Yar tallah17

             *YAR.   TALLA*

                 *CHAPTER17*

masu Kin ta take haduwa, a duniya yayanta ne kawai ya taBa sonta, sai kuwa Hamid, mutum na farko daya nuna mata qauna da soyayya ita kanta duk da bata san meye so ba, amma ta san tana son Hamid dan ta san wahalar da take sha gidansu ta linka ta nan gidan sau goma, amma kullum burinta ta samu ta bar ” gidan ta koma gida k0 ta hadu da Hamid dinta kuIlum addu’arta kenan musamman idan tazo kwanciya bacci.
“Wayyo Allah ya Ubangiji gani gare Ka
Jin alamun tafyar da tayi, ya sata saurin dago kai. Dr. ne ya dawo daga rakiya, gaban Saude yayi
Wata mummunar faduwa tayi saurin ja da baya tana ba shi hakuri, da kukanta dan gani take dukanta zaiyi  Dr… yaja ya tsaya cak yana kallonta yama rasa
me zai mata ya huce haushinsa, ya lumshe idanuwansa lokaci guda ya bude ba tare da yayi magana ba ya matsa da niyar isa inda take ashe bai sani ba ta ajiye tiren kayan abinci a gun «
Sai dai yaji yayi karo da wani abu,
fasa wata ‘yar siririyar qara yayi ya durkusa, ya rike babban dan yatsansa, wanda tuni har ya soma zubar da jini abin ka da lallausar farar fatar da hutu ya jika, hankalin
Saude yayi masifaffan tashi, tayi kan shi tana _ fadar ~
‘Wayyo Allah na shiga uku na lalace “ta rike kafar tana kuka, ‘Wallahi ba da gangan na ajiyeba
Na rantse da Allah ” ya runtse.idanuwansa ba tare da yace da ita komie ba “ta rasa yanda zatayi ta kalli kan kayan abincin ashe, da yar qaramar wuqar yanka cake da ita  yayi karon harta yankeshi hankalinta ya qara masifar tashi yanda taga jini na zuba ba wai kadan ba; ta rude ta cire himar din  kanta tasa  hakori ”ta”yaga shi ta yagi kadan ta daure masa dan yantsan Dr ya bude idanuwan shi da Kyar yana kallonta yanda tabi ta gigice ta rude fada take, ‘Sannu Wallahi bada gangan na ajiyeba, ganin yanda ta fita hayyacinta yasa ya nemi fushinsa, ya rasa. Ya’sake lumshe idanuwansa saboda radadin da qafar kemasa yace ‘Dauko min wayata in kira likita. ”  .Hankalin, Saude ya qara “tashi da taji an ambaci likita, ashe abin mai girma ‘ne. Ta. sake rushewa da :kuka ita ko yau  ta san hukuncinta mai girmane  taje ta dauko masa wayar ta rankwafa ta mika masa,  ta zauna daga gefe tana ‘kallonsa
Hankalinta ya kara tashi tsoronta daya kada ’ jininsa ya qare, don taji ance jinin mutum na Karewa mutuwa zaiyi, tasa hannu ta goge hawayenta cikin muryar kuka ta “ce“K0 in kawo ‘maka gishiri ka barbada ne tunda jinin yaqi tsayawa?”
Dr. ya waro ido yana maimaita gishiri kuma?
Saude ta qara marairaicewa “Don Allah in kawo maka kada jinin ka ya qare.” Yanda ta yi maganar a shagwabe shi ya narkar da zuciyarsa yaji har cikin tsikar jikin shi. : Ta sake langwaBe kai “In kawo?”-. Bai san lokacin da ya daga mata kai ba, Saude ta zabura ta mike da gudu ta fice, Dr. ya raka ta da manyan idanuwansa masu saurin daukar hankalin‘ yan matan zamani ‘
Meke son faruwa da nine? Ya tambayi kansa. Tambayar da bashi da mai amsa masa. Saude ta dawo da sallamarta, ta durkusa ta mika masa gishirin, ya lumhe idanuwansa ba tare da yayi magana ba, tace, “In barbada maka?” ‘
Ya daga  mata kai alamar eh, ta durkusa ta ‘ ‘warware daurin’ sannan ta soma barbada masa gishirin, inda naman ya Bantale, bai san lokacin da
ye saki qara ba ya rike hannunta saboda azaba. » ‘
Saude ta watsar da gishirin  ta rike qafar tana fadar, “Yi hakuri don Allah‘da zafi ko?”
Ya girgiza mata kai alamar a’a, ita kanta ta san ya fada ne kawai. Ta rankwafa kanta ta shiga hura masa .da iskar bakinta , tana yi tana sharar kwalla yau Allah kadai ne zai Cece ta a gidannan. ‘
Wani irin‘ tausayin; yarinyar ne ta kama kowace Kofa ta ‘jikin sa tausayinsa da ya gani Karara a idanuwanta ya narkar da zuciyarsa, yaji tamkar yasa hannu . ya shafi gashin kanta wanda kana kallon shi kaga gashin Fulani‘: ta daure shi tamau kamar gammo a kanta, ya Kara laushe idanuwansa a hankali. A haka har likitan yazo ya same su, ta yi saurin , share hawayenta tare da gaishe da likitan ya amsa cikeda kulawa sannan suka gaisa da Dr. ya zauna yana fadin garin yaya haka? Dr cikin sanyayyar muryar shi yace ‘Tsautsayi kawai likita yace to allah ya kiyaye gaba .” Ya fada yana kallon shi cikin kulawa ya
Janyo yar akwatinsa ta duba marasa lafiya, ‘ saude ta miqe da hanzarinta, Dr ya, dubeta. . ‘
Yace ina zaki kuma
Cikin sarkewar murya irin ta wanda ya gaji da kuka tace, “Zan fita ne ba zan iya kallo ba.”
Ya zuba mata idanuwansa yanda take maganar yafi komai daukar hankalinsa, ganin bai ce komai ba yasa ta juya ta fice ita kanta ta soma tsarguwa da kallon da yake mata yau, wanda ta kasa hada shi da irin Wanda ya saba yi mata a da.
Kai tsaye Saude ta wuce daya Bangaren, tana shiga falon tayi karo da Dillaliya a rabe gefen kujera ita kadai sai kace munafuka. Saude ta karaso da azamarta cikin doki ta zauna tana fadar “A’ a Dillaliya kece yau a gidanmu, sannu da
zuwa, ina wuni?” Dillaliya ta watsa mata wani kallo mai kama da
harara, kafin ta ce“Ina ne gidan naku? Lallai samun
wuri tusar asuba, ashe ke nan har gidan
, ya zama naku, kai gaskiya ne, anzo birni an asha jar ‘miya ai dole a mance mafari.
To idan kin manta bari in tuna miki gidanku na Katsina, a Katsinar ma qarshen gari inda k0 wutar nefa ba ta wadaci unguwarku ba, gidanku na nan gidan qasa an masa faci da buhu yana nan yanda ki ka bar shi kuma za ki koma ki same shi munafuka an samu wuri an Bade sai juya mazaunai ake ke da
matar gidan baku da bambanci, fata ta murje anyi * kilin
Toki sani kin kusa komawa gida,’dan ansa ranar auren ki wata biyu yau saura wata guda, keda Garba Gurgu, yana nan yana jiran ki.”
Gaban Saude yayi wata mummunar faduwa taji ‘ tamkar ta dora hannuwa aka ta rusa kururuwa, saboda tashin hankali da kaduwa. Ta kifa kanta da kujera ta saki wani irin kuka mai ban tausayi.
Dillaliya ta’ tabe baki tana fadar, “Kuka kama yanzu’ ki ka fara ni kam ina amsar albashin ki zan wuce yanzun nan don tun safe nake nan a jibge kamar kayan wanki, ungo wannan nataccen saurayin ki Hamid yace a kawo miki.”
Da sauri Saude ta dago kanta don ganin abin da take mike mata. Wata doguwar ambulan ce, ta sa hannu ta karBa jiki na rawa.
Dillaliya‘ tace, “Har na shiga mota ya zo da kansa har tasha ya kawo mini, ya gama ni da Allah ,in kawo miki,‘ ke kin san in bacin ya biya ni kudi masu kauri ai ba zan kawo ba.
Saude dai juya takardar kawai take, tana jin wata irin soyayyar Hamid na mata yawo a zuciya, jin bai manta da ita ba shi ya mantar da ita kukan da take.
Ta mike cike da dokin san ganin abin dake cikin ambulan din, Dillaliya ta dube ta, ‘Gidan wa zaki ai bamu gama ba, kiyi maza ki tattaro mini abin da kika tara ko‘kina nufin haka nan ki ka zauna ki ka
saki baki da ciki kina ta kwasar dadi keda ki ka iya cin dadi eye?
Cikin sanyin jiki Saude tace ‘Kiyi hakuri Dillaliya wallahi ban ajiye komai ba, tunda nazo babu abin da aka bani.”
Dillaliya taxce“Ke dalla tashi’ can har sai an ba ki ke baki iya ‘yan tattare-tattare ba, duk dan wani abinda kikaga anyi sake dashi ki tattaraki boyeba?
Saude tace “Subhanallahi! Haba Dillaliya sata fa kenan?”
Dillaliya tace “Ke gafara can sakarya ai idan ba ki sata kin Boyeba bikinki yazo ke za a bari da abin kunya, idan ko kin sata kin bada an boye miki ai kin san abin da ki ka yi ”
Wani irin takaici ya kama Saude wai a tura mutum sata yanzu idan‘ yar tace zata sanya ta? Cikin sanyin muryar tace, “Bari in shiga Dillaliya ki gaida gida ki gaida su ‘Yar Baba da Inna Laure da Baba na gode
Dillaliya ta hayayyako mata cike da masifa “Idan ubanki ya bani kudin motar ba saiki tilasta ni na gaishe su munafuka, mutuniyar banza, ai duk kyan gawa dai cikin Kasa za a turbune ta sai muga qarshen jin dadi da kyau.”.
Saude dai ba ta kula taba ta fice abin ta, tana shiga bangaren ta, ta fada kan gadonta ta zauna zaman
Dirshan ta balle ambulàn din ta zazzago abinda ke ciki
Wasu kudi suka fado yan dari bibbiyu rafa guda tare da yar qaramar wayar saluka
Saude ta shiga jujjuyawa cike da mamaki ta qara zazzagawa saiga wani zobe ya fado tare da wata yar takarda da aka cika da kyakkyawan rubutu ta zubama rubutun ido dukda batasan abinda aka rubuta dinba amman rubutun ya burgeta ta dauki zoben na azurfa dan sirir tana jujjuyashi shima zoben ya birgeta ta zura zoben a dan yatsanta qarami na hagu
Zuciyarta ta kwadaitu dason sanin abinda ke rubuce a cikin takardar
Ta linketa da kudin ta boye sannan ta dauki wayar tana lallatsawa dukda bata iya wayaba amman zuwanta gidannan ta iya kunnawa da kashewa da kuma amsa kira sbd akwai wayar tarho da akasa a dakin don kiran gaggawa
Saude ta kunna wayar tana qara jujjuyata wayar na kunnuwa kira na shigowa dukda batasan lambar wayarba amman zuciyarta ya bata hamid ne don haka hannunta na kyarma ta daga kiran ta kara wayar a kunne tareda sallama
Wani sanyin dadi ya bugi zuciyar hamid lokacin da siririyar muryarta ta daki kunnensa muryar da har ya fiddah rai da sake jinta a duniya cikin doki dajin dadi yake magana
Amin wa,alai kumussalam ya habibati saudat nasan zuwa yanxu saqona yaxo gareki hakane?
Murmushin dake fuskarta ya qara qawatuwa kafin tace hakane yaya hamid dillaliya ta kawomin dazu ashe baka mance daniba yaya hamid?
Hamid yace wat? Haba sudat ai idan har zan iya mancewa dake to wlh zan iya mancewa da kaina saudat soyayyata gareki ta gaskia ce kuma ta ginu ne tun daga lokacin dana fara ganinki kuma inhar ba daina numfashi nayi ba sudat bazan taba barinki ba sainaga kin taka wani matsayi a rayuwa na miki wannan alqawarin
Cikin farin ciki dajin dadi saude tace na gode yaya hamid
Yayi wani murmushi wanda har saida ta jiyo sautinsa yace gaskia saudat dina ta fara girma haka bakinki ya bude ?
Murmushi kawai tayi bata tankaba hamid yace saudat nasha wahala lokacin dana dawo na iske bakyanan wlh saida nayi tamkar zan haukace kamin in samu insan inda aka kaiki amman bansan ko waccce anguwa bace ba a cikin abuja saida na biyo ta hannun wannan matar yanxu ya kike ganin za,ayi don muna cikin  matsala fa
Saudat an fada miki ansa ranar aurenki? Saude tace eh an fada mini
Toya kike gani abuja zanzo in sameki ko ko ya za,ai ?
Cikin kidima saude tace ina?
Ka rufamin asiri masu gidan bazasu bariba
Saidai kawai ka bari inna samu dama kawai na gudo
Hamid yace to yaushe ?donni nanda sati daya jirginmu zai tashi zuwa qasa mai tsarki aikin hajji burina kafin satin duk yaddah za,ai ayi kawai a daura mana aure don wlh saudat ina tsoron in rasaki
Saude taja‘numfashi kafin tace, “Insha Allahu Yaya Hamid duk yanda zanyi kafin satin zan yi ba zaka rasa niba da yardar Allah.”
‘ Dadi Ya kama Hamid nan yaci gaba da jan ta da hira, su kan Su ba su san sun ci lokaci ba sai da suka
jiyo ana kiran sallar Magariba.”
Hamid yace “Lah! Saudat kin ga kin shagaltar dani mun ci lokaci har haka, bari inje inyi sallah zan kira ki zuwa dare kin ji sweaty na?”
Dariya kawai ta yi shi kuma ya kashe wayar, wani sanyin dadi ya cika masa zuciya.
Ta murgina ta sake mirginawa cike da shaukin soyayya kusan sai nace ban taba ganinta cikin irin wannan farin cikin ba ‘ ’ “”
Washe gari Saude na cikin shirin tafiya aikinta,
taji karar wayarta, ta matsa inda ta Boye ta ta dauka ta kara a kunne tare da rairo sallama
Hamid ya amsa tare da gaishe bata amsa ba sai dai ta maido masa da gaisuwar ya amsa suka gaisa sosai, can ya nisa kafin ya ce“Kin san me wai  ashe jiya yayanki yazo gidanku, ban sani ba sai daga baya na samu labari?”
Cikin zakuwa Saude ta ce, ‘Kai don Allah Yaya hamid yanzu yana ina don Allah?” ~
Hamid yace“Nima abin da yasa na baro Kaduna ke nan cikin daren nazo Katsina, amma sai na samu wai matar gidanku tasa mahaifinku yayi masa korar kare, suka dinga watso masa kaya waje  cikin daren ya bar Katsina, amma ya barma maqotanku saqo abaki
Saude ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya ji take tamkar ta shake kanta saboda baqin ciki
Hamid yace,
nifa ba wai na fada miki ba ne don ki tayar da hankalin ki ba, ki yi hakuri tunda ya dawo yanzu wata rana ma , zai sake dawowa, don wallahi tallahi na yarda da Kaunar da ke tsakanin ku nasan in har yana da rayuwa ba zai mance da rayuwarki ba Saudat ki yi haquri don Allah kinji?” Haka dai ya yi ta lallashinta sannan ya kashe wayarsa.
Saude ta qara fashewa da kuka mai cin zuciya
dama she Yaya Rabi’u yana raye? Ashe ‘dama bai mance da niba? Shin kowace irin rayuwa yake yi a

Hmm labari dai nata tafiya cikin kwanciyar hankali kuma ta wani barin sai nake ganin kamar Dr Ahmad nason ya fada tarkon sofa idan ya fara son saude ya kuke ganin zata kaya tsakanin asmau da sauden hamid da saude da kuma garba gurgu da saude kai akwai rikici fa mu tara gobe daidai wannan lokacin donjin ci gaban wannan qaya taccen labarin
Naku har kullum
*ABDULLAHI ISMAIL SALANKE*

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE