Yar tallah14

        *YAR.  TALLA~BOOK2*

      

                 *CHPTER14*

TUNda suka fara tafiyar Saude ke raira
kukanta, a hankali har sai da suka kusa
kawowa Suleja, sannan wani bacci mai
nauyi ya dauketa  Ba ita ta farka ba sai da taji
Dillaliya na tayar da ita, Saude ta bude ido ta ga har
sun kawo tasha, mutane nata fita, sannan ita ma ta bi ayarin masu fitan
Tun da suka sauka tasha Saude keta faman zare na-mujiya, ta zo garin da ba nata ba, za ta iya rantsewa tunda take ko gidan Mutum Daya bata taBa zuwa ba, to balle ta tsallaka Kano k0 wani garin da ke kusa‘ da su, amma yau ga ta cikin ‘Abuja tsamo-tsamo. Ikon Allah. .
Dillaliya ta tsaida musu tasi tasha suka shiga, Saude dai na biye da ita da idanuwa sai faman waige-waigen idanuwa take. A hankali ta ga sun shigo cikin rukunin wata unguwa wadda kai tsaye za a kira ta da G.R.A
Unguwar shiru ba ka Jin motsin komai sai kukan tsuntsaye da haushin karnuka ga manyan shuke shuke da suka sa titin unguwar tsakiya, kowane gida ka kalla ka san na wani kusan ne, gaba daya babu gidan da bana wani babban mutum ba a unguwar.
Saude na cikin kallon jerin gidajen ta ji Dillaliya na fadar.
“Nan za ka ajiyemu.”
A hankali Saude tabi kofar gidan da aka ajiye su din, da kallo wanda za ta iya rantsewa tunda suka taho gidaje
kadan ne suka kai shi kyau da tsaruwa. Saude ta zuro qafafuwanta ta fito kamar yanda ta ga Dillaliya tayi, ta tsaya Dillaliya ta biya mai tasi din sannan ta yi gaba Saude ta bi bayanta. Kai tsaye katafaren gate din gidan suka nufa makeken gaske mai kama da Kofar shiga gari, ga wasu manya-manyan shuke-shuke da suka zagaye gidan gaba daya. Dillaliya ta tsaya tana latsa wata ‘yar karamar na’ura da ke like a bangon gidan. ‘ Wani irin tsoro da faduwar gaba suka bugi Saude anya kuwa, ba tahowa akai da ita a saida ita ba, don tana da yakinin wannan ba gida bane sai dai k0 wata ma’aikata ta sarrafa naman mutane Ba ta gama tunanin ba ta ji qarar tura gate din take tayi ido hudu da wasu manya-manyan qarti har hudu, bakikkirin dasu majiya qarfi, sun bude qofar, suna qokarin shiga suka ga wata bakar mota
yar dunkulalliya mai daukar hankali ta ratsa ta
shiga cikin gate din
Dillaliya ta janyo hannun Saude da niyar su shiga, qartin nan suka yo kansu da wata irin masifaffiyar tsawa wadda tasa ‘yan cikin Saude
juyawa gaba dayansu,fitsari ya fara kwace masu a wando, ita kanta Dillaliyar ta firgita, don cikin rawar murya take fadar.
“Kuyi hakuri wurin matar gidan muka zo nice wadda na taBa zuwa da Hajiya Kande, wan,,,,,,
“Shut up! I don ’t speak Hausa.” ,
Tuni ‘yan cikin Dillaliya suka juya, .don ita dai k0 zo in kashe ki da Turanci bata sani ba, ido ya ‘ raina fata ta dubi Saude tana fadar.
‘ ‘ “Me suke cewa?”
Cikin muryar kuka Saude tace, nima“Ban sani ba 
Dillaliya ta harzuka “Yanzu ashe duk makarantar da kike zuwa asarar kudin tara kawai ake baki san komai ba?’ ‘
Saude dai ta yi shiru ba ta ce komai ba. Mutanen nan suka maida kofa suka rufe suka bar su nan tsaye,
Dillaliya na ta faman saukewa Saude kwandon masifa, don ba ta iya Turanci ba. Kunji fa rashin‘ kunya.
A hankali motar da ta shigo cikin gidan mai bakin gilas’ ta faka a qatuwar harabar da aka tanada dan ajiye motoci, aka bude gidan direba da hanzari, wata ‘yar budurwa ta fito cikin shigar suite baqaqe da gani ba zata wuce shekara ashirin da shidda ba  Tana fitowa ta bude gidan bayan motar tare daja gefe ta kame qam, wata kyakkyawar macece ta fito, mai
masifar kyau kai kace Balarabiya ce k0 Baturiya saboda tsananin kyau da hasken fata Tana sanye cikin shigar wani danyen leshi mai kyan gaske, wanda tsadarsa ta tasamma dubu dari da wani abu, anyi masa dinkin riga da siket matsatstsu irin dinkin matan manya na Legas, dan qaramin mayafi ne saman kafadarta wanda  dora shi kawai ta yi a gefen kafadarta, kanta an kafa mata wani masifaffen dauri mai kama da daurin inji, qafar nan tana sanye cikin wani masifaffen takalmi mai tsinin gaske da ‘yar Karamar post din su a hannunta Idonta na sanye da wani qaton bakin gilas wanda: ya mamaye rabin fuskarta.  Kai tsaye zaka lye. kiranta da ‘first Lady’ saboda haduwarta. Tana fitowa daga motar ta dubi yarinyar
’dake tsaye, cikin wata irin murya mai kama da rada rada ta soma magana cikin harshen turanci.
“jeki shigo dasu.”
Yarinyar ta amsa da ‘okey  Tare da juyawa da sauri ta wuce ita kuma ta nufi cikin gidan nata tana wani irin taku, da wata irin faskekiyar waya a ‘hannunta. ;
Dillaliya da ta gaji da ruwan bala’i sai kuma ta yi shiru tana tunanin mafita, can dabara ta fado mata ta
Ciro ‘yar qaramar wayarta baby Nokia ta lallatsa lambar Hajiya Kande ta kara a kunne; tun kafin ta
soma magana ta ji an bude wata qaramar kofa yarinyar. Tace come and enter
Dudda Dillaliya ba ta san abin da ta ceba, amma ta fahimta ta hanyar yi masu nuni da hannu da yarinyar tayi, don haka ta zabura ko kallon Saude ba tayiba tayiciki, don haka itama tamike da sauri  ta bita
Kan Saude yayi masifar daurewa lokacin
data shiga cikin harabar gidan, gabanta ya shiga wata rugurguza da bugawa mai tsanani, yarinyar ta yi masu jagora har zuwa wani qaton ginin bane hawa hudu, wanda tamkar da gilas kawai aka yi shi, dama da hagu duk iri daya ne, suka nufi Bangaren dama suka tattaka wata matattakala wadda ba tafi hawa shida ba, sannan suka ratsa ta wata Kofa mai fadi, anan ma mace ce tsaye qikam kamar an kafe ta, tana sanye ita ma da bakaken suita jikinta, sai da ta sa wata ‘yar na’ura ta daddana a jikinsu sannan suka ‘ wuce cikin kofar da za ta sada ka da qaton falon gidan. Saude ta bi matar da kallo a zuciyarta tana fadar, ikon Allah yanzu ita kuma wannan aikinta kenan”
Kamshin rom freshner da turaren wuta dan Maiduguri shi ya dakar masu hanci su duka hakan ya tabbatar masu da sun iso falon, qaton gaskene wanda aka zagaye da kujeru saiti uku, kuma kowane
kalarsa daban. Kai batun ma in tsaya in, labarta muku haduwar falon duk wani bata lokaci_ne na barwa mai karatu ya yi imaging dinsa a zuciyarsa.‘Yarinyar wadda zan iya kira da Ingozi ta yi» masu nuni da cikin falon suka tafi suka zauna dirshan a ‘qasan kafet din duk da kujerun da ke zube kamar a cikin store. Yarinyar ta juya ta tafi abinta tabar. su  nan
zazzaune kamar masu zaman gaisuwa,; sai :rarraba
idanuwa suke ba Sauden baaa ba Dillaliyar ba, wadda sai kace bata taBa zuwa ba.
Tun suna tsammanin fitowarta har .suka soma . cire rai da za ta fito, don sun share fiye da awa biyar a zazzaune suna zare namujiya, sanyin AC sai kada su yake suna faman karkarwa. Tuni sun gama’fidda rai da fitowarta, ga gajiya ga wata~ masifaffiyar yunwar da ke kwakwalarsu, sai faman gyangyadin gajiya suke. , Kamshin turarenta shi ya farkar dasu; gaba daya Suka wartsake suna daidata nutsuwarsu,. idanuwan Saude na zube a kan matar wadda ta nufo inda suke tana lallatsa faskekiyar wayar dake-hannunta, Allah mai halitta abin da Saude ta iya fada kenan a zuciyarta, saboda yanda ta ga tsabagen kyau kwance a jikin matar, wadda ba za a kira ta da doguwa ba ba kuma gajeriya ba ce, sai dai a kira ta da tsaka-tsaki. Ba ta da qiba sosai, amma kuma ba ‘siriri ba ce sosai saidai tana da jiki daidai-daidai.
1page is missing
A yanzu ma takalmi ne mai tsini a kafarta, sai dai babu gilas yanzu a fuskar ta.
Ta karaso cikin falon ta fada kan kujera ta dora kafa daya kan daya ba tare da ta dago ta kallesuba
idonta na kan wayar hannunta ta rinka amsa: masu gaisuwar da suke ta faman kwarara mata
Duk azaton Saude za ta basu hakurin  shanyar dasu da ta yi amma sai taga kwata-kwata ma hankalinta baya kansu yana kan wayar dake hannunta ne
falon ya dan dauki shiru, Dillaliya na nazarin ko ta fara. Maganane
Cak matar ta mike wadda ba zata haura shekara talatinba
muryar nan tata kamar mai rada ta soma magana.
‘Ki yi hakuri baiwar Allah ina da abin yi  yanzu haka koda kikaga nazo nazauna dan insaurarekine dama na lura kamar akwai wani important issues ne shi yasa na ce aje a shigo daku, yanzu banida lokaci inada apointment da karfe sha daya.’ Tana maganar tana tafiya. ’
Dillaliya ta fara bada hakuri cikin rawar murya tana fadar, “Ki yi hakuri ranki shi dade, wailahi na dan saurara ne ki fara magana kada in fara kiga kamar na yi rashin da’a a gabanki, dama ba wani
abu ba ne yar aikin da kika ce kina so CE na kawo miki guda tun wancan watan‘ lokacin da mukazo ni
Da Hajiya Kande taya ku murnar cin nasarar lashe zabe kika ce kina san yar aiki guda mai nutsuwa za ki Kara shi ne na tsaya na binciko miki na kawo miki
Matar ta dan dakata daga tafiyar da take ta waigo a hankali, ta daura dara-daran idanuwanta kan Saude tana qare mata kallo sama da Kasa, tamkar wadda ta ga wani abun kyama a tare da ita, ta dauke kanta tana ‘ latsa wayarta cikin rashin kulawa tace, “Is okey. ”
Ta dan karkace tasa hannunta saman hannun
kujera ta janyo sai ga wata ‘yar loka, shake da kudi bandir-bandir yan ‘ dubu-dubu, ta zaro masu yawa ba tare da ta Kirga ba ta cillawa Dillaliya tana fadar, “Ki hau mota, sai da safe.” ‘ Ba tare da ta~ saurari godiyarta ba ta yi gaba abin ta, dad’i ya kashe Dillaliya ta tashi jiki na Bari. tana fadar, “Ke kuwa kin yi nasara Saude, da ta dauke ki don Hajiya Kande ce min ta yi ta kawo mata yara ‘yan mata sun fi guda talatin tana cewa ba su yi mata ba, don haka saiki kula ni dai kin ga tafiya ta.”
Ta mike ta bar Saude na zare namujiya, zuciyarta na faman kaiwa da kawowa, a yanzu ma kukan ya gagare ta’ saboda tashin hankalin da take ciki yanzu yafi gaban kwatance, tunaninta daya yanzu wace irin rayuwa ce za tayi a gidan da ba ta san kowa ba?
Wane irin‘ qalubale ne yanzu kuma za ta fuskanta? ‘ Ta Iumshe idanuwanta Kirjinta na barazanar ‘
fashewa, ga‘ bacci, ga yunwa, ga gajia, ga uwa-uba fargaba da tashin hankali da suka‘ dabaibaye zuciyarta. Tana nan zaune tana muzurai ta ga wata dattijuwar mace ta shigo falon sai dai ita da ganinta Bahaushiya ce wadda shekarunta ba zasu wuce
arba’in ba. Ta dubi Saude cike da kulawa kafin tace, “Ki taso muje in nuna miki masaukin ki.”
Saude ta yunkura ta mike tana jin tamkar za ta. kifa saboda rashin kuzari. Ta wata hanya ta ga sun bi ta cikin falon sai ga su sun flto wani Karamin bedroom shi daya, ba wasu karikitai a cikinsa sosai, ‘ karamin gado ne kwara guda mai kyan gaske kwanciyar mutum guda, sai wardrobe dinsa a gefe, shi kenan sai kafet da ke malale a dakin mai laushi.
Matar ta juya ta dubi Saude tana fadar, ‘Nan shi ne dakin da Hajiya ta ce a sauke ki da fatan za kiyi . farin ciki, don gaba daya ma’aikatan .gidan nan masaukinsu a waje yake sai gashi  ke daga ~zuwan ki anwareki, natayaki murna.” ‘
Saude dai ba ta ce komai ba don ita abin dake cikin zuciyarta yafi gaban wannan. Ta zauna gefen gadon wanda ya sha lallausar shimfida ta ci. gaba da bin dakin da kallo, wanda take ganinsa ‘tamkar wata
aljannar duniya. Matar ta sa kai ta fice saboda ganin hankalin Saude baya kanta.
Ba ta jima da fita ba sai gata ta dawo hannunta riqe da plate da ke rufe, tare da pure water ta ajiyewa Saude ta juya ta fice. Jikin Saude har rawa yake wurin saukowa ta bude plate din, ta kafe idanuwanta saman abincin. Shinkafa ce jaloup babu ko wadatar kayan miya a cikinta. Saude ta sa cokali ta soma ci, sai dai bakinta ya gaya mata dan ba ta yi tunanin
shinkafar za ta yi dadi a yanda ta ganta ba.
Hannu baka hannu kwarya haka ta rinqa cin abinci, lokaci guda ta kawar da shi, sannan ta dauki ruwan ta fasa ta shanye shi tas. Tana sauke ledar ta saki wata‘ nannauyar gyatsa, idonta ya soma lumshewa ta yunkura ta haye kan gadon ta kwanta. Tana kwanciya wani barci mai nauyi ya dauke ta.
Bata sake motsawa ba sai lokacin da ta jiyo ana ta kiraye-kirayen sallar Asuba, ta yunkura ta mike tana faman zazzare idanuwa can ta hango wata kofa jikinta na rawa ta nufe ta, ta bude ta tsaya sororo ‘ tana kallo; ‘an qawata wurin da kayan qawata bandaki. ‘ ‘ ‘ Da sauri Saude ta maida ta rufe dan ita a zatonta wani dakin hutawa ne, ta dawo ta zauna tana san yin
sallah amma ba ta san inda za ta kama ruwa ba, balle
, ta dauro alwala. Da ta gaji da zama ne ta koma ta
kwanta. ‘ Sai dai a yanzu ba barci take ba. idonta biyu, tana kwance tana tunani, wai ita ce yau a kwance saman
lallausan gado irin wannan, ko a mafarkinta bata taba tunanin hakan ba. Fargabarta guda yanzu yanda ta ga matar gidan da ganinta tasan bata da mutunci, dan tunkan su hadu wani irin tsoranta ya mamaye zuciyarta‘ Tana nan kwance tana juyinta, ita kanta ba ta san awannin data kwashe ba, ta ji motsin ana shigowa dakin ta yunqura ta tashi zaune tana kallon mai shigowar.
Matar Jiya ce ta shigo da sallamar ta, a yanzu ma hannunta na dauke da plate da cup a sama sai ruwa guda daya a dayan hannun ta ajiye, Saude da ke kan gado ta amsa mata sallamar ta tare da gaishe ta, ita kuma matar ta dan zuba mata idanuwanta kafin ta ce“Yau dai kin yi kwanciyar kadaici k0 ya ki kaji gidan namu?”
Saude ta yi murmushi ba tare da ta tanka ba, matar ta Kara gyara zama tana fadar, “Kin ga dai matar gidan sai kin yi takatsantsan dan ba ta da kirki, yanzu dubi duk dukiyar mai gidan nan amma abincin su daban na masu aiki daban.
Haushi ya kama Saude a duniya ita akwai ta da surutu da naci amma ba ta iya gulma ba, dan haka cikin qosawa ta dubi matar tana fadar, ‘Don Allah inane bayan gida in je in kama ruwa har yanzu ban samu na yi sallah ba ”
Matar ta ce, ‘Wane bayan gida kuma bacin wancan.”
, Saude ta waro  ido tana fadar, “Yanxu wancan kewaye ne?” Matar ta yi murmushi tare da fadar,
“Taso muje in nuna miki yanda za ki yi amfani da ‘su
Saude ta yunkura ta mike ta bi bayan matar. Daya bayan daya ta rinqa nuna mata yanda ake amfani da komai da yake kwanyar tata a bude take, a
take ta dauka, don haka suka fito, matar ta tafi ita
kuma ta haye saman gadon ta janyo plate din ta bude, soyayyan dankalin turawa ne da kwai sai ruwan tea dan tsururu mai kama da fitsarin godiya. Dadi ya kama Saude yau za ta yi karin kumallon ‘yan gayu. Ta tisa dankalin tana ci tana faman santi a zuciyarta yanzu dama wannan shi ne rayuwar da masu aiki ke yi a gidajen da aka kai su aikatau? A gaskiya suna morewa don ita in dai za ta rinka samun abinci mai rai da motsi irin haka, to ai ba aikin da za,a sata a ,ciki batayiba bayan ta kammala sannan ta kwashe kayan ta ajiye gefe ta mike ta nufi bandakin ta dauro alwala ta tayi sallarta. Tana gammawa ta kishingida saman kafet din aiko nannauyan barci ya dauketa saiji tayi matarnan tazo tana tashinta ki tashi hajia nason ganinki
A falo yanzu nan da minti biyar Hajiya zata sauko ki gana da ita.”
‘Yan cikin Saude su kai wata masifar juyawa, alamun tsoronta ya bayyana a fili qarara. Matar ta-yi murmushi ta mike tana fadar.
“Hajiya na da matukar kwarjini a idanuwan kowa, ki dake ki fitO yanzu dan kar ta riga ki fitowa ki samu matsala.”
Ba ta jira abin da Saude za tace ba ta juya ta fice, ta yunkura da hanzarinta ta nufi bandaki ta wanko fuskarta da bakinta jikinta sai faman rawa yake tamkar wadda za ta gana da Azara’ilu ta fito falon, Wanda yake tas-tas tamkar ba a shigwarsa saboda tsabar gyara.
Saude ta raba daga qasa ta zauna zuciyarta na barazanar fashewa, don ta san yau za ta wuni anan ba ta fito ba. Sai dai da mamakinta ba ta kai minti biyar da zama ba ta jiyo Kamshin turarenta mai kwantar da hankali, zuciyar Saude ta tsananta bugawa da sauri-sauri, tamkar ana buga ganga, da Kyar ta iya daga kai kadan ta dan saci kallonta.
Sanye take da wata dakakkiyar shadda baka ‘yar Mali, dinkin riga da siket sun bala’in kama ta, an yi mata aiki da jan zare da fari da kuma kore, kwalliyar nan da gani ta kanti ce, tun daga hannuwanta zuwa qafafuwanta da wuyanta gwala-gwalai ne sai daukar ido suke takalmi ne baki mai masifar tsini a Kafarta.
A yanzu idanuwanta rufe suke da baKin gilas din da . ya mamaye mata fuska,‘da makullin mota rike a hannunta tana kadawa, ta qaraso ta zauna saman daya daga cikin kujerun da ke baje a falon ta dora
Qafa daya kan daya tana kadawa Saude ta zube tamkar mai shirin yi mata sujjada. Asma ta taBe baki tana yatsina fuska tamkar wadda
ta ga abun Kyama ta daga mata hannu.
“Ya isa bana san yawan gaisuwa, ya ya sunan ki?” . ~ Muryarta na rawa ta ce, “Sande.”
Ta yamutsa fuska tamkar ba .za ta sake magana ba can ta ja fasali kafin ta ce, “Malama Saudat na san dai kin san nan k0 gidan waye a qasar nan ko to baki da bukatar sai na maimaita miki?”
, Ta dan yi shiru tamkar wadda maganar ke mata ‘ wahala kafin ta ci gaba, “A dan jiya zuwa yau nasa a , dan yi mini binciken ki a bugi cikin ki dan a fahimci idan kina da yawan surutu. Is oke zuciyata ta nutsu da na dauke ki aiki, ni dai ba mazauniya ba ce ‘yar siyasa ce ba ni da time din kaina ma ballantana na wani, kullum cikin sabgogina nake;
Don haka na ce a samo mini yarinya mai nutsuwa wadda _zata kula da maigidana.  za ki tsaya ‘yar aiki a sashin maigidan, idan ki ka gaza kula da shi kuma zaki fuskanci fushina. Aikin ki shine zaki rinqa kula da abincinsa, abin shansa,
gyaran sashinsa, wurin hutawarsa. Ki nutsu ki fahimci abubuwan da yake so da wanda baya so akwai lokutan da baya san magana, ki nutsu ki fahimta kar ki kuskura ki rinKa cika shi da yawan
magana, baya san yawan kallo koda yaushe yana bukatar abu mai sanyi kusa da shi Yana cin abinci sau hudu a rana, yana shan fruits
da daddare around 12:am kuma yana shan coffee, yana tashi daga barci qarfe bakwai, yana motsa jiki a lokacin da ya farka yana gamawa zai sha tea, sannan ya tafl ya watsa ruwa. Yana karyawa da misalin
Qarfe goma na safe.
‘ Wannan shi ne tsarinsa, da fatan za ki kula, duk yan aikin da na daukar masa rashin fahimtarsa ne da basayi kesa inakorarsu. Ayanzu kece damata ta qarshe daga ke idan ki ka kasa kula da shi ba,a ‘ buKatar a Kara kawo masa wata, don haka ki tsaya ki nutsu ki fahimce shi ban san sakarci, idan kin yi aiki irin yanda yake so ni zan rinqa biyanki nera dubu ashirin duk wata. Da fatan kin fahimta?”
Saude ta daga mata kai a sanyaye, amma . a kasan zuciyarta ta yi masifar karaya, don ta san bama zata iya ba yaudarar kanta kawai tayi data amsa. ‘
Asma ta yunkura ta mike ta dubi matar da ke tsaye wadda da alama ita ce ma’aikaciyar sashinta, tace “Ki ba ta kaya ta saka, aikinta zai fara daga

Wohoho mu tara gobe daidai wannan lokacin donjin ci gaban wannan taqaddamar
Naku haR kullum
*ABDULLAHI ISMAIL SALANKE*
KE cewa GOBEMAAA da LABARIII

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE