YAR SHUGABA CHAPTER 25

YAR SHUGABA 
CHAPTER 25
A hankali ya juyo ya fuskace ta, ido cikin ido suke kallon juna harna tsawon minti biyar, Yaya Aryan ya katse kallo tare da sauke ajiyar zuciya a hankali, fuskansa babu yabo ba fallasa, bai furta mata komai ba ya juya zai cigaba da tafia, cikin sauri ta sha gabansa tace “haba Yaya Aryan ya zaka wuce baka ce min komai ba, yanzu na sauka ajirgi dawo wata kenan, ko gida banje ba naji sha’awar zuwa wurin nan, zuciyata ce ta jawoni ashe kai ne zan gani, dan Allah kace wani abu ko baka farin ciki da gani nane” saita k’arashe maganar cikin shagwab’a. Kallonta yayi sama da k’asa sai ya yatsine fuska yace “ke wacece ban ganeki ba fa?” damm Basma taji zuciyarta ta buga, tace cikin tsoro da sark’ewar murya “Haba Yaya Aryan nice baka gane ba, Basma ce fa” ya d’aure fuska yace 
“Malama kiyi hak’uri ni ban ganeki ba, zaki iya tafiya” ai Basma cikinta ne taji ya murda, tayi sauri ta dafe tana ambaton Allah, kuka ta b’arke dashi mai k’arfl, cikin kuka tace “haba Yaya Aryan dan Allah karka azabtar da zuciyata, ya zaka ce baka gane ni ba” juyawa yayi ya cigaba da tafiya bai bata amsa , sakamakon hawaye da ya cika masa ido, yayi gaba abinsa ko waiwayanta baiyi ba. Cikin kid’ima Basma ta bar gurun da gudu, mutane sai kallonta suke, mota ta shiga tana kuka, da kyar ta iya lallashin kanta tace wa driver ya wuce da ita, duk abinda take yi akan idon Yaya Aryan. Da sauri ya shiga mota yabi bayansu domin ya tabbatar da gida zata wuce, karta kuma wucewa wani wurin, a hankali yake bin bayansu, hawaye nabin idonsa karatun Alqur’ani ya sanya yana bin karatun a hankali. Basma abin duniya ya dameta, gaba d’aya farin cikin data dawo dashi ya gushe, a haka suka isa gida ta sauka tabiya mai taxi, trolley taja tun daga bakin gate security suka fara mamakin ganinta, gaisheta suke tana d’aga musu hannu, Yaya Aryan tunda ya tabbatar gida ta shiga, saiya wuce gida cike da damuwa, zancen zuci ya shiga yi “Nasan yau na b’atawa Basma rai, Amman hakan da nayi shine dai-dai, dan bai kamata na nuna wani abu ba saboda, da auren wani a kanki Basma”. ‘ Ma’aikatan gidan suka rugo da gudu suna k’ok’arin amsar trolley ta, d’aga musu hannu tayi sai duk suka matsa, ta cigaba da tafiya jiki a mace, ta isa tsakiyar gidan saita tsaya k’am tana kallon wani part ya kamata ta fara zuwa, tana tsaye tana nazari da tunanin ina zata nufa, saiga Yaya Ahmad sunjero da Khadija tana rik’e da Walid a hannunta, tsayawa tsak suka yi suna kallon Basma daga nesa, Yaya Ahmad ya murza idonsa ya bud’e su sosai danya tabbatar da ita dince, Deeja tace 
“Yaya Ahmad ko kaga abinda na gani?” cike da mamaki yace “nagani Deeja, nima naso tambayarki, gani nake kamargizo
 take min” da sassarfa Yaya Ahmad ya isa wurinta, tana ganinshi ta saki kuka mai cin rai ta fad’ajikinsa, Yaya Ahmad ya rungumeta cike da farin ciki, ya dago fuskarta yace “Basma da gaske kece kin dawo garemu, dan Allah karka sake tamya ki barmu” d’agata yayi sama yayi juyi da itace sai ya direta, hannunta ya kama suka wuce part d’in Momy, Deeja rufa musu baya tayi cike da murna. Suna shiga part d‘in Momy suna tare da Ammi, sai Leema da take zaune tana bama Walida nono, da gudu Yaya Ahmad ya shiga yana jan Basma saida suka je gaban Momy suka tsaya suna haki, yace cikin murna “Momy ga Basmanki ta dawo” Momy mik’ewa tayi ta rungumeta sai ta shiga kukan farin ciki, ai cikin k’ank’anin lokaci kowa na gidan ya hallara falon Momy dan ganin Basma, murna da farin ciki ba’a magana, tunda daga bakin gate zaka jiyo hayaniyarsu. Anty Husnah a sittin ta tuko motanta tazo gidan, part d’in Momy ta nufa, aka cigaba da murna da ita, sun kira dangi a waya an sanar musu da abin farin ciki, Abba baya k’asar, yana k’asar Russia. Yaya Ahmad ne ya kirashi ya sanar mishi da abin farin ciki, Abba yayi murna yace ya bama Basma wayar suyi magana, Basma ta amsa wayar suka gaisa, Abba yace “Basmata da fatan kin dawo laflya babu wata Matsala k0?” murmushi tayi tace Abbana lafiya lau” yace Basma Allah ya miki albarka, insha Allah nan da mako guda zan dawo, zan shirya miki kaya taccen liyafa dan murnan dawowarki, bana so ki fita ko nan da k’ofar gate, kuma ki gayawa Ahmad duk abinda kike so ya siya miki, in ma kina son fita Ahmad ya kaiki inda kike so ko Naufal” cikinjin dad’i tace “to Abbana Allah ya dawo mana da kai lafiya” ya amsa da 
Amin” saita bama Yaya Ahmad wayar, Abba yace ya sanya shi a hand free, ya sanya shi kowa na saurare, Abba yace 
“jan kunne zanyi wa kowa, kar a kuskura a b’atawa Basma rai a ririta min ita har na dawo, duk wanda yayi k’ok‘arin b’ata mata rai jikinsa zai gaya masa, kuma inna dawo saina sab’awa mutum” duka suka kwashe da dariya, daga nan saiya kashe wayan. 
Basma bata samu kanta ba sai dare, kowa so yake ya zauna da ita suyi hira, hakan ya 
sanyata farin ciki sosai, sai dai a k’asan zuciyarta tana cike da damuwa akan abinda yaya Aryan ya mata. Bayan tayi wanka tayi shirin barci ta kwanta akan lallausan gadonta, Kakace ta shigo tace 
“tashi zo muje sashi na kiyi barcin acan” Basma cikin shagwab’a tace “haba Kaka, wlh na gaji ki barni nayi barci na anan” 
“naki in barki d‘in, tashi maza mu tafi” haka ta mik’e tana zunb’ura baki suka fito, suka yiwa Momy sallama suka wuce part d‘in Kaka Ma’u. Suna shiga ta wuce d’akin Kaka ta fad’a gadonta, Kaka tace “ki min a hankali karki karya min gado fa, dan mijinki ba iya biya zaiyi ba” Basma ta b’ata rai tace “ni ance miki ina da miji ne?” dariya Kaka tayi ta zauna gefen gadon, tajawota ta d’aura kanta bisa cinyarta tace 
“Basma naji duk abinda ya faru, tun farko da sunji shawarata da basu had’a auren nan ba tunda baki so, yanzu gaya min kina so ki koma d‘akin mijinki ko a raba auren?” 
Hawaye ne ya gangaro mata a ido a ranta tace “wanda nake so ma yace bai sanni ba, to meye amfanin raba aure” Kaka ta katseta tace “Ki bani amsa kinyi shuru kina kuka, babu fa 
mai miki dole akan zamanki dashi, wannan tsakani na dake ne” Basma ta nisa tare da share hawayenta tace “Kaka ni dama na fad’a abinda ke faruwa ne tsakanina da Yaya Shureym saboda kowa yasan rayuwar da nake a gidansa, bawai dan a raba auren mu ba, kuma kaka Yaya Shureym sharri zina yamin shiyasa nima na fasa komai, dan haka zaman aurena yana hannunku sai abinda kuka ce” Tana gama fad’an haka ta rushe da kuka, ta d’auke kanta akan cinyar Kaka, ta mirgina ta gyara kwanciya tana shasshekan kuka, Kaka tayi murmushi tace ‘Ni kam Basma banga abin kuka anan ba, sannan ina baki shawara kiyi Addu’a da niman zab’in Allah akan zamanki da Shureym”. Basma bata tanka mata ba ta ta share hawayenta tace a ranta “ai kullun cikin Addu’a nake, maflta kawai Allah zai fidda min” Da tunani har barkatai barci ya d’auketa. ‘Washe gari’ 
Basma na dinning tana karyawa sai ga sallaman Yaya Shureym ya shigo, d’aure fuska tayi ko kallon inda yake bata yi ba, harya k’araso kusa da ita ya ja kujera ya zauna yana kallonta kamar sabon maye, sai had’iye yawu yake, Basma ta k’ara mishi kyau ta d’anyi k’iba kamar ba Basmanshi ba, cikin sanyin murya yace “Basma ina kwana kin dawo lafiya?” d’ago kai tayi ta kalleshi kana ta cigaba da cin abincin ta, bata furta masa komai ba, cije leb’ensa yayi yace “Basma dan Allah ki yafemin da duk abinda na miki, dan Allah ki k’ara bani dama domin na gyara kuskuren dana aikata miki, Basma wlh ina son ki karki yarda a raba auren mu plss my baby love” Hararenshi tayi ta mik’e tareda jan tsaki ta bar wurin, cikin zafln nama yabi bayanta ya kama mata hannu, cikin b’acin rai ta juyo ta wanke shi da mari tace cikin fad’a “karka kuskura k’azamin hannunka ya kuma tab’a fatarjikina, na tsaneka Yaya Shureym bana son ganinka” tana gama fad‘an haka tayi gaba abinta tana juya duk sassan jikinta. Duk wannan abin ya faru akan idon Kaka Ma’u, yayi k’okarin bin bayanta, Kaka ta dakatar dashi tace “kai Shureym bani son shirme, kasan dai Basma ba zata saurareka ba yanzu, dan haka ka bari ta huce in dai kana so ta koma gidanka” Zuwa yayi ya durk’usa gaban Kaka yace yana hawaye “yace Hajiya dan Allah ki taimaka min kisa baki Basma ta koma d’akinta, nayi alkhawari zan gyara kuskurena” Kaka ta dafa kansa tace “kaje zanyi k’ok’ari akai, sannan kayi Addu’a sosai akan in komawarta alkhairi ne Allah ya tabbatar, in kuma akasin hakane to ya zab’a muku mafi alkhairi” haka Shureym ya fita zuciyarsa na masa zugi da radad’i akan Basma. Basma, Meena, Leema, Deeja suna zaune a d‘akin Deeja gaba d’aya hira suke yi na yaushe rabo, Meena tace “Basma baki bamu labarin ina kikaje ba” Basma tayi dariya ta soma basu labarin zuwanta k’asar Etopia da kuma zuwanta Makka, harta k’are basu labarin, Leema tace “lallai kinyi k’ok‘ari, da fatan dai kinyi Addu’a Allah ya raba auren ki da Shureym a makka, dan wlh bana fatan ki cigaba da zaman aure dashi” Deeja tace “in kuma shine alkhairin fa?” Meena ta harareta tace “haba Deeja kamar baki taya Yayanki Aryan kishi, kinsan dai shine muradin Basma” Basma ta ya mutse fuska tace “waye kuma Aryan?” a razane duk suka juyo suna kallonta, ta cigaba da cewa, “aini ba Aryan a duniyata yanzu, dan ban sanshi bama” Leema ta kwashe da dariya tace “wlh karya kike yi Malama, ga sonsa ina gani a cikin kwayar idonki kina wani zancen baki sanshi ba” Deeja murmushi tayi tace “Antyna me Yayana ya mikine haka?” Hararansu tayi tace “ban sani ba, kawai dai ban gane wanda kuke magana bane” murmushi suka yi Deeja tace a ranta “yanzu haka akwai abinda ya mata, toma ina suka had’u da har za suyi fad’a? lallai dai akwai wani abu a k’asa” nan suka cigaba da hira Basma dai ita kad’ai tasan ya takeji a ranta game da Yaya Aryan, har yau sonsa bai ragu ba a zuciyarta, k’aruwa ma yake yi, tana azabtar da zuciyarta a kan dole sai ta daina tunanin shi, amma ta gaza yin haka. 
‘Baya kwana Biyar’ 
Yau kwana Biyar kenan da dawowar Basma, gida ya cika da ‘Yan Uwa ana hidimar sunan Meena, yarinya taci sunan Fatima sunan Ammi, suna kiranta da Najwah. Da yamma aka shirya waliman suna, family an hallara gaba d’aya a cikin gidan daga can baya, an sanya tempol da fararen kujeru ga kuma table a tsakiya, an yiwa wurin decoration, iyaye Mata da yaransu Maza da Mata sun hallara a wurin, iyayensu maza ne basa wurin, hatta Umma tazo da Yaya Aryan. Sunsha kwalliya sai k’amshin turaren ke tashi, Basma tasha kwalliya riga da siket ta sanya na leshi pink color mai fulawa fari da bak’i, d’inkin ya amshi jikinta, bata sanya gyale ba, tasha d’auri tamkar gwagwaro, sai k’amshi ke tashi a jikinta, ta sanya takalmi mai tsini masu igiya, taku take d’as-d’as kamar wata hawainiya, haka ta isa gurin ta rik’a bin ko wani b’angare tana gaidasu, mai jawabi ya soma jawabi nan fa aka soma ciye-ciye ga sauti na tashi, Basma ce ta fara bud’e wurin da rawa cike da salo dan birge masu kallo, duk wannan abinda take yi bata san Aryan na gun ba. 
Shureym ya tashi ya fara mata mannin kud’i nan fa wuri ya kaure da ihu, ganin Shureym a bayanta yana rawa sai tajuyo ta galla masa harara tayi tsaki ta fice daga wurin rawan, can baya taje ta samu wuri ta zauna tana maida numfashi, wayarta ta ciro ta shiga bugawa kanta salfee, d’ago kan da zata yi ta waiga gefenta, sai karaf suka yi ido hud’u da Yaya Aryan… 
Hmm 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE