YAR SHUGABA CHAPTER 17

YAR SHUGABA 
CHAPTER 17
K’aran bugun k’ofar shine yayi dai-dai da Shureym ya dawo hayyacinsa, da sauri ya sauka akan gadon, cikinjin haushi da borin kunya ya kwaSHi kayanshi a hannu ya fita a d’akin, da gudu-dugu ya fad’a d’akinsa tare da sanya key. Basma kuka take tana cewa “Allah ya isa bazan yafe maka ba, mugu azzazulumi insha Allah harka mutu baza ka cimma burinka a kaina ba” furucin Basma na k’arshe shine ya sanya Safeena ajiyan zuciya, dama fargabanta shine ace ya samu Basma, tasan lallai kashinta ya bushe, gashi Basma ta fita komai na kyawun sura, sannan ta tabbatar Basma bata bin maza lallai zai sameta a budurwa, kallon Basma tayi cikin tausayawa, da sanyin murya tace cikin tsawatarwa 
“Kad’an kika gani in dai Shureym ne, mugune shi sosai haka yakemin nima, karki k‘ara yanda haka ta faru in ba haka ba wataran zai kashe ki, maza tashi ki gasa jiki a toilet, kuma karki sake barin k’ofarki a bud’e, dan Shureym ya wuce yanda kike tunani” tana gama fad’an haka ta fice a d’akin. Basma wani sabon kuka ta saki, da kyar ta iya sakkowa daga gadon, tana bin bango harta shiga bayi, ruwa ta had’a mai zafi ta shiga ciki, ta kai kusan rabin awa tana ciki, kana tayi wanka ta fito, mirror taje ta tsaya tana kallon yanda fuskanta ya kummbura, hawaye ne ya sauka a kuncinta mai zafi, fuskan ta tayi ja sosai, gashi kumatunta ya kunbura da lebenta, idonta yayi k’anana gaba d’aya ya sauya mata kamanni, hawaye ta share tace a fili “Abba Ku kuka jamin” kaya ta sanya marasa nauyi ta cire zanin gadon ta ta sanya wani, taje ta kulle d’akinta ta koma gadon ta kwanta cikin k‘ankanin lokaci barcin wahala ya d’auketa. 
Shureym saida ya samu yayi wanka kafin ya samu nutsuwa, nadama ne ya lullub‘eshi akan abinda yayi wa Basma, ga kuma kunyar Safeena da yakeji, wannan dalilin ne ya hanashi fitowa sai kawai ya kwanta har barci ya d’aukeshi. Safeena kuwa ta kasa ta tsare a falo tana jiran fitowan Shureym, jin yayi shuru bai fito ba saita gyara zama ta kunna tv tana kallo, sai bayan k’arfe biyu Shureym ya fito daga d’akinsa, ya had’e giran sama dana k’asa yana hura hanci duk na borin kunya, Safeena tana ganin shi sai ta kwashe da dariya, dan gaba d’aya ya bata dariya sai wani basarwa yake yi, zama yayi gefenta yace cikin fushi “meye kika gani na dariya a jikina?” ya mutse fuska tayi tace cikin tsiwa “wlh Shureym kaji kunya, banda Allah yasa nazo na ritsaka, da ka kashe musu Yarinya, kanata cika min baki akanta, ashe duk burga ce irin nad’a Namiji, Allah ya kyauta maka, kuma ka sani Basma Yarinya ce imma zaka amshi hakk’inka, to ba da k’arfi zaka amsa ba saika bita a hankali” Tana gama fad‘a ta mik’e ta shige kicin, abinci ta zubo masa ta mik’a masa, murmushi yayi ya amsa tare da cewa “Tnx my Baby, banyi tunanin zakiyi saurin saukowa haka ba” hararenshi tayi ta koma ta zauna tare da d’aura k’afa d’aya kan d’aya, ya soma cin abincin tace
“Shureym ina Sonka sosai, bazan iyi dogon fishi da kai ba, da ace d’azun baka rufe d’akinka ba, har na sameka a ciki, da saina sauke maka kwandon rashin mutunci, amma na sauko, sai dai yanzu na daina yarda da alk’awarinka domin nasan watara saika karya shi” zai yi magana ta d’aga masa hannu tace “kai dai ci abinci kawai”. 
Bayan la’asar Basma tayi shigar doguwar riga abaya brown, tayi rolin da gyalen,jaka ta d’auka bak’i ta sanya takalmi bak’i, ta same su a falo bata kalli inda suke ba tayi hanyar fita, da sauri cikin tsawa Shureym yace “ke ina zaki?” tsayawa tayi cak bata juyo ba kuma bata ba shi amsa ba, saida ya kuma maimaita tambayan, amma shuru bata masa ba, k’arshema tasa kai ta fice, a zuciye ya mik’e zaibi bayanta, Safeena na rik’e hannunsa tace “haba Shureym wani irin abune wannan, ka duketa d’azun ka kumbura mata fuska, ka sani ko asibiti zata je, ka rabu da ita taji da kanta mana” cike da mamaki ya juyo ya kalleta yace “Safeena yaushe kika zama haka? da har zaki tausayawa wannan shaid’aniyar yarinyan’ murmushi tayi tace “Shureym ni mace ce mai rauni, dole ne inyi saurin tausaya mata akan irin lahanin da kaso 
yi mata, tana gama fad’an haka ta d’aure fuska, kana ta wuce d‘aki. 
Basma tana flta ta tari taxi asibiti ta fara zuwa, likita ya dubata ya bata Magani da kuma alluran zazzabin da takeji, daga nan saita wuce wurin wani gidan abinci, zama tayi ta sanya aka kawota drink da snacks, nan taci tana nazarin wani mataki ya kamata da d’auka, a haka ta gama komai saita wuce wani studio na kusa da gidansu, ta shiga ta sanya aka d’auki hoton fuskanta kana aka wanke aka bata ta dawo gida. Bata samu kowa a falon ba saita wuce d’akinta ta bud‘e ta shiga tare da sanya key, wani jaka ta ciro ta bud’e da wani k’aramin key, ta ciro diary d’inta ta shiga rubuta abin da ya faru da ita na wannan ranar, sannan ta maida cikin jakan tare da sanya wannan hoton aciki, sai ta maida ta rufe ta ajeshi cikin wani dirowa, ta dawo kan gado ta zauna tare da rafka tagumi. Wannan diary d‘inta ne tun ranar da suka sauka a k’asar America, ta fara rubuta duk abinda yaya Shureym yake mata na muzgunawa a ciki, dan ya zame mata tarihin da zata rik’a tunawa. 
Wayarta ta ciro a jaka ta kunna, sak’onnin text suka fara shigowa, gaba d’aya text d’in yan uwanta ne, d’aya bayan d’aya ta rik’a karantawa, wani tayi kuka wani tayi dariya, nan take kewar family d’inta ya taso mata, WhatsApp d’inta ta bud’e, sakonni suka fara shigowa, ta mance rabonta da hawa online, group ta shiga na family d’insu, nan fa tayi sallama suka fara amsawa cike da murnan sake ganinta, duk suka gaisa na yaushe gamo, Meena ce tace “ke Besty akwai labari muje group d’inmu” nan suka koma group d’in su mai sunan ‘Manyan Mata, One family“ Leema ma ta shigo can sai ga Deeja ta shigo, yanzu su had’u ne a group d’in, sunata murnan ganin Basma, nan suka shiga hira, Meena tace “kinsan kuwa Leema da Deeja ciki ne dasu” Basma cikin farin ciki tace “Dagaske? kice mun kusa samun yara” “Eh wallahi, two month yanzu” “ikwan Allah, yanzu fa mun kai 3month da aure, lallai abin ba wuya, to Allah ya musu albarka ya rabasu lafiya, to Meena kefa?” Meena tace “Ni nawa lmonth ne yanzu” “lallai kuce kun girma, Allah ya inganta” Deeja tace “waya sani ko kema kina da naki a k’unshe bamu sani ba” dariya tayi sosai tace “wace ni, ai in gaya muku banda komai, ina planning tukunna” Leema tace “Malama ki fad’a mana gaskiya kawai” “Hmmm Allah kuwa gaskiyar kenan” nan dai suka cigaba da hira, sun shafe lokaci sosai suna hira, sallama su kayi saboda dare yayi sosai a Nigeria, su kuma Basma yamma ne a 
nan. Cike da kewar family d’inta ta mik’e ta shiga kicin, abinci ta shiga girkawa. 
‘Bayan Mako biyu’ 
Basma ta shirya da yamma k’arfe hud’u, tayi shigar riga da wando na Pakistan, tayi rolin da gyalen shi,jaka ta d’auka da takalmi ta kawarta, yau tayi sa’a ba kowa a falon, taxi ta tare ta nufi wurin cin abinci, yau drink kawai ta sha, saita Ciro wayarta ta hau online tana chart dasu Meena, wani saurayi ne mai tsayi kyakkyawa, ya tako a hankali harwurin da Basma ta zauna, ya tsaya tare da yi mata sallama, cike da kulawa ta amsa tare da d’ago kanta, cikin harshen labarabci yayi mata magana yace 
“In zauna?” murmushi tayi tace “eh” sai ya zauna ya cigaba da magana “Ni sunana Bilal dan k’asar Sudan, nazo nan karatun masters d’ina ne” murmushi tayi cikin larabcin tace “sunana Basma Bulama ni ‘yar Nigeria ce” cike da mamaki ya kalleta yace “kina nufin ke ‘yar Nigeria ce?” Tace 
“kwarai kuwa” murmushi yayi yace 
nayi miki kallon ke ‘yar k’asar labarawa ce, shiyasa ma nazo nayi miki magana, ashe ‘yan Nigeria sunajin labarci sosai haka” dariya tayi tace “sosai kuwa munaji, domin muna da makarantu acan na larabci” yace
“good, yanzu meya kawo ki America?” murmushi tayi tace “Hutu muka zo tare da family na” yace “masha Allah, in ba damuwa zan iya zama abokinki?” murmushi tayi tare da yin tunani kad‘an tace “eh ba damuwa” nan su kayi exchanging contact d’insu, tare da alkawarin zasu had’u washe gari in Allah ya kaimu, nan ya taka mata ta shiga taxi kana ya wuce shima yana farin cikin had’uwa da Basma, cikin k’ank’aninin lokaci ya kamu da Sonta. Basma irin tsarin matar da yake burin aura ce, dama ashe a Nigeria suna da kyawawan mata haka? 
Tambayan da yayiwa zuciyansa kenan, harya k‘osa dare yayi gari ya waye su k’ara had’uwa. Basma tana isa gida ta same su zaune a falon, kallon arziki bata yi musu ba ta wuce su, Yaya Shureym yace “Basma wai ina kike zuwa ne?” cikin b’acin rai tace 
“inda ka aikeni, kuma ka fita cikin rayuwata in ba haka ba zan maka abinda baka tsammani daga gareni” tana fad’an haka tayi gaba, bud’e murya yayi yace “wlh in kika kaini mak’ura zaki sha wuya, mara kunyar banza” ‘tsaki tayi ta bud’e d‘aki ta 
rufa da k’arfi ya buga gam, kana ta sanya key, tayi wanka tare da d’auro alwalan Magrib. ‘Washe gari’ 
Ya kama week end, yau Shureym yana gida yana hutawa tare da matarshi Safeena, da misalin k’arfe biyun rana Safeena ta fito, tazo d’akin Basma, bugawa tayi amma kusan minti biyu shuru Basma bata bud’e ba, saida ta kuma bugawa tare da bud’e murya tace “Basma ki bud’e Safeena ce” murmushi Basma tayi ta sauko a kan gadon ta bud’e mata, da murmushi a fuskan Safeena tace “Basma dan Allah kin iya wainar fulawa?” Basma tayi murmushi tace “eh na iya” 
“to dan Allah kiyi hak’uri ki d’an yi min mana, saboda Kuku basu iya ba, kuma wlh marmarinsa nake, in kuma ni nayi bazan iya ci ba” murmushi Basma tayi tace a ranta “shegiya yanzu haka ciki ne dake, kuma in dai wainar fulawa ce za kici kuwa” tace a fili OK muje nayi miki” 
“yauwa sis nagode bari najiraki a falo” murmushi kawai Basma tayi bata ce komai ba, tace aranta “wato yau kinzo da fuskan arziki kenan, saboda zaki more ni, dole a fake da cemin sis” kicin ta shiga, cikin minti talatin ta had’a mata wainarfulawa, taji kayan had’i kuwa, saita kawo mata harda ruwan sha, ta aje bisa table na falon, Safeena na gani ta Shiga lashe baki,jiki na b’ari ta jawo table ta shiga cin wainar, ai had’iyan farko ya tsaya mata a wuya, da sauri ta tashi da gudu ta fad’a bayin dake falo, ta shiga kwara amai kamar zata amayar da hanjin cikinta, Basma zama tayi a falon tana zuba dariyan mugunta, Safeena a galabaice ta fito ta zauna tana maida numfashi, Shureym ne ya shigo falon yana fad’in “Safeena Iaflya haryanzu aman bai tsaya ba, ko zamuje asibiti ne?” cikin kasalan murya Safeena ta nuna Basma tace “kaga wacce ta sani amai, nace ta min wainar fulawa saita zabga masa yaji da gishiri loma d’aya nayi na kasa had’iyewa saida na amayar dashi” cikin b’acin rai ya kalli Basma yace “dan Ubanki kashemin mata zakiyi k0, saboda kina bak’in ciki da abinda ke cikinta k0, to wlh maza tashi kije ki dafa mata wani wainar, kuma in kika yi kuskure jikinki zai gaya miki” Jikin Basma a sanyaye ta koma kicin ta kuma b’ata lokaci ta had’o wani wainar ta kawo mata, Safeena ta saki ciki ta soma ci harda lumshe ido dan dad’insa saida ta cinye tas kana ta kora da ruwa. Shureym ya kalli Basma yace D’auko wancen da kika b’ata ki cinye, dan wlh baza kimin asanar abinci ba” cikin k’unk’unai tace “wlh ni na k’oshi” belt d’in wandonsa ya zaro ya rik’e, yaje ya d’auko plet d’in wainar fulawan ya dire a gabanta yace “wlh sai kinci in kuwa baki cinye ba jikinki zai gaya miki” ai da sauri ta sanya hannu ta d’ibo, tana kaiwa bakinta, zafln yaji da gishiri ya d’arsu a kan harshenta, ai da sauri ta furzar tare da goge harshen, Shureym ya zuba mata belt d’in a gadon bayanta, ai saita tsandara ihu ta shiga sosa bayan, bai hanashi sake zabga mata belt d’in a jikinta ba, ya shiga jibgarta tare da cewa saita cinye shi, Safeena dariya ta shiga yi tare da d‘aura k’afa kan table, saida yayi mata lilis kam ya dena dukanta, kuka take tace 
“Allah ya isa Shureym, haka kawai ka maidani baiwarka, wlh sai kayi nadaman abinda ka aikatamin, azzalumi fasiki, maci amana” wani wawan naushi ya kai mata a baki, nan take bakinta ya fashe ya shiga zubda jini, da sauri Basma ta dafe bakinta tana kuka, tashi tayi dakyar ta isa d’akinta… 
Hmm

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE