YAR SHUGABA CHAPTER4

YAR SHUGABA 
CHAPTER 4
An shirya gagarumin gasa na rawa a k’asar England, Basma na d’aya daga cikin masu fafatawa. In ta dawo daga school babu abinda take yi sai gwajin rawa, su Leema suke k’ara mata k’arfin gwiwa. 
Ranar taro, k’aton hall cike yake mak‘il da mutane maza da mata, ko wanne yana mazauninsa, ga kuma masu tantance rawar daga gefe, zaune suke akan kujeru na alfarma, ga dogon table a gabansu an d’aura kayan motsa baki da kuma abin sha, masu fafata gasar su Hamsin ne, a ciki ake son a fidda zakara guda d‘aya wanda aka tanada mak’udan kud’i da key na mota sai kuma hular Queen na rawa ga wanda taci, sai na biyu dana uku kyautar kud’i. Gasar maza da mata ne, Ganin yawansu da Basma tayi sai zuciyarta ya tsinke ta karaya, gani take ba lalle ne taci ba,jere suke akan layi wannan na bin wannan, sun sanya riga top mai dogon hannu sai kuma wando dogo pencil ya matse jikinsu, rigan ta kama su daga sama zuwa ciki, k’asan kuma ya bud’e, tsayinta ya kawo rabin cinya. Wasu sun sanya hula a kai wasu kuma sun baje gashin su a baya, shigar Basma tayi mata kyau, ta dunk’ule gashinta ta sanya hula, ba wani makeup a fuskanta amma tayi kyau sosai. Basma itace ta goma sha shida a cikin jerin layin. 
D’aya bayan d’aya suke fitowa suna gwada rawan su, alkalai suna dubawa tare da rubuta makin, ‘yan kallo kuma suna ihu in rawar tayi musu kyau ga masu gwajin. A haka layi yazo kan Basma, cikin salo da kwarewa ta fara rawa mai ban sha’awa, a hankali take komai cikin nutsuwa, lauye duk sassan jikinta take yi tamkar roba, ta d‘auki tsayin minti ashirin tana rawa, nan fa hall ya kaure da ihu da alama rawarta ya birge su. Alkalai suka dakatar da ita suka ce ta tafi, na gaba yazo ya nuna nashi. 
Da haka har aka gama tantance rawar su Hamsin. Daga cikin alkalai wani ya mik’e yace cikin harshen turanci, zasu cire mutane goma daga cikin su, domin fafatawa na k’arshe, washe gari zasu yi rawa a cikinsu za’a tantance Mutum na farko dana biyu har zuwa na uku 
da sauran numbers. Nan fa hall yayi tsit ana son aji su waye zasu shiga gasa ta k’arshe. An fara kiran Mutum na farko da haka har akaje kan Mutum na tara, Basma bataji sunanta ba sai ta sadak’ar da ta rasa gasar, wanda basuji sunan su ba sai kuka wasu kuma damuwa ya bayyana a fuskokinsu, Basma bata an k’araba taji an kira sunanta Basima MB ce ta goma, da yake da haka tayi regista da sunan ta basima MB, saboda basaja, kuma ita ba ‘yar k’asan ba ce. Ai hall saiya kaure da ihun su Leema da Meena sauran Mutane ma suka tayasu ihun. Da haka aka tashi taro Maza hud’u mata shida sune zasu fafata a washe gari. ‘Washe gari“ 
Hall ya cika mak’il da Mutane flye dana jiya ma, nan kowa ya samu guri ya zauna, yau shigan dasu Basma sukayi kusan irin na jiya ne sai dai an sauya launin kalan kayan da suka sanya jiya. Alk’alai suka baza ido, na farko ya fito ya fara fafatawa, har aka kai na biyar, daga nan sai aka tafi hutun tak’aitaccen lokaci. Bayan an dawo aka d’aura har zuwa na k”arshe ta fito wato Basma, nan ta soma kafa tarihi domin rawar ta na yau yasha ban-ban dana jiya, Basma ta dage iya iyawanta, sai baza rawa take tamkar ba ita ba, inba ka mata kallon caf ba bazaka shaida Basma ce ba, domin tayi shiga na b’adda kama. Saida tayi rawa sosai sannan aka dakatar da ita, alk’alai sun fita a hall sunje had’a marking, sai da suka b’ata kimanin rabin awa kana suka dawo kan high table suka zauna, sun fara fad’an sakamako daga na goma ne, har suka zo kan na shida ya rage saura mutum Hud’u, Basma na ciki, a haka har suka fad’i na Hud‘u dana uku, saura Basma dawata ‘yar k’asar England d’in, sai aka tafi hutun rabin sa’a, nan fa kawayen su Basma suka rufe ta da Murna Addu’a suke Allah yasa itace mai nasara. Burin Basma ko na biyu tazo zatayi farin ciki tunda ta kafa Tarihi a fagen rawa. Koda aka dawo daga hutun takaitaccen lokaci, hall d’in yayi shuru ana jiran aji wacce tayi winning, mai fad’an sakamako saida yayi shurun minti biyar kafin ya furta first position Basima MB kece ki kai nasara, d’ayan kuma ta zama na biyu, hall d’in ya kaure da kuwwa, nan take aka d’aurawa Basma Hular Queen, wannan dalilin ne yasa Basma take amsa 
sunan Queen Basma. Sunyi hotuna kala-kala hatta gidan TV na k’asarsun nuna gasar a TV. 
Taro ya watse, su Meena cike da farin ciki suke, kana ganinsu kasan yau suna cikin murna, har gidan da suke zama aka kaiwa Basma motarta da kuma kud’in data samu. Tun daga wannan lokacin su Leema fankama da d‘aga kai ya k’aru, Basma kuwa sunan ta sai da ya shiga cikin k’asar England sosai, kowa na sonta har wani respect d‘inta ake. Ana saura shekara d’aya su gama karatunsu su dawo k’asarmu, Mahaifin Basma ya fito takaran shugaban k’asan Nigeria, Mahaifin Meena ma ya fito takaran Gomnan jahar Kaduna. Abu kamar wasa da lokacin zab’e yazo duk suka ci zab’en. Mahaifin Basma President Mukhtar Bukar Bulama sai kuma Gomna Ibrahim Abubakar, yana amsa sunan Alhaji Bukar wanda ya rik’eshi. Farin ciki wurinsu Basma ba a magana musamman suka dawo Nigeria akayi bikin rantsar da iyayensu, tun daga wannan lokacin sai suka chanza salo suka k’ara sauya rayuwansu ga mutane, suka keb’e kansu, musammam aka samu escot suke binsu Basma England suna basu kariya, feeling da d’agawa ya k’aru a wajensu Leema. 
Su Basma sun kammala karatunsu sun dawo gida, ta matsawa president saiya gina mata gidan huta a Abuja, haka ya sanya aka mata k’erarren gini aka zuba kayan da ta buk’ata, koda suka dawo Abuja suka sauka, domin yanzu Alhaji Mukhtar yadawo Abuja da iyalensa suna gidan shugaban k’asa, su Meena da Leema suma nan suka sauka, sun k’i komawa 
gidansu saida suka shafe wata guda kan suka wuce gidajen iyayensu. 
Akwai wani lokaci da Basma ta tafi kano hutu, tunda Hajiya Sa’a ta ganta saita k’udurta wa ranta Prince Shureym ya samu mata, tayi alkawari yana dawowa zata turashi yaje gun Basma su dai<daita koda baya sonta, burinta Shureym sai ‘yar babban mutum zai aura. Saboda wannan k’udirin nata ne yasa ta k’ara shigewa Momy mahaifyar Basma, dole yasa ta shirya da Ammi, domin tasan tabbas sai tabi ta wajenta tunda Basma a hannunta take, Hajiya Sa’a bini-bini tana Abuja, kasan tuwar su Ammi basu san nufinta ba sai suka sake mata suka saba sosai, zumunci ya k’ara kulluwa mai k’arfl. Duk wannan abinda Hajiya Sa’a takeyi Shureym bai sani ba yana can America, shi a can ya had’u da wata ‘yar Yola mai suna Safeena, soyayya sukeyi sosai, sunyi wa juna, Alkwarin aure in sun dawo k’asarmu. 
Hajiya Sa’a tayi k’ok’arin had’a Basma da Shureym a waya suna gaisawa, da kyar ta shawo kan shureym bayan tayi masa bayani akan Basma, ya amince amma da sharad’in zata barshi ya auri Safeena, haka ta amince masa, ita dai burinta Shureym ya auri “Yar Shugaba“ a matsayinsa na D’an Sarki. Da dubara Hajiya Sa’a ta soma tusa maganar a wajen iyayen Basma, kuma su a zuciyarsu hakan yayi musu dad’i sosai. Basma kuma suka fara soyayya da Shureym kamar gaske. 
Leema kuma ta kamu da son Yaya Jamal amma shi ko kad’an baya sonta baya ma shiga hanyarta, Duk da haka bata daina harka da Jalal ba. Meena kuwa soyayya take da Yaya Naufal kamar zasu cinyejuna. 
Su Basma koda suka dawo Abuja basu sauya rayuwar da suka fara ba a England, da zarar sun tafi gidan Hutu tofa bazasu dawo gida ba sai sunje wani babban club dake cikin garin Abuja, sunyi abinda ran su ke so, sannan su koma gidan Hutu su kwana ba tare da kowa ya san rayuwar da suke ai katawa ba. ‘Hmmm adai jure zuwa rafl…‘ Bayan sun dawo da shekara guda, Meena ta tafi Abuja. Leema ma ta bar kano ta tafi Abuja da nufin zasu Dubai siyayya. Duk suka had’u, suka shirya tsaf suka tafi Dubai, achan ma saida suka lalubo babban club can suka b’arje lokacin su, da zasu dawo su Meena da Leema basu gaya ma iyayensu zasu dawo ba, Queen ta kira aka zo a ka d’aukesu a airport, direct hotel suka je suka kama Leema da Meena domin so suke su wataya kan su koma gida, ita kuma Basma gida ta wuce sai ta cewa iyayenta su Meena suna gidan hutunta. 
A fitan da Basma tayi ta fita d’auko su Meena a hotel don suje gidan hutunta, bayan ta d’auko su ne a hanyar zuwa gidan Hutunne suka had’u da Aryan har suka kusa bigeshi, Basma ta tofa masa miyau takuma sanya aka mareshi. ‘Cigaban labari…‘ 
Basma sun wuce gida gaba d’ayan su, bayan sun isa sai suka wuce part d’in Abbansu domin tasan breakfast d’insu yayi ready a can, suna shiga duka iyayan nasu suka bisu da kallon sha’awa a nutse suka k’arasa suka kwashi gaisuwa, President dake zaune a dining ya kalle su yace yarana kun girma fa sai aure tunda kun gama karatu, dariya duk suka yi, Basma a tsagwabe tace “Ni Abba ba yanzu zanyi Aure ba sai na kai 25yrs tukunna lokacin na kara wayo” duka mutanen falon suka sanya dariya amma banda Momy da take doka mata harara, koda suka had’a ido da juna sai tayi saurin kauda kai, dan tasan laifln da tayi. Nan suka zauna suka karya duka, bayan sun gama ne Abba yace “Basma ki sameni a falon sama” Cikin farin ciki tace “to” kana ta mik’e tabi yansa, Ammi ma bayansu ta bi, Momy kuma ta kalli su Meena tace 
“wai ku yaushe za kuyi hankali ne, kun dawo amma kunk’i zuwa ku kwana anan k0? sannan nayi waya da Hajiya Sa’a tace ai ke Leema baki sanar musu kin dawo ba, ke kuma Meena Maminki ma bata san kin dawo ba, to wallahi ranku duk sai ya b’aci, inna sanya k’afar wando d’aya daku, ku tashi kuje sashi na kujirani gani nan zuwa, in ba haka ba saina ci muntuncin ku” 
Sum-sum suka mik’e suka tafi part d’inta, su Na’im da Anwar suka mik’e suka ce 
“Momy mun tafl Makarantan hadda” Da murmushi a fuskanta tace 
“To sai kun dawo ku mai dankali sosai banda wasa” suka ce “to” sannan suka wuce. Momy ta danna k’araurawar kicin, da gudu ma‘aikatan kicin d’in suka fito tare da risinawa, umarni tayi musu dasu kwashe kayan abincin su gyara wurin, cikin sauri suka mik‘e dan cika umarninta. Momy ta mik’e tayi wurinsu Basma. 
Ta same su Ammi zaune suna jiran fltowar Abba, koda ya fito sai ya samu guri ya zauna yace “Basma nayi waya da Mai Martaba ya sanar dani dawowar Shureym gobe insha Allah, dan haka sai ki tsumayi zuwansa domin a nan zai fara sauka in yayi mana kwana biyu zai wuce Kano” sunkuyar da kai tayi k‘asa tace cikin ladabi “To Abba” Ammi tace 
“sai ki d’auki su Meena a mota kuje kuyi siyayya dan had’a masa kayan tarba” Momy tayi tsaraf tace su Meena yau d’in nan zan turasu su koma gida, domin duk iyayensu basu san sun dawo ba” ido bude Ammi tace “kaji min ja’iran yara, shiyasa suka k’i kwana anan, to Allah ya shirya mana su” duk suka amsa da “Amin“ Abba ne ya ciro bandir d’in kud’i na ‘yan dubu-dubu ya mik’awa Basma yace “Ga wannan kud’in ko kinada bukatarwani abu” cikin natsuwa tace “Abba akwai kud’i a account d’ina fa” “Eh nasan dasu wannan cash ne ai” Basma cikin farin ciki ta amsa tayi godiya, saita mik’e ta fito tabar iyayan nata anan ta nufi sashin Momy. 
Can ta samu su Meena sunyi jugum-jugum, kwashewa tayi da dariya tace 
“wow yau kun shiga hannu Momy mai fiddaku sai Allah“ hararanta Leema tayi tace ai duk ke kikaja mana, munce bazamu zoba kika wani damemu, gashi yanzu ta tsaremu, dama ni ita nakeji, dan ta cika takurawa Mutane” ta k’arasa maganar dayin tsaki, kan basma ta basu amsa sai ga Momy ta shigo, zama tayi ta zuba musu ido tace “ku shirya yanzu nan driver zai kaiku airport, ke Leema ki wuce Kano a jirgin sama, Ke kuma Meena jirgin k’asa zaki bi ki sauka a Kaduna”. Leema kamar zata yi kuka tace Momy ki bari gobe in Allah ya kaimu sai mu tafi” Momy tace cikin fushi “rufemin baki yau d’in nan zaku tafi, maza ku tafi driver suna jiran ku”jiki na rawa suka mik’e suka fita saida suka biya gidan hutun Basma da kuma hotel d’in da suka sauka suka kwashi kayansu kana suka tafl Airport sai gida, Momy ta kai dubanta ga Basma tace “Wato ke Basma har yanzu ba kida hankali ko? bana hanaki kwana a wannan gidan hutun ba, shine kika kwana jiya baki sanar dani ba saboda Ammi ta d’aure miki kiyi yanda kika ga dama k0” cikin shagwab’a tace Momy “wallahi dare tayi ne shiyasa ban dawo ba” 
“dalla can yimin shuru, ni tunda kika tafi”: England kika dawo kedasu Leema kuka sauya hali, na rasa me kukeyi a wannan gidan” da sauri ta d’ago tace 
“babu abinda mukeyi fa. hutawa kawai muke sai wanka a swimming pool” 
“ok naji, yanzu dai na sanya abokan naki sun tafi, naga dalilin fltanki kullun, gobe in Allah ya kaimu zan aike ki gidan hajiya Aisha k’awata” cikin sauri ta katseta tace 
“Momy gobe ne fa Shureym zaizo kinga bai kamata na flta ba, ki aiki su Na’im mana pls” hararanta tayi tace 
“bazan aike su ba, ke nake so ki tafi, tashi ki bani wuri” cikin shagwab’a Basma ta mik’e tare da buka k’afafunta ta bar sashin Momy harda kwalla, ta nufi part d’in Ammi. 
Momy ta girgiza kai tace “ohh ni Maryamu ka haifi d’a amma Baka haifi halinsa ba, Allah ka shirya min Basma” tana gama fad’an haka sai ta mik’e ta shiga d’akinta. 
Hmm muje zuwa

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE