YAR SHUGABA CHAPTER 32
YAR SHUGABA
CHAPTER 32
‘Washe Gari’
Da k’arfe bakwai na safe Yaya Ahmad ya kama hanyar gidan Yaya Aryan. Yana isa yayi hon Mai Gadi ya bud’e masa yayi parking ya isa bakin k’ofar falon yayi nocking, Yaya Aryan dake kwance a kan doguwar kujera ya mik’e cikin nauyin jiki ya isa bakin k’ofan ya bud’e, sai yayi arba da Yaya Ahmad, sai da gaban Aryan ya fad’i, matsa masa yayi ya shigo cikin falon duk suka samu guri suka zauna, sai suka gaisa, Yaya Ahmad yace “Ina Basma fa?” Yaya Aryan yace “tana d’aki, laflya na ganka da sassafe haka?” “Lafiya lau, nazo nayi magana daku ne, dan haka kira min Basma tazo” Bai ce komai ba ya mik’e ya isa bakin k’ofar Basma, sai ya ki shiga ya tsaya bakin k’ofar yana bugawa tare da cewa “Basma, Basma ki tashi ga Yaya Ahmad yazo”Cikin magagin barci ta farka ta mik’e tare da bud’e murya yace “to”. Yaya Ahmad duk yana kallonshi, a ranshi yace ‘ko me ya hanashi shiga d’akin oho’ Yaya Aryan ya dawo ya zauna. Basma ta fito sanye cikin doguwar riga ta yane gyale a kanta, zama tayi a one seater ta gaishe da Yaya Ahmad ya amsa cikin kulawa, shuru ne ya biyo baya na tsayin minti Uku, daga bisani Yaya Ahmad yace “Aryan, Basma nazo domin muyi magana ne, a gaskiya ban yarda da bayanin da kuka min ba jiya, shiyasa nazo Yau dan jiya na kasa barci, Dan Allah karku b’oye min komai” Basma da Aryan suka kalli juna suka had’a ido, Basma zata yi magana Aryan ya riga ta yace “ka yarda da abinda muka ce maka mana domin ba komai” Yaya Ahmad yayi murmushin k’arf’ln hali yace “Basma in shi ba zai gaya min ba ke nasan ba zaki b’oye min ba, dan haka gaya min me yake faruwa?” Hawaye ne ya soma zarya a idon Basma, ta d’ago ta kalli Yaya Aryan, sai ya fara girgiza mata kai alamar karta gaya, Yaya Ahmad ya kira sunanta sai ta mai da kallonta gare shi yace “Basma ina jinki” Basma ta share hawayenta ta gaya wa Yaya Ahmad abinda ke damun Aryan, sai dai bata gaya mishi matsalan da suke fuskanta ba yayin saduwa sai ta boye wannan. Yaya Ahmad ya kurawa Aryan ido sai ya sun kuyarda kai zuciyarsa na masa zafi nan take idonsa suka yi jaa. Yaya Ahmad yace Basma d’auko key d’in motanki ki shirya ki tafi gida” Da sauri duk suka zuba masa ido, d’aure fuska yayi yace “Nace ki tashi kiyi abinda na sanya ki” ya fad’a maganar cikin tsawa,jikinta na rawa ta mik’e tare da fashewa da kuka.Aryan mik’ewa yayi cikin fushi yace “Me kake nufi da ta tafl gida ba tare da izini na ba?” Murmushi yayi yace
Saboda ba kada lafiya, ba zata zauna ba domin tabbas matsalan ka zai iya shafanta” yaya Ahmad ya fad’i hakan ne domin ya tunzura Aryan dan ya tabbatar da ciwon nasa. Aiko Aryan ransa ya k’ara baci. Basma sai gata ta fito tana ta kuka, Yaya Aryan ya tare mata hanya ya kama hannunta gam kansa ne yayi mugun sarawa sai ya rik’e Kan da d’ayan hannunsa, Basma tace “Yaya Aryan ka barni na tafi ko zakaji sauk‘in abinda ke damunka” Yaya Ahmad ne ya matso wurin ya fincike hannun Basma, ya kama Aryan ya zaunar dashi tare da kama kansa da k’arfi, Addu’a ya fara tofa masa nan take ya ture Yaya Ahmad suka fara dambe. Basma ihu ta some security da suke gidan suka fad’o falon a sukwane suka kama Yaya Aryan yana cijewa. Yaya Ahmad ya fad’a kitchen d’in Basma ya d‘ibo ruwa a cup ya soma karanta Addu’o‘i yana tofawa a ciki, bayan ya gama ya soma watsawa Aryan ajiki,wani k’ara ya saki yana gunji, haka yayi ta watsa masa har sai da yayi shuru yana gunji. Da sauri Yaya Ahmad ya kira Naufal yace “Naufal kana ina ne? ina so kaje gidan Malam Hashim ku tawo tare dashi gidan Aryan Akwai Marsala ne” bai jira mai zai ce ba ya kashe wayan. Cikin tashin hankali Naufal ya mik’e ya flto, gidan Malam Hashim ya wuce ya d’auke shi suka nufi gidan Aryan. Sun isa gidan cikin sauri suka fad’a falon, Aryan yana jin shigowar su ya saki k’ara, Malam Hashim ya kunna garwashin wuta ya sanya wasu Magani a ciki ya soma turara d‘akin, Malam Hashim ya fara karanta wasu Addu‘a yana tofa masa, Aryan yana gunji ya fara magana “Zan fita, Zan fita, Zan flta, karku k’ona ni” Malam yace Bama buk’atar kiyi magana ku tafi kawai” “Ni bazan tafi ba saboda ina son Basma” Malam yace “Meyasa kike son ta sannan baki shiga jikinta ba saiki shiga jikin mijinta?””Saboda tana burgeni, tun tana k’arama nake bibiyarta don na shiga jikinta amma ban samu hanya ba, saboda a jikinta banida mazauni dan Kakansu Bukar ya shayar dajikokinsa magun guna na tsarinjiki gaba d’aya babu wani jinnu da zai iya cutar dasu” “To meyasa kika Shiga jikinsa bacin Basma kike so?” Soyayyan Basma yasa na shiga jikinsa, shima na jima ina son shiga jikinsa, ran nan ya kwanta ba tare da yayi Addu’a ba har barci ya d‘auke shi. shine na samu hanyar shiga jikinsa, kuma bana so ya kusanci Basma saboda son da nake mata banson kowa ya rab’eta” “Kina mace maye na son shiga jikinsa, wannan ai ba soyayya bace, tunda kina cutar da shi, dan haka zan konaki da Ayar Allah” “Kar ku kona ni zan tafi har Abada bazan dawo ba”
Malam ya watsa masa wani ruwan Magani, k’ara ya saki yana birgima nan take yayi shuru kamar ruwa ya d’auke. Aka sanya karatun Al’Qur’ani Suratul Bak’ara, nan take barci ya kwashe shi.
‘Hmmm duk abinda wasunku ke zargi akan Sihiri akaiwa Aryan kunata zagin su Mami, to ba Sihiri ke damunsa ba, ba ruwan Mami, Yaya Shureym, balle kuma Jidda.‘ Bayan komai ya lafa Yaya Ahmad ya kira su Ammi ya shaida musu abinda ya faru. Cikin tashin hankali suka zo gidan su Aryan. Sun zauna jugum-jugum sunajiran Aryan ya farka, cikin ikwan Allah kuwa sai gashi ya farka yana mai Ambaton Allah, zama yayi yana kallon Mutanen falon d’aya bayan d’aya, yana kai kallonsa ga Basma da take kuka sai ya yun k’ura da kar yace “My Basma me ya same ki kike min asaran hawayenka” Haka ya isa wurin ta ya kama hannunta ya mik’ar ya zaunar da ita a bisa cinyarsa, sam ya manta da Mutanan dake falon, Momy cikinjin kunya ta mik’e ta fita daga falon, Ammi ma fita tayi tabi bayan Momy, Yaya Ahmad yace “To Love Birds hala ka manta da mutanan dake d’akin ne?” Dariya yayi yace “ba dole na manta daku ba, Pretty na tana kuka” Duk sai suka sanya dariya, nan Malam Hashim ya bashi wasu Magani da zai yi amfani dasu na wanka da sha sai hayak’i, sannan kuma ya bashi shawarwari akan ya kula da ibadansa da kuma yawai ta karatun Al‘Qur’ani da Azkar, Yaya Aryan yayi masa Godiya, nan suka yi musu sallama gaba d’aya suka tafi Gida. Yaya Aryan ya zauna gefen Basma yace “Babyna Allah yasa na samu lafiya kenan, kin ga yanzu bana jin komai in ina zauna gefenki” Hawaye ta share ta d’aura kanta bisa ciyarsa tace “Myn wallahi na firgita da lamarinka sosai, insha Allah ka warke hakan bazai sake faruwa ba”. Nan dai suka samu suka karya, suka sake wanka, Aryan yayi amfani da magun-gunansa, sai suka dawo falo suka zauna suna hira suna soyewa abin gwanin sha’awa. Bayan Kwana Biyu’ Aryan ya warware sosai babu sauran wani damuwa, da dare ya siyowa Basma kayan ciye ciye, suka baje a falo su ka ci abinsu, bayan sun kammala k0 wanne ya wuce d’aki domin yin shirin barci. Wani Rigan barci Basma ta d’auko,ta d’aga sama tana kallon rigan,jin-jina rigar take yi tana ayyana wa a ranta Anya zan iya sanyata kuwa?‘ Aryan daya jima da shigowa yana kallonta, yace “Dama kin mai data kin aje, dan karta bani wahala wajen cirewa, ki bari gobe in Allah ya kaimu sai ki sanya ki min kwanliya da ita da dare kafin mu kwanta“ Da sauri ta juyo dan harta tsora ta, kunya ce ta rufeta akan maganan daya fad’a, maida rigan tayi ta ajiye. Arya yazo ta bayanta ya tsaya, d’aukarta yayi cak ya ajeta bisa gado. ‘Nima daga nan nayo waje, na basu guri tare da yi musu saida safe! ’Washe Gari’
Da misalin k’arfe shida na safe, Basma ce kwance bisajikin Yaya Aryan yana lallashinta akan tayi barci, sai shagwab’a take zuba masa. Da kyarya samu tayi barcin, sai ya gyara mata kwanciya ya ja mata bargo, ya sauka ya zauna gefen gado, dafe kansa yayi cike da mamakin yanda ya samu Basma a cikakken Budurwa, tambayan kansa yake “Dama Basma bata tare da Shureym ba kenan, lallai Allah kaine Mai cikakken iko, hak’ik’a babu wani Sarki sai Kai, kuma Kaine Majib‘incin dukkan Al’amuranmu, Alhamdulillah da wannan babban kyauta daka bani, nasan ba wayauna bane ba kuma dubara na bane”. Hawayen farin ciki ne ya sauka kuncinsa, ya shiga jero Addu’a tare da yiwa Allah kirari, saida ya karanto sunayen Allah D’ari ba d’aya, ya cika da salatin Annabi s.a.w, sai ya shafa. Basma ta bud’e ido tana kallonsa, ashe barcin nata bai yi nisa ba, ta taso a hankali ta rugumeshi ta baya tace “uhum, uhum, Myn yunwa nakeji ka bani abinci inci” Jawota yayi ya birkito ta akan jikinsa suna kallonjuna, hura mata ido yayi yace “kina kallo na kamarzaki had’iye ni, ko d’an kunyan nan ma” runtse ido tayi yana dariya tace “kai Yaya Aryan ka daina cewa haka mana ba ina sonka bane, Ni dai ka bani abinci zanci” tom bud’e ido muyi magana, me kike so in miki wanda zai saki farin ciki sosai, Hasken Rayuwata kin bani kyauta mafi girman kyauta wanda yazo min a bazata, Basma nayi mamakin samunki a cikakkiyar…” Bai k’arasa ba Basma ta had’e bakinsu guru d’aya saida suka yi tsayin minti biyar, kana ta
zaro bakinta a nashi ta kalleshi ido cikin ido, tace”Myn Kai ne kad’ai nake so, kuma kaine Allah ya zub’a da zaka mallakeni, Yaya Aryan so nake muje Asibitoci, Gidan Marayu, da Gidan Kurkuku mu basu taimako da abinda Allah ya bamu, in kamin wannan kad’ai, zanyi farin ciki sosai mara yankewa”. Rungumeta yayi tsam ajinshi tamkar zai maidata cikinsa, wani sabon so da K’aunarta ke k’ara ratsa zuciyarsa yana yad’uwa a duk sassan jikinsa.
To Readers nasan yau dai na saku farin ciki’_.
Mu tara domin ci gaba da sauraron wannan qaya taccen littafin