YAR SHUGABA CHAPTER 5

YAR SHUGABA
CHAPTER 5
‘washe gari’ 
Basma ta tafi aiken Momy da misalin karfe sha biyu na rana, gidan hajiya Aisha ta tafl ta kaimata sakon Momy. A hanyarta na dawowa ne saita wuce gidan hutu ta dauko wasu kayanta kana ta kama hanyar gida, escot na biye da ita a baya, ta hau kan babban hanya bata ankara ba ta bige wata Yarinya, cike da tashin hankali ta koma bakin hanya tayi parking, bodyguard suka fito a motansu suka nufa wacce ta bige, saboda tsoro Basma ta kasa fitowa, sun ganta kwance cikin jini a sume, cikin sauri daya daga cikin ascot din ya isa gun basma yace Hajiya Yarinya ta suma fa” cikin sarkewan murya tace “ku sata a motanku a seat na baya, sai kuzo ku biyu ku shiga tawa motan tunda ku hudu ne” cikin sauri ya amsa “yes Madam” ya tafl tare da cika umarnin data basu. 
General hospital direct suka wuce, aka wuce da ita emergency room, cikin sauri Basma ta dauki wayarta ta kira Yaya Ahmad ta shaida masa suna cikin asibity ta bige wata yazo da sauri, baifi minti biyar da kiranshi ba saiga shi yazo yace “ina take?” cikin damuwa tace 
tana emergency room” bata kaiga karasawa ba ya wuce ciki. 
Zarya ta shiga yi hankalinta a tashe ganin ma ashe ba karamar Yarinya ta bige ba budurwa ce, an dauki kusan minti talatin kafin duka likitocin suka fito, da sauri Basma ta tari Yaya Ahmad tace “Yaya ta farfado kuwa?” cike da tausayawa kanwar tashi ganin yanda ta burkice yace 
“ta farfado yanzu dai ta samu barci kuma anyi mata dressing inda taji ciwo, nan da awa guda zata farka insha Allah”. Da karfi Basma tayi ajiyan zuciya tace “Alhamdulillah” sai Yaya ya jefo mata tambaya yace “in kikaje ne har kika bigeta?” gefe ta koma ta samu wuri ta zauna, shima binta yayi ya zauna, nan ta bashi labarin yanda ya faru. Ya girgaza kai yace “Allah ya kyauta gaba, amma meyasa kikayi driving da kanki” murmushi tayi tace 
“Yaya Ahmad wlh kawai hakanan naji ina sha’awartuka kaina” Dariya yayi yace 
“hmm su Basma rikici, kije gida kawai saiki turo Shugaban mai kula da sashin Ammi Baba kulu tazo ta zauna da ita, tunda ke yau nasan kinada bako ya kusa sauka ma”, murmushi tayi tace “tom Yaya Ahmad bari naje anjima zan dawo insha Allah” “ok sai kin dawo, ki kula da kankifa” 
“insha Allah Yaya zan kula” suka rabu cikin farin ciki. Tana isa gida taje ta samu Baba Kulu ta sanar da ita sakon Yaya Ahmad, driver zai kaita, cikin sauri Baba kulu ta tafi. Basma tasa masu aikin Kicin na bangaran Ammi ta sanar musu abincin da za suyi mata na tarban bakonta. Sai ta nufi sashin Momy ta samesu zaune da Ammi suna magana ta gaishesu kana tace 
“Momy na kai mata sakon tace za kuyi waya” Momy tace 
“ok, amma naga kin dade ko kin biya gidan hutun naki da kika saba?” murmushi tayi tace “a’a Momy wallahi a kan hanyar dawowa na gida, na bige wata, yanzu haka tana asibity, na tura Baba Kulu ta zauna da ita zuwa anjima zan koma” cikin tashin hankali Ammi da Momy suka hada baki 
“subhanallah da fatan dai abin da sauki” murmushi tayi tace 
“da sauki kamar yanda Yaya Ahmad ya sanar dani shiyasa na taho ma” Ammi tace “to Allah ya bata laflya ya kuma tsare na gaba” duk suka amsa da “Amin”. Saita shiga dakinta dake sashin Momy. 
Tana Shiga ta fada makeken gadonta wayarta tajawo ta duba taga miss call din su Meena, kiranta tayi bugu buyu ta dauka, Meena bata jira Basma ta yi magana tace “wlh Basma ba kida kirki,jiya ko ki kiramu kiji ya muka sauka” cikin natsuwa tace 
“Afwan ya habibty, nima Momy saida tamin fada, haushin haka yasa ban kiraku ba” Nan dai suka shirya, Basma ta bata labarin accident din da tayi, Meena ta mata Allah ya kyauta na gaba kana suka kashe wayar. 
Basma ta kuma kiran Leema itama mita tayi mata korafi kamar yanda Meena tayi nan ta bata hakuri suka yi hira kana suka yi sallama. Bayan sallan asri Basma tayi wani wanka ta sanya bakar jallabiya mai dauke da kwalliya pink color, tayi rolin da gyalen abayan, saita fito, abinci ta dauka a baske kamar yanda Momy tasa aka dafawa mara lafiyan, saita shiga mota driver yajata zuwa asibity. 
Ta nufi dakin da aka sauyawa mara lafiyan, ta shiga ta sameta zaune jingine da pillow, idonta a lumshe da alama tana hutawa ne, Baba Kulu ta amshi kwandon abincin tace “sannu Basma” cikin fara’a Basma ta ce “yauwa Baba Kulu, ya mai jiki, da sauki, ta farka tun dazu amma fa kuka take tayi min, wai ita zata tafl, da kyar na lallashe” cikin kulawa Basma ta kai dubanta ga mara lafiyan, wuri ta samu gefen gadon ta zauna ta kama hannun mara laflyan tace cikin sanyin murya 
“baiwar Allah ya jikin da fatan dai babu wata damuwa” idonta cike da hawaye tace “laflya lau ni naji sauki, ni dai ku taimaka ku kaini gida, wlh nasan hankalin Umma na da Yaya a tashe yake in basu ganni ba” cikin nutsuwa Basma ta kuma cewa “kiyi hakuri, ya sunanki?” cikin damuwa tace 
“Khadija” girgiza kai tayi a laman gamsuwa tace kiyi hakuri kici abinci zan kira likita yazo ya bamu sallama saina kaiki gida” cike da fara’a tace “nagode Hajiya” Basma tayi murmushi tace “sunana Basma ba Hajiya ba” itama Khadija murmushi tayi kawai batace komai ba. Baba Kulu ta sanya mata tuwon semo miyar agushi, ga wani plet din ta sanya mata farfesun kayan ciki ta kuma zuba mata drink na 5alive a cup,  kan gadon tajera mata, cikin kulawa Deeja tace “nagode Baba” dama da dan yunwanta ta fito zuwa wurin saro kwai, bata kaiga siyowa bane Basma ta bigeta, saita bude ciki ta kwashi girki Basma sai kallonta take yi, a zuciyarta tana yaba kyawun khadijan sai dai a irin shigan da taganta dashi ya tabbatar mata masu karamin karf’l ne, hakanan taji Kadijan ta kwanta mata a rai saboda ta lura tanada saukin hali, bayan ta gama cin abincin suka kawo mata wurin wanke hannu ta wanke kana ta kalli Basma tace. 
“Hajlya au, kince sunankl Basma k0” ta gyada mata kai alaman eh, ta cigaba dacewa “ke nakejira ki kira likita in tafl gida, wlh Ummata zata damu da Yaya Aryan, murmushi Basma tayi mata ba tace komai ba a zuciyarta tana maimaita sunan Aryan, hakanan taji sunan tayi mata dadi. 
Wayarta da dauka ta kira Yaya Ahmad bai bata lokaci ba yazo, yace “Basma ashe kin dawo?” eh Yaya Ahmad na dawo, dama Patient dinka ce tace a sallameta zata gida” dubansa ya kai wurin Khadija yayi mata murmushi yace “haba dai kiyi hakuri ki kwana gobe saina sallamaki” Deeja ta zaro ido waje tace cikin tsoro wlh Ummata nakeji da Yaya Aryan, kuyi hakuri Ku sallameni” shima Yaya Ahmad cikin zolaya ya zaro ido yace “tafdi, ni bazan sallameki ba sai gobe in Allah ya kaimu” ai sai Deeja ta fara fidda kwalla, Basma tace 
“Yaya kaga kuka take yifa, ka sallameta kawai sai a bata magunguna, in yaso ni da kaina zan dawo maka da ita sai ka kara dubata” cikin fara’a yace “Basma rabu da ita wasa nake mata, dolena na sallameta kafln ta nima hanyar guduwa” dukansu sai suka sa dariya amma banda Deeja da ta sunkuyar da kai kasa tana murmushi. 
Yaya Ahmad ya rubuta mata sallama yace 
“Basma zaki dawo da ita nan da kwana biyu” “OK Yaya insha Allah zan dawo da ita”. Nan Yaya Ahmad ya kira driver ya kwashi kayan su yasa a mota, ya kalli Baba Kulu yace “Baba kuje gida ni zan kaisu Basma”, cikin kulawa Baba Kulu tayi godiya kana ta tafl. Ya kai dubansa ga Basma yace “muje ko, da fatan ta sanar miki da inda take” “0k, Yaya ba damuwa zan tambayeta a mota”. Sai suka kama hanya, Yaya Ahmad ya shiga dasu shopping complex ya siya mata kayan 
ciye-ciye, kana suka dauki hanyan gidansu Deeja. Abangaren su Umma kuwa Yaya Aryan zaune yake a gidan yayi jugum, Umma ma tayi tagumi tace wlh hankalina ya tashi haryanzu ace bata dawo ba? ban taba aiken Deeja ta dade haka ba, gashi kaje har wajen masu kwai bata ba labarinta, sunce ma bata jeba, Allah yasa ba sace min ‘ya akayi ba” ta karasa maganar tana matsar kwalla, Yaya Aryan cikin damuwa yace “Umma kiyi hakuri insha Allah za’a ganta, bari na kara fita in duba k0 Allah zaisa muji wanda yaganta” ya mike tare da cewa “Umma saina dawo” ta amsa da “to Allah yasa a dace”. 
Sun shigo Layin su Deeja sai tace 
“Ku saukeni a nan in karasa, nagode Allah ya saka da alkhairi” Basma ce tajuyo da sauri, da yake tana kusa da Yaya Ahmad dake tukasu, tace 
“haba dai Khadija, ki bari mu kaiki har gida mana”, cikin dishewar murya tace 
“a’a Ku bari kawai na tafi” cikin kulawa Basma tace “daga nan zuwa gidanku da nisa?” tace a’a ba nisa nan sama ne kadan” Basma ta kai dubanta ga Yaya Ahmad tace 
“Yaya saukemu anan mu karasa, kila bata so wasu suga an sauketa a mota ne” cike da kallon tuhuma yace “kinsan dai ba tare muke da escot ba” Basma ta gyada kai 
“na sani Yaya Ahmad, insha babu abin da zai faru” “0k, kuje bari najira ki anan, amma karki dade, tace “Tom Yaya na tnx. Sun kama hanyargidan su Deeja, suna zuwa kofar gidan Deeja tace “ga gidan mun kawo” Basma tace “0k mu Shiga” Deeja tana shiga ta hango Umma zaune tasha kuka idonta yayi ja, da ganinta tana cikin damuwan rashinta ne, da gudu ta karasa ta fada jikin Umma tace “Umma na dawo“ cikin damuwa Umma tace “Khadija ina kika tsaya tun .dazu kin samu hankalinmu a tashe?” tace “Umma tafe nake da bakuwa“ da sauri Umma ta kai dubanta hanyar waje ta hango Basma tsaye tana kallonsu, da sauri ta mike tace “lale sannu da zuwa, karaso ciki mana” da murmushi a fuskarta ta karasa, wuri ta samu ta zauna kan tabarma cikin nutsuwa tace “Umma ina yini” nan suka gaisa kana ta yiwa Umma bayanin duk abin da ya faru, Umma tayi godiya da kulwanta sannan tace 
“sun yafe ba komai, nan dai Basma ta mike tayi musu sallama tare da aje musu bandir din ‘yan budu dai-dai har dubu Hamsin, ga kuma siyayyan da Yaya Ahmad yayi mata, Umma cike da tsoro tace 
” ‘yar nan mun yafe ki.dauki kudinki” cikin fara’a Basma tace “Umma nima ‘yar kice, wannan kyauta nayi ma Ummata ne, kiyi hakuri ki amsa” da farin ciki 
Umma tayi mata godiya, sai suka rakata har kofargida, kana ta wuce su kuma suka shiga gida. 
Basma ta tafl cike da tausayinsu ganin irin gidan da suke ciki, hakanan taji a zuciyarta tana son ta taimaka musu, amma tana tunanin ta wace hanya zata taimakesu, da haka tayi nisa cikin tunani bata ankaraba taji tayi karo da mutum, da sauri ta dago ta kalle shi, ido Hudu suka yi da juna, nan take zuciyarta ta buga, haka shima nashi ya buga, Aryan sarai ya gane ta, haka itama ta gane shi, cikin yanayi na ko in kula Aryan yace Ke ba kida hankali ne zaki rika taflya ba kya kallon hanya, ko makauniya ce ke da kike tafiya bakya kallon gabanki, ko har gefen hanya kina takama dashi ne?” cike da jin zafin abinda ya gaya mata, wato ma ya ganeta ta fada a zuciyarta, tace cikin tsiwa “Kaine ba kada hankali kazami kawai, kuma kaine makaho da baka ganin kan hanya” cike da kunan zuciya ya d’aga hannunsa ya kwashe ‘ta da mari, abinda bai taba yiba kenan ya daki mace, nan fa mutane suka fara taruwa, Basma ta dafe kuncinta tace “ni ka mara? kasan ko wacece ni?” yace “Na mareki koke wacece, kiyi abinda za kiyi, kina tsammanin zan mance bakar fuskarki ne? Mara tunani kawai, dalla bace min da gani” ya karasa maganar cikin zare mata ido, nan take tsoranshi ya mamaye mata zuciya, cikin kuka gudu~dugu Basma ta bar wurin tana kokarin isa wurin motansu. Shi kuma yabi bayan ta da kallo yayi kwafa sannan ya cigaba da tafiya. Tunda take ba’a taba wulakanta ta irin na yau ba, tana isa ta fada mota,Yaya Ahmad cikin tashin hankali yace laflya Basma me aka miki? meya faru? haka yajero mata tambaya babu amsa, illa a cikin kuka tace “Yaya Ahmad muje gida, muje gida”. Cikin tashin hankali ya tada mota ya figeta a guje. Aryan yana tafiya ya fara tunani, a wani bangare na zuciyanshi yana farin cikin rama marin da yayi, wani bangare kuma yana gargadinsa, meyasa ya mareta, nan take wannan tunanin ya rinjayi wancen sai yaji zuciyansa yayi masa ba dadi da haka ya karasa gida. Basma  ansha mari hmm ko kunga laifln Aryan daya rama? muje zuwa…‘ 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE