YAR SHUGABA CHAPTER 18
YAR SHUGABA
CHAPTER 18
Bayi ta shiga ta gasa jikinta da ruwan zafI domin dukjikin yayi mata tsami, bayan ta flto ta samu ta sanya kaya ta fice zuwa studio, photo ta d’auka aka wanke mata, fuskanta ta fito da kyau bakinta a kubbure, ta dawo gida. Rubutawa tayi a diary d’inta kamar yanda ta saba, kana ta koma ta ajiye shi a mazau ninsa, ta had’a tea tasha kana ta d’aura da pain relief tasha, saita bi lafiyan gado.
“Nigeria“ Gudu take tana ihu, Abba kawai take kira tana cewa “wayyo Abba zai kasheni kazo ka taimake Ni, Momy na wai bakwa sona ne kuka bari zai kashe ni” a razane Abba ya farka daga barcin tare dayin Addu’a “‘A’uzu bi kalimatil lahit taammat min sharri ma kalak’a’” gumi ne ke tsatsowa a jikinsa, gaba d’aya hankalinsa ya tashi,jingina yayi jikin gado, Momy ta farka a barci saita ganshi zaune, tashi ta yi ta zauna, cikin muryan barci tace
“yallab’ai lafiya ka zauna cikin wannan Daren?” agogan dake manne a d’akin ta kalla, k’arfe biyu da rabi na dare, sharce zufa yayi ya dafe kansa cikin damuwa yace “Hajiya Maryam wlh mugun mafarki nayi da Basma, hakan ya nuna kamar tana cikin Matsala” Momy ta gyara zamanta tace cikin natsuwa “Abba wannan aikin shaid’an ne kawai, amma Basma bata cikin matsala, saboda munsan wa muka bama ‘yar mu fa, kawai dai kila ka sanya ta a ranka ne saboda rashinta na tsayin lokaci da bata tare damu” ajiyar zuciya yayi yace
“a gaskiya jiki na ya bani Basma tana cikin damuwa, insha Allah gobe in Allah ya kaimu da sassafe zanje America dan ganin lafiyar ta” ajiyar zuciya Momy tayi tace
“Allah ya kaimu goben nima saina maka rakiya” murmushi kawai yayi ya tashi ya shiga bayi, alwala ya d’auro ya shiga jero sallan Nafila, itama Momy bata kwanta ba, tashi tayi itama tayi alwala tare da gabatar da nata Nafilan. ‘Washe gari’
Da misalin k’arfe Bakwai na safe su Abba sun gama shirin tafiya, Abba ya hana Momy taflya yace tayi zamansa ba zai kwana ba shima, Yaya Naufal tare da muk’arrabansa suka wuce airport ba tare da b’ata lokaci ba, dama jirgin President na jiran zuwansu, shiga suka yi suka kama hanya sai America. ‘America’ Basma na kwance a d’aki sai nishi take fitarwa da k’arfi, numfashinta na fita da kyar, ta rufa da bargo amma duk da haka bai hanatajin sanyi ba, sai kerma jikinta yake yi, zufa ne ya lullb’eta hawaye na fita a idonta, a wannan lokacin tana buk‘atar taimako.
President suna isa, aka turo motoci daga gidan shugaban k’asar America ya kwashe su, sun gaisa dashi kana suka ci abincin, shi Abba ya kasa cin komai drink kawai yasha, burinsa bai wuce yaga Basma ba, wayarsa ya ciro ya kira Shureym, bugu biyu ya d’auka cikin ladabi yace
“Abba ina kwana?” Abba ya amsa fuska sake yace “Shureym gani nazo k’asarku, ina gidan shugaban k’asa, kana ina kazo ka kaini gidanka, domin mu gaisa da Basma”
Ai bai k’arasa maganan ba jikinsa ya d’auki rawa, muryansa har tana sirk’ewa dan fargaba yace “Abba naje wurin aiki gani bisa hanya zanzo” “0K saika zo karka b’ata lokaci fa domin yau zan koma”
“to Abba, insha Allah gani bisa hanya”. Sai suka kashe wayar. Ai jikin Shureym na rawa ya tafl gidanshi, ya kira Safeena ya shaida mata zuwan President, itama hankalinta ya tashi, yana isa ya shiga gidan a sukwane, ya samu Safeena a falo tana kai kawo, da sauri ya kama hannunta yace “kije gidan k’awarki, anjima in sun tafi zan kiraki ki dawo” jiki na rawa ta fice a gidan, d’akin Basma ya nufa ya bubbuga k’ofar amma shuru, hankalinsa a tashe yace “Basma dan Allah ki bud’e, Abba ne yazoo zani na d’auko shi, dan Allah ki rufa min asiri zan gyara mistake d’in dana miki pls Basma, bari naje da sauri kinga ma kirana yakeyi” bai jira amsarta ba ya fice da sauri.
Hawaye Basma ta cigaba da fitarwa tace
“Bana son ganin kowa, gwara na mutu ma” tsaki taja ta mik’e da kyar ta shiga bayi wanka tayi ta sanya atamfa, riga da sket, bud’e k’ofard’akin ta tayi, kana ta koma kan gado ta kwanta saboda zazzab‘in bai saketa ba. Sun iso gidan Shureym sai rawan jiki yake yi, yana fargaban Basma karta tona masa asiri, koda suka shiga falon sun zazzaunawa, sai Shureym yace
Abba bari na kirata” murmushi yayi yace
Basma fushi take dani, dan tasan da zuwana, ya kamata ace mun sameta a tsakar gida dan tarbanmu, barni da ita bari naje na lallasheta” Gaban Shureym ne ya buga damm, amma sai yayi na maza yace
“0K Abba ga d’akinta chan” ya nuna masa d’akin da hannunsa, Abba mik’ewa yayi da sassarfa ya wuce d’akin, turawa yayi a hankali tare da sallama, Basma na kwance ta runtsa idonta hawaye me zafi na zarya a idonta, kanta ta sanya cikin bargo ta share hawayenta, ta amsa sallaman a zuciyarta, Abba matsawa yayi gaban gadon cikin lallashi ya fara magana “haba shalelen Abbanta fushi kike dani, kiyi hak’uri kinji Basma na, aiki ne ya hanani zuwa, wannan tafiyan musamman dan ke nayishi”Kukanta ne ya flto fili, da sauri ya yaye bargon, sai yaga tana rawan sanyi, da sauri ya isa gareta ya dagota, jikinta ne yaji yayi zafi kamar wuta, yace
“ya salam Basma bakida lafiya ne?” Langwab’ewa tayi a jikinsa, da sauri Abba ya d’auketa yayi falo da ita, ai Shureym yana ganinsu, gabansa yayi mummunar fad’uwa, rai bace Abba yace “yanzu Shureym har zaka iya tafiya aiki ka barmin Basma kwance batada lafiya?“ cikin in ina yace “em em Abba ayi hak’uri, nima na flta nabarta tana barci, ban zata zazzabi take ba” Abba yayi tsaki yace “shirman banza, Amanar dana baka kenan nace ka kula min da ita shine zanzo na ganta haka, Yarinya duk ta lalace ta fita hayyacinta” zama yayi da ita akan kujera ya kalli fuskanta, ai gabansa ne ya dad’i, da k’arfi ya furta “Basma me ya sameki a fuska? ya bakinki ya kumbura haka, me yake faruwa ne wai?”
Basma banda kuka babu abin da yake yi.
Jikin Shureym ya d’auki rawa cikin sark’ewan murya yace “Abba fad’uwa tayi, santsin tyles ne ya kwashe ta ta fad’i, ina ga fad‘uwan da tayi shine ya saukar mata da zazzab’i” Basma mamaki ne ya cikata da irin k’aryan da Shureym yake fad’a, Abba ya kalli Basma yace “wai hakane Basma?” cikin kuka tace “eh” wani nannauyen ajiyar zuciya Shureym ya saki ba tare da kowa ya gane ba, Abba yace “to Shureym zan ‘tafi da ita Nigeria, inta samu sauk’i sosai sai na dawo da ita” da sauri
Shureym yace “haba Abba kayi hak‘uri, ka barta anan, zan kaita asibiti a dubata da kyau, kojiyan ma na bata pain relief tasha, bansan jikin nata yayi zafi haka ba da tun safe munje asibiti” Ajiyar zuciya Abba yayi yace “to shikenan bari mu tafl, sai ka d’auketa yanzu ka kaita asibiti mu zamu wuce kawai, Allah ya sauwake” ya kalli Basma yace “Basma su Amminki da Momy suna gaidaki, Yayanki Ahmad ya so zuwa, aiki ya rik’eshi” murmushi tayi tace a hankali “ina amsawa” ta kalli Yaya Naufal ta gaisheshi, ya mata sannu da jiki, duk ta gaisa da wanda suka rako Abba, bandir d’in kud’i mai yawa Abba ya bama Basma yace ga wannan kud’in in kina buk’atar wani Abu” cikin murmushi tace “Abba akwai kud’i a guna fa” eh na sani ki k’ara da wannan d’in” godiya tayi masa da kuma Addu’an Allah ya sauke su laflya, ta bada sakon gaisuwa wurin su Ammi da duk family d’in ta. Shureym ya kamata kamar gaske sai wani lallab’ata yake, haka suka yi musu rakiya har mota, Basma tana d’aga musu hannu tare da zubda hawaye, Abba tausayinta ya kamashi kwalla ne ya faru a idonsa, shanyewa yayi tare da d’auke kansa, har suka bar haraban gidan.
Shureym mota ya sanya Basma ya wuce da ita asibiti, likita ya bata Magani da kuma allurai nan akayi treatment d’inta, sannan ya biya da ita wurin siyayyan kayan ciye-ciye, ya siya mata su ice cream, kana suka dawo gida, d’aukanta yayi cak ya kaita d’akinta, bisa kan gadonta ya direta, ya zauna a bakin gadon, yace cikin sanyin murya “Nagode Basma da kika rufa min asiri a yau, nayi nadaman duk abin da na ai kata miki, Basma wlh ina sonki sosai, ke kikeja nake dukanki, pls ki amince mu fara zaman aure kamar kowa” Hararansa tayi tace “Shureym ina so ka sani, a duniya kaine mutumin da nafi tsana, kuma kar kaga na rufa maka asiri, kawai na kyaleka ne saboda Iyayena su suka jamin duk wulak’ancin da kake min, ka mai dani baiwarka mara gata da gali’hu, wlh ka sani na baka talala ne kayi duk iskancin daka ga dama, wlh nasan akwai limit, wataran ko ance ka min wlh bazaka yi ba, dan haka ka tashi ka fita min a d’aki mayaudari kawai azzalumi” lyaka fushi ya fusata ya zuciya, amma sai dakewa yayi bai furta komai ba, ya fice ad’akin tare dajawo mata k’ofa. Kuka ta saki mai tsuma zuciya tace
“Abba kun cuceni, da gatana na zama baiwa, Ina “YAR SHUGABA‘ na zama mara galihu” saida tayi kuka mai isarta, kana ta mik’e ta fita falo, kud’in da Abba ya bata ta d’auko su a inda ta bari, d’aki ta koma ta rufe, ta aje kud’in a inda take adana kud’inta, murmushi kawai tayi ita kad’ai tasan matakin da zata d’auka akan Shureym.
Safeena bata dawo ba sai cikin dare, ta shiga d’akinta, wanka tayi ta fito tana tsaki, zama yai tace “gaskiya Shureym na gaji da wannan auren boyen, ya kamata a fito da zancen nan kowa ya sani, Ni da Mijina auren halal, amma ina guje-guje sai kace auren tsiya mukayi, to wlh da
sake, ka kira Maminka ka sanar mata na gaji da wannan wasan kuran da nake da danginka” Sassauta murya Shureym yayi cikin lallashi yace “Haba my baby love, meye na damuwa? da zaran kin haihu magana zai bayyana a dangi, ran nan nayi magana da Mami ita tace haka, dan haka ki kwantar da hankalinki,yanzu cikinki ba wata hud’u bane, nan da 5month in kin haihu komai zaiyi dai-dai” Ajiyar zuciya tayi tace “to shikenan baby wlh d’azun naji haushi sosai, kawai an sani yini a gidan mutane“ murmushi yayi ya kamota, nan ya shiga jefa mata zazzafar soyayyansa, tuni ya mantar da ita damuwar da take ciki
Hmm