YAR SHUGABA CHAPTER 21

YAR SHUGABA

CHAPTER 21
Da misalin k’arfe uku na dare, Basma ta tashi ta gabatar da sallan Nafila, Addu’a tayi da niman yardan Allah akan abinda take shirin yi, haka ta zauna tayi ta tasbihi, hargabani’n sallan Asubahi, kana ta k’ara yin alwala tayi raka’atanil fljn’, sannan ta gabatar da sallan Asubahi, azkar ta karanta, sai ta tashl’ ta nad’e sallaya, idonta a rufe ta fad’a gado, murmushi ta saki, a ranta tace “ashe ma Yaya Shureym mugun wawa ne, da nasan haka yake da saukin kai da tuni nasan abinyi, wai su sun d’auka da gaske period nake, hmm kana tunanin cin zalin da kayi min da sharrin da kamin kasha ni masilla ne, wlh saina d’auki fansa mafi muni a gareka, azzalumi kawai” tsaki taja saita gyara kwanciya, cikin k’ank’anin lokaci barci mai nauyi yayi gaba da ita. Sai k’arfe goma na safe ta farka, wanka tayi ta shirya cikin riga da sket English wears, ba wani makeup da tayi, fitowa tayi taga su Yaya Shureym suna Karin kumallo, murmushi ta sakar musu saita k’arasa wurin taja kujera ta zauna, gaishe su tayi suka amsa cikin kulawa, tace “kuyi hak’uri na makara ban tashi da wuri na had’a mana breakfast ba” murmushi Safeena tayi tace “Basma kenan, karki damu ai nice da girki, nasa kuku ya had’a mana tunda ni gaskiya bana girki” Basma harta kai hannunta zata jawo food wormer sai ta janye hannunta jin Safeena na fad’in kuku yayi musu breakfast, da sauri tace “gwara da ban zuba ba, dan bazan iya cin girkinsu ba” mik‘ewa tayi ta wuce d’aki, shi dai Shureym saurarensu yake yi yana kai loman abinci, a ransa yana yabawa Basma “yanda take k’ok’arin yin abinci da kanta duk irin matsayinta da take dashi na 
‘YAR SHUGABAN K’asa, amma ita Safeena ba ‘yar kowa ba sai iyayin tsiya, k’ilama bata iya bane, dan Ni ban tab’a cin girkinta ba” Maganar Basma shine ya dawo dashi daga zancen zucin da yake, tace 
“Yaya Shureym bari naje naci abinci” kallonta yayi sama da k‘asa yace “amma kinsan yanzu ba zan yarda da wannan fitan naki bak0” marairaice fuska tayi tace “yaya takeway kawai zanyi na dawo” d’aure fuska yayi yace “ni bawai fitan bane damuwa na, kawai bana so ki had’u da d’an iskan saurayinki d’in nan ne” idon Basma ya ciko da kwalla bata ce komai ba, saita juya zata koma d‘aki, dakatar da ita yayi yace “kije amma na baki minti talakin, in kika bari ya wuce, to kinfi kowa sanin hukunci na, bawai na bari bane sanyi kawai nayi” bata tanka mishi ba, ta wuce abinta tana kissima abinda zata aikata mishi. Tana fita studio ta wuce, wayarta ta basu ta nuna masu hotunan da take so a wanke mata, tana gama musu bayani ta wuce siyan abinci. Cikin sauri ta dawo ta basu kud’insu ta karb’i hotu nan da wayarta, ta adana su a jaka, kana ta fita cikin sauri, taxi ta tara ya sauketa a gida ta shiga da sauri. Ta taddasu a falo, 
“sannunku da hutawa” tace, kana ta nufi d’akinta, Yaya Shureym ya dakatar da ita, damm taji gabanta ya fad’i, amma saita dake tajuyo, kallonta yayi yace “amma kinsan kin d’auki kusan minti arba’in ko, daga siyan abinci shine zaki d’auki 
wannan lokacin” marairaice fuska tayi tace 
“haba Yaya Shureym, kasan k‘asar nan bafa Nigeria bane, duk yanda na tadda layi sai an sallami wanda suka rigani kafin a bani, suba ruwansu da cuwa-cuwa, kuma bada motan gida na fita ba, da taxi ne” 
Kallonta yayi a takaice kana ya d’auki telephone ya kira masu gadin gidan, tare da duk ma’aikatan gidan, bayan sunzo yace tare da nuna Basma “karku sake ku barwancen ta fita a gidan nan sai in na baku izini” duk wannan bayani a cikin harshen turenci yake musu, cikin girmama suka amsa masa kana ya sallamesu suka fita, mik’ewa yayi yazo inda ta tsaya kana ya amshi ledan take away d‘in, yace “muje na taya ki ci” gabanta ne ya shigo dukan uku-uku, burin ta karya buk’aci ganin abinda ke cikin jakarta, haka sukajera suka shiga cikin d’akin, Safeena wani bak’in kishi ne ya tirnik’eta, tsaki taja tace 
“ni sam bana burin wata mace ta rab’i Shureym, amma shegiyar yarinyar nan ta zame mini k’arfen k’afa, bari mu koma Nigeria saina raba wannan Auren, dan in ba haka ba, Shureym ya sameta kashina ya bushe, dan na shiga uku, dani da banza duk d’aya ne a gunsa” mik’ewa tayi ta wuce d’akinta cike da damuwa. 
Suna shiga ya fincikota, a tsorace ta kalleshi, jakanta ya amsa, ai Basma Addu’a ta fara yi a cikin ranta domin ta gama tsorata, duk tunaninta bud’e jakar zaiyi, da mamaki sai taga ya aje akan dressing mirror din ta, wani ajiyar zuciya ta saki a hankali, dawowa yayi wurinta, hannunta ya kama suka zauna kan kujera, jawota yayi kan jikinsa wanda hartanajin saukar numfashinsa a gefen kuncinta,juyo da fuskanta yayi, suka kallijuna ido cikin ido, sha’awar Basma ce kwance a kwayar idon Shureym, itama kuma tsana ce kwance a cikin kwayar idonta, bata ankara ba saita ji ya had’e bakinsu, ya soma sumbatarta, duk yanda taso kwace kanta ta kasa, k’arshe hak’ura tayi sai da yayi iya ka yinsa kana ya saketa, kuka taso yi amma saboda karta nuna damuwa saita shanye su, mik’ewa yayi yace daga yanzu wannan ne irin hukuncin da zan rik‘a miki, in dai kika sab’awa umarni na” sai ya fice. 
Da gudu ta mik’e ta shiga bayi. brush ta soma yi tana dirjan harshenta, tana yi tana kuka, takai kusan minti Sha biyartana aikin abu d’aya, sai da taji bakinta ya soma yi mata zafl kana ta dena brush d’in, wanka tayi ta fito ta sanya kaya marasa nauyi, saita rufe k’ofarta,ji tayi bata jin yunwa, abincin da ta siyo saita sanya a fridge, d’auko wannan jakar tayi ta ciro diary d’inta, ta shiga rubuta labarin fitanta da Bilal, da harya kawo mata ice cream data manta a motansa, Yaya Shureym kuma daya ganshi ya kulla mata sharri, dama ta rubuta labarin tun farkon had’uwarta da Bilal a cikin diary d’in, saita d’aura da labarin bayan dawowarsu daga Nigeria, haka ta rubuta komai abinda ya faru, sai ta sak’ala hotunan data d’aukesu a cikin diary. Maida shi tayi majiyansa, saita mik’e ta dumama abincin da ta siya a microwave, bayan ta gama ta gabatarda Sallan Azahar sai ta bi lafiyan gado. 
‘Kasar Monaco‘ 
Jidda ta matsawa Aryan wanda duk iya wulakanci yayi mata, amma tak’i rabuwa dashi, k’arshe dole ya sakko suka cigaba da mutunci kamaryanda ya buk’ata, don ya sanar mata shi sam ba zaiyi soyayya da ita ba, Aryan yayi waya da Umma ya sanar mata saura wata Uku ya dawo Nigeria, tayi masa Addu’a sosai kana tayi masa fad’a da nasiha akanjin tsoron Allah, yayi mata godiya yace “Umma inna dawo zanje Gombe na dawo dasu Malam da Inna su dawo wurinmu mu zauna dasu” Umma tayi farin ciki sosai tace “gaskiya ne, tunda Allah ya bud’a mana yanzu sai su dawo kusa damu, in yaso duk bayan lokaci sai mu rik’a zuwa Gombe muna gaisawa da sauran dangin mu”. Nan suka yi sallama tana sanya masa Albarka. 
Nigeria‘ 
Abba ya tattauna dasu Ammi da Momy akan zancen Basma, ya bama Momy hak‘uri akan abinda ya faru, sun sasanta kansu kana ya gargad’i kowa akan kar abari su Meena suji komai, kamar yanda suka yanke da sauran iyayen kafin su tafl. Haka aka rufe maganar ba tare da sun fltar dashi ba. Deeja ta damu Yaya Ahmad akan ya sanar mata abinda ke faruwa, hak’uri ya bata yak’i gaya mata, duk yanda su Meena suka sojin abinda ke faruwa amma ba suji komai ba a wajen mazajensu, k’arshe hak’ura suka yi da niyyar tambayar Basma, sun kira ta, itama tak’i gaya musu tace “ku kwantar da hankalin ku, za kuji komai nan gaba kad’an” dole suka hak’ura badan sun so ba. 
‘America’ 
‘Bayan kwana Hud’u’ Ya kama yau kwana biyar kenan da dawowar su Basma, cikin dare Basma ta tashi ta d’auki Jakar da diary d’inta ke ciki, ta gama sanya duk abinda ya kama, ta sanya wayar da take amfani wajen d’aukansu Yaya Shureym a ciki, ta barta a kunne, sai ta sanya dukkan gwalagwalan zinarinta a ciki da kayan amfaninta, saita kullejakar. Tashi tayi ta shiga had’a kayanta gaba d’aya a cikin trolley guda uku, hatta takalmanta bata bari ba, bayan ta kammala tas, sai ta sanya duka trolley d’in a cikin kitchen dinta ta kulle, Sallan Nafila ta gabatar, ta shiga kwararo Addu’a akan abinda take shirin aikatawa, Allah ya bata sa’a ya taimaketa, Sallan Asubahi aka kira ta gabatar da raka’atanil fajri, sannan tayi Sallan Asubahi tayi azkar na safe, saita tashi ta sanya sallayan a cikin d’aya daga cikin trolley, gado ta fad’a ta kwanta ta soma sharb’an barci. ‘Da safe‘ Misalin k’arfe tara na safe, Yaya Shureym yazo yana buga mata k’ofa, kamar bazata bud’e ba saboda barcin da takeji, zuwa tayi ta bud‘e k’ofar tace “Yaya Shureym lfya kake buga min k’ofa? wlh barci ke damuna” cikin murmushi yace “Lafiya lau, ina so ki d’an had’a mana breakfast kafln mu dawo daga asibiti, zan kai Safeena ne ba ta jin dad’in jikinta, daga nan za’ayi mata awon ciki” murmushi tayi tace “tom Yaya Allah ya bata laflya” fitowa tayi ta tadda Safeena a falo sannu tayi mata saita amsa a yatsine, murmushi Basma tayi tace a ranta “kisha kuruminki Malama, yau zan bar miki mijinki” a fili kuma tace “d’an Baba yana baki wahala,Allah dai ya raba ku lafiya” ta amsa a takaice kana suka wuce. Kitchen Basma ta shiga, ta gayawa kuku Breakfast d’in da take so su had’a musu, kana ta koma d’aki da sauri, ta shiga fito da duk trolleyn ta falon, ta aje a bayan kujera, saita rufe su da wani zani. 
Wanka ta tayi, ta sanya doguwar riga bak’a mai aiki purple, sai ta yi rolin da farin gyale tayi kyau sosai, d’akinta ta bud‘e ta fita farfajiyan gidan da gudu a tsorace tana ihu, da sauri duk ma’aikatan gidan suka fito, cikin harshen turanci ta shiga gaya musu “wani Abu ne a d’aki na Ku taimakeni Ku ciremin” suka tambayeta “meta gani” tace “Ni bazan gane ko miye ne ba” Da sauri duk suka shiga falon suka soma dubawa, d’akinta suka shiga su duka, da sauri tabi bayansu, k’ofar ta jawo da k’arfl ta sanya key ta rufe su, cikin sauri taja trolleyn kayanta har waje, ta bud’e gate ta fitar dashi, a haka harta fidda kayanta duka, su kuma sai ihu suke akan ta bud’e su, kyalkyacewa tayi da dariya ta d’auki hand bag dinta ta fice abinta, tana fita ta samu taxi ya kwashe mata kayanta sai airport. Suna isa ta ja kayanta, zuwa minti sha biyar an gama checking kayansu sun shiga jirgi, minti goma da shigansu jirgi ya daga zuwa k’asarmu Nigerian) 
Hmm ‘Su Basma an shuka tsiya  koya cakwakiyar zai kasance sai kun jini a next chapter…“ 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE