Yar tallah19
YAR TALLA
CHAPTER19
“Me nake gani haka Dr? ‘Yar aikin ce ke cin abinci a food flask dinka, kam babban ……. ’
Ya watsa mata wani kallo lokacin da ya kashe wayar yace “To k0 rai yayi baki ne? Ai dai anawa take ci ba a naki ba k0? Yayi mata tambayar cike da ‘ isa da gadara. _
“ Asma ta qara shaqa kafin tace ‘Hmm! Dr. kenan amma dai .ka san wannan ba qaramin kaskanci bane da zubdawa kai girma kayi bak0? A. Zo a iske yar aikinka na cin abinci a kwanan ka,
‘yar aikin ma ‘yar Kauye, jaka dakikiya, wadda talauci yayi masu daurin …..
Dr. yayi saurin daga mata hannu ‘ya isa haka Asma, kin sanni sarai bana san cin fuska don Allah tunda ban aika miki da katin gayyata ba ki bar nan, banasan ciwon kai.’
‘ Takaici ya kashe Asma, ta matsa daf da shi tare da sassauta mur’ya tace ‘Yanzu Dr saboda ‘yar aikin ka kake cimin fuska haka?” ‘ Ya ce ‘Amma kin sani Sarai ba a gaya mini yanda zanyi ko?’ Haushi ya kama ta ta juya a zafafe ta bar masa falon, ya taBe baki ya juya wurin Saude wadda “ lomar abinci tayi wa tsaye a maqogaro tun dazu ta gaza hadiyewa, saboda tsabar firgici da tsoratar da tayi
Dr. ya zauna bakin kujerar dake fuskantar ta yana fadar.
“Ki nutsu kici abincin ki sosai ga likita nan zuwa.’
Hawayen da suka taru a kwarin idanuwan ta suka gangaro cikin kuka tace, ‘Wayyo Allah na kaja mini Allah kadai ya san abin da za ta yi mini yau na
banu na lalace! ’
Dr. yace ‘Kuka kuma Saudat? Yanzu nan har an yi abin kuka? Lallai ashe kina da kukan jini nan gaba. ’
Saude ta Kara rushewa da kuka, ‘Wallahi gida zan tafi”
Dariya ta kama Dr. ya ce, ‘Ashe matsoraciya ceke lallai Saudat na tabbata da Asma taji haushin ki da k0 sama da qasa zata hade anan ba za ta kyale ki ba, ta riga ta san halina ne sarai don haka bata damu dake a kaina zata dauki matakin don haka kima kwantar da hankalinki kici abincin ki ’
Saude ta ture abincin tare da fadar, ‘Na qoshi.’
“Me? Ai wannan ne baki isa ba k0ki dauka ki cinyeshi ko yanzun nan in kira ta ince kince tazo ta kwashe kwanukan kin gama.’
Saude tayi saurin waro ido waje tare da janyo
abincin da saurinta taci gaba daci, yayi dariya a , zuciyarsa sosai yace matsoraciya.
Tun kafin ta gama cin abincin likitan yazo ya duba ta sosai tare da rubuta mata wasu magunguna, ya kira direba yasa yaje ya siyo mata su, ya dinga lallashinta yana rokon ta a kan ta rinka shan magungunan, sannan ya bata ta tafi Cikin tsoro ta shiga sashin nasu don gani take Asma na nan na jiranta. ‘ .
Tana shiga sashinta ta maida qofa ta rufe ta ajiye magungunan ta haye kan gado ta janyo wayarta da .taketa faman ruri tun dazu taci gaba da wayarta.
Washe gari da yamma tana zaune a bangaren Dr.
tana aiki, zuciyarta sai faman sake-saken neman mafita take saboda wayar dasu kai da Hamid jiya da
daddare
Dr. ya sauko daga samansa yana sanye. da qananan kaya irin na hutawar turawa, ya tsaya daga gefen kujera yana kallon Saude wadda ke durkushe tana ‘goge goge
‘ . Jikinta ya bata tamkar ana kallonta, don haka tayi ‘saurin waiwayawa, tsaye ta gan shi a gabanta ya harde hannuwansa a kirji tamkarmai nazarin wani abu. Saude tayi saurin durkushewa tana masa sannu
da fltowa, bai amsa mata. ’ba‘ sai ma ya sake gyara tsayuwarsa. “Me yasa baki san hutawa?”
Saude ta dan kalle shi kadan kafin ta ce ‘Ai aikina ne shi yasa.’
Dr. yadan dauke kai kafin yace, ‘Ai kin kusa barinsa, saki wannan aikin ma taho mu fita mu sha iska.”
Bai jira abin da za tace ba ya yi gaba abinsa,
Saude ta raka shi da idanuwanta. To me yake nufi da ita? Ba dai korarta za suyi ba? Da sauri ta zabura ta bi bayansa.
. Hadaddan wurin shakatawa ne wanda aka kashewa dubban nerori wurin Kawata shi, don an zuba abubuwan ban sha’awa da debe kewa. Saude ta . koma jikin wani dodon roba, tana kallon Dr. wanda ke wasa da dan biri, can ya dago ya yafito ta da hannu alamar ta zo duk da tsoron da ya cika mata zuciya haka ta dake ta tafi inda yake, ta tsaya daga gefe tana kallon su, ba ta ankara ba taji ya fizgo hannunta ya hada da na birin, yana wa birin magana cikin harshen turanci.
Mutuwar tsaye tayi don tana bala’in tsoron sa sosai, don ma yana dan Karami, sai ta ga ya ’fadi’ Kasa alarnar gaisuwa. Dr. yayi dariya yana kallonta yace “Ana gaishe kifa?” Kallonsu kawai take bata ‘ iya yin magana ba, birin ya mike yana ta faman zazzagaya ta yana tsalle-tsallen murna. ‘ ,
Dr. ya janyo hannunta suka nufi wani.‘ qaton lilo
na roba mai matattakala ya dan kalle ta da murmushi a fuskarsa ya ce “In hau za ki jujjuya ni’?’ ‘Duk da
haushin riKon da yayi mata sai da tayi dariya saboda yanda yayi maganar.
Yace, ‘Okoy, dariya ma na baki to bari in dora ki in jujjuya ki.’ Tun kafin ta yi wani yunkuri taji ya sure ta ok ya dora saman lilon.
Saude ta fasa wata uwar kara saboda razana, don ita gaba daya ma lilon tsoron shi take yi, dariya ta bawa Dr. sosai na kauyancin nata, don haka yana dariya yana jujjuyawa da ita, mutuwar zaune ta yi ta . runtse idanuwanta tana sauraren ikon Allah, shi kuwa dariya kawai yake mata, yana zolayarta ganin ba shi .da niyar daina juya tan yasa ta bude idanuwanta tana shirin kuka, ta hau rokonsa.
‘Don Allah don Annabi ka sauko da ni.’
Dr. ya tsaya da lilan ya matsa yana fadar, ‘To sauko tunda ba kya so.’
Saude ta waro idanuwa don ta san ko da kudi aka bata bazata iya saukowa ba, ya yi murmushi tare da mika mata hannunsa ta rike sannan ya sauko da ita, yana mata dariya yace matsoraciya duba ki ga aku na .kallon ki. ’
Saude tayi saurin juyawa, caraf ya riKo hannunta ya jata da saurinsa. Haushi ya kama ta yanda ya maida ita kamar Karamar yarinya. Saman wasu kujerun roba ya zaunar da ita shima ya zauna, suka
sa zagayayyan tebur din a tsakiya. Saude tabi abin . da aka dora’ saman tebur din da kallo, wanda a kai ‘
‘ rafin din shi gwanin burgewa. Dr. ya miKa hannu ya dauko ya mika mata ta tsaya tana kallon shi ya miqa mata tare da fadar.
“Karba mana.’
Ta mika hannu ta karba,tana kokarin bude rafin leda din. Dr. ya yi saurin tsaida ita yana fadar, ‘tsaya tsaya waya fada miki idan aka bawa mutum gift budewa yake’a take bakauyiya ai bari ake sai an tafl.’ Yana maganar cike da zolaya. .
Saude ta zumBuro baki” jin ya kira ta da bakauyiya, dariya ta kama shi ya ce, ‘A’a ‘yanmata ashe kin iya fushi irin haka?”
Ta dauke kanta ba tare da tace Kala ba. Yace, ‘ ‘Wai fushin ki keyi da gaske am so sorry, tuba nake -kaina bisa wuyana.’
Dariya ta kubce mata yanda yayi maganar a ladafce sai kace ba YallaBai din data sani ba, ganin dariyarta yasa ya mike yana fadar
“Taso muje kin ji ana ta kiran sallah a_ masallaci.’ ‘
Saudeta tashi ta mika masa gift din daya bata, ‘ya dan zuba mata idanuwansa babu alamun wasa a fuskarsa ya ce ‘Da shi za ki tafi kyauta ce daga gare‘ ni.’ Yana gama fada ya juya ya yi. gaba abinsa, ba tare da ya saurare abin da za tace ba.
Tsabar mamaki da kaduwa su suka hana Saude furta komai, har sai da ya kusa bacewa ganinta
saunan ta iya wage murya tana fadar, “Na gode kwarai.’ Hannu kawai ya daga mata ba tare da ya juyo ba
ya Bace abinsa, ita ma tayi gaba cike da zullumin
abin da aka nannade haka. Tana .shiga dakinta ta fada kan gadonta ta yi zaman dirshan ta shiga bude kyautar, ta ciro wani
kyakkyawan kwali mai kyan gaske da zanen waya waya a jikinsa.ta gani Saude tabi hoton wayar da kallo kai da gani ka san tayi tsadar gaske, a zuciyarta ta furta ‘Allahumma arzuquni” tasa hannunta ta bude kwalin.
Gabanta ya yi wata mummunar faduwa tayi ‘ masifar firgita ganin sabuwar wayar kwance cikin kwallin, ta ciro ta tana jujjuyawa, touch screen mai shegen kyau, wadda ta san ko da kudi aka hada ta ba za ta iya kunnata ba.
Saude ta riqe wayar tare da dafe kai, yau na shiga uku ni Saude, wai me ke shirin faruwa da nine? Wasu irin hawaye suka ziraro daga idanuwanta ta lura mutumin nan so yake ya jaza mata bala’in da ba zata iya dauka ba, yanzu tsautsayi yasa Hajiya ta samu labari ya kenan?
Motsin taflyar da taji ne ya sa ta zabura ta maida
wayar cikin kwalinta ta tura a qarkashin filonta, tana faman‘muzurai. Aunty ce ta shigo da sallamarta suka
gaisa sannan ta ajiye mata wata leda Saude ta mika hannu ta janyo ledar tana duddubawa.
Sabulan wanka ne dana wanki tare da kayan shafawa da mayuka, ta ajiye‘ leadar gefe ta koma ta kwanta tana fatan gari ya waye ta je ta maida
masa wayarsa, don ba zata yarda ba ya jaza mata tashin hankali da bala’in da ba za ta iya dauka. Ba
Dole nema ta runtse ido ta fada masa‘ ya fita daga rayuwarta ita dai ba kowan kowa bace hakan kuma ba yana nufin bata san mutuncin kanta bane da wannan tunanin bacci barawo ya sace ta.
Washe gari da safe Saude ta tafl Bangaren Dr. Ahmad babu kowa a falon nasa don haka ta zage ta shiga aikace-aikacenta qarfe goma daidai ya sauko daga samansa yana sanye da jallabiya sabuwa ruwan toka mai hade da hularta
Suna hada ido da Saude ya yi saurin qarasa saukowa daga matattakalar yana fadar, “Zo. nan Saudat.” *
A hankali ta dago ta kalle shi tare da gaishe shi cikin girmamawa kamar yanda ta saba. Ya amsa’ a tsanake sannan ya jefo mata tambayar da ta sanya ta saurin dagowa tana kallonsa, ya qara‘gyara tsayuwarsa tare da maimaita mata tambayar.
“Na ce laflya baki bude kyautar da nayi miki ba
Ko baki iya bane?” Ya karasa maganar cike da tuhuma. ;
Saude ta dukar da kanta tana kallon kafet din dakin cikin nutsuwa ta soma magana.
“Kayi haquri Yallabai ba wai ban yaba ba ne kawai dai naga kyautar ba ta cancanta dani bane shine yasa nayi’ tunanin maido maka, amma ka yi hakuri
Dr. Yayi wani takaitaccen murmushi tare da zama saman hannun kujera ya zauna yana kallonta a nutse kafin ya ce ‘Dama ita kyauta cancanta ce ke sawa ayita idan kuwa cancanta ce to ke kuwa kin ‘ wuce wadda a kai miki kinfi qarfin hakan.
Kuma idanma ba ki sani ba ina so yau ki sani dangantakata dake tamkar hannu da ido ne yanzu sannu a hankali zan shafe hawayen da ke kwaranya daga idanuwanki insha Allahu sai na wanzar da dariya a idanuwan dake ta zubar hawaye, kin fahimta?”
Saude ta girgiza masa kai tana fadar, ‘A’a Yallabai yin hakan yana nufin zaka tsamo ni daga rijiya ka jefa ni kogi ne Yallabai ka yi tunani zan iya shiga matsala wajen Hajiya, na tabbatar idan ta samu labarin kudirin da kake nufo ni da shi zata dauki kowane irin mataki a kaina,
Dr Ahmad ya kada mata kai yana fadar, ‘Ko
kusa Saudat babu wandu ya isu ya yi wu mutum ”abinda Allah bai masa ba haushin me Asmu za ta ji
don kawai ina kokarin taimaka miki meye abin da zai tunzura ta a ciki? Ni ban ganshi ba, kuma koma
akwai ba zai dame ni ba, zan yi Kokari har sai na sauke alkawarin da na dauka.”
Idon Saude ya ciko da hawaye cikin muryar kuka tace, ‘Na san ba zai dame ka ba YallaBai amma ni zai dame ni, wata qila ma ya zamo silar barina duniyar gaba daya. ’
Dr. Ahmad ya ce, ‘Hakan ma ba za ta kasancewa ba Saudat ki daina ma fada.’
Saude ta ce, ‘Idan ya kasance fa?”
Shiru yati yana kallonta Saude ta yunkura ta mike hawayen da suka ciko daga idanuwanta suka samu damar zubowa cikin kuka tace, ‘Zan bar gidan nan dole zan bar shi, dan ina tsoron abin da zuciyata ke hangowa ina jiyewa kaina, dan idan ma wani abu ya same ni babu wanda Zai yi kukan rashina, babu bani da shi…. Kuka ya ci Karfinta sosai.
Dr. Ahmad ya yunkura ya zagayo ta gabanta yana kallonta cikin sanyayyar muryar shi ya soma magana.
‘Duk inda ki ka nufa a fadin duniyarnan sai na nemo ki, babu inda zaki shiga ki layance min. Ina tare dake Saudat har: sai naga kin yi dariya sai naga rayuwarki ta inganta kin samu farin ciki mai dorewa
na yi wa kaina wannan alkawarin kuma zan cika shi ko da hakan yana nufin rasa komai na a rayuwata.’
Saude ta yi saurin juyawa tana kallonsa ya daga’ mata kai yana fadar, “Tabbas kisa ido kiyi
kallo.’ ‘Ya juya a sukwane ya fiCe daga falon ya bar ta
nan tana kallon qofar da ya fita. Wani irin kuka ya zo mata, tsoronta daya a duniyar nan matarsa Asma; don ta san ba lallai bane ta yi musu kyakkyawar .zargi ba, tana tsoron ta yi musu mummunan zargin da zai‘sa ta yanke mata hukunci daidai da zarginta. Saude ta Kara rushewa da kuka don har ta hango irin bala” in da za ta iya fuskanta Haka ta karasa aikinta tas ta baro Bangaren nasa, yinin yau haka ta yi sa a kwance. Da daddare kuma Hamid ya kira ta ya Kara caza mata Kwakwalwa. “Wai Saudat meke damun ki ne shin k0 kin mance da yau saura sati uku auren ki? Na lura hankalin ki kwance yake tun yaushe nake fama dake kina gocewa. Saudat idan harkin soma san Garba ne ki fada mini in fidda raina kawai, amma don me zaki tayi min yawo da hankali kice yau ki ce gobe, idan kin san ba zaki iya fitowa daga gidan ba ki ‘fada mini ni in zo da kaina in dauke‘ki.’ ‘Saudat ta ja numfashi ba ta taba tunanin ya iya bude wuta haka ba, ta ma rasa ta inda zata fara, don . haka ta kwantar da murya tana ba shi hakuri tare da yin .
masa alkawarin duk rintsi gobe zata gudu ta bar‘ Abujar. » ,
Abun duniya duk ya ishi Saude tunaninta daya take yanzu hanyar da za ta bi ta bar. gidan ga YallaBai yana nema ya taso ta gaba tsoronta daya ma yanzu kar ya ruguza mata al’amuran ta, wannan tunanin ne ya hana Saude barci da wuri sai kusan biyu da wani abu na dare ta kwanta, don sai data harhada kayanta tsab na barin garin. .
Sallar Asuba ma da kyar ta iya yin ta saboda baccin da yaci qarfinta. A kan sallayar ma wani sabon baccin ya sake dauke ta. Ba ita ta farka ba sai qarfe sha daya da mintina. Ita kanta ta yi mamakin tsawon lokacin da ta dauka tana bacci, don haka ta mike da hanzarinta zata shiga bandaki ta ji kukan wayarta, don haka ta dawo ta dauka. ‘
Tun kafin ta qarasa sallamar ya katse ta ta hanyar fadar, ‘To yaya kin taho k0 kuwa yanzun ma baki samu damar ba? .
Saude ta sauke numfashi tare da fadar, ‘Nina fada maka Yaya Hamid insha Allahu yau zan bar gidan nan duk rintsi, saboda ni kaina nafi ka kaguwa dana bar gidan nan don Allah ka kwantar da hankalin ka insha Allahu babu abin da zai faru.’
Yace, ‘Hmm! Saudat kenan na lura baki san irin son da nake miki ba shi yasa har kike fadar kar in damu wallahi yanzu kasancewa ta da ke ne kawai zai ba ni farin ciki a rayuwata, don Allah Saudat kada ki ci gaba da nisanta kan ki dani please; ’
Tausayinsa ya kama ta ita kanta ta soma jin irin yanda yakeji yanzu don haka cikin sanyin murya
ta ce, “Kayi hakuri Yaya Hamid ni kaina. ina jin
yanda kake ji a yanzu, kuma nan da wasu ‘yan
awanni zan maka kyakkyawan albishir.”
. Hamid yace Allah yasa ki gaggauta kin ji?”
’lnsha Allahu.” Ta ce cikin sanyin murya, sannan ta. kashe wayar ta mike da nufin maida ta wurinta, zuciyarta ta yi. wata mummunar bugawa.
A tsaye yake jikin qofar ya harde hannuwansa a kirji ya tura mata idanuwansa da ke sanye cikin farin gilas gaba daya ya tattara duk wata nutsuwarsa a kan Saudat taji.tamkar ta kurma ihu saboda tsabar: tsoro da kaduwa duk ta dabarbarce,.
, Dr. Ahmad ya taka a hankali har zuwa gabanta ya mika: mata hannu, “Bani wayar.”
Ba musu ta miqa‘ masa wayar hannunta na rawa. Yace, ‘miqo min har da waccan dana baki.’ Jikinta na faman bari ta juya ta dauko masa, ya karba kawai ya juya ya fiCe abinsa ba tare da ya ce da ita komai ba
Saude ta fada saman gadon jagwab kamar an zuba kayan wanki har wata zufa ke tsatstsafo mata, ta daura hannu a kai .Wayyo Allah na! Ya Ubangiji gani gare“ ka
, Asma. ta fado kamar an jefo ta, ‘ ‘ Saude ta Zabura ta miqe a tsorace tana kallonta,
Ta tsaya tana watsa mata wani malalacin kallo. Saude ta durqushe a gun, tsantsar firgici ta bayyana a fuskarta bakinta sai kyarma yake wurin fadin
‘In…ina… ina wuni
Asma ta tabe baki tare da jan wani dogon tsaki, ta shiga zagaye dakin tamkar mai neman wani abu ta kai ta kawo ta kai ta kawo, ta dinga binciken ta sai data gaji sannanta juyatafice batare datace uffan ‘ba.
Saude tayi suman tsaye, me keson faruwa ne da ita ne? Ta yi masifar firgita, ita dai ta san ta shiga . tsaka mai ‘wuya, don da za a auna ta a lokacin babu abin da zai hana a tabbatar da hawan jininta, kukan ma ya gagare ta sai muzurai kawai take yi.
‘ Wasa-wasa lokaci ya soma tafiya tana nan zaune, ” tabbas idan ta yi wasa lokaci zai qure mata, don gangar jikinta ce kawai zaune a gun amma zuciyarta na wurin
Dr. Ahmad. Tsoron ta daya Allah yasa ya yanke mata hukuncin da za ta iya dauka. Wasa-wasa ta lurawankin hula zai iyakaita dare,don hakata yanke shawarar tashi ta je ta ba shi hakuri, ba yanda ta iya haka ta lalalBa ta mike: jikinta amace ta nufi Gangaren nasa.
Sallamar da take shirin yi ta makale a
makogoranta, tsaye yake goye da hannayensa a baya wadanda ke rike da wayoyin da ya karba wajenta, duk da bayansa take saboda ya bada
baya, amma hakan bai hana ta fahaimci yana cikin yanayi marar dadi ba, tsoronta ya qaru matuka tana fargabar ya yi mata mummunan zargi.
Jin shigowarta yasa Dr. juyawa a hankali yana kallonta da jajayen idanuwansa ba tare da ya ce mata kala ba. Saude ta durkusa a gabansa muryarta a sanyaye tace ‘Don Allah ka yi hakuri Yallabai wallahi ba…
Dr. ya yi saurin daga mata hannu alamar ta dakata, ya yi taku daya zuwa uku ya matso gabanta cikin razananniyar muryarsa wadda ke fita a hankali ya fara magana.
“In yi hakuri laifin me ki ka yi min? Kina tunanin raina ya baci ne don na kama ki kina kula maza?” Ya girgiza kai.
“K0 daya Saudat ko a jikina, ko da kuwa duk mazan duniyar nan samarinn kine ba zai rage ni da ‘ komai ba, illah dai kawai na tausayawa rayuwarki dake qoKarin rugujewane, ke yarinya ce Saudat ba zaki gane waye da namiji ba sai ran da ya buga miki irin nasa tambarin, ranar ne zaki fahimci irin wautar da ki kai a baya.
Ni ba zan takura ki ba in ce dole sai yanda nake so za ki yi rayuwa ba, a baya wauta na yi da rashin bincike wanda yasa na dauka zuciyarki shararriya ce
babu wani datti a cikinta, ashe ban sani ba tuni kin shigar da soyayyar da take nema ta makantar da ke ta
kai ki ta baro ki.’ Ya dan yi shiru yana kallonta yana girgiza kai, sannan ya mika mata wayarta.
“Ungo ga wayarki.”
Hankalin Saude ya qara masifar tashi bata san lokacin da idonta ya kawo kwalla ba, sai dai ta ji zubar
su saman kuncinta. Dr. ya waro ido cike da mamaki
kafin yace ‘Kukan me zakiyi kuma Saudat ai na dauka firgicin ki‘na raba ki da masoyin ki ne da na yi kuma sai nace na bar ki da shi, to meye kuma abin kuka?”
Saudat ta sa hannu tana share hawayenta, wanda sukaqi tsayawa ta soma magana cikin kuka. “Kayi hakuri wallahi ba da wani namiji nake magana ba Hamid ne.”
Nan ta kwashe labarinsa ta bashi tun daga sakon da ya aiko Dillaliya da shi har zuwa wayar da suka yi. ~ Dr. yaja numfashi kafin yace ‘Saude kenan, a dan labarin da kika bani na fahimci kina son Hamid shin haka ne?”
Saude ta ji tamkar ya dora mata Dala da Gwauron Dutse aka, ta rasa abin da za tace masa ma.
Dr. ya sake cewa, ‘Dake nake magana fa Saudat kin mini shiru
Da kyar ta iya dagowa ta kalle shi, yayi mata masifar kwarjinin da baza ta iya kallon idanuwan shi ta fadi abin dake zuciyarta ba. Murya: shi a sanyaye ya sake maimaita mata tambayar a karo na uku, bata
san yanda a kai ba sai dai ta samu kanta tana mai girgiza masa kai, alamar a’a.
Shin meye dalilin saude na cewa batason hamid mu tara gobe daidai wannan lokacin donjin yaddah zataci gaba da kayawa
Daga
*ABDULLAHI ISMAIL SALANKEN ZAZZAU*