Yar tallah 4

*YAR TALLA*

                 CHAPTER4

*Tace kuma wlh ragin sule kikayi a jikinki zan fanshe sannan ban yarda da ki dawomin da ko kanxo ba anan muka tasaya*
Zamu tashi a
Saude dai bata kulataba ta wuce tana sharbar kwallah
Rabiu dake wanki ya tsame hannunsa daga cikin ruwan wankin ya dauko kofin garin ya bita da gudu
Ya jawo hannunta ya kaita kan dakalin wani kofar gida ya zaunar da ita gamida sauke tiren tallar a gefe ya zuba mata idanuwansa
Kukan me kike? Tallar ce bakyason zuwa?
Saude ta girgiza kai alamar a,a tana share hawaye da bayan hannunta
Rabiu yace idan ba tallar bace bakyason zuwaba to menene?
Taja majina tanata faman sheshsheqa kafin tace  na gaji yaya kafata ciwo take gashi banida takalmi ga zafin rana fasona sai jini yake famanyi
Wani irin abu ya tsikari zuciyar. Rabiu ya tsirama kafar ido
Wasu hawaye suka ciko idanuwansa gashi bashi da ikon iya taimaka mata
Don shi kansa kafar tashi babu takalmi. Tabbas da tausayawa qaramar yarinya kamar saude tayi tafiya babu takalmi
Yaddah ake tsala rana yau ga uwa uba kafar duk ta tsatstsage da faso
Rabiu yasa yatsa ya goge kwallar data tarar masa muryarsa a sanyaye yace
Kiyi haquri kije insha allahu zan samar miki takalmin da zaki dinga sakawa dakin dawo kinji?
Ta daga masa kai ya miqa mata kofin garin ta karba ta shanye ta miqa masa kofin
Ya amsa ya karbi tiren ya dora mata ta tafi
Yana tsaye yana kallonta harta bace
Sannan ya juya ya koma gida
Laure ta watsa masa harara tace ni naci uwar zariyama ballentana bita zaizai
Bai tanka mataba ya duqa yaci gaba da wankinsa harya gama
Ya shanya wankin sannan ya nufi kofar dakinta ya durkusa daga waje
Inna na gama ina alalata
Inna laure ta dago daga kwancen da take saman katifa ita da yarta
Ta watsa masa wani irin kallo tace abincinma wato har kaso biyu zaka dinga ci kenan
Koba dazun na giftaka naga  kanacin garin kwaki ba? Dallah ni tashi ka bani wuri ta doka masa tsawa
Rabiu ya miqe tamkar almajiri ya nufi bakin rigiya ya janyo ruwa guga guda yayi alwala ya nufi dakinsu yayi sallar asuba da azahar a hade
Sannan ya kwanta nanfa gajiyar daya kwaso ta rufeshi
Saude tasha yawon tallarta harta godema allah amman alalar ko rabi bata samu ta saida ba nanfa idonta ya ciko da hawaye ta soma bin jama,a tana hadasu da Allah su siya
Danladi ya tabo abokinsa ilu kai baba yarinyar canfa tana cikin matsi ina yawan ganinta a cikin tasharnan anya ba zamu far matAba kuwa?
Ilu yace nimafa na dade ina wannan tunanin to amman abinda ke tsoratani yarinyar karamace sosai karkaje ka balloma kanka ruwa
Danladi yace kaiko da mugun baki kake idan zakaxo muje mu fasa kawai kaxo muje malam
Mu jata kangon alhaji sani
Ilu yace kuma hakanefa to taro mana ita ni bari naje na duba mana wurin don na tabbatar da tsaro
Ya dire daga kan teburin da yake ya nufi gurinda saude take duqe gaban wani direban j.5 tana zazzage masa alala a kwano ilu ya iso wajen yace ke yarinya idan kin gama sayar masa kikaima wancan gashi can zai siya tace to ta miqama direban alalan ya karba ya somaci ita kuma ta rabe gefe tana jiransa ya gama ya bata kudin da kwanon ta qara gaba
Direban ya soma ci gaya dago sai yaga ta kura masa ido ji take dama bakinta yakekai alalar sbd tsabar yunwar dake cinta
Direban yadan daga murya yan mata ya kike kallona ko na miki ne ?
Saude tayi saurin dauke kanta yayi daria yaci gaba da cin alalarsa
Karen motar dake can gefe yace sai oga baka tambayeta ko tana ciki bane
Yace kai share wannan batasan inda ke mata dadiba
Karen motar ya sake bushewa da daria yace sai oga Allah yabar mana kai
Baice masa komaiba ya qarasa cinye alalar ya wurga mata robar ta zabura ta miqe gamida saka kwanon cikin tiren ta qarasa inda yake domin karban kudin ya kura mata ido yaya akayine?
Tace kudin zaka bani
Ta nawace?
Saude ta numfasa kafin tace ta murtala daya da gomace
Yasa hannu a aljihu ya ciro kudi masu yawa ya dubeta
Yace yanxu idan na baki wadannan kudin zaki barni nayi lalata dake
Saude ta zaro ido tana kallonsa
Ya sake maimaita mata a karo na biyu
Idonta ya ciko da kwalla alamar zatayi kuka
Yace a,a meye abin kuka yanmata karbi kudinki kisan inda kikai kuma karna sake ganin kafarki ta tako inda nake
Idankuwa ba hakaba saina turmusheki
A wurinnan ya miqa mata kudin karbi ki wuce tasa hannu zata amsa hannunta na rawa ya hada hannun da kudin ya riqe yana dariyar mugunta
Meye sunanki yan mata?
Ta janye hannunta jikinta na rawa tabar wurin a hanzarce har tana tafka tuntube wani dan kamasho da yazo giftawa ta wurin ya tintsire da daria yana fadin dan baba kabar iya shege kabi Allah kaji
Ya miqe yana fadin kai garba mufa duniya gaba muka bata ba baya ba
Garba yace shegen sama kura taga biri
Allah ya kauda abin kunya
Yace ba aminba mu abin kunya binta muke tana guduwa Allah ka hadamu da abin kunya duk inda yake
Duk wurin sukasa ihu ana sai oga Allah yabar mana kai
Ikon Allah mai tsaida wando ba zariya saude dai bata sake bi ta kansu ba ta nufi inda danladi ke zaune saman teburin cikin tasha tace kaika aika a kawo maka alala ko?
Yace eh zubomin ta murtala biyu
Dadi ya kama saude don tasan daga wannan ta siyar tana murna ta zuba masa tasa masa mai da yaji
Ya zauna ya harde gamida lashe alalannen tas yana lashe baki
Saude na zaune tana kallonsa yana gamawa ya dubeta
Kinada canjin naira dubu?
Saude ta waro ido ita tunda takema bata taba riqe naira dubunba ballentana harta samo canjinta
Ta girgiza masa kai alamar a,a
Yace to ya za,ai kenan ko kuma xo muje na samo canjin saina baki kudinki
Ta mike ta tattara kayan ta bishi
Suka soma tafiya ganin suna shirin fita daga tashar yasa ta dubeshi tace
Ina kuma zamuje?
Yace ban gane ina zamujeba canji zan nema in baki kudinki
Saude tadanyi shiru maganar yayanta ya dinga dawo mata cikin kunne tamkar yanxu yake gaya mata
Saude ki kula banda aje tallah ki tafi samo canji banda kuma kibar mutum ya tafi samun canji shi kadai
Kuma karki sake ki yarda wani ya jaki zuwa wani guri koda kuwa nan da canne
Saude ta dubeshi a,a gaskia nidai kazo muje cikin tashar a samu canjin kaban kudina don yayana ya hanani bin wani
Ya hade rai jini da yar iskan yarinya sai kuma akacemiki kowa dan iskane. To karki bini ki karbi kudinki zauna
Ya wuce zai tafi hankalin saude ya tashi tasan kan kudinnan yau inna laure kashetane kawai ba zatayi ba tayi saurin riqo rigarsa tasa kuka
Nidai wlh saika bani kudina
Ya juya a fusace ya danna mata wani mugun zaki ke dan ubanki bazaki sakeniba? Ta qara cacimo rigarsa nidai wlh saika bani kudina idan naje gida a haka dukana za,ayi
Haushi ya kama danladi yasa hannu ya dauketa da wani wawan marin dayasa saidata kife. Ya juya zai wuce wani magidanci ya kwaso a guje yana kiran
Tsaya nan danladi karka sake ka matsa mugu mai kai mata?
Yayi saurin juyowa jin muryar ogansa
Gabansa ya fadi yai saurin juyowa yace wlh oga yar iskan yarinyace wai dan uwar yarinyarnan waini zata tsare nace
Nace taje ta samo canjin dubu tace babu nace muje na samo na bata taqi yarda toya takeso nayi da itane oga ?
Ya tallabo saude gamida fadin yanxu don rashin imani wannan yar qaramar yarinyar zakaima irin wannan marin?
Yanxu wannan yarinyar fisabilillahi meta sani?
Ya zaburo cikin irin muryar yan shaye shayennan yace oga zaginafa tayi yace idan ta zageka kai yanxu zagi nawa kai mata a gabana ko kunyata bakajiba
Yi hakuri yarinya kinji Allah ya saka miki bani dubun na canja muku
Yadan sosa qeya a,a ai gurin ilu zan amso dubun na samo canjin mutumin ya girgiza kai yana fadin Allah ya shiryeka ya zaro kudi cikin aljihu ya kalli saude. Kudin naki har nawane?
Cikin muryar kuka tace murtala biyu da goma ne
Ya girgiza kai ya bata sannan ya kalleshi na ranta maka ka samo canjin ka kawomin kudina
Dan ladi ya turo baki yana dan harare harare ya wuce kamar zaikai duka
Mutumin ya dubi saude yace wuce ki tafi kinji Allah zai saka miki yace ai harda laifin iyayenku mata dake turoku tallah cikin maza basu san da irin mazan da zaku hadu ba don ko cikin masallaci zakukai tallah sbd tsoron Allah sai an samu mutanen banza ballentana cikin tasha inda yayan banza ke taruwa wadanda daman can lalatattu ne ya za,ai ace baza ai barnaba fisabilillahi balle ke yarinya qarama
Wuce kije Allah yayi miki sakayyah
Haka saude ta wuce gida  jiki na rawa da yamma lis don tuni rana ta fadi a lungun gidansu ta hadu da rabiu cikin taron jama,a wai ana duban wata
Saude ta lallaba ta janyo hannun rigarsa yayi saurin juyowa yana kallonta yayi murmushi tana fadar
Tun daga nesa na hangoka duk ka keresu tsawo
Rabiu ya dungureta yana daria yace ke kuma sarkin sharri ko?
Daria itama tayi tana fadin anga watanne yaya?
Yace a,a munadai dubawane amman munasaran za,a ganshi kedai ki zauna da niyyar azumi gobe
Tace ai nima tsayawa xanyi yaya ka dagani inga watan
Yayi murmushi yana fadin so kike yau inna laure tayi kujera dake kenan ko? Ya riqo hannunta
Yace wuce mu tafi kinga har  yara sun fara tsokanarki
Saude ta juya taga dandazon yaran daketa tsalle suna waqa
Yar tallah qazama yar tallah bata wanka yar tallah bata wanki yar tallah bata sallah yar tallah saidai yawon tallah
Ta dago idonta cike da kwalla ta kalli yayanta tace aidai yaya ina sallah ko?
Kai kawai ya daga mata sbd yaddah abin ke sukarsa a zuciya ya daura hannunsa saman kuncinta inda shatin yatsu suka kwanta wurin yayi jajir abinka da jar fata
Muryarsa na rawa yace waya mareki haka saude?
Muryarta na rawa ta shafa wurin tace wanine ya mareni a tasha yaya wai don naqi binsa ya samo canJi
Rabiu yaja numfashi ai gara dabaki bishiba saude shida Allah
Sai a lokacin ya lura da jinin daya kwanta a idonta yAja hannunta suka tafi yanajin zuciyarsa na suya fiye da radadin marin da taji
Suna shiga cikin gidan inna laure dake duqe bakin rariya tana tsane gero ta dago ganin kwanikan duk sun baci da qasa
Jar ubannan kai badai barin alalar kikaimin yauba ?
Saude tace a,a na saida wanine ya mareni harna fadi waidon naqi binsa ya samo canji
Inna laure ta daka mata tsawa ke gafara can munafuka tantiriya idan yace ki bishi ya samo canji to sai meye ?
Koyana iskanci dai ai bazaiyi da keba a balla qashi ko,a karya qafa bani kudina ni ki wuce
Saude ta warwaro kudin a habar zani ta miqa mata. Ta karba gamida kirgawa taga sun cika cas ta ninkesu ta soke akai
Rabiu ya dubeta dauki gora kije kiyi alwala kiyi sallah
Inna laure ta zaburo bazatayi sallar
Maza ga kudi kije ki siyo icce ki daura sanwar tuwo kai kuma ka tattara kayan tallar ka wanke
Idon saude ya ciko da kwalla ta kafama yayan nata ido
Laure ta zaburo mata to yar iska gama kallon nasa kixo ki amshi kudin
Ko ubankima bai isa ya hanaki yin tuwonnan ba ballentana wani banza jaki can zakizo ki karba kokuwa sai naxo nayi miki dukan kawo wuqa?????

Hmmm su inna laure manya
Alhamdulilahi…
Another Friday, the Master of all days has come again.
The Most Sacred Day With Countless Blessings and Mercies of Allah.
May Allah Shower His Countless Blessings On You and Your Family on This Holy Day.
May Allah reward you abundantly.
Jumma Mubarak.
*NAKU HAR KULLUM*
*ABDULLAHI ISMAIL SALANKE*

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE