YAR SHUGABA CHAPTER 34
YAR SHUGABA
CHAPTER 34
Yaya Ahmad yana zaune a bakin gado Deeja na zaune nesa dashi tana kuka sosai, cikin damuwa yace
“Haba Deeja don Allah ki daina kukan nan haka,Allah ya bamu kyauta banga dalilin da zaisa ki zubar min da ciki ba, Plss Babyna kiyi hakuri ki daina zancen cire cikin nan” Dagowa tayi idojajir, cikin kuka tace “Yaya Ahmad yanzu fa Walid bai wuce wata biyar zuwa wata shida da haihuwa ba, ya zaka ce in bar cikin nan ajikina na, Walid fa zai walaha nima haka”
“Ni banga wani illa a shayarwan Walid ba, muddun yana cin abinci, kuma cikin nan watan shi guda ne kinga da sauran lokacin har zai sha na kusan wata biyar fa, in kin yaye shi zan kaiwa Momy shi”
Kuka take sosai tace “Nifa Allah sai an cire cikin nan” Cikin bacin rai yace
“Wallahi Khadija in kika kuskura kika cire min cikin nan sai nayi mugun sab’a miki” yana gama fad’an haka ya gyara kwanciyarsa ya kwanta ransa na masa zafl. Kuka take sosai, ganin kuka bazai fissheta ba ta mike tayi ta Shiga bayi ta wanke fuska, ta dawo tayi shirin barci, ta kwanta da niyyar da sassafe zata je ta gaya wasu Ammi.
‘Washe Gari”
Da misalin k’arfe takwas na safe, Deeja ce a tsaye a bakin k’ofa, Yaya Ahmad ya rufe d’aki yana ta masifa akan ba zata flta ba, ita kuma ta kafe saita fita, Waya ya ciro a aljihunsa ya kira Yaya Aryan, yana d’auka suka gaisa yace “Aryan dan Allah kuzo part d’inmu kaida Basma yanzu pls” bai jira mai zai ce ba ya kashe kiran. Cike da mamaki Aryan yake bama Basma labari, ba shiri suka fito suka nufi part duinsu Deeja. Nocking su kayi, ya bud’e musu suka shiga suka zauna, sun samu Deeja sai kuka take yi, Yaya Ahmad ya karanto musu abin da ke faruwa, Yaya Aryan ransa ya baci sosai cikin damuwa yace
“Khadija ina kika koyi wannan halin, ba irin wannan tarbiyan Umma ta baki ba,Wallahi kin bani mamaki, Allah ya baki kyauta ki raina, wasu na can suna nima da kudinsu ido rufe amma Allah bai basu ba, karki zama mai budulci mana, babu abinda kika rasa a wajen Mijinki, in kuma dan Walid ne ai ke Doctor ce kinsan babu wani illa akan haka, karki sa inraina wayonki” Ya k’arasa maganar cikin hasala, Basma ta koma gefen Deeja ta dafa ta tace “Kawata kuma ‘yar uwata, don Allah ki sanyawa ranki ruwan sanyi, in dai kula da Walid ne matsalan, na d’auki Alkhawarin zai dinga yini a hannu na, Nono kawai zan kawo shi ya sha, kuma ni zan siya masa abincin yara da ake dama musu kullun dare zan bashi ya rika kwana a wurina har ki yaye shi, amma in kin yarda” Deeja ta rungume Basma tace “Na yarda kuma najanye kudirina zan bar cikin dama ba wai dan bana so bane sai dan ina tausayin Walid”
Nan dai su Yaya Aryan su kayi ta mata nasiha jikinta yayi sanyi, har sai da taji tsanar kanta akan batawa Yaya Ahmad rai da tayi tsakanin jiya da yau, tunda suka yi aure basu tab’a samum sabani ba, ta mik’e da gudu ta fad’a jikin Yaya Ahmad tana kuka tace “Ka yafe min Mijina wallahi sharrin shaidan ne da yaso cin galaba a kaina, insha Allah hakan ba zai kuma faruwa ba” Cikin farin ciki Yaya Ahmad yace “Ni banyi fushi dake ba, dama burina ki gane gaskiya, kuma Alhamdulillah tunda kin gane, na yafe miki Deeja na”
“Nagode Mijina” sai ta mik’e tace “Basma taso muje mu had’a breakfast, tunda kunzo, nasan kuma baku d’aura komai ba k’ilama mu muka tadaku a barci” “A’a, mun tashi ban dai daura komai bane” sai ta mik’e suka shiga kitchen. Yaya Ahmad ya yiwa Yaya Aryan godiya sai suka cigaba da hira, anan Yaya Aryan ya sanar masa da zancen Organization da yake so su Basma suyi, Yaya Ahmad yayi na’am sosai da abun, kuma hakan ya sashi farin ciki sosai, sai suka yanke bayan sati biyu mai zuwa za suyi zaman Meeting, Aryan yace zai kira su Shureym da Jamal ya sanar musu da komai. ‘ Sai wajen karfe Goma suka kammala had’a breakfastd’in, sukajera a kafet d’in tsakiyar d’akin, nan suka baje suka yi hani’an, daga bisani Basma ta d’auki Walid a hannu ta suka wuce part d’in su dashi.
‘Bayan Sati Biyu“
Su Aryan ne zaune a falonsu, gaba d’aya sun had’u don gudanar da Meeting din su. Yaya Ahmad ne yayi Sallama tare da gabatarda bayanai akan musabbabin had’uwarsu, Yaya Aryan ya d’aura da bayanai masu ma’ana, nan duk su Yaya Adam suka yi Na’am da lamarin. Suka yanke shawaran za suyi kokarin Registration din k’ungiyar, sannan zasu sanar da lyayansu akan abinda suka yanke, sun san tabbas zasu samu goyen baya sosai. Sun tsara Ranar taro karshen wata a Kaduna, a Babban filin Murtala Square dan Kaddamar da kungiyar da kuma fara bada Tallafi ga Mahalarta Taron. Yaya Shureym yace “Na d’auki Alkwarin samo Ma’aikata Masu llimi wanda suke niman aiki, kuma Masu gaskiya har Mutane Talatin ta bangaren Kano” “Yaya Jamal yace “Nima zan kawo Mutane Talatin ta bangare na, kunga an samu Ma’aikata Sittin kenan, sai mu yanke musu Albashi Dubu d’ari-d’ari, sannan zamu ware Mutane Talatin wanda zasu rik’a bincika mana halin da Mutane suke ciki na ko wani Jaha, ta kafafen gidan TV, Radio, ‘yan jarida, da kuma sarakuna, dakatai. Mai Anguwa da sauransu. Mutane Talatin kuma za su rik’a had’a mana bayanai ta na,urar Computer, a Manyan Office din da zamu bude Kano,Abuja, Kaduna. A hankali zamu bud’e Offisoshi a sauran Jahohin” Cikin farin ciki suka tafa masa raf-raf-raf. Yaya Ahmad yace “Alhamdulillah wannan Abu yayi kyau, amma ya kamata a samu Mutane Ashirin wanda za su rik’a supplying kaya daga Kasuwanni, Abinci, kayan masarufi, sutura,
keken guragu, keken dinki dana sak’a, da duk kayan amfani wanda Mutane zasu amfana dashi, sannan a samu Mutane Goma Drivers wanda za su rik’a zirga-zirga a duk States d’in da muka shirya bada Tallafi” Nan ma suka yi mishi tafi, Yaya Aryan yace “Da fatan sunan Organization d’in yayi muku?
“QUEEN BASMA (‘YAR SHUGABA) FOUNDATION”
nan duk suka had’a baki da hakan yayi musu, domin Basma ta cancanci haka. Yaya Adam yace “Wato ni kun maidani sectary mai shigar da bayanai, to ga bayanan dana daukar mana gaba d’aya, amma karku manta akwai wanda tallafin kud’i suke nima, wasu kuma na karatu, wasu aiki, wasu Sana’a da dai sauransu, ya zamuyi dasu?”. Yaya Ahmad yace “Wow, wannan magana taka yazo akan gab’a, akwai companoni da Abba yake kokarin budewa a ko wani Jaha a fad’in Nigeria, ina ganin zamu bada sanarwa a ko wani taro in za muyi, don masu niman aiki su turo applications d’in su ta email dinmu, Ma’aikatan mu masu shigar da bayanai sune zasu rik’a dubawa suna zaban wanda suka can-canta” Yaya Aryan yace “Gaskiya ne, kuma zamu duba duk buk’atan Mutane sai muyi musu akan abinda suka raja’a akai, amma bada Sadakar Abinci wannan wajibi ne a duk taron da zamu yi sai mun bada shi” Nan dai suka kare magana da yin Addu’a akan kudirinsu. Sunyi Murna sosai gaba d’ayansu, suka ci suka sha da ciye-ciye,. Daga nan suka dunguwa zuwa gidan Abba dan yi masa bayanin abubuwan da suka tattauna. lyayan nasu sunyi matuk’ar murna, sun kuma goya musu baya wanda daga Karamin organization ya koma Babba, don Abba yace za su sanya hannu a cikin lamarin, hatta makarantu za’a bud’e ta karkashin kungiyar, sannan kuma akwai Scholarships da zai bayar, zai tafi a karkashin “Queen Basma (‘Year Shugaba) Foundation‘ donmin Tallafawa marasa karfl zuwa Kasashen waje don cigaba da karatunsu. Mu samman Abba ya kara yanke ranar Meeting gaba d’aya Family akan K’ungiyar, kam kaddamar da taron
Kungiyar. Su Yaya Aryan sunyi murna sosai kamma Basma da ake komai dominta, sun k’ara Mutane Goma wanda za su gudanar da aiki Akan wanda zasu fita kasar waje karatu in sun samu Scholarship. Ma’aikatan nasu sun zama guda d’ari kenan, Nan suka watse cikin farin ciki kowa ya koma gidansa. Yaya Aryan da Basma suna zaune a dinning suna cin abinci, Yaya Aryan yace “Babyna kinga yanda kudurinmu yake ta bunkasa ko?” Ta d’ago tare da kai loman abinci bakinta tace “uhum ai Yaya Aryan Yau farin ciki ne ya rufe ni, Alhamdulillah Ala Kullu Halin, babu abin da zance sai Allah ya barmu tare, Myn kai Haske ne a rayuwata” Tasowa yayi ya rungumeta ta baya yace “Allah ya miki Albarka Babyna, ya bamu Zuri’a dayyiba yasa Aljanna ta zame mana makoma” Ta amsa da Ameen tare kankame hannunsa a kirjinta. Amai ne taji ya taso mata ba shiri, da sauri ta toshe bakinta tana yunk’uri, da sauri ya d’uketa ya kaita toilet din dake falo, sai da ta amayar da abincin da taci duka har sai da ta fara kakari babu abinda ke fita sai majina, nan da nan ta gala baita, d’auraye mata jiki yayi ya dawo da ita falo, d’aki ya shiga ya d’auko key din mota, ya dauko mata gyale ya kama ta suka fito waje, suka shiga mota
Mai Gadi ya bude musu Gate ya fice da gudu zuwa Asibiti.
Hmm su basma ko dai an kusa zama uwa ne