YAR SHUGABA CHAPTER 26
YAR SHUGABA
CHAPTER 26
Murtuke fuska tayi ta galla masa harara sai ta kauda kai, Yaya Aryan yayi murmushi ya kura mata ido, gaba d’ayaji tayi ta takura a gurin, mik’ewa tayi zata bar wurin, garin sauri takalminta ya turgud‘e saura kiris ta fad’i, da sauri Yaya Aryan yace “subhanallah” juyowa tayi idonta ya ciko da kwalla ta kalle shi tana ya mutse fuska alama taji zafi murmushi ya sakar mata, murguda masa baki tayi ta wuce,wannan karan murmushin da yayi har fararan hak’oransa saida suka bayyana. Anyi taro an washe lafiya kowa yaje gida lafiya.
Basma tana zaune a d’akin Momy suna hira da Momy, sai ga Yaya Shureym ya shigo,ya risina ya gaida Momy kana ya zauna, Momy ta mik’e ta basu guri, shuru suka yi na mintuna, Yaya Shureym yace
“Basma dan Allah ya kamata ki tausaya min, ina son ki son da bana yiwa kai na, ki yafe min my Basma” fuskarta tamau tace
“ina Anty Safeena?” tambayan yazo mishi a bazata, har yakan manta da yana da Safeena, cikin sanyinjiki ya bata labarin barinta gidan da komai daya faru, murmushi tayi ta mik’e ta isa gabansa tace
ga wayata samin number ta” jiki na rawa ya amsa ya sanya mata sai ya mik’a mata wayan, komawa tayi ta zauna, ta shiga kiran number, bugu d’aya ta d’auka, suka gaisa, Basma tace “nasan baki gane ni ba, Basma ce, na dawo kwana Biyar kenan daya wuce, ina so gobe in Allah ya kaimu ki biyo jirgi kizo Abuja” Cikin farin cikin da borin kunya tace “laaa Basma kin dawo, Alhamdulillahi, sai dai ba kud’i a wurina haryau Shureym bai zo yaga babynmu ba” ta k’arasa maganar cikin damuwa, Basma ta nisa tace “ki turomin number account d’inki zan miki transfer, sai ki siya abin da kike buk’ata kishirya a nutse, ko zuwa jibi sai kizo cikin farin ciki Safeena tace”nagode Basma Allah ya saka da alkhairi, dan Allah ki yafemin duk abinda na miki, ni kunyarki ma nakeji” Basma tayi murmushi tace karki damu komai ya wuce ai” nan suka yi sallama Safeena jikinta yayi sanyi. Shureym duk yana sauraren maganar da suka yi, bayan ta aje wayarya d’ago cikin fuskan tausayi yace “Basma dan Allah ki saurare ni, ki tausaya min plss” d’aura kafa tayi d’aya kan d’aya tace
“wai nace kamin wani laifi ne? aure ne dai nace ba nayi, ka fita sabgata pls”
Tana gama fad’an haka ta mik‘e, da sauri ya mik’e ya isa gabanta ya tsaya, kallonshi tayi sama da k’asa ta kauda kai, hawaye ne ya cika idonsa ya soma kwaranya a kuncinsa, zuciyarta ne ya karaya cikin sanyin murya tace “Yaya Shureym ni banga abin damuwa anan ba, tun farko kace baka sona Safeena kake so, shiyasa na sanya tazo ka d’auki matarka kutafl, Yaya Shureym jiki nafa kake so bani ba, dan haka nayi Alwashin baza ka samu yanda kake so ba” tana kaiwa nan ta wuce ta bashi guri. Zama yayi dirshen a kan tiles, kansa ya kama yana fidda hawaye sosai, Momy ce ta fito ta k’asaro wurinshi ta zauna tace “Shureym kayi hak’uri in her komawar Basma d’akinka Alkhairi ne zata koma, ka barwa Allah komai” da sanyin jiki ya yiwa Momy godiya ya mik’e jiki ba kwari ya tafl. ‘Bayan kwana biyu‘
Safeena ta zo, ta sauka a gidan amma ta rasa wurin wa zata, saboda tasan babu wanda zai amsheta, kiran Basma ta yi a waya ta sanar mata da zuwanta, bayan minti biyar Basma ta fito cike da fara’a ta amsheta, part d’in Momy ta wuce da ita ta sauketa a d”akinta, masu aiki tasa suka kawo mata abinci da kayan motsa baki, zama tayi suka k’ara gaisawa, Basma ta d’auki babyn tayi kama da Yaya Shureym, Yarinyan ta kwantawa Basma a rai taji dama nata ne, hira suka yi sosai Safeena ta nima gafararta da ta yafe mata akan abinda ya faru, Basma ta yafe mata. Wanka Safeena tayi ta sauya kaya, Basma ta sanyata tayi kwalliya tayi kyau sosai, fitowa suka yi ta kaita d’akin Momy suka gaisa, suka je d’akin Ammi nan ma suka gaisa ba yabo ba fallasa, duk suka gaisa da mutanan gidan, daga k’arshe ta kaita d’akin da Shureym yake ta fito ta basu wuri. Safeena tana ganin Shureym, sai farin cikin ya rufeta, duk haushin data d’auka dashi nan take ta huce, Shureym ya amshi babynsu yana kallonta cike da soyayya, anan suka zauna suka sha hira, shi kanshi Shureym yayi missing Safeena, nan suka sha soyayya kamar sabbin ma‘aurata, Shureym yace “Safeena ki taya ni rok’on Basma akan ta koma d’akinta” murmushi tayi tace “ba ruwana kunfl kusa, yanda Basma ta sauko ta nuna min babu komai ta yafemin, karka zo ka had’ani da ita ba ruwana” jikinsa ne ya kuma yin sanyi. ‘Washe gari’ Abba ya dawo, gida ya cika da farin ciki, Basma na mak’ale da Abba shi kuma sai ririta ta yake yi, bayan komai ya lafa Abba yayi kiran Family Meeting a washe gari, sannan kuma da murnan taron dawowar Basma, cikin k’ank’anin lokaci aka shiga shirye-shirye. Washe gari musamman aka kira mai kunshi ta zane duk matan gidan, Basma tasha kunshi tayi kyau, musamman suka kira masu makeup suka zo gida suka yiwa Matan gidan hatta iyayensu, tun k’arfe d’aya gida ya gama cika da Family, kowa nata hada-hada, masu abinci musamman aka kira su daga hotel suka kawo abinci kala-kala, duk cinka sai dai ka hak’ura ka barshi. Da k’arfe biyu, Abba suna tare da Dady, Mai Martaba, da kuma iyayensu Mata da Kaka Ma’u, sai Yaya Ahmad da Yaya Adam, sai Yaya Naufal da Yaya Jamal, Yaya Shureym shima yana gun, Basma ce kad‘ai sai Anty Husnah. Aka bud’e taro da Addu’a, Dady yayi Bisimillah yace “Yau dai gamu dukanmu mun had’u, ga kuma Shureym da Basma, zamu tattauna akan zancen aurensu, yanzu mu iyaye me muka ga ya dace akan wannan lamarin, meye shawaranmu akai?” Ummi ce ta fara magana Mahaifiyar Meena tace “Ni ina ganin ayi sulhu Basma ta koma d’akinta” ai gaban Basma dam taji ya buga amma saita dake, Shureym wani murmushi ya saki a ransa wanda har sai da ya bayyana a fuskansa, Mami ma tace “Gaskiya ne ayi hak’uri ayi sulhu Basma ta koma d’akinta” Ammi tayi tsaraf tace “Ni ban amince ba” Momy saboda kawaici bata furta komai ba, Maman Leema Hajiya Murja tace “ina bayanki Ammi nima ban amince ta koma ba, yanzu yayi mata haka nan gaba ya kenan?” Dady ne yace “bafa jayayya nace muyi ba, magana ta fahimta nace muyi” Mai Martaba yayi gyaran murya yace “kwarai kuwa, ni anawa ganin a tambayi Basma inta amince ta koma d’akinta shikenan” Abba yace “gaskiya wannan itace magana, Basma inta amince zata koma shikenan, in kuma bata amince ba Shureym ya sauwak’e mata, daga
yanzu ba zan kuma titasta mata ba” Dady yace “Hajiya Kaka baki ce komai ba?“ murmushi tayi tace “ina jinku ‘ya’yan nan, in naji ba dai-dai ba zanyi magana, yanzu dai a tambayi Basma inta amince zata koma” Dady ya kai dubansa ga Basma yace “Basma kinji abin da muke magana akai shin zaki koma d’akin Mijinki Shureym ko kuwa ya sauwak’e miki?” Ta d’auki kusan minti biyu kaf’ln ta soma magana tace “Dady Ni banda magana sai hukuncin da kuka yanke, nasan tabbas ba zaku cutar dani ba” saita k’arasa maganar tana kuka. Shuru ne ya d’auki falon na tsayin minti biyu,Yaya Ahmad yace “Basma karki cuci kanki fa, ki fad’i abin da ranki ke so” Yaya Naufal yace “kai ma kasan zab’inta ai, baso take ta koma ba, kuma muma bama so ta koma wallahi” Anty Husnah itama tace “kwarai kuwa nima ban goyi baya ta koma ba, kawai ya maida mana Yarinya sai kace baiwarsa” Yaya Adam ne yace “muyi hak‘uri, Shureym dai yayi kuskure mu taru mu yafe masa” Yaya Jamal yace “hakane kuskure kam an riga anyi shi, sai dai a koke gaba” Dady yace “ya isa haka, ke Basma ki fad’i abin da ranki ke so kar gaba kizo ki kuka damu” Mai Martaba yace “ina ganin mu basu sati guda su sasanta kansu, in sunk’i sasantawa, sai mu mu d’auki mataki mu kuma zama akai” Nan suka amince da wannan shawaran ta Mai Martaba, Shureym idonsa ya ciko da kwalla bakinsa na rawa yace “Abba tunda Basma ta baku zab’i, dan Allah ku bani Matata, wlh ina sonta kuma na gane kuskure na” Dady yayi murmushin su na manya yace “Shureym kenan, kaje ka sasanta da Matarka kawai, in kun dai-daita shikenan, saika d’auketa Ku tafi”. Basma ce ta gyara zamanta cikin sanyin murya tace “Dady ina son inyi magana” Dady yace “an baki dama” tace “Dama akan zancen Safeena ce matar Yaya Shureym, dan Allah kuyi hak‘uri ku karb’eta a matsayin sirikarku, kuskurene sun riga sunyi, ku yafe musu itama ta shigo cikin dangi, kunga yanzu sun fara tara zuri’a, bamu san iya adadin zuri’an dake tsakanin su ba, kuskure dai sunyi dan Allah Ku yafe musu, yanzu na kirata tazo dan ku gana da ita” Shureym wani soyayyar Basma yaji yana fusganshi, farin cikin ya lullub’eshi, Dady ya nisa yace “da kyau d’iyar albarka, kinyi tunani mai kyau, kai Shureym kira mana ita tazo nan” nan take Shureym ya kira Safeena, cikin minti goma sai gata ta shiga falon kanta a sun kuye, zama tayi gefen Basma, ta gaishe su, nan suka cigaba da tattaunawa, daga bisani Safeena da Yaya Shureym suka nima gafaransu, nan take suka yafe musu. Suka d’add’auki yarinyar data haifa suka sanya mata albarka, sai a sannan Mami ta nima gafarar Basma akan irin abinda tayi mata, Basma ta yafe mata, nan taro ya watse cike da farin ciki, Mazan suka tafi masallaci dan yin sallan La’asar, matan ma suka wuce b’angarensu dan gabatar da nasu Sallah.
k’arfe Hud’u kuma su zauna wurin liyafan waliman dawowar Basma, wanda Abba ya shirya mata. .
Hmm ko su basma zasu sasanta nanda sati guda muje dai zuwa muji ya zata kaya