YAR SHUGABA CHAPTER 22
CHAPTER 22
Jirgin su Basma ya sauka lafiya, drop ta d’auka taxi, ya kaita asibitin da Yaya Ahamd yake aiki, nan ta nufa, ta ciro trolley d’inta guda biyu da kuma wannan bak’arjakar da diary ke ciki, ta jasu zuwa cikin asibitin, gefe ta tsaya ta samu d’aya daga cikin masu gadi yana ganinta ya washe baki dan ya ganeta suka gaisa tace
aam Baba Dr Ahmad yana ciki kuwa? cikin ladabi yace “yana ciki, motansa yana cikin wancen barandan yayi parking d’inta“
Murmushin jin dad’i tayi sai ta ciro wata farar takarda mai d’auke da wasik’a a ciki tace “Baba Dan Allah ka taimaka ka kai masa wannan kayan, sauri nakejirgi na jirana, ka gane ni ai?” cikin dariya yace
“kwarai Hajiya na gane ki” murmushi tayi ta k’irga dubu Ashirin ta bashi tace
“Baba ga wannan saika ci goro ko” jiki na rawa ya amsa yayita shi mata da albarka, kiran wani matashin saurayi yayi d’aya ne daga cikin drivern asibiti, yayi masa umarni daya d’auki d‘aya daga cikin trolley, shi kuma Baba yayi mata sallama ya sanya wasik’ar a aljiunsa, kana ya d’auki d’ayan trolley da kuma bak’arjakar suka shiga cikin asibiti. Basma binsu tayi a baya har saida taga sun isa k’ofar office d’in Yaya Ahmad, kana tadan tsaya, tana ganin sun Shiga sai tajuya cikin sauri ta isa bakin gate, taxi ta koma ta shiga, da gudu suka bar unguwar. Mai gadi suna Shiga, Yaya Ahmad ya kalle su cike da mamaki yace
“Malam wannan kayan fa daga ina?” da dariya a fuskansa yace “Uwar d’akinta tace na kawo maka” cikin mamaki yace “wace uwar d’akin naka?” yace “Basma mana, ita tace na kawo maka domin tace tana sauri ne ana jiranta, tace in baka wannan wasikar ma” saiya mik’a masa, cike da tsoro da mamaki Yaya Ahmad ya mik’e yace “Basma kuma?” da sauri ya fita a office d’in, Baba mai gadi da d’ayan saurayin suka rufa masa baya, gate ya nufa yana hangen k0 zai ga Motan da tazo a ciki, babu kowa bamu alaman wata mota, Baba mai gadi yace “kaga ikwan Allah sun riga sun tafl, acan fa na hangi mota taxi wanda ya kawo ta, nima nayi mamaki dana ganta a cikin taxi” ajiyar zuciya Yaya Ahmad yayi ya shiga wasi-wasi da damuwa, komawa office yayi ya Shiga bud’eja kukunan, tabbas kayan Basma ne a ciki, bak’arjakar ne ya nima bud’ewa amma arufe take babu key a jiki, zama yayi kamar wanda yayi aikin gajiya, dan jikinsa duk a mace yake, da kuma tsananin fargaba da zuciyansa yake ciki, bud’e wasik’ar ya yi, ya soma karantawa kamar haka… ‘ASSALAMU ALAIKUM’
‘Yaya Ahmad da fatan duk kuna lafiya, nasan zaka yi mamaki da ganin kayana ba tare da na bari mun had’u ba, Yaya Ahmad ina cikin damuwa na tsani rayuwar dana ke ciki, dan haka zanyi nesa da kowa ko zanji saukin abinda ke damuna, Yaya Ahmad kafi kowa sanin bana son auren da a kayi min, amma na hak’ura nayi biyayya gasu Abba, na d’auki alk’awarin yiwa Yaya Shureym biyayya in zauna dashi, amma kash sai dai shi a gunsa akwai mugun nufi a zuciyarsa game dani, a ranar da muka shiga jirgi zuwa garin America lokacin aurenmu, anan cikin jirgi Yaya Shureym ya fara shayar dani ruwan bak’in ciki, wanda har yau ina cikin shansa, Yaya Ahmad na so gaya maka komai a wancen lokacin, saina ce bari nayi hak’uri bai kamata in fara kai k’ara ba, kuma ma duk abindazan fad’a ba mai yarda dani akai, sai kai kawai nasan zaka yarda tunda kai kasan halinsa, d’aurewa nayi tun daga ranar dana tafi na bar gida harzuwa yanzu, Yaya Ahmad bari na tak’aice maka bayani, duk kan k’arin bayani da kuma labarin zamana a America yana cikin wannan diaryna na rubuta shi, da kuma wasu hotuna a ciki wanda zasu zame min shaida, duk a cikin wannan bak’ar jakan, akwai kuma wayata a ciki wanda akwai wasu hotuna a ciki, ga system d’ina ka aje min shi, key d’in dana baka rannan ka aje min shine mabud’in wannan jakar, ina so ka kai gida ka bayyana wasu Abba komai dake cikin jakar nan, tare da karanta musu wannan wasik’ar da kuma abinda ke cikin diary na, Yayana nagode da kulawanka, nasan kaida Momy ne zaku fl kowa shiga damuwa, dan Allah ka bama Momyna hak’uri, kuma nayi muku alk’awari duk inda nake zan kula da kaina zan kare mana martaban gidanmu da mutunci na, insha Allah zan kiyaye duk kan hakk’ok’in Allah wanda ya rayata akaina, kuma zan kare igiyar Aure na.‘
‘Hawayena ba zasu daina zuba ba, har sai naji a raina kun yafe min laifin dana yi muku akan tafiya da nayi na barku, Ina sonku duka dangina. Abbana ku yafenin Ammi na kar kuyi fushi dani, zan dawo amma ba nan kusa ba, hasalima a yanzu bansan ina na nufa ba Bissalam’* ‘Yarku Basma… Kafin ya gama karantawa, hawaye ya gama wanke masa fuska, tashin hankali ya shiga mara misali, da sauri ya share hawayensa ya sanya wasik’ar cikin aljiunsa, kiran wani mai gage masa office yayi, ya taya shi fita da trolley, mota ya sanyasu, ya shiga mota zuwa gida cike da tashin hankali.
Basma suna isa airport ta biya mai taxi, ta ja trolley d’inta wanda ya rage guda d’aya, saita shiga ciki, ba wani b’ata lokaci suka shiga jirgi sai zuwa k’asar Etopia,jirgunsu na d’agawa taji gabanta ya fad’i, kewar family d’inta ya cika mata zuciya,ji tayi dama jirgin zai tsaya ta sauka, runtse idonta tayi tace a ranta Anya na yiwa iyayena adalci kuwa? anya na yiwa kaina adalci? shin ya za suji in suka ji labarin na tafi, Allah sarki Yaya Ahmad ban kyauta muku ba” Ajiyar zuciya tayi tace “Shureym kaine silan komai, dole in yi nesa da kai da kuma mugun nuflnka a kaina, na tsaneka ba zaka tab’a cimma burinka a kaina ba, kuma so nake ka gane kuranka kasan
cewa ni Basma ‘yar halak ce” saitaja tsaki ta gyara zamanta. Carbi counter ta Ciro a hand bag dinta, ta shiga salatin Annabl s.a.w, nan take taji natsuwa ya ziyar ceta, murmushi tayi saita lumshe idonta kamar mai barci.
Yaya Ahmad yana isa gida yayi parking, da sauri ya fito ya kwalawa wani driver kira, cikin sauri yazo, jakan ya ciro ya ce ya d’auki d’aya, shima ya d’auki d’aya ya rik’e da bak’arjakar, falon Abba ya wuce dasu, suna shiga suka aje, ba kowa a falon sai ya sallami driver. Zama yayi dirshen a k‘asan kafet, ya rafka tagumi tunani yake ta ina zai fara, wayansa ya ciro ya kira Amminsa cikin tashin hankali yace “Ammi kina ina? ki zo ina falon Abba” bai jira me zata ce ba ya kashe wayar, haka ya kira Momy itama, ya kira Naufal, ya kira Husna k’anwarsu, cike da damuwa duk suke f’Ito, duk tunaninsu mutuwa akayi, kiran Deeja matarsa yayi ya kuma kira Meena itama, Ammi da Momy har rige-rigen shiga falon suke, tsayawa suka yi cirko-cirko ganin Yaya Ahmad shi kad’ai a falon, Meena ma cikin sauri ta isa falon haka ma Deeja, duk zama suka yi suna jero masa tambaya, Abba dake sama hayaniyar su yaji sai yayi sauri ya fito, ganin su gaba d’aya a falon ya tada masa hankali, saukowa yayi cike da fargaba yace “lafiya kuka taru anan?” Ammi tace “Yallab’ai, Ahmad ya kira mu yace mu taru anan, ni wlh duk hanlina a tashe yake, bamu san dalilin kiran ba” Ahmad mik’ewa yayi zai flta a falon, da sauri Abba ya tsaida shi “kai ina kuma zaka? bana son shirme, kazo duk ka tayar mana da hankali” hawaye ne suka ga ya sauka masa a kuncinsa, sai ya share bai ce komai ba ya fice, ai iya ka tashin hankali sun shiga ciki, domin basu tab’a ganin hawayen Yaya Ahmad ba da girmansa, danshi mutum ne mai d’auriya, da wuya kaga abinda zai tayar masa da hankali balle ya sashi kuka. Suna cikin zama na damuwa sai ga Yaya Naufal ya shigo, baifl minti biyar ba Anty Husna itama ta shiga, duk suka zauna suka gaishe da iyayan nasu tare da tambayan musabbabin had’uwarsu, kafln su basu amsa, Yaya Ahmad ya shigo ya nufl wurin trolley da suka shigo dashi, ya jawo su zuwa tsakiyar falon, Momy ce taji gabanta ya fad’i duk yanda akayi wani abu ne ya samu Basma dan tasan trolley ta ne, Yaya Ahmad ya zauna ya soma musu bayanin yanda Baba mai gadi ya kawo masa kayan, sannan ya bud’e wasikar ya soma karanta musu, iyaka tashin hankali sun shiga, Abba mik’ewa yayi ya soma safa da marwa, Yaya Ahmad ya gama karantawa ai sai Momy ta fashe da kuka, su Meena ma haka, Ammi ce tayi jarumta tace “innalillahi wa inna ilaihir raji’un, yanzu wannan kayan ta ne kenan, ta tafl da sauran?” Yaya Ahmad yace “eh na bud’e na duba, ya tabbata kayan Basma ce” Key ya ciro, dama fltan da yayi d’azun shine yaje ya d’auko a d’akin sa, ya sanya ya bud‘ejakan, diary d’in ya ciro ya bud’e, shafln farko labarin shigansu jirgi a ranar da suka bar gida a matsayinta na Amaryan Shureym, Yaya Ahmad ya shiga karantawa, ai sai duk suka d’auki salati, lokacin da yazo wurin da ya koma kusa da Safeena a cikin jirgi da kuma kissing d’in da safeena ta mishi, basu k’ara tsinkewa ba sai da ya bud’e d’ayan shafln bayan saukarsu a America, da irin marin da Yaya Shureym yayi mata, kai komai saida ya karanta. Yaya Ahmad ya shiga labarin irin dukan da Yaya Shureym ya fara yiwa Basma, hoton fuskanta data d’auka ya gani ya mik’e ya nunawa Abba, Abba runtse idonsa yayi saboda tsananin b’acin rai.
Yaya Ahmad sai da ya karance musu tas abinda ke cikin diary, sun d’auki kusan awa biyu suna aikin sauraren Yaya Ahmad yana karanta musu, lamarin daya fi d’aga musu hankali shine labarin Safeena, da Basma ta bayar a matsayin wai Safeena matar Shureym ne, ga hotuna nan duk sun gani, a cikin jirgi ta k’arasa labarin yanda ta fito daga gidan Yaya Shureym, ta kulle ma’aikatan gidan a d’akinta.
Abba wani gumi yaji yana saukar masa, Ammi tayi tagumi tana yiwa Allah tasbihi, Momy k0 hawaye ke fita a idonta, ta kasa furta komai sai Addu’a take a ranta, falon yayi shuru sai shasshek’an kukan su Meena ke tashi, hatta Anty Husna kuka take yi, Yaya Naufal hatta shi sai da ya zubda hawaye ganin irin yanda Shureym ya sauyawa Basma fuska saboda duka, Abba ne ya nisa cike da damuwa yace “duk wannan damuwar nine naja, da ban had’a wannan auren ba da duk hakan ba zai faruba, lallai Shureym kaci mutunci na kuma kaci Amanar zumunci, Amma zanyi maganinka, in har na rasa Basma, wlh kaima saika rasa rayuwanka, kai Ahmad maza ka shirya da kai da Naufal, ku kira min mai Martaba yanzu da kuma Ibrahim su zo yanzu, mu tafi American domin muje muga Matar da Shureym ya aje a gidanshi a matsayin Matarsa, na tabbatar Mai martaba bai san da wannan Auren nashi ba” Nan take su Yaya Ahmad suka kira su, suka kuma shaida musu gasunan zasu biyo jirgi, basu sanar musu komai ba, sun dai ce kirane ta tagaggawa daga president.
‘Bayan awa biyu’ Su Mai Martaba sun iso fadar Shugaban k’asa, ba b’ata lokaci ya sanar musu America zasu domin tabbatar da wani lamari, Dady ne yace “to an sanar da Shureym da zuwanmu” Abba yace “bai sani ba kuma ba za’a sanar musu ba, sai dai kawai su ganmu, in munje mun dawo zan sanar muku da komai” Damuwa ne ya ziyarci su Mai Martaba, haka suka kama hanya suka wuce airport, cikin minti sha biyar jirginsu ya d’aga sai K’asar America.
Sun bar su Momy a falon sunyi jugum-jugum jugum ko wanne da abinda yake sak’awa a rai, babban damuwar su da tashin hankalinsu shine ‘ina Basma ta nufa…‘
Hmmm