YAR SHUGABA CHAPTER 20

YAR SHUGABA 
CHAPTER 20
Safeena cike da damuwa tace “amma Shureym anya bakajawo tonuwar asirinmu ba, domin in dai Basma taji cewa ka kai karanta ne, tofa zata gaya duk abinda ya faruwa, da kuma dukanta da kake yi” Runtse idonsa yayi ya bud’e, cike da damuwa yace “wlh Safeena raina ne ya b’aci, idona ya rufe sam ban kawo haka ba, sai yanzu da kika tunatar dani, yanzu ya kike ganin za’ayi” cikin damuwa ta rafka tagumi tace ina ganin karka gaya mata, kace kawai ana nimanku ne, inya so inta je can taji komai, kuma na fison dama kowa yasan dani a family d’inku dan nagaji da b‘oye-b’oye” cike da damuwa Shureym yace “haba safeena bai kamata ace abinnan ya fasu yanzu ba, kawai ki tayani da Addu’a kar asirinmu ya tonu” yana gama fad’an haka sai ya mik’e ya shige d’aki, Safeena ta bi bayansa da kallo, ta yatsine baki tace “ba Addu’an da zanyi, in maganar ta fito karshe dai ace an raba aurenka da Basma, kuma abinda nake so kenan”. Shureym yana shiga d’aki ya kira Maminsa ya sanar mata duk abinda ke faruwa, hankalinta ya tsahi ta shiga yi masa fad’a, tace yanzu kazo kaja asirina zai tonu, a gaskiya ba yanzu naso ace maganar nan ya fito ba, domin hakan zai iyi barazana ga aure na, kuma kaima za ka fuskanci fushin Mahaifinka, gaskiya zan San abinyi” tana gama fad’a ta kashe wayar. ‘ Kai komo ta shiga yi a d’akinta tana tunanin hanyar da zata bullowa lamarin, zama tayi tayi dogon nazari, murmushi naga tayi sai tace “Allah ya kaimu goben, na samo maflta”. Da dare Shureym ya kira Basma a waya, yasan in yaje d’akinta ba zata bud’e ba, yace “ki shirya gobe in Allah ya kaimu zamu tafi Nigeria, Dady ya kirani yace muje akwai Family meeting, dan haka ki shirya da wuri da sassafe zamu tafi” cike da murna tace 
“Allah ya kaimu” saita kashe wayar. Mikewa tayi, tayi rawa da tsalle, tana murnan zata ga family d’inta, kaya ta shiga had’awa kamar wacce zata bar garin duka ba dawowa. Zan iya cewa barci b’arawo shine ya saceta, amma sam ta kasa sukuni, kosawa tayi gari ya waye. ‘Washe gari’ Yau Basma harda yiwa Safeena sallama sai fara’a take mata, Safeena tace 
“hoo su Basma za’a tafi min da miji sai dariya kike, to Allah yasa in kin tafi karki dawo” harara Yaya Shureym ya galla mata, saita gimtse sauran maganarta tana dariya k’asa-k’asa, Basma kuwa cike da dariya tace “Ameen ya rabbi, nima bana fata na dawo, kuma mijinki gakl’ ga shi, babu abinda zan miki dashi, ni dai na barki lafiya” saita fice tare da jan trolley kayanta. 
Safeena ta bisu har mota tare da musu Addu’a, haka suka wuce airport, Shureym yana cike da damuwa, Basma kuma cike take da murmushi.‘
Nigeria‘ 
Gidan President ya cika da dangi, sunzo sunata zumunci, da yake ya kama yau rana ce ta Juma’a, mazan gidan duka suka taru suka tafi babban masallacin Juma’a na Abuja. 
Bayan sun dawo gida, iyayen maza da mata suka had’u a babban falon bak’i na shugaban k‘asa, anan aka shirya musu abinci a tsakiyar falon kan babban dadduma daya mamaye falon, yara kuma suka baje nasu liyafar a part d’in Ammi, can suke hidimarsu. Bayan sun gama cin abinci suka shiga hiran zumunci, Abba (President) ya kalli Dady (Gobno Ibrahim) yace “Ibrahim yanzu gamu duk mun had’u gaba d’ayanmu, ina so ka sanar mana musabbabin had’uwarmu anan daka buk’aci muyi” Dady ya nisa ya d’ago ya kalli Abba yace “naso ace Shureym da Basma sunzo tukunna sai kuji bayani a bakinsu, dan dama mun had’u anan ne domin su, na tabbatar suna gab da shigowa” Mai martaba yace A’a Ibrahim ka fara sanar mana da komai kafIn zuwansu”  (Hajiya sa’a) tace “kwarai kuwa, ya kamata muji komai, domin ni hankali na ya ya shi” Hajiya Fatima (Ammi) tace “gwara ka fad’a kawai domin mu fara tattaunawa akai” ita dai Momyn Basma bata iya furta komai ba saboda nuna kawaici, Hajiya Murja MahaifIyar Leema ita ma bata furta komai ba, Ummin Meena kuwa shuru tayi cike da damuwa a fuskanta. Dady yayi gyaran murya ya gaya musu duk abinda Shureym ya fad’a masa jiya, ai duka falon sai suka d’auki salati, Momy kuwa wani irin fad‘uwa gabanta yayi, idonta ne ya kawo kwalla zuciyarta na mata suya, Abba sun kuyar da kai yayi ya kasa yin magana, duk falon ya d’auki shuru sai k’aran fanka da kukan AC ke tashi, Mami ce tace “hmmm nasan za’a rina saboda Shureym ya sanar min cewa tsawan watannin bikinsu da Suka yi, Basma tak’i bashi had’in kai suyi rayuwar aure, akwai ranar da har fad‘a suka yi nice na sasanta lamarin, har nayi masa fad’a, akan cewa yarinya ce ya bita a hankali. Shureym tunda yaji su Meena duk suna d’auke da ciki abin ya dameshi, nice nake 
lallashinsa” Mai Martaba ya katseta da cewa “meyasa kinsan da wannan matsalan yanzu tsawon wata 7 da aurensu, sai yanzu za ki fad’a da kika ji matsala ta kunno kai?” “Mai martaba gani nayi Basma ba son auren tayi ba tun farko, shiyasa nace bari mu lalkab‘ata harta hak‘ura ta yarda da shi”. 
Ba wanda ya tanka mata sai duk suka yi shuru. 
Sallaman shigiwar su Basma falon, shine ya k’atse shurun domin kusan yaran nasu duka shun shigo falon suna murnan ganinsu Basma,Yaya Ahmad na rik’e da hannun Basma sai suka samu guri suka zauna a gefe, duk yaran suka zauna, Yaya Naufal, Yaya Shureym,Yaya Adam, Yaya Jamal, Anty Husnah, Meena, Leema, Deeja, twins din Momy k’annan Basma. Falo yayi Albarka, kowa ya zauna duk suka gaishe da iyayensu, sai dai fuskokinsu babu walwala, Basma ta tashi ta isa gaban Abba ta zauna tare da sanya kanta akan cinyansa, cike da b’acin rai ya tureta tare da cewa “tashi ki bani wuri” da sauri ta d’ago ta kalleshi, cikin shagwab’a tace 
“Abba me nayi kake fushi dani” shuru yayi mata, sai duk jikinta yayi sanyi, takai kallonta ga Momy, saita kauda kai a ranta tana tausayawa d’iyarta, duk tabi fuskokin iyayan nasu babu wanda yayi mata dariya ko murmushi, duk ransu na b’ace, cikin tashin hankali tace “Wai me yake faruwa ne?” Dady ne yace Kusu Meena Ku tashi Ku fita Ku bamu wuri, Anwarda Na’im kuma kuje d’akinku kuyi karatu, ku kuma mazan ku zauna ayi maganar daku”jikinsu duk a sanyaye su Leema suka fita, Basma ta mik’e zata bi bayansu Dady ya daka mata tsawa yace “zauna karki sake ki flta, dama zaman danke a kayi shi” kuka ta fara yi ta koma kusa da Yaya Ahmad ta zauna, hannunta ya kama ya shiga lallashinta. ‘ 
Falon yayi shuru na tsawon minti biyar, Dady ya kalli Shureym yace “Shureym ina so ka sanar mana da abinda ka gayamin jiya a waya” Shureym cike da fargaba da damuwa ya shiga zayyana magana k’arya da gaskiya, bayan ya gama gaya musu abinda ya gayawa Dady sai ya d‘ora da cewa “Basma batajin maganata, ban isa in sata ba ko in hanata ba, zagi iri-iri na cin mutunci babu wanda bata yi min, zata fita da banzan shiga na fidda tsiraici, ban isa inyi magana ba” ai bai k’arasa ba Basma tayi magana cikin d’aga murya da tashin hankali tace “karya kake Yaya Shureym, wlh sharri kake min” takalli iyayenta ta cigaba da cewa “wlh Aba sharri yake min, Ammi yanzu ku kun yarda da bayaninsa, Mai martaba wlh Yaya shureym sharri yake min, karku yarda da maganar shi” ta rarrafa ta isa gaban Mominta tace “Momy in kowa bai yarda dani ba nasan ke zaki yarda dani” Momy sun kuyar da kai tayi k’asa hawaye mai zafi ya sauka a kuncinta, Abba ne ya mik’e da sauri ya wanke Basma da mari guda biyu, tare da hamb’arinta da k‘afansa yace “tir da halinki Basma, acikin zuri’ata kin fita zakka sam baki halinmu ba, kuma in kika kuma 
yin magana anan wlh jikinki zai gaya miki, mutuniyar banza kawai” Dady ne ya mik’e ya kama Abba yace “haba Yallab’ai, bai kamata ka duketa ba” komawa duk suka yi suka zauna. Momy cikin fushi tace “Tunda nake ban tab’a sanya baki a cikin lamarin Basma ba saboda ina nuna kawaici, amma yau zanyi magana, a irin tarbiyyan dana bawa ‘yata bana tunanin zata aikata abinda Shureym ya gaya, in kuma ku kun yarda toni wlh Ni bazan tab’a yarda da magan ganunsa ba, dan haka Basma ‘yata ce, nice nayi nak’udarta babu wanda zai d’aura mata k’azafln zina in d’auka” 
Saita mik’e taje ta kama hannun Basma suka yi hanyar fita daga Falon, yaya Ahmad shima miqewa yayi ya kalli shuraym yace “D’an iska banza baka isa ka yiwa ‘yar Uwata sharri ba, domin nafi kowa sanin mugun halinka, dama mazinaci kamar ka ai dole kaga kowa ma haka yake, Basma nasan abinda zata aikata nasan wanda ba zata yi ba, mak’arya cin banza dana hofi” shima sai ya bi bayan 
su Momy. suna gabda zasu fita Abba ya bud’e murya yace “Maryam wlh muddun kika sanya k’afa kika fita a falon nan to a bakin aurenki, Kai kuma Ahmad wlh in ka fita saina sassab’a maka mutumin b’anza kawai, har zaka zo ka goyon bayan shaid’ayar yarinya nan, tun farko dama ta nuna bata Son shi, dan haka kome aka ce tayi to zata iya aika shi” 
A gigice Momy ta tsaya ta juyo tana mamakin furucin Abba, mai martaba yace “Subhanallah Yallab’ai wani irin furuci ne haka?” Ammi da Ummi da sauri suka mik’e suka isa wurinta, Momy tana kukan bak’in ciki amma sam bata karaya ba dan tana bayan Basma, gabanta su Ammi suka sha, tare da rik’o mata hannu suka jata har zuwa mazauninta, Yaya Ahmad ya kama Basma ya had’ata da jikinsa yana lallashinta, haka suka isa cikin falon suka zauna. Mai Martaba yayi gyaran murya yace “Dan Allah kuyi hak’uri kar b’acin rai yasa a yanke hukunci cikin fushi, ba tare da bincike ba, ke Basma gaya mana gaskiyar abinda ke faruwa” kuka ne yaci k’arfin Basma tace Wlh ban tab’a zina ba ban tab’a ba, kune iyayena ku zaku shaideni akan haka, wlh ban tab’a ai’kata abinda yace muku ba ko d’aya daga ciki” kuka ne yaci k’arfinta saita d’aura kanta a cinyar Yaya Ahmad, jikinta ne ya soma kad’uwar jin sanyi nan take zazzab’i ya rufeta… Shuru suka yi suna sauraren kukan Basma, tausayinta ne ya kamasu, Ammi ce tace “to shikenan, ni ina ganin gaba d’aya wannan abun rashin fahimta ne, dan haka sai a sulhunta su komai ya wuce, sai su tafi, Dady yace “kwarai kuwa abinda ya kamata ayi kenan” Mai Martaba ya shiga yi musu nasiha mai ratsa zuciya, daga bisanl’ ya d’aura da cewa “President banji dad’in yanda ka d’auki wannan lamari da zafi ba, da har ka furta mummunan kalma ga Hajiya Maryam, in hankali ya gushe ai hankali ne ke nemoshi, dan Allah mu rik’a kai zuciya nesa, duk sai mu taru muyi hak’uri komai ya wuce, kai kuma 
Shureym kaji tsoron Allah, in har kana cutar da ita Allah ba zai barka ba” 
Abba yayi wa mai Martaba godiya, ya soma yiwa su Basma nasiha, bayan ya gama yace “Basma kije part d’ina ki jirani, kai kuma Shureym ka shirya zuwa gobe in Allah ya kaimu da‘ safe zaku koma, shikenan zaku iya tafiya” Haka suka watse kowa da damuwa a ransa, Amma banda Shureym da Maminsa wanda zuciyarsu yayi haske tunda an kashe magana ba tare da Basma ta tona komai ba, duka Matan suka wuce part d’in Momy, anan suka bar Mazan suna tattaunawa. Yaya Ahmad yabi bayan Basma suka zauna a falon Abba, ya kalleta cikin nutsuwa yaga duk ta rame haske kawai ta k’ara, yace “Basma me Shureym yake miki, ki gaya min gaskiya fa, dan bana son k’arya” guntun Murmushi tayi tace cikin sanyin murya “Yaya Ahmad babu komai, kawai dai kasan halinsa na saurin fushi, anan ne muke dan samu sab’ani, amma bayan haka ba komai” kallonta yake cike da zargin abubuwa kala-kala domin sam bai gamsu da amsar da ta bashi ba, sai yace “shikenan tunda ba zaki fad’a ba, in ya kusa kashe ki saiki fad’a” murmushi tayi tace “Ni ba zai ma kashe ni ba” mik’ewa yayi yace “bari na kawo miki abinci da maganin zazzab’i kisha, dan d’azu naga har kad’uwan sanyi kike yi” murmushi tayi tace “wlh Yaya tsabar shiga shock ne ya sani zazzab’i, amma ka kawo min zansha ko kaina zai rage min ciwo” harya fara tafiya sai tace “Yaya d’an tsaya in baka ajiya” zage Jakarta tayi ta ciro wani k’arakin key guda d’aya, sai ta mik’e ta isa wurinsa tace “Yaya dan Allah ka ajemin wannan key d’in inna tashi amsa zan maka magana sai ka bani” d’aga key d’in yayi yace key d’in miye ne wannan?” murmushi tayi tace na sirrina ne, ni dai ka ajemin wataran zan maka bayani akansa” gyad’a kai kawai yayi sai ya fita, tare da juya 
key d’in a hannunsa, yana tunanin ko na miye. Abba ya samu Basma a sashinsa, zama yayi ya kirata, sai tazo ta zauna gefensa a k’asa. kanta ya d’ora bisa cinyarsa, sai ya shiga yi mata fad’a daga k’arshe yayi mata nasiha, kuka Basma take yi mara sauti, a haka Yaya Ahmad ya samesu shima ya zauna ya zubawa Basma abincin ya mik’a mata yace taci, Abba ne ya kalle shi fuska a d’aure ya shiga yi masa fad‘a akan abinda ya aikata d’azun, hak’uri Yaya Ahmad ya bashi da alkhawarin hakan ba zai sake faruwa ba, nan suka zauna suka cigaba da hira, har Basma ta kammala cin abincin kana ta mik’e zata fita da kulolin abincin, dakatar da ita Abba yayi yace “Basma barshi Ahmad ya tafi dasu, ki hau sama kiyi wanka jakar kayanki yana d’akin kusa da nawa, anan zaki kwana” rau-rau tayi da idonta tace “Abba ina son inga su Meena da su Ammi ne fa” murmushi yayi yace “anjima in zamuci abincin dare zaki gansu, dan haka kiyi abinda na saki” hawaye ne ya ciko idonta, kawai saita haura sama zuwa d‘aki, ta shiga rusa kuka sai da tayi mai isanta kana ta shiga bayi dan tayi wanka, zuciyarta na nazarin abinda yasa Abba ya hanata ganawa da ‘yan uwanta. Da dare Momy ce zaune a falon Abba sai Basma. magana Momy ta shiga yi tace “Basma anya kina jin dad’in zama da Shureym kuwa? In yana miki wani abu ki gaya min” murmushi Basma tayi tace “Momy ba komai” kallonta tayi sosai tace “Basma ada ba kya b’oyemin matsalanki, amma meyasa yanzu zaki b’oyemin?” murmushi ta kuma yi tace 
“Momyna ba komai fa” murmushi kawai Momy tayi tace “to shikenan, ki dai k’ara hak’uri, aure ba abin wasa bane ibada ce ta samun Aljanna, sannan ina mai gargad’inki Basma akan k’in amincewa da kikayi dashi a matsayin mijinki, ina ganin shine dalilin da yasa ya k’ulla miki sharri, dan haka a kul d’inki ki tabbbatar kin bashi hakk’insa, mijinki ne kuma halas d’inki ne, nasan baki sonsa amma ki sanya a ranki shine wanda Allah ya zab’a miki, dan haka ki amshi k‘addarar ki sai Allah ya baki ladan akan haka, kuma duk inda kike ki rike mutuncinki dana aurenki” Kuka Basma ta shiga yi, tana cewa a ranta “duk yanda zan fahintar daku akan zamana da Shureym ba lallai wasu su gasgata ba, domin ya riga yamin mugun tabo wanda inna fad’a za’a ce na fad’a danna kare kaina ne, bana so kusan komai yanzu sai nan gaba kad’an a lokacin da kowa zai gasgata magana ta” 
 tace “insha Allah Momy zan ki yaye, nagode da kika aminta dani, kika bani yardanki a lokacin da kowa yaki yarda dani, Momy na Allah ya biyaki da gidan Aljanna” rungumeta Momy tayi tare da sanya mata albarka. Washe Gari’ 
Su Basma sun fito zasu koma America, iyayan nasu suka k’ara musu nasiha, kana gaba d’aya gidan suka tafi rakasu zuwa airport. Basma ta tsaya gaban Yaya Ahmad tace Yayana zan tafi na barku zanyi missing d’inka sosai” murmushi yayi mata yace “kin san ni kullun cikinsa nake, Allah ya kare ki daga duk kan abin k’i“ saita rungumeshi tana fad’in “Ameen” a haka tayi ta bin kowa tana musu bankwana, tana zuwa wurin Abba sai ta rungumeshi ta soma kukan shagwab‘a, Abba murmushi yayi yace “Queen Basma ai bata kuka, dan haka ta daina b‘ata hawayenta Abbanta kullun yana tare da ita” murmushi tayi na jin dad’i tace “Abba ka daina fushi dani k0?” “kwarai kuwa, ba kiga yau rakiya harda ni ba. ai na huce tun jiya, Abbanki bazai iya dogon fushi dake ba, dan haka ki kwantar da hankalinki, Abbanki na sonki” murmushi tayi tace nagode Abbana” 
Bayan tayi sallama da duk family d’in ta, sai suka wuce suka shiga jirgi tanata waigensu, tana d’aga musu hannu. Suna shiga jirgi ta fashe da kuka mai tsanani. 
Tsanar Shureym ya dad’u a ranta,  ayyana irin abinda zata yi ta rama take a ranta, a haka har barci ya kwasheta, sai da jirginsu ya sauka ta farka. Haka suka wuce gida a tsakaninsu babu um babu um-um. 
Suna isa Safeena ta rungume Shureym, cike da farin ciki tace “nayi kewarka Mijina, da fatan babu wani damuwa” murmushi yayi yace “babu” cikin tsokana Basma tace “Acici baki ganni bane, tona dawo sai kiyi hak’uri Addu’anki baici ba” d’aure fuska tayi tace “nifa bana son rashin kunya waye acicin?” dariya Basma ta kwashe dashi, Shureym yayi mamakin ta yanda ta saki kamar ba ita bace mai kuka d’azu, tace 
“haba Anty Safeena meye na d’aukan wuta, nifa ba ruwana da fad’a yanzu, in zaki sauko mushirya tom” murmushi Safeena tayi ta kalli Shureym tace “halan an zane ta sosai ne shiyasa ta koyi ladabi” murmushi yayi bai ce komai ba, Basma tace “ni dai bari naje nayi wanka nazo muyi hira, dan naga surutunki zai hana ni yin abinda ya kamata” tana gama fad’an haka tayi gaba abinta, tana dariya wanda ni mai rubutu ni 
kad’an nasan ma’anarsu. Hmm
Sake baki duk suka yi suna kallon Basma, zama Shureym yayi ya bama Safeena labarin komai, murmushi tayi tace 
“lallai kace abun yaso ya jawo damuwa, to Allah ya kyauta, shiyasa naga Basma ta sauko” Shureym yace “tunda ta sauko kema sai ki sako a zauna lafiya, nifa a gaskiya dama ina son Basma, kawai dai bana son b’acin ranki ne” d’aure fuska Safeena tayi tace “to kayi ta sonta mana sai me” murmushi yayi ya mik’e ya bata wuri, dan yasan ya tsokano fad’a. 
Basma tana gama shiryawa ta fito falo, danbun nama ta dibo a plet da yawa tana ci, zama tayi a kan kushim tace “Anty Safee ga danbun nama ko zaki ci” galla mata hara tayi tace kina zaune a gun zaki cemin in ci, ki zuba min ki bani in kina son naci” dariya tayi taje kusa da ita ta aje plet d’in tace mai da wuk’ar, gashinan kici, ni bari na shiga kicin na d’aura mana abinci, dan yanzu ba zan yarda kuku na mana girki ba” Safeena sakin baki tayi tace “ikwan Allah, Basma an girma anyi hankali” juyowa tayi tace “haba Anty Safee, me kika mai dani ne, dama can da girma na” dawowa tayi gabda Safeena saita d’auketa photo a wayanta, tana cin danbun nama, hasken wayar yasa ta d’ago tace 
“kambu d’aukata kike ko?” dariya tayi ta k’ara d’aukanta, sai da tayi mata kala biyar kana ta dena, tace “zan aje miki ne in kin haihu na nuna miki, a lokacin da kike kwad’ayin Danbun nama” tana gama fad’an haka ta shige kicin tabar Safeena cike da mamaki. Tana shiga kicin ta tsaya ta zab’i hoton da Safeena ta fito sosai a ciki, saita goge sauran, kyakkyawan murmushi tayi, sai ta shiga d’aura abincin daren. “Bayan Sallan Isha’i’ Su Shureym ne zaune a dinning Safeena na gefen damansa, Basma na dayan gefen hagunsa, suna cin abincin da Basma tayi musu, delof d’in kuskus da hanta wanda yaji kayan lanbu, sai farfesun kayan ciki da kuma juice d’in kwakwa wanda yasha madara. Santi dukansu suke yi amma banda Basma da taketa musu dariya, tashi tayi ta shiga d’aukarsu photo tace gwara na d’auke ku in rik’a kallon lokacin da kuke santin abincina na farko da kuka fara ci” basu kawo komai aransu ba sai suka yi ta dariya, Basma murmushi tayi kawai, ita kad’ai tasan me take kitsawa a ranta. Bayan sun kammala cin abinci, suka koma babban falonsu suka zauna, Yaya Shureym ya shiga yi musu bayani “Safeena da ke da Basma Ku duk matana ne, ina so mu mance rayuwar da muka fara a baya, mu dawo mu soma rayuwa na aminci da juna, Basma ki yafemin muzguna miki da nayi, sannan nagode da kika rufamin asiri akan aurena da Safeena da kuma abinda nayi miki, ke Safeena ki d’auki Basma a k’anwarki, ke kuma Basma ki d’auki Safeena a matsayin Yayarki, dan Allah mu kiyayi b’atawajuna rai, dan haka yanzu zan raba muku kwana, ke Basma tunda na aureki ban tab’a kwana a d’akin ki ba, dan haka zanyi miki sati d’aya na amarcin da banyi ba, ke kuma Safeena sai kiyi hak’uri in na gama kwanakin, sai na rik’a kwana biyu-biyu 3 ko wani d’aki, in kuna da magana sai kuyi Safeena tace “ba komai Shureym nima na yarda makaman yak’i na, na d’auki Basma k’anwata, dan haka na yarda kayi mata kwankin Amarcinta” Basma kuma tace 
“Nagode Yaya Shureym nagode Anty Safeena, sai dai zan nima afwanku akan cewa, yau na fara period kuma ina yin tsawon kwana shida kafin na gama, dan haka nace me zai hana ka rik’a kwana a wurin Anty Safeena, in period d’in ya d’auke sai kayi min kwana kin Amarci na” saita k’arasa maganar da sun kuyarda kai k’asa, alamanjin kunya, dariya duk suka yi 
Shureym ya kalle Safeena yace 
“me kika ce game da bayanin Basma” murmushi tayi tace “sai abinda kace tunda kaine Mai gida” dariya yayi na jin dad’i yace “shikenan mun karb‘i uzurinki, in ya so bayan kwana shida saiki amshi girki” farin ciki ne ya lullub‘e Safeena, domin dama bata jin zata kwana ita kad’ai a d’aki dan tanada b’ukatar mijinta. Nan dai suka shiga hira, Basma ta mik’e tace “bari na mana salfee” sai duk suka mik‘e suka shiga d’aukar hotuna, wani ta d‘auki Shureym da Safeena suna dariya ga katon cikinta ya fito, wani yana rungume da Safeena, wani kuma su d’auka su uku selfee, wani kuma Safeena ta d’auki Basma da Shureym. Bayan sun gama Basma ta yi musu sallama ta wuce d’aki, suma d’aki suka wuce dan yin shirin barci. 
Basma tana shiga d’aki ta rufe da key, tsalle tayi akan gado ta kwanta, tare da yin murmushi, can kuma sai ta fashe da kuka…. 
‘Tofa shin wai me Basma take shiryawa ne? Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE