barjikin motar cike da tsiwa tace 
“Matarka k0 Karuwa?” Ai bata rufe baki ba ya tawo da sauri ya wanketa da mari, a razane ta dafe kuncinta tace “Ni ka mara akan wannan yar iskan, to Allah ya isa mugu fasik’i kawai” tana gama fad’an haka tabar wurin da gudu, ta shige gaban motan daya d’auki kayansu ta zauna, driver ya tukasu suka wuce. Cike da k’unar rai Yaya Shureym ya girgiza kai yayi kwafa, iya ka k’uluwa Safeena tayi, amma ta share suka shiga mota tana sake-saken irin matakin da zata d’auka akan Basma, Lallai dole saita fahimtar da ita cewa ita matar Shureym ce. Suna isa gidan, ta shiga babban falon gidan Driver ya shigo musu da kayansu, d’akuna uku ne a cikin falon, k0 wanne da kaya aciki wanda President yasa aka sanya musu komai na buk’ata aciki, Basma ta zauna akan kushim tana jiran su Shureym su shigo, koda suka shigo sai suka zauna suma, Yaya Shureym ya kira wani kuku, sai gashi da gudu yazo, da yake gidan ai’nahi anan Shureym yake zama, ya Umarcesa daya kawo musu ruwa, da sauri yaje ya kawo musu ya dire musu goran ruwa biyu da cup, yaje zai aje goran ruwa a gaban Basma, sai Safeena ta dakatar dashi cikin turanci tace “kai zonan” jikinsa na b’ari ya isa gurin ya risina, tace 
“daga yau Ni zaka rik’awa aiki amma banda wacen ‘yar iskan, domin Mijina ni kad’ai yake aure” tana kaiwa nan tayi shuru,jiki na rawa Kuku ya amsa mata yabar gurin. Cikin ko in kula Basma ta mik’e tace “Yaya Shureym Ina ne d’aki na?” Hararanta yayi yace “ban sani ba mara kunyar banza, wlh nan ba Nigeria bane da zaki min iskanci na d’auka, koda kika ga ina lallab’a ki, dama ina yi ne dan ayi auren, saboda kar in b’atawa Iyayena rai, kuma ki sani bana son ki, biyayya ga Iyayena yasa na aureki” Gaban Basma ne ya shiga bugawa da sauri, saboda tashin hankali, ya cigaba da cewa “kinga wannan sunanta Safeena, itace zab’ina, kuma munyi aure da ita wata guda daya wuce cikin sirri, ba tare da kowa ya sani ba, daga ni sai Mami na data goya min baya, dan haka in kina son zaman lafiya a gidan nan, to dole sai kin bita sauda k’afa, inba haka ba wlh na lahira saiya fiki jin dad’i” Basma durkushewa tayi a gurin, saboda k’afafunta bazai iya d‘aukanta ba, ta shiga rera kuka wiwi, sai ya kwashe da dariya yace wawuya nasan kin d’auka son ki nake ko, tashi dalla ki bani wuri, ki wuce d’akinki shine na gefen hagu, na tsakiya kuma nawa ne, na gefen dama na Safeena ce, kuma na haramta 
miki shiga d‘akina” yana kaiwa nan ya mik’e ya kama hannun Safeena suka wuce d’aki. Basma cikin tashin hankali taja trolley kayanta, ta shiga d’akin daya gaya mata, katon d’akine mai d’auke da katon gado, sai daga gefe an jera kujeru set, sai bayi da kicin a ciki, kalan d’akin da kayan ciki purple da ash color ne, rufe d’akin tayi da key, ta shiga wanka, kanta ta sanyawa ruwa sosai, saboda zafln da yake mata, tayi kuka kamar zata shid’e, daga bisani tayi wanka ta d’auro alwala ta fito, kaya ta sanya mara nauyi, ta sanya hijab ta tada sallah, sai da ta rama duk Sallolin da ake binta kana tayi Addu’a, ta mik’e ta shiga cikin d’in d’akinta, komai data ke buk’ata akwai aciki, dan akwai k’aramin store a ciki, ruwan tea ta dafa, ta zo ta diba cin-cin d’in data tawo dashi a plet, ta zauna taci kana ta d’aura da danbun Namam kaza, bayan ta gama sai ta kwanta akan doguwar kujera, ta runtsa idonta ta shiga tunanin wani irin rayuwa zatayi yanzu, kuma wani mataki zata d’auka akan Yaya Shureym da Safeena wacce yake ik’ira rin matarsa ce, hawaye ne ya sauka a kuncinta, a flli tace cikin kuka “babu wanda ya jamin wannan rayuwa sai ku Abbana, dan haka ba wani matakin da zan d’auka ma, domin ko me ya sameni kune sila” 
Ta goge hawayenta, ta d’auko wayanta ta shiga kiran Momy, ta sanar da ita sun sauka lafiya, nan sukayi sallama, ta kira President ta sanar masa da sun sauka lafiya shima, haka kuma ta kiranl Ammi ta sanar mata da sun sauka lafiya itama, bayan ta gama wayan, sai ta tuna da Umma, sai tayi murmushi, itama ta kira ta suka gaisa, Umma tayi mata nasiha sosai akan biyayyan aure, kana suka yi sallama, saita kashe wayen gaba d’aya ta gyara kwanciya, bata dad’e ba barci ya d’auketa. 
A Nigeria‘ 
Mutanan Biki duk sun watse sai dai-dai da suka rage, ta b’angaren Amare kuwa sunata cin Amarci hankalin su kwance, kowa yana cikin farin ciki. Ta b’angaren Yaya Jalal ya samu Leema ta yanda bai yi tsammani ba, domin gaskiya tasha gyara wajensu Momy, duk da dai bata isa ta maida mudurcinta ba, amma dai ya gamsu sosai da ita, Leema ‘ta kasance cikin 
murna da yanda Jalal ya saki jiki da ita, tamkar babu wani abin da ya faru a baya. 
A K’asar Monaco“ 
Yaya Aryan ya cigaba da rayuwa shi kad’ai, da Umma kawai yake waya su gaisa, da sun gama saiya kashe wayan. Kullun soyayyan Basma k‘aruwa yake a zuciyansa,yanzu da baya ganinta yaf’l shiga tashin hankali da damuwa, ya k’ara ramewa sosai, burinsa yanzu bai wuce Basma ta kwantar da hankalinta ba, tayi rayuwan Aure cikin farin ciki da annatsuwa. Ya duk’ufa sosai wajen karatunsa, yana k’ok’arin kafa sabonr ayuwa. 
‘Bayan mako guda‘ 
A America’ Basma tunda ta kulle kanta a d’aki, bata kuma bud’ewa ba hartsawon mako guda, komai a cikin d’akinta take yi, hatta girki da kanta take yi, taci ta wanke kayan data b’ata, tun yin aikin na bata wuya kasantuwar bata saba yi ba, har ta fara sabawa, Allah yasa ta iya girki, domin Momy ta koyawa Basma girki dan gaba zai mata amfani, kamar yanda yanzu ya soma mata amfani. Yaya Shureym suna falo suna hira, Safeena tayi pillow da cinyansa, hankalinsa na kan k’ofar d’akin Basma, hira take mishi amma sam baya tare da ita, sha’awan Basma na d’awainiya dashi, sannan ya fara damuwa da rashin ganinta da baiyi ba, tun ran da suka zo, bai sake tozali da ita ba, Safeena ganin baya tare da ita ya barta tana ta surutu, sai ta d’ago kai tana kallon direction d’in da yake kallo, gabanta ne ya fad’i cikin jin haushi tace 
“Baby tunanin me kake yi haka? Ko ka fara sonta ne?” Firgigit ya farka, cikin inda-inda yace “ba komai, me zanyi da Basma, Allah ya kyauta” cikin fushi tace “k’arya kake yi, d’akinta fa kake kallo, kana ce min ba komai” murmushin takaici yayi domin ya soma gajiya da yawan k’orafinta, kawai ba yanda zaiyi da ita saboda yana sonta, kuma baya son b’acin ranta yace “kedai kin cika kishi, kawai ina tunanin yarinyar nan ne, akan tunda muka zo ban ganta ba, ina tsoron kar wani abu ya sameta, domin in wani abu ya sameta wlh zamu shiga cikin matsala, kinsan ‘YAR SHUGABA‘ ce, gwara na rika duba lafiyan ta domin president ya bani amanarta, ko ba komai kuma ‘Yar Uwata ce” Safeena cikin nuna ko in kula tace “wannan kaita shafa” tana gama fad’an haka ta mik’e ta shiga d’aki tanajan tsaki, binta yayi da kallo yace a fili”Safeena sarkin kishi” sai ya mik’e ya nufa d’akin Basma… 
Hmm

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE