YAR SHUGABA CHAPTER 3

YAR SHUGABA 
CHAPTER 3
‘WACECE QUEEN BASMA?‘ 
‘Yace a wurin Alhaji Mukhtar Bukar Bulama, wanda yake shugabancin k’asarmu Nigeria a yanzu. Asalin Mahaifinsa d‘an Maiduguri ne Kanuri, mahaifiyarsa kuma mai suna Asma’u ‘yar Gombe ce Fulani, Alhaji Bukar Bulama babban d’an kasuwa ne, yana fita k’asashen waje sosai, yajima baiyi aure ba saboda yanayin kasuwancinsa, Mahaifin Asma’u Alhaji Salis, abokinsa ne k’ud da k’ud wanda a sanadin kasuwanci abotansu ya had’u, ganin Ahaji Bukar Bulam baiyi aure ba yasa Alhaji Salis ya bama Alhaji Bukar auren ‘yarsa tilo d’aya Asma’u. 
Suna zama a cikin garin Kaduna a Unguwar Rimi, Alhaji Bukar an sanshi sosai, Mutum ne mai tausayi da taimakon talakawa, yaransa biyu a duniya Mukhtar da Halimatus Sadiya, sun taso cikin gata da kulawa kuma Asma’u tayi k’ok‘ari sosai wajen basu tarbiyya mai kyau. 
Mukhtar yana gama primary mahaifinsa ya turashi karatu k’asar Germany a can ya fara secondary school d’insa. Tafiya ya kama su Alhaji Bukar zuwa Gombe sanadin rasuwan mahaifiyar Asma’u, bayan sunje basu dawo ba har akayi Addu’an bakwai kana suka kamo hanyar Kaduna, basu fita daga Gombe ba akan hanyarsu suka bige wani yaro, cike da tashin hankali suka nufi Asibiti dashi, aka karb‘esu emergency, an samu yaron ya farfad‘o, amma baya iya magana sai zaro idonsa yake waje, Likita ya basu tabbacin yaron ya samu Matsala a kwakwalwansa, hankalin Alhaji Bukaryayi masifar tashi, sunyi iya bincike ganin an gano iyayan yaron amma shuru ba a gano ba, da haka ya d’auki yaron ya wuce dashi Kaduna da nufin in ya samawa yaron lafiya ya maidashi wurin lyayensa. ‘ Alhaji Bukar suna dawowa da kwana biyu ya shirya zuwa kasar Germany da iyalensa domin duba lafiyan Yaron daya bige, wanda baya iya magana. Da isarsu da kwana biyu cikin ikon Allah Yaron ya soma magana, sunan shi kad’ai ya iya tunawa Ibrahim, amma banda haka bai tuna komai ba, Likitoci suka tabbatar musu da Yaron ya samu mancewar kwakwalwa (loosing Memory). Abin ya damu Hajiya Asma’u sosai hakan yasa Alhaji Bukar ya bar Ibrahim a wajen Mukhtar ya fara karatu shima, sai suka tarkato suka dawo Nigeria. ‘Bayan shekaru mai tsawo‘ Su Muktar sun dawo Nigeria wanda dukkansu sun gama karatunsu sun samu aiki, har zuwa lokacin Ibrahim bai dawo cikin kwakwalwansa ba. Sadiya kuma tana karatu a KASU, tun dawowar su MukhtarAllah ya daurawa Sadiya son Ibrahim, Abu kamar wasa har mahaifiyarsu ta ganeta saita kwab’eta, abinda basu Sani ba shima ta wurin Ibrahim d’in ya kamu da son Sadiya, daga bisani ya bayyana mata zuciyanshi suka fara soyayya. An sanya bikin su Ibrahim da Sadiya ba b’ata lokaci, wanda Alhaji Bukar yace ta cigaba da karatunta a d’akin mijinta, Mukhtar shima yana soyayya da k’anwar Sarkin kano mai suna Fatima, soyayya tayi k’arfi wanda hakan yasa aka had’a bikin su duka a kayi. Anyi biki sosai na manyan Attajirai, ko wacce ta tare a sabon gidanta da Alhaji Bukar ya siya musu a unguwar sunusi. 
Wata rana Alhaji Bukarya shirya taflya k‘asar Dubai shida Mahaifin Asma’u, domin kula da kasuwancinsu dake can, a hanyar dawowarsu jirginsu yayi hatsari suka rasu. tashin hankali ba’a sanya masa rana, wannan Family sun shiga cikin damuwa da k’unci na rashinjigonsu, 
Hajiya Asma’u ta zama ba Uwa ba Uba ba Miji sai sauran danginta da yaranta. Hakan ya girgizata wanda haka yasa ta samu ciwon hawan jini. Su kuma su Mukhtar sun rasa Bango abin jingina  Ibrahim yayi kuka matuk‘a domin da bazar Alhaji Bukar yake taka rawa, har yau baisan shi waye ba ko danginsa, yasan dai su Hajiya Asma’u basune iyayensa ba, ya kasa tuna komai na danginsa. Bayan Addu’an Arba’in duk dangi suka watse, an rab’e musu gadonsu, Muktar ya had’a duka dana k’anwarsa Sadiya dana Ummansu ya cigaba da kasuwanci dasu sannan yana aikinsa. Shi kuma Ibrahim sun bashi wani kaso mai tsoka daga dukiyar nasu kamar yanda mahaifinsu ya rubuta a cikin dairy d’insa, Ibrahim ya amsa yana godiya harda kukansa, daga nan shima ya cigaba da business. 
Hajiya Fatima matar Muktar ta haifi d’a Namiji mai suna Ahmad, bayan shekara guda ta kuma samun ciki, bata so ba amma dole ta hak’ura saboda Alhaji Mukhtar yana son abinsa, haka ya d’auki Ahamd ya bama Ummansu ta cigaba da rik’onsa. 
Bayan wata tara ta kuma haifo d’anta Namiji mai suna Abubakar suna kiransa da Naufal. Sati biyu da haihuwarta Allah ya azurta Alhaji Ibrahim samun k’aruwa da d’a Namiji wanda suke sanya masa suna Jamal. Sun raini ‘ya‘yansu cikin Kauna da soyayya, sun basu tarbiya sosai domin kud‘insu bai hanasu tsayawa bisa tarbiyyan yaransu ba. 
‘Bayan shekara biyu‘ Hajiya Fatima ta kuma haifo ‘ya mace suka sanya mata Asma’u suna kiranta da Husnah. Ta b’angaren Hajiya Sadiya ita bata k’ara haihuwa ba tana rik’e da d’anta Jamal. 
Alhaji Mukhtar ya rik’e mukamin Commissioner har kujera uku, soyayyar da ya samu wurin Mutane yasa ya flto takaran gomna, cikin ikon Allah ya samu. Ta b’angaren Ibrahim shima yana ta samun mukamai a wurin aikinsa dukiyarsu sai hab’aka take ta ko ina. Alhaji Mukhtar ya k’ara aure da ‘yar wani hamshak’in mai kud’i a garin Kano ‘yar Alhaji Buba mai Naira itace ‘yarsa tilo guda d‘aya mai suna Maryam, anyi Biki sosai na manyan Mutane, Alhaji Mukhtar ya tare da ita a gidansa na Gomnati, gida d’aya ya had’asu da Hajiya Fatima, suna zaune zaman lafiya ba tashin hankali. “Bayan shekara Hudu‘ yana kujeran Gomna, Hajiya Maryam ta Haifi ‘yarta mace k’atuwa ga kyau, suka sanya mata suna Basma, Basma ta taso cikin gata da soyayyan iyayenta, Yaya Ahmad yana sonta sosai tun tana k’arama suka shak‘u sosai, bata shiri da Yaya Naufal, Anty Husnah kuwa duk inda zata suna tare, tun tana k’arama ta koma hannun Hajiya Fatima, Nono kawai ke kaita gun Momynta. Itama Hajiya Sadiya ta k’ara haihuwar ‘ya mace aka sanya mata Ameena suna kiranta da Meena, tserayen wata biyu ne tsakanin haihuwar Basma da Meena. Yaya Ahmad da Yaya Naufal kusan tare suka wuce k’asar Malesia karatu, Yaya Ahmad yana karanta Medicine Yaya Naufal yana karana Biochemistry. A lokacin Anty Husnah tana secondary school. 
Basma kuma tana primary. Hajiya Fatima wanda suke kira da Ammi ta gama sangartata duk wani rashin ji ta sani, ga tsokanar fad’a a makaranta, duk wani kiriniya tare suke yi da Meena da yake makarantar su d’aya. A daffafe suka kare primary saboda irin kai k’aransu da iyayen yara keyi, kasantuwar iyayensu manya ne shiyasa ba’a koresu ba. 
Hajiya Maryam ta k’ara haihuwar yara Maza ‘yan biyu Anwarda Na’im, anyi shagali sosai da haihuwarsu, su Basma kuwa murna har kunne. So tari Hajiyar Maryam wanda suke kira da Momy bata ragawa Basma tayita mata fad’a hakan yasa Basma bata son kwana a 
b’angarenta sai wurin Ammi saboda Ammi na kula da ita bata son b’acin ranta. 
An d’aurawa Anty Husnah aure da Jabir d‘an senator, sun had’u a makarantar A,b,u Zaria inda ta fara karatu, an d’aura auren tana cigaba da zuwa makaranta. A wannan shagalin bikin ne akayi taron da ba‘a tab’a yiba, mutanan Gombe, Maiduguri, kano duk sun hallara, matar Sarkin Kano yayan Ammi, Hajiya Murja tazo bikin wanda ta taho da ‘yarta mace sa‘ar su Husnah mai suna Haleema suna ce mata Leema, tun daga nan su Basma aka samu kawa, da zasu tafi Leema ta kafe saita zauna wurin Ammi, haka mahaifiyarta ta barta mai martaba Sarki Abdallah ya amince Leema ta zauna wurin Ammi domin yasan gidan Gomna Muktar Bukar Bulama akwai tarbiyya. Abdullahi shine ya gaji sarautar gidansu bayan rasuwan Babansu, Yayane ga Hajiya Fatima, uwa d‘aya uba d’aya suke, yana da mata biyu Hajiya Sa’a itace Uwar gida tana da yara biyu duk Maza Adam shine babba sai Shureym shine k’arami, sai Amaryansa Murja yarta guda d’aya ce itace Leema, sun d’aura son duniya sun azawa Leema kowa na dangi yana sonta, tun tana k’arama ta taso cikin sarauta, gimbiya Leema ‘ya ga Sarki Abdallah. Hajiya Sa’a Mace ce yar k’arya da son duniya ta shigewa Hajiya Maryam Momyn Basma, amma Momy tak’i sake mata saboda halayyarsu bai zo d’aya ba, Hajiya Sa‘a basa shiri Sam da Ammi wato k’anwar mijinta, hakan yasa Momy tak’i sakejiki da ita. Hajiya Sa’a ta sangarta Shureym da gata, ta d’aura son duniya ta bashi saboda tana ganin shine zai gaji kujaran Babansu, shiyasa tun yana k’arami take kiranshi da Prince Shureym, hakan yana masa dad’i sosai. Adam shi kuma Mutum ne salihi ba yida hayaniya hakan yasa nasu yazo d’aya da Hajiya Murja, a wurinta yake komai. Shureym yana America yana karatun Engineering, shiko Adam Madina ya tafi karatunsa bangaren Islamic studies. Basma, Meena, Leema duk makarantar d’aya suke secondary, a part d’in Ammi suka tare domin Ammi ita bata kwab‘a musu, Meena ta kwaso kayanta ta dawo gidansu Basma gaba d’aya. Alhaji Ibrahim Baban Meena ya samu cigaba sosai, wanda yaita samun K’arin girma a wurin aikinsa, ya tura Yaya Jamal karatu inda su Yaya Ahmad suke k’asar Malesia yana karanta Business admin. Gomna Muktar Bukar Bulama ya sauka a kan kujeran Gomna bayan shekara takwas daya shafe akai, ya k’ara samun kurajeran Sanator wanda ya wuce Abuja, sai weekend yake dawowa gida Kaduna. Dukiyarsu na gado sai hab’aka yake yi. 
Su Yaya Ahmad sun gama karatunsu gaba d’aya duk sun dawo, Yaya Ahmad ya fara aiki a babban Asibiti dake garin Abuja, Yaya Naufal kuma ya karb’i kasuwancin Abbansu ya cigaba da juyawa. Yaya Jamal ma dukiyar Dadynsa ya cigaba da rik’ewa. ‘ 
Ta b‘angaren Mutanan Kano kuwa Yarima Adam ya dawo ya fara lecturing a BUK, shi kuma Shureym bai riga ya kammala masters d’inshi ba. Su Basma an zama ‘yan Mata sun gama Secondary School yanzu suna England suna karatu. Basma na karanta Micro Biological, Leema tana karanta Pharmacy, Meena kuma tana karanta Law. 
Tunda suka koma England rayuwarsu ta k’ara sauyawa, sun had’u da ‘ya’yan turawa da kuma ‘yan k’asashe daban-daban, Basma tunda ta soma karatu saita natsu ta zama mara son magana, amma fa akwai tsiwa in aka tab’ota, Meena kuma akwai shegen surutu, Leema kuma akwai ji dakai da kuma k’asaita na Sarauta. 
Sunyi farin jini sosai saboda suna da k’ok’ari sosai. Meena ta had’u da wata yar ajinsu ta koya mata zuwa club, abu kamar wasa Meena in bata je club ba bata jin dad’i, tun su Leema na mata k’orafin ta daina zuwa har taja ra’ayin Leema ta fara zuwa. Abu na farko da suka koya shine Meena ta shiga group d‘in ‘yan shaye-shaye, tun bata iya ba harta kware sosai wajen zukar sigari da shan kwayoyi. 
Leema kuma Mace ce mai yawan sha’awa, in Meena ta jata cikin group d’insu saita kasa sakewa a haka harta had’u da Jalal suka fara soyayya tun bata sakewa harta sake dashi, Jalal ya fara flta da ita yawo kullun sai sun fita A hankali yayi ta jan ra’ayinta gareshi, tun tanak’in amince masa harta bashi kai bori ya hau. Tun daga nan suka d’inke da Jalal, ya mai da ta tamkar Matarsa shine mutum na farko da yasa fara sanin ta a ‘ya mace. A hankali Leema ta raba shi da duk ‘yan matanshi, Basma kullun cikin musu nasiha take akan sun 
gurb’ata tarbiyyan da iyayensu suka yi musu dasu gyara halinsu. Meena tayi murmushi tace “ke bazaki gane ba, meye amfanin zuwanmu k’asar waje bamu waye ba, ai wannan itace wayewar, kinga ni shaye-shaye kawai nakeyi ita kuwa Leema da Jalal take harka, kinga ta samu abinda zuciyarta take so”. Basma tayi tsaki tace 
“Allah ya kyauta” Murmushi Leema tayi tace “ki shirya yau muje club dake Allah za kiji dad’in wurin sosai” Basma tace 
“Kun dameni da zancen club d’in nan, yau dai zani inga abinda akeyi a gun shikenan kunyi farin ciki ko?” cikin farin ciki suka ce 
“wow munyi Murna kema zaki shigo sabon rayuwa ki huta da rayuwan duhun kai” 
Sunje club gaba d’ayansu, yanda Basma taga wurin sai ya sanyata farin ciki musamman data ga ‘yan rawa sai hakan ya kwanta mata arai, dan a duniya Basma tana son rawa, kawai 
sai ta mik’e ta nufi wurin rawan ta hau, cike da mamakin mutane suka bita da kallo,ji tayi k’afarta ya k’asa d’aukarta, dan gani tayi ido ya mata yawa bazata iya ba, su Meena ne suka fara kiranta “common Besty ki fara” nan kowa ya fara ihu suna mata kirari dan ta fara, nan kanta yayi chargy taji wani k’arfl da dakewa saita fara rawa cikin salo naban namaki, sai wurin ya kaure da ihu, dan tayi matuk’ar burgesu, ba wanda yayi tsammanin ta iya rawa haka, hatta su Leema sunsha mamaki. Nan aka fara mata yayyafin kud’i kan basma ya k’ara kato saida tayi sosai kana ta sauko, koda ta samu guri ta zauna sai mai wurin ya kawo mata kud’in data samu bud’en bakinta tace ya barshi. Murna sosai yayi ya mata godiya. ‘ Tun daga wannan rana Basma ta fara zuwa club burinta bai wuce taje tayi rawa a yi mata kuwwa a fasa mata kaiba. Musamman ta shiga makarantar koyan rawa babu irin wanda ba a koya mata ba hatta na larabawa. 
Hmm

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE