Yar tallah24
*YAR TALLA*
*CHAPTER2⃣4⃣*
Taso muje gida Saudat ki huta in baki tarihin mahaifinkuda irin taskun dana shiga a lokacin aurena da shi”.
Ta riqo Saudat ta taimaka mata ta mike, ta dauki makullin motarta suka fito har zuwa
harabar asibitin inda aka tanada don ajiye motoci.
Ta bude wa Saude gidan baya ta shiga ta maida ta rufo sannan ita kuma ta zagaya ta shiga mazaunin direba tayi wa sabuwar motar key qirar Jeep mai taya a baya suka hau hanya kai tsaye Goruba road suka nufa a road ta tsaya qofar gate din wani madaidaicin gida mai kyan gaske da wadatar furanni masu tsayi tayi’ Horn kusan sau biyar sannan aka bude gate din gidan ta cinna hancin motar a ciki maigadi yana daga mata hannu tayi cikin gidan kai tsaye harabar wurin ajiye motoci ta nufa ta raba motar tata kusa da wata Matris sabuwa dal ta kashemotar ta fito sannan ta bude wa Saude itama ta fito ta riko hannunta ta ratayo a wuyanta saboda taji dadin taka qafar sannan suka shiga falon inda qofa take a gefe suka nufi falon kai tsaye
Bai da girma sosai, madaidaici ne wanda ya cinye saitin kujeru guda da show glass tare da kayan kallo da santa table a tsakiya. Suna shiga falon qananan yaran dake zaune suna wasa suka yo kansu suna, “Oyoyo ga Momy”.
Saude tabi yaran da kallo, ‘yan qanana masu kyau dasu Dr. Mariya ta yiwa Saude masauki saman kujera sannan tabi ta kan yaran ta rungume su a jikinta tana amsa sanu da zuwan nasu, ta nuna masu Saude, “Bakuga Antynku bane? Kuje ku gaishe ta”.
Yaran guda biyu mace da namiji suka durkusa gaban Saude suna fadar, “Ina kwana Aunty”. ‘
Saude cikin karayar zuciya ta amsa da lafiya lau tana kallonsu, macer ce ‘yar babbar wadda ba za ta wuce shekaru shidda ba, sai namijin wanda bai wuce uku ba, Dr. Mariya tace, “Kannanki ne, Nabil da Nabila suna karatu ne a nan Saude su duka da maigidana Alhaji Ashiru yana aiki a central bank yanzu kizo muje ga dakin baqi can ki wanka kici abinci ki huta, sannan inzo muyi magana”. ,
Saudat ta amsa da, “To”. Sannan ta mike suka nufi dakin.
. Karamin daki ne mai dauke da gado da kujeru Kwara uku sai kayan kallo. Falon ya yi kyau sosai saboda yadda aka qawata shi da kayan dakwareshin masu kyau, akwai toilet da dan wurin hutawa a cikin falon.
Dr. Mariya ta juya ta fito ta bar Saude tanaqarewa falon kallo ganin abin take tamkar a mafarki wai ita ce yau da mahaifiyarta, ikon Allah ko’ina Yaya Rabi’u ta san da zai samu labari ba qaramin murna da farin ciki zai yiba.
Dr. Mariya ta sake shigowa rungume da sabuwar jallabiya a hannunta ta ajiyewa Saude tana fadar, “Kije ki watso ruwan ga jallabiya nan ki saka nasan za tayi miki a Saudiyya na siyo ta”.
Saude ta amsa da,‘To na gode”.
Dr. Mariya ta yimurmushi kafin tace, “Meye abin godiya kuma Saudat? Don Allah ki saki ranki ki rinqa kallona a matsayin mahaifiyarki kinji?”
Murmushi kawai Saude tayi tare da
‘sauke idanuwanta qasa Dr. Mariya ta juya ta fita sannan ita ma Sauden ta yunkura da kyar ta
mike tana tsangala kafar da kyar ta shiga bandaki ta watso ruwa ta dauro alwala ta fito
ta murza mai a jikinta sannan ta kawo jallabiyar baka ta saka ta nade kallabin rigar a kanta sannan tayi sallarta ta daga hannuwanta sama ta soma godiya ga Allah da Ya muna mata wannan ranar, Dr. Mariya ta shigo ta kawo
mata abinci ta juya ta fita, Saude ta shafa addu ar ta mike ta nufi inda kulolin abincin suke ta bubbude, tuwon shinkafa ne da miyar alayyahu taji naman kasuwa sai gasasshen kifi da kayan lambu wanda yaji curry da kayan kamshi, sannan kunun aya cikin jug wanda ya ji kwakwa da dabino da madarar gari. Gashi yai sanyi qarara
Saude ta zauna kasa tana tsatstsakurar abincin ba wani da yawa taci ba ta ajiye ta sha kunun ayar sosai, sannan ta dauki magungunan data ga an ajiye mata ta sha, ta mike ta‘nufi kan gadon ta kwanta.
Wani bacci mai nauyi ya dauke ta ba ita ta farka ba sai gab da magariba ta mike ta nufi bandaki ta dauro alwala ta fito tayi sallah,‘ tana nan zaune Dr. Mariya ‘ ta shigo da sallamarta, tana sanye da wasu riga da siket na
wata atamfa super wax mai kyan gaske
Ta raBa saman gadon ta zauna tana jiran Saude ta kammala Saude ta shafa addu’ar ta waiwayo tana gaishe da Dr.
Cikin fara’a ta amsa tare da fadar,
“Sannunki da qoqari, ai na dauka kina nan kina bacci, kin san marar lafiya bai san motsa jikinsa saukinki ma baki da qan-jiki”.
‘ Saude ta danyi murmushi tana kallon inda a kayi mata dressing din ciwonta”.
Dr. Mariya tace, “Da ma ina son muyi° magana ne shi yasa na bari ki huta ki dan samu natsuwa Saudat zan baki tarihina gabadaya ta yadda zaki cire qullatata a zuciyarki, da farko ‘dai ni . ‘yar asalin Dandagoro ce mahaifina da mahaifiyata a can suka haifeni nida yayana, kuma a ciki muka girma sana’ar mahaifinmu ita ce Kira, ana ce masa Lawai maqeri mahaifiyata kuma sunanta Badiyya, ita kuma tana sana’ar kitso ne da saka, asalin mahaifiyata bafulatana ce kuma gabadaya ita muka biyo.
Tunda na tashi ina qaramata na iya saKa ” harna fara girma mahaifina ya sani a makarantar boko Yl Yayana yayi
karamin bokonsa‘ daganan ya tafi Sakandire har zuwa Polytechnic inda yayi N C. E dinsa, amma bai samu aiki ba a lokacin duk da unguwarmu yaya Sani ne kawai wayayye
, don shine ya fara wucewa. gaba da sakandire.
Ina firamare aji bakwai lokacin har aji . bakwai ake yi, watarana na hadu da mahaifinki Bala, a lokacin ina da shekaru sha uku, shi kuma a ‘ lokacin yana, saurayi don” bai wuce shekaru asirin da biyu ba, na hadu da Bala lokacin yazo Yaya Sani’ ya yi masa wani lissafin kudi ya buga masa da calculator. Suna zaune saman dakalin. Qofar gida suna magana, ni kuma na dawo daga makarantar allo da yamma na gifta su na gaishe su zan wuce Yaya Sani ya kira ni na dawo na durkusa a gabansu’, “Gani” , Yace, “Jeki kawo mana ruwan alwala”, ‘ ‘ na amsa da, “To” sannan na tafi cikin gidan na ajiye allona na samu Umma a zaune akan tabarmar kaba tana yiwa wata mata kitso ’ ‘ na gaishe da matar sannan na wuce bakin randa na zuba‘ musu ruwan a butoci na fito na
kai musu, na dawo gida naci gaba da ‘sanwar tuwon da Umma‘ ta. dora,‘ban san wainar da
aka toya ba a waje tsakanin Yaya Sani da Bala ba kwatsam washegari Umma ta aikeni kai kudin daShi nan bayan gidanmu, na shiga gidan kafin in fito yaro ya shigo wai ana kiran ‘ Mariya. Gabana ya fadi, don nadai san ko sauraren Samari ban fara ba,kamar’ karna fita matar gidan tacemin,“kije kiga ko waye kika sani k0 yayanki ne?”
Jin hakan data fada yasa na samu kwarin gwiwar fita, a rakube na same shi jikin bango ya harde hannuwansa a Kirji yana ta faman mazurai. Ganin Bala mamaki ya kama ni, nidai na san ba haduwa muké ba, dukda. kuwa yana dan unguWannan don bama ruwana da shiga shirgin maza.
” Na dan tsaya nesa da shi na gaisheshi, ya washe baki yana amsawa kamar wanda aka , yiwa wata kyauta, nace, “Gani”
Kallona yayi sosai kafin yace, “Nasan zakiyi mamakin kiran danayi miki ko?” ”
Ni dai kaina na kasa, Jira kawai naké inji yace, ga inda zai aike ni Shikuma batare daya tsaya sauraran amsata ba yaci gaba da cewa ‘ .
“Ba komai bane yasa na kira kiba , ,Mariya wallahi Sai don na bude miki abin dake cikin zuciyata saboda naga barinsa a qirjina bai ,da wani amfani Ni dai Mariya ina dawainiya da sonki a zuciyata ba wai yanzu ba ‘wallahi tunda dadewa amma Allah bai Sa na taBa fada ‘wa kowa ba sai jiya na sanar da‘yayanki Sani, amma sai ya nuna mini gaskiya inyi haquri don kuwa ke karatu zaki har gaba da Sakandire zaki wuce, don burinsu sai kin zama likita, ba yadda banyi da shi ba AMMA ya Ki daga qarshe ma har dan saBani muka samu dashi a kanki. Na haqura na tafi gida, amma wallahi Mariya ban iya samun bacci ba a daren jiya, , idan na rufe idanuna hotonki nake gani yanayi min gizo, duk yadda naso in rarrashi zuciyata abin ya faskara, don haka na yanke shawarar~ ’ zuwa wurinki da qoqon barana don Allah Mariya ki taimaka ki soni koda da kwayar zarra ne” Ni a lokacin sai na rinka jinSa tamkar ; : mafarki don tunda nake babu saurayin daya taba tara ta da irin wannan maganar sai shi,
don haka ban wani dauki abin da muhimmanci ba na dubeshi kafin ince
“Kayi haquri, kamar yadda Yaya Sani ya fada maka niba aure zan yi ba, karatu zanyi, na gode, sai anjima”.
Inaji yana ta faman kirana, amma ban tsaya ba donni a tsorona kada wani dan gidanmu ya wuce ya ganni.
Abu kamar wasa Karamar magana ta zama babba, don kuwa duk inda zani sai naga Bala, k0 makarantar boko’ ‘ko ta allo, k0 kasuwa zani ke kamar ana fada masa gani nan zan fita, kuma in dai siyayya zanyi ko ta nawa ce shi zai biya kudin, duk wulakancin da zan masa ba yaji, ya zame min kamar wani kaska na rasa yadda zanyi da shi, tun ina wulakanta shi, har ta kai ga na gaji na sa masa ido, daga baya ma sai ya koma bani tausayi saboda yadda yake shan wulaqanci amma bai taBa bata ransa ba, idan aka aike ni kasuwa. Siyayya kuwa k0 ta kai ta nawa shi zai zaro :
Kudi ya biya yayi tafiyarsa ya barni in rasa yadda zanyi da kudin a hannuna haka na dinga Boye su a cikin buhun kayana don tsoron kar
‘ wani ya gani in shiga uku, wasa-wasa na tara ‘kudi masu tarin yawa. ~ ‘ Ahaka ahaka Saudat har saida Bala ya sarke min Zuciya na manta da duk wulakancin ‘ da nake masa ta kai ta kawo ma in ban ganshi ba, ko bacci bana iya yi a dantsakaninnan fa ‘ soyayya mai qarfi ta shiga tsakaninmu, amma babu wanda ya sani a gidanmu. ‘ Idan Bala yana son mu hadu sai ya ‘ rubuta ‘yar takarda ya soke a kyauren gidanmu dama na sani kullum saina duba kyauren don inga k0 ya soke sakonsa, idan ya sanya in dauko in ruga in Boye in karanta, bai dai wuce. sakon mu hadu Wuri kaza, karfe kaza ba, kuma duk abin da nake in dai yace yana jira wuri kaza sai naje k0da ban da lafiya ne kuwa. ‘ A haka watarana . Bala ya soke . takardarsa da yamma na dawo daga kai nika na“ , gani na duba, yana son mu hadu bayan gidanmu bayan sallar magaraba, dadi ya kama. ni don da ma mun kwana biyu bamu hadu ba, don haka ina shiga gida na sauke wa Umma nikan a tsakar gida na suri bokiti na nufi bakin rijiya .zan jawo ruwa, .Ummana :dake zaune
saman kujera‘ yar‘ tsugunne ta dube ni yadda nake ta rawar jiki kafin tace “Wai saurin me kike haka ne Mariya? Me zakiyi da wannan ruwan? ’ , ‘ “Wanka” Na bata amSa a takaice ‘ Umma tace, “Wanka kuma bacin wanda kika yi da rana?” na amsa Ba tare dana kalle ta ba nace zan Kara ne Umma, Maman su Bilkice tace in shirya in raka ta dubiya, Kaninta bai da lafia” Umma tace “Dubiyar ce kuma Mariya har sai anyi mata wani ado sai ka ce wanda zashi gidan biki?” ‘ “Yo Umma ai kamar gidan bikin ne ldan kinfa san gidansu gidan‘ yan gayu ne”. INa maganar tare da kinkimar bokitin ruwana na nufi bayi ba tare dana tsaya na saurari abin da zata ceba, Umma taja numfashi taci gaba da abin da take. “ Kafin ayi sallar magriba na gama, Shiryawa tsaf cikin sabon yadin bambalasta wanda aka yi min dan doguwar riga mai ‘ .hade da zani sun sha aikin surfani, yadin mai
kalar jinin kare, duk daba wata kwalliya aka” iya ba a lokacin amma na yi kyau sosai
Dan daman can ‘kyakkyawa ce, fara“ ce tas; ‘yar siririya kamarke Saudat,saidai ninafiki manyan idanuwa, ga gashina har baya baki sidik yayi min saje a gewayen fuska, kina kallona kin ga kyakkyawar bafulatana ‘ , Na zaro gyalena na fito tsakar gida a
lokacin Ummana tana kicin tana tuqin tuwo na leka kicin din tare da fadar.
‘ “Umma na tafi,sai na dawo” . ta amsa Itama a lokacin ma hayaki ya ishe ta,don k0
waigowa ba tayi ba tace min, “A dawo lafiya,
kada ai dare”.
Na amsa mata da, “To Umma” .
Na nufi hanyar fita, qanwa ta Zuwaira ta taso zata biyoni na hankadeta inaji tana kuka nayi gaba abina, don a lokacin Wasu » masallatan har sun gama sallah.
: Ina fita nayi karo da Yaya Sani ya dawo daga kasuwa, ya watsa min harara, “Gidan uban wa zaki?”
‘ . . Na dabarbarce ina in ’ina, sannan na samu na fada masa, “Rakiya zanayi, kuma ‘Ummama tasani”
,, “‘ Yaja tsaki ba tare daya sake kulaniba “ yayi cikin gida abinsa.
Hmm Maria da malam bala dai koya zata kaya oho muje zuwa Mu hadu gobe daidai wannan lokacin donjin Ci gaban wannan qayataccen labarin Naku har KULLUM
*ABDULLAHI ISMAIL SALANKE*