YAR SHUGABA CHAPTER 35

YAR SHUGABA 
CHAPTER 35
Koda suka isa Asibiti direct dakin Likita suka nufa, nan take aka fara mata tests da sauran gwaje-gwaje, Likita ya tabbatar musu tana d‘auke da juna biyu harna tsawon wata biyu, Yaya Aryan farin ciki sosai ya kama shi, hatta ita kanta Basma farin ciki ya rufeta, nan take Likita ya rubuta musu Magani suka siya a pharmacy na Asibiti suka kamo hanyar Gida. Suna tafe bisa hanya Aryan tuki yake a hankali kwance cikin natsuwa, wani irin nishadi sukeji mara misaltuwa, hannunsa ya d’aura kan cikinta, da sauri ta kalleshi sai ya kashe mata ido daya cikin wani salo na murya yace “Ki kula min da kanki da Unborn Baby dinmu plss” 
Murmushi tayi ta gyara zama tace cikin shagwab’a “Uhum Ni fa nayi karama da Haihuwa dan bazan iya ba Haihuwa ba ance da wahala,ba tsoro nakeji” 
Waro ido waje yayi yace “To me kike nufl” “Ni dai tsoro nakeji amma ina son cikin sosai” 
Dariya yayi yana buga sitiyarin mota yace “wow My Basma rikici, bafa wani wahala da kinyi nishi shikenan fa” 
Hararan wasa tayi masa tace “ai su Meena sun bani labarin wahalan da suka sha wajen Haihuwa, ni dai ka tayani da Addu’a karya bani wuya Myn” ta karasa maganar cikin shagwaba. Shafa gefen kumatunta yayi yace 
“Babyna kullun cikin Addu’a nake miki karki damu, insha Allah zaki Haihu laflya dashi” murmushi tayi ta amsa da “Ameen”. a haka suka isa gida cike da farin ciki. 
Bayan Kwana Biyu’ Suna kwance Basma tayi pillow da hannunsa tace 
“Baby ina so karka gayawa kowa ina da ciki, nafl so su ganshi in ya fito” “Saboda me” ya jefa mata tambaya. 
“Kunya na keji” “Uhum su kunya ko, in ya fito zanga yanda za kiyi” Mirginawa tayi ta kwanji samansa, ido cikin ido suke kallonjuna sai ya sakar mata Murmushi, murguda masa baki tayi saiya sanya hannu ya kama bakin, kukan shagwaba ta fara sai ya saki yana dariya, tace “Baby ina son shan agwaluma” “What, ya fad’a da karfi, Na manta shi ma” 
kuka ta shiga rerawa ita lallai fa zata sha agwaluma, marairaice fuska yayi yace “Baby ina zan sameshi bama lokacinsa bane fa” 
Tashi tayi ta zauna ta fara tsotsan bayan hannunta, a dole tayi fushi, tashi yayi ya zauna shima ya jawota jikinshi, hab’arta ya d’ago yace “Babyna ki fad’i wani abun wanda kika san bazan sha wuyan nima ba pls” murguda masa baki tayi tace “Farar kasa da yalo” Ajiyarzuciya ya saki ya mata kiss a goshi sannan ya sauka bisa gadon yace “zan flta yanzu na nimo miki, inna siya zan bama driver ya kawo miki domin yau ina da aiki sosai a ofFIce” Bata ce masa kala ba ya shige toilet dan ya watsa ruwa, itama mikewa tayi tabi bayanshi, ta iske shi a baho yana wanka zuwa tayi itama ta shige ciki, dole ya aje nashi wankan yayi mata sannan ya daura mata towel ta fito, Murmushi yayi yace Wannan unborn Baby yasa Basma rikici, in da banyi mata wankan ba ta fara kuka‘ duk a 
zuciya yake wannan maganar. “ 
Bayan ya idar da nashi wankan ya fito ya taddata ta sanya atamfa dinkin riga da sket, tayi makeup kamar ba ita ba tayi kyau sosai, tsayawa yayi yana kallonta ta juyo fuska tana dariya tace 
Ya aka yine ka zuba min ido ko na sauya maka ne?” girgiza kai kawai yayi ya soma shiryawa, dama ta ciro masa kayan da zai sanya, kananun kaya ne da suit, zama yayi ta shirya shi, ta sanya masa riga da wando ta daure masa belt ta kuma yi sitokin dinsa, ya daura neck tie ta santa masa suit, turarukan sa ta shiga fesa masa har saida ya amshe yana fad’an 
Ya isa haka ko so kike ki k’
arar mini Madam rikici“ 
Murguda baki tayi ta matsa ta dauko gyalenta da hand bag, ta sanya takalmi mai tudu ta d’
aura igiyan ta dauki keyn motan Yaya Aryan tace Muje aikin ko” 
Sakin baki yayi yana kallonta, murmushi ta sakar masa ta kanne masa ido daya tare da kama hannunsa tanajaaa, suka fito falo masu aikinta ta basu oder duk abinda take so suyi mata, kana ta cigaba da Jan hannunsa suka fice. Bude motan tayi ta zauna mazaunin driver bai iya furta komai ba ya shiga gefenta ya zauna ta sanya key ta tada motar ta fice abinta. 
Lumshe ido yayi ya kwanatar da kanshi a bayan seat, saida su kayi tafiya mai nisa, tayi 
parking juyowa tayi a shagwabe tace Baby ko baka so in raka ka zuwa wurin aikin ne?“ Juyowa yayi ya kalleta sai ya daure fuska cikin sigar wasa baice komai ba, hawaye ne ya ciko idonta cikin rawar murya tace “Don Allah ka yafe min kar fushinka ya sani cikin tsinuwar Allah, bana fatan in bata 
maka rai” Hannunta ya kamo yace “Waye yace kin min laifi? nasan fa duk Baby dinmu yasa ki wannan aiki saboda baya son Momyn shi da Abbanshi su rabu” ya karasa maganar yana dariya tare da lakace hancinta, itama dariya ta saki ta tada mota suka wuce wurin aikinsa. 
Yau dai Basma da Aryan a tare suka yi aiki sai yamma lis suka tashi, kasuwa suka wuce sai da Aryan ya siya mata, farar kasa, yalo, da agwaluma harma da magarya duk ya hada ya siya da yawa. Cike da farin ciki suka dawo Gida. 
Karshen Wata‘ Ana gobe taronsu gaba d’aya Matasan Maza da Matansu suka had’u a Kaduna gidan Dady suka sauka, shirye-shirye suke wanda a lokacin sun gama samun Ma’aikata sun bud’e 
manyan office a Kaduna, Kano, Abuja. A Ranar taro anko suka yi Maza fararen shadda Matan kuma atamfa mai ratsin yallow, green da fari. Filin Murtala Square ya cika da mutane domin wannan taro na kaddamar da kungiyar ‘
QUEEN BASMA (‘YAR SHUGABA) FOUNDATION.‘ Manyan Mutane Mata da Maza sun halarta da yake abin na ‘ya’yan Manya ne, hatta Dady yaje wurin da mukarabansa, Mal” Martaba Sarki shima yaje da Sarkin Zaria ya harta, Abba bai samu halarta ba saboda yayi tafiya, sunyi taro cikin farin ciki da lumana, an bazajami’an tsaro har aka gama babu wani tashin hankali k0 hatsaniya, sun raba abubuwa da dama kama daga Abinci, Suturu, Kudade ga talakawa da nakasassu, ba karamin farin ciki suka sanya a zukatan Mutane ba, kowa ya tafi Gidansa yana mai sanya musu Albarka. 
Bayan komai ya lafa duk suka koma gidan Dady, suka hada karamin walima a gidan da yamma, sun ci sun sha tare da sada hiran zumunci. Washe Gari ko wanne ya kama hanyar garinsu. *Da Dare’ Bayan Sallan Isha’i, Basma na zaune a falo tayi dirshen a kasan kafet tana cin tuwon Dawa miyar Kubewa danya, Aryan na gefenta yana cin farfesun kayan ciki tare da jelofdin cus-cus wanda yaji kayan lanbu. Basma sai surutu take yi tana cin abinci, kuma wannan ba halinta bane, Yaya Aryan tun yana amsa mata sai yayi banza da ita ya daina amsa mata, dago kai tayi ta kalleshi tace “Myn shine ka shareni ko?” “To Basma me zance miki, gaba daya kin sauya hali, wannan cikin ya sanya miki dabi’u da ba naki ba, cin abinci kike kina surutu, ta yaya abincin zaiyi miki Albarka?” Marairaice fuska tayi tace “To 
na bari Gwara dai ki bari, in ba so kike muyi fada ba, kuma ki ci a nutse dan babu mai kwace miki” Ai bai rufe baki ba ta mike a zuciye zata bar wurin, da sauri ya kama hannunsa ya soma lallashinta, da kyar ya samu ta sakko, zaman da zata yine ya lura da bayan rigarta ya baci dajini, da karfi yace “Babyna me ya kawojini ajikin ki?” A tsorace ta jawo rigan ta gani, kuka ta fara tana fad’an “Shikenan Yaya Aryan cikin ya zube, na bani” A firgice Aryan ya dauketa ya fice da ita da gudu, mota ya sanya ta ya shiga, a sukwane yabar gidan. Yaya Ahmad ya fito daga part din su zai fita, sai yaga fitan Yaya Aryan daga gidan a guje, shima da sauri ya shiga tashi motar ya rufa musu baya a sittin. 
‘A Asibiti’ 
Dakin gaggawa aka shigar da ita, a lokacin ciwon mara ya fara damunta, Addu’a take tana ambaton Allah. A waje kuma Yaya Ahmad ya cimma Yaya Aryan yana tambayan sa abinda ya faru, cikin damuwa Aryan ya labarta masa a takaice, mamaki ya kama Yaya Ahmad yace “Dama tana dajuna biyu kenan?” Aryan ya girgiza masa kai alaman Eh. Likita yayi kokari sosai wajen tsaida jinin, sannan ya d’aura mata drip barci mai nauyi ya dauketa. Likita ya flto Yaya Aryan ya tare shi, hannunsa ya kama suka wuce office d’insa, Yaya Ahmad yana biye dasu. Duk suka zauna suna sauraren Likita yace “Gaskiya da kyar muka shawo kan matsalan amma Alhamdulillah cikin bai fita ba, dan haka dole a kikaye dan Mahaifarta ba tada karfi, zata samu bed rest, komai yi mata za’ayi game da aikin gida, sannan a kiyaye yawan zirga-zirga da ita, ya zama na ta rika natsuwa wuri daya har sai cikin ya kai wata biyar daga nan ta fita daga wannan risk d’in” Ajiyar Zuciya Yaya Aryan ya saki tare da godewa Allah, Yaya Ahmad yace “Ina ganin fa jugu-jugun taron jiyan nan shine ya haifar mata da wannan matsalan” dan haka sai mu kiyaye fitanta ko ka maida ta gida wurin su Ammi” Da sauri Aryan ya dago kai yace “A’a baza ta ko ina ba zan kula da ita” Yaya Ahmad ya dafa shi yana dariya, kunya ce ya kama shi, ya manta shaf Yaya Ahmad Yayan Basma ne, nan Doctor ya rubuta Magani ya basu sallama inta farka su tafi gida. Sai karfe sha d’aya na dare ta farka, cikinta ta shafa tajuyo ta kalli Yaya Aryan tace “Ya fita k0?” tana zubar da kwalla, murmushi yayi mata tare da matsawa kusa da ita yace “Babynmu yana nan yace ba zai sa Momy da Abbanshi kuka ba” Murmushi tayi, ya taimaka mata ta zauna, sai a sannan ne ta lura da Yaya Ahmad a wurin kunya ce ta rufeta tace “Au ashe Yaya Ahmad kazo?” Dariya yayi yace “Ina zaki san ina wurin bacin ta Unborn Baby d’inki kike” Rufe ido tayi da tafin hannunta tana dariya. Gida suka wuce. Tun daga ranar kowa yasan Basma tana da juna biyu, aiki kuma bata komai sai dai taci ta kwanta, tayi b’ul-b’ul da kyau, soyayya kuma tsakanin Basma da Aryan sai abinda yayi gaba. A haka har cikinta ya kai wata tara, cikin yayi k’ato ta kunbura, Haihuwa ko yau ko gobe, Yaya Aryan yaki yarda Basma ta koma gida shike jikilan komai nata. 
Hmm

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE