YAR SHUGABA CHAPTER 36 THEND

YAR SHUGABA 
CHAPTER 36 THEND
KARSHE
‘Cikin Basma Wata Tara Da Sati Biyu“ 
Basma ce a cikin kitchen tana zuba Peppe Meat a plat, fitowa tayi tana jan kafa da alama cikinta yayi mata nauyi sosai, zama tayi akan kushim ta fara ci tare da cuna baki alamar yaji ya dame ta, haka tayi taci tana gumi tare da shan Gwabajuice, haka ta cinye tas tare da lashe hannu, da alama bai isheta ba sai ta kwalawa daya daga cikin masu aikinta kira “Uwale, Uwale” da sassarfa ta fito ta risina tace “Hajiya gani” 
“Yauwa karomin peppe Meat din nan, ki zuba min da yawa sannan ki dauko min goran ruwa da cup ki kawo min” Jiki na rawa Uwale ta wuce kitchen ta kawo mata gaba daya duk abinda take so, zama ta gyara ta cigaba da cin kayanta tanaci tana shan ruwa saboda bala‘in yaji data zuba a ciki. 
Sallaman su Meena da Deeja ne ya katse ta, ta amsa musu, zama duk suka yi suna yi mata tsiya 
“kullun in muka shigo sai mun ganki da wani abun kina ci, acici ” Meena ce take fadan haka. 
Dariya kawai tayi musu ta cigaba da cin abin ta, hira suke sosai suna tattaunawa akan taron daya gudana a garin Katsina wanda Basma bata samu zuwa ba, hakika taron ya kayatar kuma sun tattauna akan Matsalolin masu yima Yara kanana fyade, Basma tace 
Wallahi nayi missing taron kuma ba haka naso ba” Deeja ta lura da yanda Basma take yatsine fuska cikin kulawa tace yadai naga tun dazu kina ta yamutse fuska kodai abin yazo ne?” Murmushi kawai tayi tace “inda yazo kya ganni ina dirkan abinci” Dariya suka yi mata, Meena ta mike tace “Kinga bari naje na shirya Yaya Naufal ya kusa shigowa kunsan da an sakko Sallan Juma’a suke dawowa” 
Deeja ma mikewa tayi tace “Hakane ‘Yar Uwa, nima bari naje na shirya kinsan yau akwai yini a gidan Abba bayan Sallan La’asar” Nan suka yiwa Basma Sallama, sai tace Uhum masu Maza to sai ku tafi kan kuda ya riga ku” Dariya suka kwashe dashi suka fita. 
Basmaji taji cikin ta yayi mata hake-hake da kar take numfashi, gyara zama tayi ta jingina jikin kushim, a fili tace Ya Rabb ka rabani lafiya da abinda ke cikin nan, kayi masa albarka da kyakkyawan Albarkanka, Ameen, yau dai cikin nan ya daure min sosai to Allah gani gareka” Bata rufe baki ba cikin ya fara tsingulinta, da sauri ta mike tana jan kafa ta shiga daki ta dauko key na Motanta, fitowa tayi ta bama masu aikinta order akan abinda take so suyi mata, sai ta fita tana nishi, gaba d’aya ciwon mara ya soma damunta, driver ta kira yazo ta mika masa keyn Motarta tace Kaini Asibiti” ba musu ya amsa cikin girmamawa. 
Kafin sukai Asibiti ciwo ya tsananta salati kawai take yi, da sauri Driver ya kira Nurses suka zo suka shiga da Basma cikin Asibiti dakin Haihuwa suka wuce da ita, Nurse Sa’a ta dubata tana 8cm, da alama tajima tana nakud’ar a tsaitsaye inji Nurse din, Basma nakuda ta taso sosai Aryan take kira tare da Abbanta, hawaye ya na zuba, Addu’a take da niman sassauci a wurin Allah. Yaya Aryan yana gun Aiki ji yayi Kansa ya sara masa, gabansa ne ya fad’i, a lifi ya furta Basma, da sauri ya mike yabar abinda ya keyi ya soma hada kayansa,jaka ya dauka ya sanya hularsa ya flto,Massinger ne yace Yallab’ai akwai masu jiranka suna wurin Alhaji Naufal” 
Yana tafiya yace “kace su dawo ranar Monday wani uziri ya taso min“. Mota ya shige ya kamo hanyar gida, wayar Basma yaketa kira amma bata dauka ba, Basma a gida ta bar wayan, hankalinsa ne ya kuma tashi, wayar Deeja ya kira ya tambayeta Basma tace 
“Ban jima da fitowa daga part dinku ba ina ganin tayi barci ne” Cikin damuwa yace “0k“ ya kashe wayar. Basma ta cika 10cm haihuwa ta taso amai ta fara yi, haihuwarta mai fayar baki ne, amai take sosai tana yunkuri, bayan ta gama aman sai nak’udar ta lafa a hankali barci ya fara fizgarta, hutun minti biyar tayi nakudar ya dawo, cikin ikwan Allah bata kara minti goma ba ta haifo danta Namiji mai kama da Aryan sak. Yaron kato sai ihu yake Hamdala Basma ta shiga jerowa da yiwa Allah Tasbihi. 
Yaya Aryan ya shiga kan layinsu kenan wayarsa ya dauki kara, Likintansu ne ya kira shi ya dauka suka gaisa sai Likita yace “Madam tazo ita kadai Asibiti ba tare da kowa ba sai Driver, yanzu haka tana Labour Room, muna so a kawo kayan Baby” Da karfi Aryan yace “ta Haihuwa ne?” Likita yace “A’a tana gab, ku kawo kayan da sauri” Godiya Yaya Aryan yayi masa, sai ya juya akalan Motansa ya nufi Asibiti, wayar Deeja ya kira yace mata “Ki shiga part dinmu ki hado kayan Baby, da wanda Basma zata canza, da duk kayan da ake bukata a Asibiti sai ku tawo” bai jira amsar da zata bashi ba ya kashe. Farin ciki ne ya rufe Deeja ta flto da sauri, Allah yasa ta idar da Sallah kenan tasa kaya. Hada kayan tayi ta shiga wajen Meena tare suka tawo suka kira su Momy a waya suka sanar dasu. Basma an ciro Mahaifa an gyara mata jiki, kaya ya rage a kawo ta sauya, Baby ma haka, 
Yaya Aryan a sittin ya shiga d’akin Haihuwar bai jira an bashi izini ba, Nurse Sa’a ta dakatar dashi “Dan Allah Kaje waje mu gama tukuna saika shigo” Ko saurarenta baiyi ba ya isa wurin Basma ya kama hannunta gam yace cikin muryan tausayawa 
“Babyna Allah ya saukeki lafia” tare da matsar kwalla. Murmushi Basma tayi sai ta kai hannunsa wajen cikinta tace “Babynmu baya cikina yanzu dan ya fito” ware ido yayi ya shiga waige-waige, hango gadon Yaron yayi ya isa wurin, ya ganshi a cikin towel an kudun-dune shi, hannunsa na rawa ya kai ya d’auko shi, farin ciki ya sanya shi fitan kwalla, ya shiga jero masa Addu’a tare da godewa Allah, Basma na kallonsu tana murmushin farin ciki cike da so da k’aunar su. 
Nurse Sa’a ce ta amshi Yaron don su sanya masa kayansa da su Deeja suka kawo, Basma ma sanya kayanta tayi Aryan ya d’auketa cak ya kaita d’akin hutawa na masu Haihuwa. Meena da Deeja suka rufa musu baya, dai-dai lokacin Ammi tazo tabi bayansu. Momy taki zuwa saboda kunyar ‘Yar fari. 
‘Bayan Sallan La’asar‘ 
Aka basu Sallama suka wuce gidan Abba gaba daya. A side din Ammi Basma suka sauka tare da Babynsu. Nan fa kan ace miye gida ya soma cika da ‘yan barka sunata zuwa, Anty Husnah ma da sauri tazo gidan dan ganin idon Basma an zama Mama, tasha tsiya wurin su Deeja, amma kuma sun yabama kokarinta da juriya data iya kai kanta Asibiti. Abba yayi Murna da ganin jikinsa ya amsa Yaron yayi masa Addu’a tare da hud’uba. Duk sun sanar da dangi wanda suke nesa, da yawansu sun daura damaran zuwa Abuja a washe gari, kuma in suka zo sai anyi suna zasu tafi. Leema kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a Abuja don Murna, haka ma Safeena ta kosa Gari ya waye su kamo hanya, Shureym sai da yaji wani iri aransa yace “Da yanzu wannan Yaron nawa ne, Allah Sarki, na amshi wannan kaddaran tawa, ka yafe min dukkan kuskuran dana aikata”. Nima na tayaka da Ameen. . 
Ranar Suna’ 
Yaro yaci sunan ‘Aliyu’ Mahaifinsu Aryan, Suna kiransa da ‘Hydar’, ba karamin shagali suka shirya ba, wannan hidima ya tara Manyan Mutane Sarakuna da Manyan ‘Yan Kasuwa. An shirya kayataccen Walima bayan Sallan Isha’i a babban hall dake Abuja, hatta Abba dasu Mai Martaba, Dady duk sunje wurin, har Momy da take kunyar ‘yar fari taje wurin, su Kaka Ma’u, Inna, Malam kawai suka bari a gidan, Wata Babbar Malama suka gayyata tazo ta bada Fatawa akan ‘Tarbiyyan Yara A Musulunci’. 
Da farko Tarbiyyan Yara sun rataya akan Uba da Uwa wanda aka samu wannan Da daga Jikinsu. Uba dole ne ya samarwa ‘Ya’yansa Uwa Tagari haka itama Uwa dole ne ta samawa ‘Ya’yanta Uba Nagari, Tarbiyya yana farawa ne tun daga ginshikin Neman Aure. Ma’aurata dole ne a yayin saduwa suyi Addu’a kamar yanda Monzon Allah s.a.w ya koyar damu kafin iyaye su kaiga saduwar Aure, kunga kenan an fara samar da Dan ta kyakkyawa hanya, daga nan lokacin da aka samu cikin wannan da, Uwa dole ne ta zama mai hak’uri tare ya yawaita Addu’a don samun da Nagari, Uba kaima yana da kyau ka sanya ido ka bata kulawa sosai tare da Addu’a har Allah ya sauketa Lafiya. 
Wasu Iyayen sukan fara da tsinewa ciki tun kan yazo Duniya, sai kuji Uwa na cewa ‘Wannan shegen cikin ya isheni da muntsili’ ‘Na kosa wannan jarababen cikin nan ya fito na huta’ Wannan cikin kaza-kaza, tun da na ciki wata Uwar ke fara lalata shi kafin ya fito Duniya, dan haka jan kunne garemu Mata Ku kula sosai yayin irin wannan halin da kuka tsinci kanku, mugun furuci yana lalata Tarbiyyar Yaro, ki zama mai hakuri da juriya domin a wannan lokacin kina cikin wani jarabawa ne mai dinbin lada, ki zama mai yin Addu’a da niman sauki a wurin Allah yayin da cikin ya dame ki. Sannan bayan an haifi Yaro, Uba zai masa kiran Sallah da hud’uba da sunansa, a wannan lokacin da zai hanasu barci wani Uban yaita tsaki yana zage-zage, wata Uwar kuma ma kaji tace ‘wane kaza ka cika shegen kuka ai Allah wadaran wannan rikici naka’, to wallahi dole sai mun kiyaye fidda mugayen kalami akan Yaranmu. Duk abinda Uwa zata yi dole sai kin sanya ido da hak’uri da kuma Juriya, kuma dole sai kin fara gyara halayyarki kafin ki fara kafa tubalin Tarbiyyan Yaranki. Domin wasu Yaran yayin tasowarsu sukan fara koyan wasu halayya da Uwarsu keyi, koda ace mara kyaune a ganinsu mai kyaune tunda sun ga Uwarsu tayi. Dan haka dole mu Iyaye Mata muna sanya ido a kan Yaranmu domin Mune Makarantar farko ga Yaranmu. Sannan da zararyaro ya taso nuna masa yin Ibada akan lokaci, koyar dashi Addu’an safe da maraice, na shiga bayi, fita gida da sauran Azkar, kasance mai jansu a jiki kina tunatar dasu Tsoron Allah, ki sanyawa d’anki Tak’awa da kuma Tauhidi, nuna masa yanda Azabar Allah yake a ranar gobe kiyama in suka saba masa, ki tsawatar musu in suna wasa da Sallah, kijasu ajikinki a nan ne zaki rikajin dukkan matsalolin su, rika duba takardunsu na makaranta kina ganin abinda yara ke ciki game da karatunsu. . Kaima Uba ka ja ‘ya’yanka ajikinka banda daure fuska, ko daka dawo daga aiki su rika gudu suna tsoron fadanka, zauna dasu tamkar abokanka kayi wasa dasu ka tunatar dasu hakkokin Allah wanda ya rayata akan su. Ka sanya su a makaranta masu kyau, karka zama me kyashin biya musu kudin makaranta. Sannan mu sani yawan duka baya shirya yaro sai dai ya kangarar dashi, mu rika musu fada da Nasiha, karmu gaji. lnsha Allah duk abinda ya gani na sabon Allah zai guje shi, zai kasance mai gudun Bacin ranku, zai zama kamili nagari abin sha,awa gun kowa, Mutane zasu rika kwatantaku cikin sawun Iyaye Nagari, haka yaron za’a rika kwatance dashi a cikin ‘Ya’ya Nagari. Allah ya bamu ikwan Tarbiyyantar da Yaranmu bisa tafarkin Al-Qur’ni da Sunnah. Ameen ya Rabb 
Sai karfe Goma na dare aka gama wannan Walima, kowa ya koma Gida lafiya. Walimarya burge Mutane sosai game da yanda Malamarta bada bayani akan ‘Tarbiyyan Yara A Musulunci’. Anan Mami ta gane cewa tayi kuskure wajen Tarbiyyan Shureym, ta kuma d’auki Alkhawarin niman gafaransa, da gyara kuskurenta akan jikokinta. 
Bayan Wata Guda’ 
Deeja itama ta sullubo ‘Yarta Mace kyakkyawa mai kama da Basma, ranar suna taci sunan Umma ‘Aisha’. Kamar yanda aka yi taron sunan Hydar haka akayi na Aisha, an shirya Walima kyatacce akan “Tarbiyyan Yara A Musulunci’ 
Anyi taro laflya aka watse lafiya. Inna itace ta zaunawa Deeja har zuwa tayi Arba‘in. 
’Bayan Kammala Wankan Jego’ 
Basma ta gama wanka, zaune take tasha kwaliya cikin dinkin riga da sket na atamfa, Baby Hydar yana gefenta ta kwantar dashi, wayarta ce a hannunta tana latsawa da alama charting take yi, Sallaman Yaya Aryan shine ya katseta ta dago cikin murmushi tare da kallon so ta amsa masa, isa yayi kusa da ita ya zauna tare da rausayar da kai gefe yace 
“Babyna kinga yanda ki kayi kyau kuwa, kamar Baby Hydar bai ma jikinkiba meye sirrin?” Murmushi tayi wanda ya bayyana farin cikin ta tace “Myn bafa komai, Ni ce dai yanda ka sanni sai dai fa na samu kyakkyawan kulawa wurin 
Ammi dan haka ita zaka tambaya sirrin” Hararan wasa yayi mata yace “Kinsan dai babu wannan tsakanina da Ammi, a bakinki ya kamata naji komai, yanzu dai mu bar wannan maganar yaushe zaki dawo gidanmu, ina missing d’inki Baby love, da kyar nake iya barci fa” ya karasa maganar cikin muryar tausayi. Kanne masa ido d’aya tayi tace 
“Uhum Myn nifa sai nayi wata biyu zan dawo” Ido ya zaro waje yama kasa magana, da gudu ta mik’e ta bar wurin tana kwasan dariya, girgiza kai yayi ya dauki Baby Hydar yabi’ bayanta, d’akinta ya sameta ya kwanar da Baby Hydar ya matsa wurin ta yace 
“Babyna ko so kike in shiga wani hali?”Dago fuska tayi tana kallonshi cikin ido tace “Baby nima na kosa na dawo gareka amma bansan ya zanyi ba, bazan iya sanar wa Ammi hakan ba, ka k’
ara hakuri suma sunsan ya kamata na koma karka damu” ‘ 
Ajiyar zuciya ya saki tare da busa iska mai zafl yace “ki shirya zanzo gobe Insha Allah zamu ma” Ido ta zaro waje tace “ina zamu kuma Myn? kunya nakeji” 
Murmushi yayi yace “Hotel zamu domin ina da buk’atar Babyna in baso take in fara biye-biye ba” 
Da sauri ta had’e bakinta da nashi domin bata son ya k’arasa maganar, sai da suka d’auki 
minti goma kana ta janye jikinta tare da sauke ajiyar zuciya, cikin kasalan murya tace “Myn karka k’ara furta kalman da ya fito a bikinka domin kanada ni, Insha Allah zan kasance da kai a koda yaushe ba zan gaji da kai ba tunda nima inada bukatarka, zan shirya mu flta amma gidanmu zamu ba Hotel ba, domin in samar maka farin ciki sweet babyna” saita manna masa kiss a goshinsa ta mike, tana mai cewa “bari na kawo maka abinci dan nasan da wiya in kaci na rana”. 
Bud”e kofar da zata yi ne taci karo da Ammi, Ammi tace “Ina zaki kike sauri haka?” Sosa keya tayi tace “Abinci zan kawowa Yaya Aryan” “0k ga wannan ki shanye shi zuwa anjima da yamma” ta amsa goran tana godiya. ‘Bayan Sallan La’asar’ Ammi ta sameta a d’aki tace “Basma je kiyi wa Momynki Sallama yau zaki koma gida, da fatan kin gama shirya kayanki?” 
“Eh Ammi na kammala bayan Yaya Aryan ya tafi” 
“To madalla” saita fita. Tana isa part din Momy ta sameta zaune saman kushim tana karanta wani Jarlda, sallaman da tayi ne yasa ta aje Jaridar a gefe ta amsa mata, Basma ta isa gefenta ta zauna tare da kama hannunta tace 
“Momyna sannu da hutawa” “Yauwa My Basma” “Nazo muyi sallama ne Ammi tace yau zan koma gida” ta karasa maganar cike da shagwab‘a. 
Hararan wasa ta mata tace 
“Basma sai yaushe zaki girma da yin shagwaba ne?” Murmushi tayi ta langwab’ar da kai gefe tace “Uhum Momy ina dake fa kinga kuwa bazan daina shagwab’a ba, ga Abba da Ammi, ga Dady da Ummin kd dasu Kaka Ma’u duk inada ku fa” Momy tayi dariya tare da lakace hancinta tace “Ki dai ragewa su Hydar” Kunya ya rufeta ta sunkuyar da kai kasa tana murmushi tare da wasa da yatsun hannunta. Momy ta gyara zama tare da kiran sunan ta, Basma ta dago taga babu alamar wasa a tattare da Momy, natsuwarta ta tattaro tace “Na’am Momy” Momy tace 
“Basma ina son in miki tuni akan hakk’in Mijinki dake kanki, Mata da dama wasu na kuskure akan da zarar Mace ta haihu saita jingine bukatun Mijinta ta kama na Yaronta kuma wannan ba dai-dai bane, hakkin Miji shine farko kafin hakkin ‘Ya’ya,A Ranar Gabe K’iyama Allah yana fara tambayan hakkin Miji ne kafin hakkin ‘Ya’ya, sannan Aljannarki yana k’afar Mijinki inya d’aga ki shiga Aljanna, in kuma ya danne ki auka wuta. Allah yayi mana tsaru da wuta Ameen. Dan haka sai munyi karatun tanatsu sosai, Mata da dama sunajingine need d’in Mijinsu da zarar sun Haihu, wata ma ba tada lokacin wani hira da Miji ko girka masa abinci, kullun itace hidimar yaranta ba ruwanta da farin cikin Mijinta ko bacin ransa, wata ma saboda d’anta saita hana miji hakkinsa, wai adole ita mai d’a, to wallahi mu hankalta Musani shi Miji yanada matuk’ar mahimmanci dole ne mu rika kula dasu muna basu lokutanmu domin samun dacewa. Ki ware lokutanki kina tsarawa kanki ko wanne ki fita hakkinsa, Miji da kuma Yaranki, su 
Kansu mazan suna tausayawa Matan akan wasu hidimomin gidan har suke tayasu ma. 
“Maza da dama suna fuskanta kalubale a wurin wasu Matan nasu da zarar Mace ta haihu, ita kullun ba data lokacinsa, wata ma ta daina yin kwalliya, wata kuma tsafta ma ta rage, wata kuma yin abinci ma sai dole, babu wani kyale kyale da Miji zai gani a wurin Matarsa da zai sashi sha’awarta. Da ance wance kaza kin daina abubuwa kaza kin sauya, saita ce hidimar Yara sune suke hanata. Hakan kesa Mazan suna sha’awar Matan dake waje masu kwalliya da kyale-kyale, da ya samu mai sonsa saiki fara damuwa Mijinki ya sauya miki, ke 
kaza~kaza, bacin kece kika bashi kofar yin hakan. Shi dai haihuwa bazai sanya ki zama kazama ba ko ki zama mara kwalliya da gyaran jiki ba, sai in dama kin sanyawa ranki sangarci, lalaci, son jiki da kuma rashin tunani, dan haka Mata mu kula sosai, dan da wadannan matsalolin da wasummu suke fuskanta a gidan aure 
muke fara bada kofar aukuwarsa. 
Namiji kamar Yaro yakejin kansa, yana bukatar kulawa da tarairaya, ‘yar soyayyan nan k0 ‘Ya’ya nawa ki kayi baki tsufa da yinshi ba, kullun kina gyara kina tsafta Mijinki zai rik’a miki kallon yarinya ce”. Basma shuru tayi, gaba d’aya jikinta ya mutu tace “Momy yanzu kina nufin da safe kafin in fara indimar Hydar na Babanshi zan fara?” Momy ‘yar dariyarsu ta Murmushi tayi tace 
“kwarai kuwa, ba da safe bama a ko wani lokaci ma, in har Mijinki mai fitan safiya ne dole ki tashi ki fara masa hidima kafin ya fita ki tabbatar ya fita da farin ciki a ransa wanda in ya tuna zai rik’a Murmushi da farin ciki, kinga kin samar masa farin ciki wanda ko ya fita hankalinsa da tunaninsa yana wurinki zai rika Allah-Allah ya dawo gida. Ki zama mai kwalliya, canza shiga iri-iri, karki nacewa shiga guda d’aya, kamshi karya rabu dake ki zama mai amfani da turaruka masu sanyin kamshi, kuma kala-kala, karki yarda Mijinki ya fahimci kamshin ki guda d’aya ne, ya zamana daban-daban, kuma ki tanada masu taushin kamshi na kwanciya barci ne wannan kawai. Kamshi yana daya daga cikin 
sirrin mace wanda zata mallaki zuciyar mijinta cikin sauki. Sannan ki rik’a wa Mijinki Addu’a a fili da kuma a boye, in zai fita bishi da Addu’a tare da tarairaya wanda in ya tuna ki ya saki murmushi. Kuma karki kuskura ki sakarwa ‘yar aiki hidimar mijinki dan wasu matsalolin daga nan yake farawa, sai kiji ance ‘yar aiki ta aure 
mijin matar gida, wannan duk sakacin matane akan kula da hakkin Miji. Nasan duk kin 
sannan wannan abubuwan tuni dai nake miki“. 
Ajiyar zuciya Basma ta saki mai karfi tace “Momy nagode sosai, hakika duk Macen da tayi amfani da shawarwarinki zai mata amfani matuka sosai, Allah ya saka Miki da Aljanna yasa ki gama da duniya lafiya, ina alfahri da samunki A matsayinki na Uwa a gareni, love u much Mom” ta karasa maganar tana matsar kwalla. 
Momy tayi Murmushi tace “Ai Basma lokacin ma yayi mana kadan, Dariya Basma tayi ta mike tace “Momy Anty tana kokari sosai ina jinjina mata matuk’a” 
Momy ta wuce d’aki ta hado mata wasu magunguna ta bata, Basma ta amsa tana murmushi cike da jin kunya tayi mata Godiya. 
Hmm nace kunga Iyayen zamani’. Ammi itace ta mai da Basma gidanta, sai gabda Magrib ta barota ta dawo Gida. 
Yaya Aryan sai bayan Sallan isha’i ya shigo gidan, mamaki ya cika shi yanda kamshin Abinci ya cika masa hanci daga kitchen, tunani ya shiga yi, yasan tabbas ma’aikatan gidan 
sun gama aikinsu sun wuce part din su, tambayan kansa yake 
‘Waye a gidan nan?’ Dan sam bai san da dawowar Basma ba. Zama yayi a falo yana jiran yaga wanda zai fito, baifl minti biyar da zamansa ba Basma ta fito cikin shiga na English Wears riga da sket, rigar iya cibiya ya tsaya mata, sket din kuma iya rabin cinya, gashin kanta ta d’aure shi da ribom ta saki jelan a bayanta, kamshi take zubawa mai sanyin k’amshi, Baby Hydar ta sabashi a kafad’a, shima ta zuba masa nashi kwalliyar. Yaya Aryan sakin baki yayi yana kallonta harta karasa wurinsa, kwantar da Hydar tayi ta koma kusa da shi ta zauna tare da kallonsa tana murmushi ta daura kafa d’aya kan daya, hura masa iskan bakinta tayi a idonsa, ya lumshi ya kuma bud’ewa, magana zai yi ta had’e bakinta da nashi suka lula duniyar masoya, sun dauki kusan rabin awa suna faranta ran juna, daga bisani Basma ta janye jikinta tace cikin kasala 
“Muje kaci abinci” Murmushi kawai yayi ya mike ya d’auki Baby Hydar yace “Ki sameni a daki” 
Bin bayansa tayi cike da farin ciki tace da karfl “I love u Yaya Aryan” Sai yajuwo cikin kulawa tare da dage gira yace
“Love u too My Queen” Ya dawo kusa da ita ya kamo hannunta suka koma suka zauna yace 
“Basma kin zamo min haske a rayuwata, sonki halitta ne daga tsatsonjikina, zan kasance 
dake har abada taurauwata, zan cigaba sa shayar dake da ruwan farin ciki wanda yake kwaranya daga koramar masoya” Ya sumbaci bayan hannunta. 
Tace “ina sonka Mijina, Allah ya kara mana zaman lafiya da kwanciyar Hankali, ya kauda dukkan shairin Shaidan, Mutum da Aljan, ya kara maka budi na Alkhairiya da kuma Albarkaci zuri’anmu” “Ameen ya Habibty” ya amsa tare da manna mata kiss a baki, daga bisani sai suka mike suka wuce d’akinsu, dan cigaba da shayarda juna Zumar Masoya. 
‘Tammat Bi Hamdillah‘ ‘_Alhamdulillah Ala Kullu Halin_’ 
Alhamdulillah, Yau Allah ya bani damar kammala wannan littafi mai suna “YAR SHUGABA‘, 
ina mai godiya ga Allah S.W.A daya bani ikon kammlashi cikin koshin lafiya. 
‘_MASOYANA_’ 
_‘Bani da bakin gode muku masoyana masu bibiyar wannan labari, kunada yawa domin lissafaku wani sabon littafi zan cika, Allah ya saka muku da Alkhairi ya kara mana zumunci ya kuma hada fuskokinmu a Gidan Aljanna. Ameen. Addu’o’inku yana isa gareni, Nagode sosai wallahi ina sonku sosai, so wanda baida algush., so irin da yawa din nan, irin totally din nan, ina yinku ba adadi Allah ya bar kauna. Ameen. 
Wannan labari kamar yanda na fada a farko kagaggen labarine, banyishi ko dan wata k0 wani ba, hasalima idan muka fuskanci labarin yasha banban da yana yin mulkin kasar mu da ma sarauta. Na yishi ne domin ilmantarwa da kuma fadakarwa acikin siga na nishad’antarwa.‘ 
Allah ya bamu ikwan Amfani da abinda ke cikin wannan labari, kuskuren dake ciki Allah ya nisantamu dashi ya yafe mana gaba daya. Ameen._ 
sai kun jini a sabon littafi wanda zaizo nan bada dadewa ba

 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE