YAR SHUGABA CHAPTER 29

YAR SHUGABA 
CHAPTER 29
Yaya Aryan d’aure fuska yayi cikin sigar wasa, itama ta d’aure fuska kamar za tayi kuka, tace bana buk’atar sanin ko ita wacece, ga wayata kayi amfani da shi in kana buk’atan kiran su Umma, dan nima ina da contact d‘in kowa har nasu Kaka Malam, Wayanka kuma sai na d’auki mataki akanta sannan zan dawo maka da shi” Mamakinta ne ya bayyana k’arara a fuskansa, bai yi tsammanin abun har zai kai haka ba, cikin d‘aure fuska yace”Malama me kike nufi ne? yanzu fa kika gama ce min baki sona, to meye ne dan wacce take sona ta kira ni, kawai ki bani wayata ki rik‘e taki, dan ban yarda da wannan salon naki ba” Ya tsine fuska tayi tace “Yaya Aryan wallahi bazan baka wayan nan ba yanzu” tana gama fad‘a ta aje masa wayarta a gefen wani kujera 
“gashinan in ka tashi taWa sai ka d’auka” ta wuce fuuu cikin fushi kamar guguwa. Dariyan da yake dannewa ne ya kwace masa, ya shiga dariya harda rik’e ciki, Basma ta kara k’uluwa, Tafiya take ranta na suya kishi ya gama rufe mata ido, hawaye ke flita a idonta tana sharewa, a ranta tace “wai wani irin So nake wa Yaya Aryan ne haka? har da zan kasa controlling kaina”. Haka ta isa part d’in Ammi, sashinta ta wuce ta kulle kanta, kiran wani security tayi a waya tace “zan turo maka wata number yanzu kaje MTN office a bincika min waye mai number, kuma da cikakken address d’in mai number”. Cikin girgamawa ya amsa da to sai ta katse wayan. Ta jawo wayan Yaya Aryan, ta d’auki numban Jidda ta turawa security d’in. Yaya Aryan ya d’auka wayan Basma cike da nishad’i,ji yayi duniyan yayi masa dad’i saboda yanda ya gano babu abinda ya rage Sonsa a zuciyar Basma. Ammi na daga window d’akinta dake sama duk tana hangen abinda ya faru tsakanin Basma da Aryan, bata jin abinda suke cewa, Amma ta fahimci soyayya ta dawo, murmushi tayi tace a ranta “masoya Laila da Majnun, dole zan sanar da president domin  ayi bikin nan kowa ya huta tunda Basma ta gama idda”. ‘Washe Gari’ Ammi suna hira da Momy tana gaya mata labarin su Basma, Momy dariya tayi tace “Aiko wallahi wata ran zaki ga abinda idonki zai kasa gani in dai yaran nan ne” ltama dariya tayi tace “bari kawai, naje rufe window d’in ne fa, shine nayi arba da su, so nake Anjima naje na samu President nayi masa magana, don a sanya bikin da wuri ayi a gama kowa ya huta” Momy tace “aiko gwara dai ki gaya masa dan ni ba ruwana a ciki kunfl kusa, dan yaranki ne” nan dai sukaita tanaunawa. Da yamma misalin k’arfe biyar Basma ce ta fito cikin shirin fita, Yaya Ahmad da Yaya Aryan 
sun Jero suna hira da alama fita za suyi da sauri Yaya Ahmad ya k‘arasa wurin Basma Aryan na biye dashi a baya yace “Queen sai ina haka kuma haka?“ Murmushi tayi tace “Yaya Ahmad Momy ce ta aike ni zanje yanzu na dawo” Aryan ne ya kalleta yace “Bani waya ta in d’auki wani number” 
ta kalle shi a tak’aice tace “Gaskiya ban gama abinda nake da shi ba inna gama zan baka” “ok, shikenan amma ba ke kad‘ai zaki fita ba ko?” “Ni kad’ai zan Fita ko akwai matsala ne?” “Awkai saboda ban yarda kina Fita ke kad’ai ba, in dai kina son fita to lallai sai dai driver ya kaiki” Bata tanka masa ba, ya mik’a hannunsa Alaman ta bashi key d’in motan, tana turo baki ta mik‘a masa, driver ya kwalawa kira ya tawo da sassarfa, Yaya Ahmad na kallon ikwan Allah, Yaya Aryan ya mik’a ma driver key yace ga tanan ka kaita duk inda zata je, kuma ka tabbatar magriba ta muku a gida” Jiki na rawa ya amsa da to, sannan suka wuce. Ahmad yana mata dariya ciki-ciki dan abin nasu ya bashi dariya sosai. Basma kamar yanda security ya samo mata address d’in Jiddah haka tayi ta ma driver kwatance har suka kai, driver yayi parking tace “kajirani nan”. Cikin natsuwa ta isa bakin gate d’in gidan, turawa tayi k’ofar ya bud’e sai ta shiga, mai gadi na zaune a kan kujera Basma tayi masa sannu, sannan tace “dan Allah ko nan ne gidansu Jidda?” cikin sauri yace 
“kwarai nan ne, bata dad’e da dawowa daga anguwa bama Kud’i Basma ta ciro ajakarta wanda bata san adadinsu ba ta bashi,jikinsa na rawa ya amsa yana mata godiya da Addu’a, haka ta shiga cikin gidan hankali ta kwance ba tare da fargaba ko damuwa ba. K’ofar falon ta tura ta shiga, k’aton falo ne mai d’uke da kujeru da kayan alatu, daidai gwargwado sunada kud’i suma ba laifi, wata Mata ta amsawa Basma sallama, cikin natsuwa Basma ta k’arasa ta samu guri ta zauna, Matarta kafawa Basma ido domin bata wayi fuskanta ba, Basma ta risinarda kai k’asa ta gaisheta, cikin fara’a Hajiya ta amsa, 
Basma tace “Momy Jidda na nan kuwa?” 
“tana nan, bari na kira miki ita” nan take ta bud’e murya ta shiga kwalawa Jidda kira, cikin sauri ta fito sanye da k’ananun kaya sun matseta tace “Mama kaya nake sawa fa yanzu na fito wanka” “To bak’uwa kika yi gata nan, shine dalilin kiran naki” Da sauri ta karasa falon ta zauna cike da kallon mamaki tak’ewa Basma, cikin murmushi 
Basma tace “nasan baki waye ni ba, Amma inna ce miki Queen Basma ce k’ila ki iya sani na” Washe baki Jidda tayi tace 
“laa kece dama Queen Basma Yar shugaba? ai ina jin sunanki, to ya kike?” “Lafiya lau, dama nazo muyi magana ne akan Mijina Aryan” Damm zuciyan Jidda ta buga, cikin k’arfin hali tace “ban fahimceki ba?” Murmushi Basma tayi ta kai kallonta ga Maman Jidda tace “Momy nazo wurinku ne badan rigima ba sai domin inyi magana da Jidda ta fita hanyar Mijina don Allah” Mamaki ya kuma kama Jidda da Mama, Mama tace “Jidda ko yaron da ki kika min bayanin shi?” “Eh shi take magana” “Basma ta cigaba da cewa “tun jiya bayan munyi waya dake baki fasa kira ba kuma wayar tana hannu na, tona rok‘eki da ki fita hanyarsa inba haka ba duk abinda na miki ke kika ja” Ta d’auki wayan Aryan ta kashe, ta zare sim d’in ta cigaba da cewa “wannan shine abinda yake had’a ku kuke magana ko? To bari ki gani” sai ta karya sim d’in tayi masa gutsi-gutsi, kana ta ciro sabon layi data sanya aka yi masa regista tare ta sanya masa duk nombobinsa a ciki, na Jidda ne kawai aka cire, sai ta sanya ta kunna tace “na sauya masa layi” Jidda mutuwar zaune zayi domin yau ta had’u da wacce ta fita son Aryan. Basma ta mik’e ta ciro bandir d’in kud’i na dubu d’ai-d’ai taje ta aje gefen Mama tace “Mama ga wannan kici goro na gode” Mama tace “Allah ya miki albarka, nagode ki gaida manyan” Jidda ta mik’e ta bi bayanta har suka fita farfajiyan gidan, hak’uri ta shiga bama Basma da kuma alk’awarin komai ya wuce ba zata sake shiga hanyar Aryan ba, dama ita ke sonsa bashi ba. Nan dai suka rabu lafia har mota Jidda ta raka ta, kana ta koma gida cike da 
damuwa. Mama ta kalleta cikin kulawa tace “ai kinga yanzu kya bari Bashirya fito auren ki, k’iri-k’iri Yaron nan na Sonki, kika mak’ale ke kina da wanda kike So to yau kin gamu da wacce ta fiki sonshi, dan haka yanzu kya shiga hankalin ki, ni naji dad’in zuwanta ma dan yamin riba, dubu d’ari tabani gashi a rubuce” Marai-rai ce fuska tayi tace “Mama ai yanzu ma hak’uri na bata don mu rabu lafiya, bazan iyaja da ‘yar President ba, dama can nayi tunanin Aryan yafi k’arfina, baki ganshi bane Mama gayen ya had’u” Tafi can ki bani wuri, ni dai ki bama Bashir dama ya fito a yi biki nan ko na huta”. Murmushi tayi tace 
“Mama kenan, to ki kwantar da kankalin ki nima na saduda”. 
Basma tana komawa gida taje part d’in Yaya Ahmad ta same su a can, zama tayi suka gaisa ta ciro wayan Aryan ta mik’a mishi tace ga wayanka nan na sauya maka layi, kuma numbers d’in dake wancen nasa duk an maida maka su, number Jidda ne kawai bai ciki, kuma nasa an tura ma duk contact d’inka text da cewa wannan shine sabon layinka, MTN office naje acan suka min komai” Yaya Ahmad yace biri yai kama da Mutum d’azun naga text magana ne kawai banyi ba” Aryan murmush’l yayi ya amsa wayan, amma yak’i mika mata nata, tace “ka bani nawa” 
Hade ransa yayi yace “ba yanzu ba” mik’e wa tayi ta ce “shikenan ka rik’e tunda burina dai ya cika, dan na gama yin abinda nake so, Jidda ce kuma ba zata sake kiranka ba dan nayi tattaki zuwa gidansu” nan ta kwashe labari tas ta gaya musu sannan bata jira me zasu ceba ta fita tana gunguni. Dariya duk ta basu Yaya Ahmad yace Basma rikici, to kai aiki ya same ka” 
Dariya Aryan yayi yace “zata gama borinta ta daina” nan dai suka cigaba da hira suna dariya. Da dare Yaya Aryan ya kirata a d’ayan wayanta kamar ba zata d’aga ba, sai taji bazata iya share shi ba, d’agawa tayi tare da yin sallama, ya amsa, sannan suka yi shuru, can k’asan murya yace 
“My Basma ina part d’in Yaya Ahmad kizo za muyi magana” “barci nakeji“ 
“to shikenan bari naje gidansu Jidda nasan ita zata saurareni“ Da sauri ta mik’e cikin masifa tace “gani nan zuwa wallahi karka Fita” dariya ya kwashe dashi sai ya kashe wayan. Ta same shi tana d‘aure fuska, a hankali ta saki saboda irin soyayya da hira da yake mata cikin farin ciki suka rabu. 
Ammi ta samu Abba sunyi magana akan zancen su Basma, Abba yayi farin ciki nan take ya kira Dady da Mai Martaba yayi magana dasu. Washe Gari’ Duk zuka zo suka had’u suka yanke sadaki da ranar biki sati biyu mai zuwa, Mai Martaba shine ya biyawa Aryan sadaki, Dady kuma shine zaiwa Basma kayan d’aki, da kuma gyaran 
gidan da zasu zauna, Abba kuma shine zai had’a masa akwati. 
Hmm

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE