YAR SHUGABA CHAPTER 23

YAR SHUGABA

CHAPTER 23
‘Etopia’ 
Basma ta sauka a jirgi, sai rarraba ido take ko za ta ga wanda zata iya tambaya, jikinta yayi sanyi ganin tazo garin da bata tab’a zuwa ba, tsoro da fargaba ne ya cika ta, runtse ido tayi ta bud’e tace a fili 
“Hasbunallahu wa ni’imal wakil, laa ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazza zalumin, astagfirullah wa’a tubu ilai” abinda tayi ta maimaitawa kenan a zuciyarta, a hankali ta somajin k’arfin gwiwa da natsuwa, fitowa tayi bakin hanya ta tari taxi, cikin harshen turanci tace “Hotel mai kyau nake so ka kai ni” cikin harshen turanci ya mai da mata da “to shigo mu tafi”. Ya kai ta babban hotel mai kyau, ta biyashi kana ta wuce ciki, kud’in d’aki ta biya, saitaja trolley d’inta, wata daga cikin ma’aikatan Hotel d‘in suka yi mata jagora har d’akin data kama. Wanka tayi ta gabatar da duk Sallolin da ake binta, bata jin zata iya cin abu mai nauyi, telephone ta d’auka ta kira cikin Hotel d’in da a kawo mata coffee da kuma Burger, haka suka kawo mata, ta soma cin Burger taji sam teste d’insa ba dad’i, ajiyewa tayi tasha coffee d’in kawai. Tunanin ya zatayi rayuwa anan take yi, can ta tuno da rayuwarta da Yaya Aryan ta tabbatar da shi ta aura duk haka bazai faru ba, kuma ba zata sha wannan wahalar ba, hawaye ya sauka a kuncinta, tace “ya Yaya Aryan zaiji in yaji labarin na gudu” tunani barkatai tayi kamar zata kunna d’ayan wayarta saita fasa, dan tasan za’a iya nimanta ta layin, cire sim d’in tayi a wayan sai ta adana a cikin wallet d’in ta. Lafiyan gado tabi ta kwanta tana tunanin rayuwa, da haka barci ya d’auke ta. 
‘America“ 
Yaya Shureym sun dawo daga Asibiti, baifi minti 20 da wucewar Basma ba suka dawo, hon yayi amma yaji shuru ba’a bud‘e masa ba, ba gate man a wurin, saukowa yayi ya bud’e da kansa ya koma mota ya shigo da ita, bai damu daya rufe gate d’in ba, waige-waige yayi amma bai ga ma’aikatan gidan ba, tsaki yaja sai suka shiga falo. Suna shiga suka farajin ihu da hayaniya daga cikin falon, bin inda ihun ke fita suka dinga bi har suka isa k‘ofar d’akin Basma, kallon-kallo Shureym da Safeena suka yi suna tunanin su waye a ciki, Shureym ne yayi k’arfin hali ya bud’e k’ofar, arba yayi da mai gadi da sauran ma’aikatan gidan sunyi gwimi sai zaro ido suke yi, cike da mamaki ya shiga tambaya su, nan suka bashi amsa, murmushi mugunta Yaya Shureym yayi ya kalli Safeena yace “kinga aikin shaid’aniyar yarinyar nan ko, wato kwana biyu tayi lamb’o ta natsu kamar ba ita ba, amma yau tasa kai ta fita duk dokar dana sa mata, baisa ta fasa k’etare wa ba, ta musu dubara ta fice, wlh yau inta dawo Ni da ita ne, sai nayi mata dukan da tunda aka 
haifeta ba ayi mata shi ba, kuma yau saina amshi hakk’ina da k’arfln tsiya” Yana gama fad’an haka ya wuce ya bama Safeena wuri, Safeena jikinta yayi sanyi, domin ta fara tsorata da lamarin Shureym akan yanda ya damu da budurcin Basma, kishi ne ya rufeta saita bi bayansa a fusace. 
Masu gadi haka suka fita sum-sum, dan basa jin duk abin da suke cewaba, a cikin Hausa su kayi maganar, sun koma bakin aikinsu. 
Safeena ta cimmasa a cikin falon, ya zauna sai gumi yake yana kwafa yace “Yarinyar nan ni zata rainama wayo, ni bata bani hakk’ina ba taje bama wancan d’an iskan, wai ta yaya zan yarda ba bin maza Basma take yi ba” Safeena ce tace “Wai kai Shureym meyasa ka damu da Basma ne haka? yarinyar da bata sonka batasan 
kana yi ba, plss karabu da ita mana ka huta” cikin tsawa yace”ya isa, ya isa Safeena, wlh kika kuma furta kalman in saki Basma sai na miki abin da baki tunani, banda albarka cin cikin dake jikinki da saina huce haushi na akan ki, kuma in baki sani ba ki sani ina matuk’ar son Basma, son da ban tab’a yiwa wata Mace ba, ba zan yiwa kaina ba, na gaji da danne zuciyana akan Son da nake mata dan kawai in saki farin ciki, tom daga yau na daina b’oyewa ina son Matata sosai”Safeena fashewa tayi da kuka wi-wi, ta kasa ce masa komai, cikin fushi yace “Malama in zaki min shuru kiyi shuru karki k’ara min damuwa” dole ta sassauta kukan, dan tasan halinsa sarai, zai iya mata abin da bata tsammani. 
Su Abba sun shigo k’asar America gari ya soma duhu, basu b’ata lokaci ba motoci suka zo d’aukansu daga gidan shugaban k’asan America. Suna d’aukansu Abba yayi umarnin da su fara zuwa gidan Shureym, in yaso saisu wuce can gidan president su kwana washe gari su wuce Nigeria. Sun isa k‘ofar gate d’in gidan, Abba yace suyi parking a waje su shiga. Ta b’angaren Shureym kuwa suna zaune a falo ransa a b’ace yake, sai duba agogon Hannunsa yake yi har zuwa lokacin Basma bata dawo ba, ya cika yayi mak’il kamar zai fashe dan haushi, ita dai Safeena tayi turus da ciki, tayi tagumi dan yau gaba d’aya 
Shureym ya saurya mata ba wanda ta sani bane, Suna cikin wannan zaman ne ko wanne da abinda yake sak’awa a rai, sallaman Yaya Ahmad ne ya katse musu dukkan tunanin su, a zabure Shureym ya mik’e idonsa tamkar zasu yo k’asa dan tsoro, Yaya Ahmad fuskansa ba yabo ba fallasa ya shigo, su Mai martaba suna biye dashi a baya, ai nan take Shureym yaji tamkar k’asa ya bud’e ya shige ciki, cikinsa ne yayi wani k’ara alaman ya kulle masa, idonsa tamkar zasu yo k’asa ya kalli Safeena wanda itama ta gama tsurewa tana tsaye, dukansu sun gama shugowa falon, sun kafe su Shureym da kallo kowan ne yana nazarin su, atamke fuskokin su yake tamkar anyi musu mutuwa. Mai Martaba ne ya kalli Safeena yace 
“Yarinya ke wacece a gidan nan kuma ina Basma take?” Cikin rawar baki Shureym ya amshe maganar”Em em baf baf Baffa Ku zauna mana a kawo muku ruwa” Mai Martaba ya dakatar da shi yace “Banyi magana da kai ba, ke bani amsan tambayata” cikin sanyin jiki da tsoro tace 
“Ni ma Matar Shureym ce watanmu 8 da aure kenan, anyi bikinmu da wata d’aya akayi aurensa da Basma, kuma Basma tun safe da ta fita har yanzu bata shigo ba, muma zaman Jiran shugowarta muke” 
Cike da tashin hankali Mai Martaba ya kalli su President yace “kunji abinda wannan Yarinya tace kuwa? kai Shureym abinda ta fad’a gaskiya ne?” sun kuyarda kai yayi k‘asa ya kasa cewa komai, gumi ne yake karyo masa, tashin hankali ya shiga, hawaye ne ya fara zarya a kuncinsa ya kasa d’aga idonsa. Mai Martaba yace 
“yanzu Shureym abinda ka aikata mana kenan?” Dady ne ya nisa yace “da kyau Shureym yanzu sai ka fita ka nimo mana Basma mu tafi da ita, shine ran nan harkana iya kawo mana k’aranta, ashe Kaine azzalumi maci amana daka ci Amanarmu” yana gama fad’a president yayi murmushin takaici yace “am Ibrahim Basma bata k’asar nan, a yanzu haka mu kanmu bamu san inda take ba” cikin tashin hankali Dady da Mai Martaba suka ce “what” dama kunsan da haka, wai mai yake faruwa ne?” anan ne Shureym ya soma kuka wiwi yace “Na shiga uku Basma ina kika je, karki min haka, wlh ina son ki dan Allah ki dawo gareni, bazan iya rayuwa babu ke ba” wani wawan mari Yaya Naufal ya sakar masa a kumatu yace 
cikin zafin rai 
“mugu azzalumi maci amana, wlh kayi asaran rayuwa Shureym, ka b’atawa k’anwata rayuwa, ka kwashe dukkan farin cikinta, bak’in cikinka yasa ta tafi tabarmu, yanzu bamu san wani hali take ciki ba, kaci amanar zumunci” hawayen bak’in ciki ne ya zubo a idon Naufal, hakane yasa shi dole yayi shuru, kuka Shureym yake sosai yace “Abba Ku yafe min, na yarda nayi kuskure, amma dan Allah karku raba aurena da Basma, ina sonta sosai dan zan iya mutuwa in aka rabamu, dan Allah Ku nimo min Basma” Yaya Ahmad murmushin yak’e yayi dan takaici yace “Baka yi kuka ba tukunna Shureym, wasan yara kake yi” Abba yace “tunda idonmu ya gane mana komai mu wuce makwancinmu” Dady yace 
“kwarai kuwa, amma Ni fa banga ta barci ba, Basma nake so in san ina ta tafi” Abba yace “karmu damu insha Allah zata dawo cikin k’oshin lafiya, tun d’azu na sanya Commissioner ‘yan sanda Mukhtar ayi binciken airport, dan sanin wata k’asa ta tafi sai mubi bayanta” Yana gama fad’an haka suka fita, sun bar Shureym durk’ushe yana kuka cike da tashin hankali kamar k’ara min yaro, nadama ya rufe shi yana dana sani. Koda ya d’ago ko kallon inda Safeena take baiyi ba, d’akinsa ya wuce ya shiga had’a kayan shi, Allah»Allah yake gari ya waye, yaje office d’insa ya musu sallama ya wuce mahaifansa Nigeria. Safeena ma bata yi k’asa a gwiwa ba wajen had’a kayanta, dan ta tabbata barin su k’asar America yayi, kuma k’afar Shureym k’afarta, koda zai yankata gunduwa-gunduwa ne, sai ta bishi. 
Abba sun isa masaukinsu, suka ci abincin suka huta, su Dady duk suka kira matayensu akan Gobe in Allah ya kaimu su hallara zuwa abuja dukansu, ko wanne ya wuce makwancinsu. Haka suka kwana ko wanne cike da damuwa, yanzu tashin hankalinsu ina Basma ta tafi. ‘Washe gari’ 
Basma tana farkawa ta shirya cikin doguwar rigan atamfa, ta sanya farin hijabi ya kawo mata iya gwiwa, ba dan kwali a kanta da yake hijab d’in mai hula ne, kayanta ta gama had’a su, fitowa tayi daga hotel d’in tana Jan trolley d’in ta, airport ta wuce tayi duk abinda 
ya kamata, saita shige jirgi sai k’asar Saudia, zuciyarta cike da farin ciki domin zata ziyarci d’akin Allah da kuma Masallacin Annabi s.a.w, tasan cewa zata samu farin ciki acan da samuwar dukka nin natsuwa. 
K’asar Monaco’ 
Yaya Aryan tunda gari ya waye yaji gaba d’aya hankalinsa ya koma Nigeria, tunani barkatai ya shiga yi, cikin sauri ya mik’e ya shiga had’a kayansa, yana kammalawa yayi wanka ya shirya cikin Manyan kaya, Shadda ganila ash color ya sanya hula bak‘i da takalmi, tare da sanya bak’in tabarau, yayi matuk’ar kyau, hakanan ya tsinci kansa cikin nishad’i, burinsa bai wuce yaga Ummansa, ya wuce airport sai Nigeria. 
America‘ 
Su Abba sun kamo hanyan Nigeria, Shureym ya tafi office d’insa ya aje musu komai nasu, ya sallame su, sunyi-sunyi ya k’arasa aikinsa amma yak’i dole suka hak’ura, gida ya koma ya kwashi kayansa, Safeena na biye dashi ba um ba um-um a tsakaninsu, sun shiga mota da duk kayansu, shureym ya sallami duk ma’aikatan gidan ya bama wani abokin aikinsa Key d’in gidan, dama gidan na ma’aikatansu ne, airport suka wuce baifl minti talatin da zuwansu ba jirginsu ya d’aga sai Nigeria. 
‘Nigeria” 
Yaya Aryan ya sauka Iafiya, taxi ya shiga ya sauke shi a gida, yana shiga suka gaisa da mai gadi, ciki ya shiga ya wuce d’akinsa, wanka yayi ya sanya k’ananun kaya, kana ya nufl sashin Umma, bata san da dawowansa ba, domin yana so yayi surprising d’inta, yana shiga falo yaga Iya mai aikinta suka gaisa Iya tace “aiko Hajiya bata nan” zama yayi ya kira number Umma ringing biyu ta d‘auka yace “Umma kina ina na dawo ina son in baki mamaki kuma bakya gida, da safen nan ina kika je haka?” murmushi tayi tace Aryan wani irin ka dawo, ba munyi da kai sai nan da wata uku zaka dawo ba, meya dawo da kai yanzu?” dariya yayi yace “Umma hankalina ya dawo gida ne wlh, kewarku ya cikani sosai, shiyasa na dawo, yanzu kina ina ne?” tace “ina gidan shugaban k’asa wurin Khadija” yace Da fatan dai lafiya k0?” 
“lafiya lau, ka k’ara so ka gaishesu mana” 
“To Umma gani nan zuwa” haka ya mik’e ransa bai masa dad’i, yanaji kamar karya je. Khadija ta kira Umma ta sanar mata da abinda ke faruwa, dalilin zuwan Umma kenan da safen domin tayi musu Allah ya kyauta. Yaya Aryan ya isa gidan president, ya same su Umma a part d’in Momy, zama yayi a k’asan kafet, Kansa a sunkuye ya gaishe dasu Ammi, ganin falon cike da mutane ya sashi jin wani iri, sai ya fito Deeja ta biyo shi a baya. Sun zauna a barandan shan iska dake cikin farfajiyan gidan, nan suka k’ara gaisawa suka shiga hiran zumunci, Deeja bata yi gigin gaya masa abinda ke faruwa ba, Umma ce ta fito ta samesu suna zaune cikin barandan, murmushi Umma tayi, farin ciki ne ya mamayeta Aryan ya dawo da walwalansa, Addu’a tayi Allah ya bashi mata ta gari. K’arasawa tayi wurin tace “Deeja ni zan tafi in Ahmad ya dawo ki gaishe shi” Deeja ta kwab’e fuska kamarza tayi kuka tace “kai Umma baki dad’e ba fa, kuma da kinjira sun kusa k’ara sowa ma” murmushi tayi tace “haba Deeja baki ganin Yayanki ya dawo ne, so nake inje in had’a masa abinci dan nasan da wuya inya karya ma” Murmushin jin dad’i Yaya Aryan yayi yace 
“kinsan kuwa Umma nayi missing d‘in Abinci ki, kuma akwai yunwa a tare dani, ki tafl kawai nima ina bisa hanya” dariya tayi tace “yauwa Aryan saika tawo” nan tayi sallama da Deeja ta wuce ta shiga mota driver ya jata sai gida. 
Aryan suna zaune a wurin Yace 
Deeja lafiya naga gidan naku da taron mutane?” murmushi yak’e tayi tace 
“lafiya lau, president ne yayi umarni da duk a taru anan, mutanen kano da Kaduna duk sunzo, yanzu jiran isowarsu muke daga America” yace “to Allah yasa lafia, Nima ina ganin bari na gudu ba zan iyajiran su dawo ba,zuwa gobe in Allah ya kaimu zanzo na gaishesu” bai rufe baki ba, motoci suka fara shigowa cikin haraban 
gidan, Deeja tace ‘ “laaa kagama sun dawo ma muna zancen su” murmushi kawai yayi baice komai ba, yana kallon motocin da suke shigowa, da sauri ya mik’e lokacin yaga su Yaya Ahmad sun fito ya isa wurin yana dariya, suka kama hannun juna cike da farin ciki a fuskokinsu Yaya Ahmad yace “Aryan saukan yaushe?” cike da dariya yace “yau na sauka” 
to kai da mu kayi waya kace sai nan da wata uku zaka dawo” murmushi yayi yace 
“wlh naji hankali na yayo gida ne burina in ganni a Nigeria” gaban yaya Ahmad ne ya fad’i amma saiya dake, ya mayar masa da murmushi yace ‘lallai fa kace kana kewarmu” “kwarai kuwa nayi” 
Nan ya wuce wurin President ya risina zai gaisheshi,Abba ya shafa kansa, ya kama hannun Aryan suka wuce babban falonsa. 
Falon ya cika da dangi, Dady, Abba, Mai Martaba, da duk iyalensu, Ammi, Mami,
Momy, Umma, Hajiya Murja, Duk suka gaisa, suna cikin wannan zaman ne sai ga sallaman Yaya Shureym a birkice ya shigo, Safeena na biye dashi a bayansa, Mami na ganinsu gabanta ya fad’i damm, a razane ta mik’e tace Shureym lafiya na ganka haka wurjanjan” zuwa yayi ya rungumeta ya soma kuka wiwi, duk mamaki ya cika mutanan falon banda su Abba dasu suka san komai Yaya Aryan yana gefen Yaya Ahmad suna hira k’asa-k‘asa, Dady ne yayi gyaran murya yace “Kai Shureym samu wuri ka zauna, da fatan duk kun san musabbabin taruwan mu anan, akan Shureym da Basma” ai yana furta Basma Yaya Aryan ya d’ago fuskansa gabansa ne ya shiga dukan uku-uku, mutanan falon yabi da kallo amma baiga Basma ba, dama tun d’azu yake raba ido ko zai ganta, amma shuru ba alamunta, kamar zai tambayi Deeja amma saiya fasa. 
Abba yasa Yaya Ahmad ya karanta lettern da Basma ta rubuta da kuma diary d’inta, nan ya shiga karantawa iyayen sai salati suke yi dama su Mai Martaba basu san komai ba sun daije America sunga Shureym da mata, Mai Martaba jikinsa yayi sanyi, yace a ransa “lallai shureym yaci amanansa” k’arin tashin hankalinsa yanda Shureym ya maida Basma tamkar baiwansa. Yaya Ahmad ya gama karantawa,Aryan gumi ya gama jik’ashi, kamar shine yayi karatun, falon ne yayi shuru, Ummi tace “ai biri yayi kama da Mutum, kazo ka kawo k’aranta harda yiwa Yarinya k’azafi,nidama ban yarda ba, ashe kai ne ke cutar da ita” Mai Martaba yace 
“ka kyauta Shureym, yanzu amanarda muka baka kenan, kaci amanata da zumuncinmu ban tab’a tsammanin haka daga gareka ba” cikin kuka Shureym yace 
“Baffana ku yafe min sharrin shaid’an ne” Mai Martaba ya katse shi yace “yi min shuru mutumin banza kawai, yanzu ya akai kayi aure har ban sani ba, wasu iyaye ne 
ka samu suka jagoranci auren?” 
Cikin tashin hankali Shureym ya basu labarin yanda aka yi aurensa da safeena,jikin kowa ne yayi sanyi jin cewa Mami itace ta goya masa baya wajen yin aure, Ammi cikin fad‘a tace “ai dama Hajiya Sa’a na dad’e da sanin Yayana bai yi sa’an mata ba, kin cika kyakkyawar makira mai raba kan zumunci, ina ce kece kika matsa kika hura wuta dan ganin Shureym ya auri Basma, ashe da mugun nufi a ranki, sannan har kina goyawa d’anki baya ya auri wata, tun farko da ya nuna baya son Basma me yasa zaki matsa ya aure ta, da munsan da haka wlh daba zamu tab’a bari ya auri Basma ba” 
Mami ne cikin tsiwa da makirci tace “ya ishe ki Hajiya Fatima, ba zan d’auki cin fuska ba” Mai Martaba ne ya daka mata tsawa yace Mutumiyar banza, dama duk cikin gidana kece mai bani matsala, kuma kisani kamar yanda kika had’a auren Shureym da wancen Yarinya to tamkar kin datse igiyar aurenki ne, saboda kinsan ba na son zama da munafuki mara tsoron Allah” Afirgice Mami tace cikin kuka “haba Mai Martaba tuba nake, dan Allah karka min haka, nasan nayi kuskure bazan kuma haka ba, ka k’ara hak’uri dani, dan Allah ka gafarta min zan gyara halina” 
Saita kai kallonta ga Shureym ta cigaba da cewa “Kai Shureym maza ka saki Safeena don Mai Martaba ya maida aurena” cikin fad’a Mai Martaba yace “karka kuskura ka furta saki akanta domin wlh saina sab’a maka, aure dai ka riga kayi, sai ka san inda zaka aje musu Yarinya kuma ba dai gidana ba, sannan in kika sanya Shureym ya saki Yarinyan mutane wlh saina tsinke duk igiyar aurenmu dake wanda yayi saura” 
Abba ne ya katse shi da cewa “haba Mai Martaba, in rai ya b’aci hankali karya gushe, dan Allah ka maida aurenka da Hajia Sa’a ka kuma yafewa shureym, kuskure dai an riga anyi, sannan ni dai zan tsare Shureym har sai anga Basma, dan alkawari na d’auka akan haka” Dady yace “ni dai duk kowa yayi hak‘uri a sulhunta, aure dai ya riga yayi, dan haka sai mu jira dawo war Basma, in tace zata zauna da mijinta shikenan, in kuma tace bazata zauna dashi ba, to ba mai yi mata dole” 
Kuka Momy take wiwi, tace “ni dai Ku aje duk wannan bayanin, ku tashi ku nimo min Basma, ba zan jure rashinta ba” Kuka Shureym yake tare da sambatu “Dan Allah Basma ki dawo gareni wlhi ina son ki, bazan jure rashinki ba, Basma nayi miki 
kuskure ki yafemin” Su Meena ne suke hararanshi shike da jin haushinsa, Yaya Adam ya daka masa tsawa, 
“Dalla yi mana shuru mutumin banza, haka kawai ka tada zaune tsaye, ana zaman lafiya, duk abinda ka dauko insha Allah kanka zai tsaya, kuma babu abinda zai tab’a zumuncinmu” Yaya Aryan ya mik’e tsaye fuskansa a tamke cike da damuwa, baicewa kowa komai ba, ya nima fita daga falon, Yaya Ahmad yace “Aryan ina zaka ka tsaya mana” waigowa yayi idonsa na fidda kwalla, ya bud’e baki zaiyi magana, sai kawai yaji wani abu ya tokare masa k’irjinsa,jiri ne ya dibeshi sai ya fad’i k’asa da k’arfi, da gudu Yaya Ahmad ya isa wurinsa, Deeja ce ta saki wani k’ara tace 
“Yaya Aryannnn” cike da firgici duk suka isa wurinsa, cikin tashin hankali suka wuce dashi Asibiti… 
Hmmm nanfa ake yinta

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE