Yar tallah20
YAR TALLA
CHAPTER20
ASHA KARATU LAFIYA
Dr Ahmad ya ajiye wata nannauyar ajiyar zuciya kafin yace “Kije zan neme ki.’
Saude ta share hawayenta ta mike a sanyaye ta tafi Dr. Ahmad ya bita da rinannun idanuwansa wanda sukai jawur.
Saude tana shiga dakinta ta fada kan gadonta ta fashe da wani irin kuka mai sauti, ita kanta ba zata iya misalta tashin hankalin da take ciki ba, zuciyarta na wurin Hamid ta san dole ya neme ta tunda ta sanar da shi yau za ta bar gidan, shin idan ya kira ta bai same taba wane irin zargi zai mata? Kila ma ya rabu da ita. Wayyo ni Allah na! Ta Kara rushewa da wani sabon kukan. Yinin ranar haka tayi shi babu wata walwala a tare da ita.
. Da yamma liqis
Dr. Ahmad ya aiko aka kira ta, don haka ta wanke fuska ta murza mai da hoda, duk wai don karya gane kukan data sha, sannan ta fice.
Da sallamarta ta shiga falon nasa, yana zaune saman daya daga cikin kujerun falon, ya harde tamkar wani basaraken Balarabe, shigar ta manyan kayan tayi masa masifar kyau ta Kara fitowa da cikar kamalarsa da kwarjininsa.
Saude ta durqusa dan nesa da shi kadan kafin tace, ‘Sannu dahutawa YallaBai.’
Dr. Ahmad ya dan zuba mata idanuWansa kafin yace, ‘Me ya samu idanuwan ki Saudat, kuka ki ka rinka yi tun tafiyar ki k0?”
Da sauri ta girgiza masa kai alamar a, a ‘Hmmm! Saudat kenan me yaSa kike san boye mini damuwarki alhalin duk wani motsin ki sai zuciyata ta fassara mini shi Ya girgiza kai tare da fadar ‘Tashi muje ki min rakiya cikin gari.’ ,
_ Da hanzarinta ta yi saurin daga kai tana kallonsa Dr ya mike; tare da fadar kar kice komai biyo ni kawai. Saude ta mike. jikinta a sanyaye tana shirin fashewa da kuka yana kallonta bai kula taba ya yi gaba abin sa. Saude ta bishi tana matsar kwallarta ita dai so yake kawai ya jaza mata tashin hankalin da ba zata iya dauka ba kawai. Suna fitowa harabar gidan ta samu masu tsaron lafiyarsa wadanda suke a lungu da sako na gidan sun nufo sa, wasu kuma sun nifi wurin motocinsa wadanda yake fita dasu
Dr. Ahmad ya daga masu hannu kawai ya nufi wata shareriyar Jeep mai qofa takwas fara mai bakin gilas, daya daga cikin masu gadin nasa ya take da gudu ya bude masa kofar baya ‘
Dr Ahmad ya juya yana kallon Saude wadda ke tafiya tamkar‘ yar kaciya, yayi mata nuni da hannu alamar ta shiga taji tamkar ya dora mata dukkanin tashin hankalin duniya taja ta tsaya cikin
tsananin kidima
Dr Ahmad ya dan matsa daf da ita muryarsa Kasa
kasa yace ‘Zaki shiga k0 k0 sai na dauke ki na shigar dake da kaina?” .
Ganin yanda ya matso ta ya tabbalar mata zai iya yin abin da ya fada din don haka ta janyo dauriyar duk duniyar nan ta dorawa kanta, ta taka a sanyaye ta ’ shiga motar, tana zama shi ma‘ya shigo aka maido masu kofar aka kulle
Saude taji tayi mutuwar zaune idan tace bata cikin tsananin rudu da kaduwa ta san ta yaudari kanta. Ta lumshe idanuwanta tana sauraren bugun zuciyarta ta san ita yau tata ta Kare ba abin da zai hana Asma na samun labari tasa bindiga ta. Harbeta
Shiru babu wanda yayi magana a cikinsu. Sai Dr. Ahmad neya dan mika hannun shi ya latsa gefen motar, sai ga wasu hadaddun labulaye sun zagaye motar , ya mika hannu ya bude na’ura mai KwaKwalwa (Computer) din dake gabansa wadda ke jikin motar ya kunna, sannu a hankali ta kama tamkar talabijin din bango.
Ya koma ya jingina yaci gaba da latselatsensa ba tare da ya kalli inda take zaune ba, kowa da abin da
yake sakawa a zuciyarsa.
Ba ta san sun iso ba sai dai ta ji an bude masu qofar, Dr. ya rufe computer din ba tare da ya kalle ta ba yace ‘Fito muje. ’ Bai tsaya ba ya sa kai ya fito don haka ita ma ta ziro qafafuwanta ta fito tana kallon harabar wurin da suka shigo.
wurin gyaran jiki ne wanda ya amsa sunansa a cikin garin Abuja daga sama anyi rubutu da manyan ..
baki a jikin wani karfe ANNURI beauty QUEEN rubUTun ya bada haske
‘ Dr Ahmad ya yi gaba Saude na biye dashi har suka iso cikin masu take masa baya daya yayi saurin isa ya bude musu qatuwar kofar ta gilas tareda gaishe su
suka shiga qaton wurin mai kamar an gina shi da’ zallan gilasai Da kyar Saude ke dosana kafarta’ dan gudun kar ta fasa gilas din
Suna shiga ciki su kabi wata qofa mai kama da ofis,‘ Dr. ya tsaya gaban wata mata cikin Harshen turanci su kai magana sannan ta miqa masa wata yar lakarda yayi wani dan rubuce rubuce ya miqa. mata tasa hannu, ’ sannan ta mike tayi masa nuni da wani kujerar dake gefe da dan tebur dinta guda a gabanta; wanda aka dora News paper a sama, ta kawo masa lemu da cake sannan taja hannun Saude. .
“Come and enter my frnd Saude ta ce ikon Allah ai ke kika san shi
Tasa hannunta cikin na Saude suka shiga cikin wurin qaton wurine na gaske wanda aka zubama duk wani” injin ‘ k0 wata na’ura ta gyaran jiki ‘Matar ta kira wata babbar mace Bahaushiya wadda ba zata wuce shekara arba in ba ta nuna mata Saude Sukai magana cikin harshen turanci da matar ta mikawa Saude‘hannu da murmushi a fuskarta tana fadar.
“You are welcome my sis. ‘
Saude tayi sukuti tana kallonsu cike da takaicin turancin banzan da suke mata. K0 matar ta lura ne Oho ta canja harshe zuwa Hausa.
“Sannu da zuwa ‘yar uwa muje k0?”
Ba musu Saude tabi ta suka nufl Bangaren gyaran gashi, ta zauna a kai mata gyaran gashi sosai sannan suka wuce Bangaren gyaran jiki, inda a kai mata dilka da halwa lokaci guda, daga nan a kai mata gyaran qafa
da na akaifa. Tun kafin a qarasa dama Saude ta gama tsurewa da
tsabar kyan da ta gani kwance a jikinta, ita kanta bata taBa sanin haka ta hadu ba sai yau😂 , don k0 Indiya sai
haka, saboda idan baka san taba aka ce maka Ba’indiyace ba yanda za ai kai musu. ‘
Ita kanta ta san sun ci lokaci, don k0 da bata duba agogo ba ta san dare yaja sosai. Ana gamawa suka fito inda Dr. Ahmad ke zaune rike da jarida yana dubawa suna Karasowa ya ajiye jaridar ya mike yana kallonta tamkar wadda ta fado daga sama, lokaci guda kuma ya lumshe idanuwansa ya bude ya juya ya koma wurin ‘yar Baturiyar nan wadda ke ta latse-latse cikin computer ya mika mata A.T.M dinsa tasa ta cire kudin sannan suka fito daga wurin.
Ita dai Saude kallonsa kawai take, amma tambayoyi ne cike fal da cikinta, wanda ta tabbatar ba
Babu mai amsa mata su sai shi kadai. Suna mota wanda suka shiga kamar dazu direba ya jasu suka fice daga » harabar wurin Saude ta lalubo duk wani karfin halinta kafin ta iya bude baki ta kira sunansa.
“YallaBaii’ ,.
Dr. Ahmad ya dago da idanuwansa daga saman wayarsa yana kallonta kan yace, ‘Ya dai Sande?”
““ Ta dan sha Jinin jikinta kafin tace ‘Ina so in dan ‘ yi wata‘ yar tambaya.” ce
Dr ya dauke kansa daga kanta kafin yace, ‘Tun » kafin kiyi tambayar na san abin da zaki tambaya don haka ki yi haquri ki hadiye zan baki amsa da kaina ‘ idan lokaci ya yi.-’
Zata sake magana ya daga mata hannu, hakan yasa ta ja bakinta ta tsuke a dole, ta bar zuciyarta na faman‘ dukan tara-tara. Suna isowa gidan ta .kwasa da sauri da niyar ta riga shi shiga gidan, Dr. ya yi saurin tsayar da
ita ta hanyar kiran sunanta, taja ta tsaya cak ‘ Da kansa ya Karaso har inda take ya daidaita tsayuwarsa a gabanta kafin ya soma magana, ‘Ki shirya gobe da safe zamu fita.”
Saude tayi saurin dago da fuskarta tana kalloh shi shima ya zuba mata idanuwan nasa wanda babu alamar fargaba a cikinsu,idanuwanta suka kawo kwalla cikin muryar kuka ta soma magana.
“Ni wallahi ,ba zanje ba na gane so kawai kake ka jaza min bala’in da ba zan iya dauka ba na rantse da . Allah babu inda zani 🙅…. ‘ Ta Kara rushewa da kuka.
“Don Allah don Annabi ka taimake ni kar ka jaza min bala‘in matarka don Allah…’
Dr. Ahmad yayi wani murmushi wanda ya tsaya iya laBbansa kawai kafin yace, ‘Ashe kina da baki haka? Da kyau. Toki dai shirya‘ fita gobe koma meye zai faru ai kina iya daukarsa idan kuma baki zoba to ki tabbatar ni da kaina zan shigo in dauke ki kin san kuma zan iya, don haka sai da safe.’ .
Ya juya ya yi gaba ya bar ta tana masa rakiya da kallon dake cike da mamakinta karara, don a yanzu hawayen ma sun daina zuba. Mamaki da fargaba suka kashe ta, ita kanta ba ta san tsawon lokacin da ta dauka a tsaye ba, don sai da tayi da gaske sannan ta iya jan qafafuwanta ta yi gaba.
Tunane-tunane da damuwa yau su suka hana Saude barci da wuri, shekarunta sunyi Karancin da zata iya yankewa kanta hukunci, data gaji da tunanin sai ta kifa kanta samaun filo ta shiga kuka mai sauti, sai da ta yi mai isarta sannan ta yi shiru don kanta, babu wanda ya lallashe ta, sai ajiyar zuciyar da take ajewa akai akai. A’ haka barci barawo ya sure ta ba tare data sani ba. ‘
Tun da garin Allah ya waye Saude ke zaune saman gadonta ta zuba uban tagumi da hannuwa bibbiyu, kana kallonta zaka tabbatar da tsantsar damuwarta, ba « ta ankara ba taji an turo kofa za a shigo. ,
Gabanta ya yi mummunar faduwa ta zabura ta miKe tana faman muzurai don duk a zatonta Dr. Ne
Aunty ta turo Kofa ta shigo da sallamarta Saude taja wata ajiyar zuciya sannan ta koma ta zauna Aunty ta ‘ ‘dube ta da kulawa kafin ta ce, “Lafiya kuwa Saudat?”
‘ Saude ta dake kafin tace, ‘Me kika gani Aunty?” ‘Na ga duk kin yi wani wurjanjan ne kamar ba kya cikin hayyacin ki.” ‘
Saude ta girgiza kai ‘A’a lafiya ta qalau kawai dai
.tunani ne.” ~ Aunty ta dan zuba mata ido kafin tace, ‘Kai Saudat ban yarda da keba jeki gaban madubi ki kalli ‘ kanki da kyau, kiga yanda kika koma, wannan kyan da daukewar lokaci guda na mene ne?”
Gaban Saude ya kara mummunar bugawa duk ta dabarbarce ta rasa abun fada. ‘
Aunty ta girgiza kai tana wani murmushi wanda ‘bai kai zuciyarta ba tace, ‘Saudat ke nan ni ba tun yauwaba na fara zargin ki, sai dai a yau na kara . tabbatar da zargina, Saudat gyaran jiki ki kaJe,”
Gaban Saudat ya Kara wata mummunar bugawa a “ karo na biyu, idanuwan nan suka yo warwaje . Aunty tace“Hmmm! Saudat kenan me yasa kike
Kokarin yaudarar kan ‘kine? Me yasa ki ke nema ki dorawa zuciyarki wahala ne? Shin Saudat kin yi tunanin wannan kyan naki zai iya daukar hankalin maigidan nan ne? K0 kusa wallahi k0 da wasa don Yallabai ya wuce duk wani tunaninki ’ ki Don idan har kyau na daukarsa to duk inda ake Zuwa auro: kyakkyawar mace a fadin duniyar nan:
‘yana da kudin da zai iya aurarta ke k0 siyowa ake yi yana da kudin siyan ta.
Saude duk yanda baki tunani Yallabai ya wuce da sanin ki nasan YallaBai tun kafin ya auri Asma’u asalina ‘yar aikin gidan suce. Saudat wallahi . wallahi yar gidan shugaban Kasa har falon Hajiyarsa tazo nemansa, amma ya fice ya bar mata gidan bai kula ta kanta ba. Saudat duk yanda ki ke ganin YallaBai ya wuce ’nan, don jin kansa da mazantakarsa ya wuce yanda kike ganinsa a cikin gidan nan, donni kaina ba zan iya kirga yawan ‘yan matan da yayi ba tsakanin Abuja da sauran jahohinnan ba. Saudat ina guje miki daukar Dala da Gwauron Dutse aka, don idan ki ka bari Asma’u ta samu labari ina mai tabbatar miki sai kin raina kanki.
Don k0 da ki ke ganin kamar basu damu da juna ba, to wallahi suna son junansu don kuwa auren soyayya su kai kamar za su cinye junansu. ‘
Asalin Asma ‘yar asalin nan Abuja ce mahaifinta shi ne Ministan kudi na Nigeria a lokacin kafin ya sauka daga kujerar. Mahaifinta abokin mahaifin Yallabai ne ba zan taba mantawa ba sun taba zuwa gaishe da mahaifin Yallabai da Asma da mahaifinta da mahaifiyarta a lokacin shi mahaifin Yallabai yayi yar rashin lafiya.
Anan ne suka hadu da Asma da Yallabai, tun farkon soyayyarsu sun ‘tiffita qasashe masu yawa,
Soyayyarsu ta dauki tsawon lokaci kafin a tsaida maganar aurensu A lokacin ne kuma iyayensu suka sanya su harkar Siyasa Cikin sati biyu a kai bikinsu aka gama cikin ma,aikatan da aka baiwa Asma Hajiyar Yallabai ta ‘ hada masu dani na dawo gidansu da zama.
A lokacin basa wannan kasa basa wancan kasa cikin wata guda ba baifi su zauna nigeria sau biyu ba Daga baya ne kuma aka fara kamfen to sannan ne suka zauna aka fara yaqin neman zabe ita da shi duka kowa yana neman tasa kujerar shi yana neman dan majalisar tarayyar Abuja, kuma cikin ikon Allah kowa ya samu.
To a lokacin ne fa kowa ya kama gabansa, haduwa ma sai tayi masu wuya suna cikin gida daya, amman sai suyi wata wani lokacin basu hadu ba, sai dai k0 cikin dare, amma idan wannan yana Nigeria to shi wannan ya bar kasar,idan wannan ya dawo to wannan ya tafi wurin meeting. Haka dai abin yaci gaba da kasancewa
Kafin zuwan ki Asma ta samarwa YallaBai ‘yan ‘ aikin da zasu rinka kula da shi sun fi biyar duka an karesu kowacce da tata matsalar har zuwa kanki Saudat da ki ke ganin Asma ba qaramar mai arziki ‘ bace duk yanda ki ke tunanin rashin mutuncinta ya
wuce nan musamman a kan mijinta‘ Don tana da masifaffen kishin da ba ki tunani zata iya yin komai a kansa, don haka Shawara ‘nake baki
Don ina sonki saude ki kama kanki tun kafin
Yallabai ya lura da takun ki, idan kunne yaji Ta tabe baki tare da juyawa ta fice
Saude ta saki wata ajiyar zuciya mai qarfi shin in ban da abun Aunty ma ita ko giyar wake ta sha ai bata fara hada kanta da YallaBai ba, balle da hankalinta .dama abin da take gudu kenan mummunan zargi, shin yanzu ma idan suka sami labarin fitarsu jiya ya kenan? Ta girgiza kai cike da fargaba ta yunkura ta mike don tsoron kar yazo da kansa ya Kara jaza mata wani zargin, ta zura takalmanta sannan tafi ta nufi bangaren nasa. :
Tana shigowa falon shi kuma yana saukowa daga
matattakalar benan, sanye yake da shigar qananan kaya, koriyar riga da bakin wando sai takalmin qafarsa “ na fata, yau babu gilas a fuskarsa don haka kana ganin fararen idanuwansa fat masu kama da farar takarda, sumar kannan tasa ta sha gyara sai sheki take hannunsa na rike da makullin mota. , Saude ta durkusa a qasa jikinta a sanyaye tana gaishe shi. Dr. Ahmad ya amsa mata cike da kulawa kafin ya ce, ‘Saudat ya na ga kamar kina cikin damuwa lafiya dai k0?” ‘
Kai kawai ta girgiza masa alamar ba komai Dr. Ahmad ya Kara matsowa daf da ita ya sa hannu ya mikar da ita tsaye cikin raunanniyar muryarsa yace,‘ “Ban yarda da babu komai ba Saudat, ki fada mini meke damun “ki, ?” Ya yi tambayar yana nuna kansa,’ , Saude ta girgiza masa kai alamar a’a. ‘
YacE to waye?” Idonta ya kawo kwalla ta yi
shiru ba tare da ta yi magana ba, dan tana motsa ~ bakinta kuka ne zai kubce mata
Zuciyar Dr ta cika da tausayi muryarsa a sanyaye yace ”‘Saudat kina cikin damuwa na fahimci yanda ki keji a tawa zuciyar kiyi hakuri insha Allahu komai ya kusa zuwa qarshe Taso muje Saudat.
Tayi saurin kallonsa da idanuwanta dake cike taf ‘da kwalla tana qokarin yin magana ya dora danyatsansa saman labbanta alamar tayi shiru kar ta ce komai, sannan ya yi gaba abin sa. Saude ta lallaba ta mike ta bi shi tana goge kwallarta.
Yau da kan shi ya ja motar cikin wata qaramar mota ‘yar dunkulalliya mai‘ kofa biyu wato sport car, iya shigar mutum biyu ce mai bakin gilas irin wanda duk nacin ka ba ka isa ka gane wanda ke ciki ba.
_ Kai tsaye wurin da suka je jiya ta ga sun nufa ita ‘dai kallonsa kawai take kamar jiya haka suka shiga yayi rubuce~rubucensa aka shiga da ita wajen ‘Washing and dressing. > ‘ Cikin awannin da basu fi uku ba aka gama mata ’ kwalliyar ta tsab cikin wasu hadaddun kaya . read made riga da siket English wears bakin siket da falmaran mai jinin kart. Falmaran din ya kawo mata ‘har kusan kugu mai dogon hannu sai bakin siririn gyale wanda aka nade mata tamkar nadin Larabawa ya tsaya iya wuyanta Gyaran gashin da , akai mata ya zubo ta gefen fuskarta ya sauka har
Kafadarta; Rigar ta ciki ta kamata sosai surarta dukta bayyana tabi ta lafe jikinta, falmarar din mai budaddan gaba ce hakan yasa babu abin da ta rufe
. Takalmin kalar baqi ne mai tsini sai jakarsu ‘yar Post mai dan girma. Suna‘ gama mata suka sa camera suna mata hotuna dan su~kan sun san tayi masifar haduwa k0 gasar sarauniyar Indiya zata iya kyan da zata yi kenan. Ni kaina dai marubuciyar ban san Saude ta hadu haka ba sai yau, lol ta koma tamkar wata jugunanniyar hadaddiya wayayya classical.
Shi kan shi uban gayyar duk yanda ya so daurewa sai daya tofa ,
“Kai Saudat wannan cinyewar fa haka? Dama haka ki keda kyau ko dai idona gizo yake min wallahi am so suprise
Saudat dai iyakar ta ido, sannan ya biya kudin suka fito
A mota ma sai daya dubeta, “Kin san wallahi kin yi kyau gaskiya Momy za ta yaba dake
Saudat tayi saurin kallonsa, ‘Momy kuma?”
Ya daga mata kai “Ita fa dan yau yawo zamu sha tun daga gidan sister Farida har gidan Uncle B da ‘ gidanmu inda aka haife ni yau za ki ga Momyna da Dad dina ai za kiyi farin ciki ko?”‘
A sanyaye Saude ta daga masa kai amman zuciyarta cike take da zargi da kuma dumbin fargaba ‘
Tafiya su kai mai nisa sosai kafin su iso Maitama, Dr. yaja ya tsaya a bakin gate din wani gida wanda ya ke zagaye da manyan furanni masu kyan gaske yayi horn ,maigadi ya bude sannan ya cinna hancin motar cikin gate din gidan.
Ya samu wuri yayi fakin ya dubi Saude fito muje ranki shi dade k0 sai na fito na bude miki? Saude ta yi saurin watsa masa wani kallo mai kama da harara.
Ya yi wata dariya harda kyalkyalawa kafin yace ‘Wannan kallon fa yallabai ne fa.’ Saude tayi saurin turo kofar ta fito tana gunkuni irin na shagwababbun yara Dr. ya fito daga motar yana zolayarta. Maigadi ya kwaso da gudu ya nufo su ya zube gaban Dr. yana kwasar gaisuwa, ya Ciro kudi masu yawa ya mika masa ya shiga godiya tare da kirari. Dr. ya dubi Saude ‘Muje’ Ba musu ta juya ta bishi suka nufl cikin gidan. .
Ita dai ta gama saduda duk yanda Allah ya yi da ita mai kyau ne ta riga ta fidda rai da rayuwar gaba daya. A bakin qofar falon suka tsaya yana Kwankwasa qofar, can taji wata murya na fadar, “Who is knocking?”
“Brother. ”Daga can suka ji ta fasa wata uwar Kara da takun gudunta. Dr. ya murmusa ya kalli Saude tayi saurin janye idanuwanta. Tana bude qofar tayi wani tsalle ta fada jikinsa tana dariya, Saude ta saki ido da baki tana kallon su. Ikon Allah su kuma haka tasu dabi‘ar take?
,ckin dariya take fadar. Woo my bros; ,nayi kewarka.”
‘Dr: Yayi dariya tare da janye ta daga jikinsa yana nuna mata Saude tare da fadar “You see her? This is my Saudat
‘ Da sauri ta maida hankalinta kan Saudat, ta sake juyowa tana kallon shi tana fadar, “Are you sure?” ‘
Ya yi wani takaitaccen murmushi yana fadar, yes am sure my sis.’ ”
Ta yi wani tsallen murna ta dafo Saudat tana fadar “Wow my bross wallahi na ji dadi sosai, Saudat ‘ sannu da zuwa mu shigo don Allah.’ Saude dai kallon su kawai take tana dafeda . kafadarta har cikin falon, tsararran gaske wanda yaji kayan alatu na more rayuwa iri-iri Da kanta ta zaunar da ita tana fadar. ‘Zauna nan my sis, da me dame ki keso a kawo miki yanzu, tun daga snacks, lemo abinci, fruits, duk komi ki fada don wallahi naji dadin zuwanki my bros na gode fa.” Murmushi kawai yayi mata, ta Kara jawo Saude a jikinta ‘Nace don Allah ki saki jikinki munfa riga Mun zama daya yanzu dan na san nan ba da dadewa ba ‘ zaki shigo cikinmu haka ne? ”
Saude dake jin manganun tamkar saukar markade ta yi tamaza ta daga mata kai. Faridat tace ‘Gud ’ Ta dubi Dr kai kuma fa yaya me ka keso k0 , ,
duk kun bani zabi? Ya ce a a karki wahalar da kanki dan yanzu haka gidan Uncle B za muje daga nan zamu wuce gidansu Dad, don haka kl kawo mana lemo kawai
Faridat ta bata fuska ta hau diredire tana fadar, wallahi ban yarda ba Allah
Dr. ya yi wata qasaitacciyar dariya kafin yace, ‘Waike har yau ba za ki girma ba k0 kin manta ke kika aje Affan da Ummyta ne?”
Dariya tayi ta juya ta bi wata hanya cikin falon nata, tana fita Saudat ta yi saurin kallonsa tana shirin yin magana ya yi saurin daga mata hannu alamar ta yi shiru, a dole ta ja bakinta ta tsuke
Gaba daya falon ya dauki shiru sai dai kukan A.C da talabijin din da ke ta faman haukanta ita kadai. Ba tafi minti goma ba sai ga ta ta dawo dauke da wani qaton tire ta ajiye saman tebur, lemukan kwali ne guda hudu sai kofuna masu kyau sai robobin Faro biyu, sai fruits kala-kala sai wani tangaran din da aka zuba dambun mama a ciki, sai daya plate din hadaddan chips din dankalin turawa ne. Farida ta dube su.
“Don Allah kuba ni minti goma zuwa sha biyar k0 dan wani abu ne marar nauyi in girka muku.”
Dr yace‘Kin san Allah sauri muke wannan ma is okay. ” Ya tashi ya matso inda Saude take zaune da
muryarshi qasa-qasa yace, ‘Tunanin me kike Madam”? Kallonshi kawai tayi bata tanka ba.
Faridat ta yi murmushi tana fadar, ‘Wallahi Yaya ‘
ka iyi zabe: kuma mai kunya, amma Bufullatana ceko?”* Murmushi yayi tare da fadar, ‘Bana san sa ido fa.’ . Tayi dariya tana fadar, ‘Ai dan Safwan baya nan ne “ wallahi daka sha tsiya, ya tafi ya dauko su Affan daga makaranta, amma don Allah yaushe zaku dawo don . gaskiya ni dai wannan zuwan ba nawa bane
Dr. yace‘Sai ki tambayi Madam din dan in gobe tace in dawo da ita kin san zan iya.”
Farida ta yi. saurin riko hannun Saudat tana fadar, ‘Don Allah don Annabi ki taimaka Anty Saudat ki dawo kin ga dai ni yanzu qanwar ki ce
Yanda ta yi maganar ya tilastawa Saudat yin dariyar da ba ta shirya ba, har da Kyakyatawa a haka Farida taja ta jikinta har ta samu ta saki jikinta da ita sosai kamar sun dade da haduwa, kasancewar Farida mai shegen surutu ga barkwancin tsiya da iya bada labari.
Inda suka bambanta da Dr kenan ita tafi shi Magana shi kuma bai da magana sosai; amma kamar su daya kamar an tsaga kara, har wajen tsawon kana ganin su kaga ‘yan gida ‘daya. .. ~ Da wayo da wayo sai da Dr yayi da gaske sannan suka samu suka bar gidan Farida, ta hadowa Saudat ~ kayayyaki cike da wata qatuwar jaka mai girma Kirkinta ya bawa Saudat mamamki, kwata-kwata ba ruwanta da Jin kai k0 miskilanci irin na Dr
Suna cikin mota sun dau hanya Saude ta dube shi da alamun damuwa karara a fuskana tace
‘ “Zuciyata na cikin duhu kuma a cike take da
sarkakarkun al’amura masu rikitarwa ina cikin rudani ’ don Allah ka fidda zuciyata cikin duhun da take ciki ka fada min me yasa kai wa ‘yar uwarka Karya a kaina, k0 shi ma hakan duk yana cikin taimakon nawa‘ne?”
Dr. ya yi wani? murmushi ba tare da ya kalle ta ba yace, ‘Kamar kin sani duk yana ciki, kuma daga yau deel din namu zai Kare da fatan kin gane?’ Ba‘tace
masa komai ba tayi shiru zuciyarta na kaiwa da , kawowa
Katon gate ne ta ga sun tinkara katafaren gaske ‘ mai kama da‘ qofar shiga gari.. Saude ta saki hanci da ido tana kallon gate din yayin da shi kuma yake faman horn, masu gadi biyu ne suka bude kofar Sannan suka ‘shiga katafaren gidan ya sauke gilas din motar: yana ; gaisawa da masu gadin sannan ya wuce.
Kai tsaye Katuwar rumfar da aka tanada dan ajiye , motoci ya nufa ya faka motar tsakanin motocin da su kai jerin gwano a cikin rumfar Dr. ya bude motar yana . kallon Saude ya ce,’ ‘Yau ga ki har gidansu YallaBan
ki, da fatan kin yi farin ciki.” . Kallon shi kawai ta yi ta juya ta bude murfin motar ‘ ta fito, shima ya fito yana fadar “A’a ba kiyi farin cikin ba kenan? Lallai yarinya aiko zaki fadawa Momy Yayi gaba ta bi bayansa
Ma’aikatan gidan da keta faman aikace-aikacensu, , ‘ mai ban ruwa nayi mai aske fulawoyi suna ganinsu .suka nufo su suka zube suna kwasar gaisuwa, ita dai ‘ Saude ta gaza amsawa duk kunya ma ta ishe ta, yanda suke ta faman kiranta da Hajiya, a zuciyarta tace Allah Sarki ai duk mune dan ta san da sun san wacece ita da ba su gaishe ta ba. ‘ Suna wucewa Dr. ya dube ta ba walwala’a fuskarsa yace, ‘Duk wanda ya gaida ke ki rinKa amsawa, don zasu dauka wulaqanci gare ki. ’
Ba tace masa komai ba ta ga sun nufi wata Katuwar kofa ya tura suka shiga cikin katafaren falon.
Babu kowa a cikin falon sai ‘yan aiki guda biyo suna ta faman goge-goge suna shigowa suka zube suna kwasar gaisuwa, Dr. ya nunawa Saude wurin zama sannan ya nufi wata kofa, ‘yan aikin kuma suka fice suka bar Saude na ta faman zazzare namujiya a cikin
falon. . Tsawon mintinan da suka kai goma
, sannan ya tito hannun shi sarke dana wata magidanciyar mace dan ba za a kira ta da tsohuwa ba, saboda a qalla shekarunta ba zasu wuce arba’in da _ ‘yan kai ba. Tun kafin su qaraso Saude tayi saurin‘
saukowa Kasa daga saman kujerar da take sama, matar
ta wage baki har hakoranta suka bayyana wanda aka likawa hakorin Makka, ta ture Dr. wanda ke rabe da . kafadarta ta riqo Saude tana fadar. ‘
“ ‘Kai ni sakar ni kaji tunda baka gajiya sannun ki da zuwa Saudatu zauna nan kinji
Ta zauna tare da ita saman kujera, tana amsa gaisuwar da Saude ke mata cikin sarkewar murya
Momy ta dubi Dr. tana fadar, ‘Kai sai ka cemin amaryar taka Bafullatana ce gaskiya nayi murna saki jikin ki Saudat mu gaisa ki dauke ni tamkar
mahaifiyarki kinji ko?’ Kai kawai ta daga mata
Momy tayi murmushi cike dajin dadi tana fadar,
‘ ‘Allah Sarki je ka kira Dad dinka na san yana Bangarensa yana jiran ka Dr ya mike da zumudinsa ya fice.
Yau dai Saude taga ikon Allah ta ga inda soyayyar da da mahaifa take yanda suka rinka nan nan da ita tamkar zasu goya ta don Dad din na zuwa Dr cewa yayi sai anyi siyan baki
Kamar wasa dattijon yace ‘Au! Kace gaisuwa da neman iri ku ka zo.’
Dr, ya ce, “Eh Dad ba komai
dad yace To amaryar taka za taje Saudiyya?”
Dr yace eh Zata Dady ” ~ yace
‘To an biya, mata.” *
Dr ya ce, ‘Ai bai isaba Dad wallahi inafa sonta da yawa
” Dad yace, ‘Toka hau sama ka dauko mata makullin
Motar da nayi niyyar yi mata takwuici.” ; musamman sabod ita nasa aka kawo motar daga london jiyannan kuma aka iso da ita maza jeka dauko mata makullin a sama
😀😀 Dr fa ya riqe wuta ya Zata kaya Mu tara gobe daidai wannan lokacin donjin ci gaba
Murace taimun mugun kamu yau shiyasa kukajini shiru ban leqo duniyar matasaba amman Ina tare daku a koda yaushe Naku har KULLUM
*ABDULLAHI ISMAIL SALANKEN ZAZZAU*